‘Ka Biɗi Jehovah Da Kuma Ƙarfinsa’
“Gama idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayana kansa mai-ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.”—2 LABARBARU 16:9.
1. Menene iko, kuma yaya mutane suke amfani da shi?
IKO yakan iya nufin abubuwa da yawa, kamar nuna ƙarfi, izini, ko kuma tasiri bisa wasu; inganci na aiwata ko aikata wasu abubuwa; kuzari a jiki (ƙarfi); ko na zuci ko na ɗabi’a. Mutane ba su da misali mai kyau a yadda suke amfani da iko da suke da shi. Ɗan tarihi, Lord Acton, yayin da yake magana game da iko a hannun ’yan siyasa, ya ce: “Iko yana lalatarwa kuma cikakken iko yana lalatarwa sosai.” Tarihi na zamani yana cike da misalai da ke nuna gaskiyar maganar Lord Acton a ko’ina. A ƙarni na 20, “mutum ya sami iko bisa wani” fiye da dā. (Mai-Wa’azi 8:9) ’Yan mulkin cin zali sun ɓata ikonsu sosai kuma sun ɗauki rayukan miliyoyin mutane. Iko da ba shi da ƙauna, hikima, da yin gaskiya haɗari ne.
2. Ka bayyana yadda wasu inganci na Allah Jehovah suke shafan yadda yake yin amfani da ikonsa.
2 Ba kamar ’yan Adam da yawa ba, Allah yana amfani da kyau da ikonsa. “Gama idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayana kansa mai-ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Jehovah yana nuna ikonsa a hanya mai kyau. Haƙuri ne ya sa Allah bai halaka miyagu ba tukuna, don ya ba su zarafi su tuba. Ƙauna ce ta motsa shi ya sa rana ta haskaka akan dukan irin-irin mutane—masu adalci da marasa adalci. A ƙarshe, yin gaskiya zai motsa shi ya yi amfani da ikonsa mara iyaka don ya halakar da wanda yake jawo mutuwa, Shaiɗan Iblis.—Matta 5:44, 45; Ibraniyawa 2:14; 2 Bitrus 3:9.
3. Me ya sa ikon Allah dalili ne mai girma na gaskatawa da shi?
3 Iko na ban mamaki na Ubanmu na sama dalili ne na gaskata shi da kuma amincewa da shi—duk cikin alkawuransa da kuma cikin tsarewarsa. Ƙaramin yaro yana samun kwanciyar rai tsakanin baƙi lokacin da ya riƙe hannun ubansa, tun da shi ke ya san ubansa ba zai bar kome ya same shi. Hakazalika, Ubanmu na sama, wanda “mai-iko ne garin yin ceto,” zai tsare mu daga azaba mai ƙarƙo idan mun yi tafiya tare da shi. (Ishaya 63:1; Mikah 6:8) Kuma yadda yake Uba nagari, Jehovah koyaushe yana cika alkawuransa. Ikonsa mara iyaka yana sa ‘maganarsa ta yi albarka kuma a cikin saƙonsa.’—Ishaya 55:11; Titus 1:2.
4, 5. (a) Menene ya faru lokacin da Sarki Asa ya gaskata da Jehovah sosai? (b) Menene zai iya faruwa idan mun dangana ga ’yan Adam su magance mana matsalolinmu?
4 Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu ƙuduri aniya kada mu manta da tsarewa na Ubanmu na sama? Domin yana yiwuwa yanayi su sha kanmu kuma mu mance inda muke samun kwanciyar rai na gaske. An ga wannan a misalin Sarki Asa, mutum wanda ya gaskata da Jehovah. A lokacin sarautar Asa, rundunan Kushawa masu ƙarfi miliyan suka kai ma Yahudawa farmaki. Da ya gane cewa rundunan magabtansa sun fi shi ƙarfi, Asa ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, banda kai babu wani mai-taimako, shi shiga tsakanin mai-iko da wanda ba shi da ƙarfi: ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama muna dogara gareka, a cikin sunanka kuma mun zo yaƙi da wannan babban taro. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu: kada ka bar mutum shi rinjaye ka.” (2 Labarbaru 14:11) Jehovah ya ji roƙon Asa kuma ya sa ya ci nasara mai girma.
5 Amma, bayan shekaru da yawa na hidimar aminci, amincin Asa cikin Ikon ceto na Jehovah ya kumanta. Don ya guje burgan runduna daga mulkin arewa na Isra’ila, ya juya ga Syria don taimako. (2 Labarbaru 16:1-3) Duk da cin hanci da ya bayar ga Sarkin Syria, Ben-hadad ya hana Isra’ila daga yi wa Yahuda burga, alkawarin da Asa ya yi da Syria ya nuna bai amince da Jehovah ba. Annabi Hanani ya tambaye shi: “Ko Kushawa da Lubimawa ba taron runduna mai yawa ba ne ainun, da karusai da mahaya dayawa ƙwarai? duk da haka domin ka dogara ga Ubangiji ya bada su a cikin hannunka?” (2 Labarbaru 16:7, 8) Duk da haka, Asa ya ƙi jin tsautawar nan. (2 Labarbaru 16:9-12) Yayin da muka fuskanci matsaloli, kada mu dangana ga ’yan Adam su magance mana. Maimako, mu amince da Allah, domin dogara cikin ikon ’yan Adam lallai zai kai ga cizon yatsa.—Zabura 146:3-5.
Ka Biɗi Ikon da Jehovah Yake Bayarwa
6. Me ya sa ya kamata mu ‘biɗi Jehovah da ƙarfinsa’?
6 Jehovah zai iya ba bayinsa iko kuma ya tsare su. Littafi Mai-Tsarki ya aririce mu mu “biɗi Ubangiji da ikonsa.” (Zabura 105:4) Me ya sa? Domin in mun yi abubuwa cikin ikon Allah, za mu yi amfani da ƙarfinmu, mu amfane wasu, maimakon la’anta su. Ba inda za mu samu misali mafi kyau na wannan sai a wurin Yesu Kristi, wanda ya yi mu’ujizai da yawa cikin “ikon Ubangiji.” (Luka 5:17) Yesu zai iya ba da kansa ga zama mai arziki, mashahuri, ko ma sarki mafi iko duka. (Luka 4:5-7) Maimako, ya yi amfani da iko da Allah ya ba shi ya horar kuma ya koyar, ya taimaka kuma ya warkar. (Markus 7:37; Yohanna 7:46) Lallai wannan misali mai kyau ne a garemu!
7. Wane inganci na musamman muke ginawa yayin da muke yin abubuwa cikin ƙarfin Allah maimako cikin namu?
7 Ban da haka ma, idan mun yi abubuwa cikin “ƙarfi wanda Allah ke bayaswa,” zai sa mu kasance da tawali’u. (1 Bitrus 4:11) Mutane waɗanda suke biɗa ma kansu iko za su zama masu girman kai. Wani misali shi ne Sarkin Assuriya Esar-haddon, wanda cikin fahariya ya sanar: “Ina da iko, ni mai iko duka, ni jarumi ne, ni mai girma ne, ina da girman iko.” Akasin haka, Jehovah “ya zaɓi abubuwa marasa-hikima na duniya, domin shi kumyatadda masu-ƙarfi.” Da haka, idan Kirista na gaske yana fahariya, ya yi fahariya cikin Jehovah, don ya san cewa abin da ya yi bai cim ma haka da ƙarfinsa ba. ‘Ƙasƙantadda kanmu a ƙarƙashin hannun mai-iko Allah,’ zai kawo ɗaukaka na gaske.—1 Korinthiyawa 1:26-31; 1 Bitrus 5:6.
8. Menene ya kamata mu yi da farko don mu samu iko daga Jehovah?
8 Ta yaya muke samun ƙarfin Allah? Da farko, muna biɗa ta wurin addu’a. Yesu ya tabbatar ma almajiransa cewa, Ubansa za ya ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda suke roƙonsa. (Luka 11:10-13) Yi la’akari da yadda wannan ya ba almajiran Kristi iko lokacin da suka zaɓi su bauta ma Allah maimakon shugabannen addinai waɗanda suka ce su daina yin wa’azi game da Yesu. An amsa addu’arsu ta gaske, lokacin da suka yi addu’a don taimakon Jehovah, kuma ruhu mai tsarki ya ba su ƙarfi su ci gaba da yin wa’azin bishara da ƙarfin zuciya.—Ayukan Manzanni 4:19, 20, 29-31, 33.
9. Ka faɗi tushen ƙarfi na ruhaniya na biyu, ka kuma ambata wani misali na Nassi don ka nuna aikatawarsa.
9 Na biyu, za mu iya samun ƙarfi na ruhaniya daga Littafi Mai-Tsarki. (Ibraniyawa 4:12) Ikon kalmar Allah a bayane yake a kwanakin Sarki Josiah. Ko da wannan Sarkin Yahudiya ya riga ya cire gumakan arna daga ƙasar, Dokar Jehovah da ya gano cikin haikali ya motsa shi, ya daɗa wannan aikin tsabtaccewa.a Bayan Josiah ya karanta Dokar da kansa ga mutanen, dukan al’umman suka yi alkawari da Jehovah, kuma suka sake ɗaukan mataki na biyu, na kawar da bautar gumaka kwata-kwata. Sakamako mai kyau da Josiah ya samu na sabontawa shi ne cewa “dukan kwanakin ransa ba su rabu da bin Ubangiji.”—2 Labarbaru 34:33.
10. Wace hanya ce ta uku muke samun ƙarfi daga Jehovah, kuma me ya sa take da muhimmanci?
10 Na uku, muna samun ƙarfi daga Jehovah na cuɗanya ta Kirista. Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su halarci taro kullum domin su “tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayuka.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Lokacin da aka saki Bitrus daga fursuna ta hanyar mu’ujiza, yana so ya kasance da ’yan’uwansa, sai ya tafi gidan uwar Yohanna Markus, inda “mutane dayawa su ke a tattare, suna addu’a.” (Ayukan Manzanni 12:12) Hakika, da dukansu sun zauna a gida su yi addu’a. Amma sun zaɓi su haɗu su yi addu’a kuma su ƙarfafa juna a wannan lokaci mawuyaci. Kusan ƙarshen doguwar tafiya kuma mai yawan hatsari na Bulus zuwa Roma, ya haɗu da wasu ’yan’uwa a Butiyoli, daga baya ya haɗa da wasu da sun yi tafiya don su sadu da shi. Yaya ya ji? “Sa’anda Bulus ya gan su [na bayan], ya yi ma Allah godiya, ransa ya ƙarfafa.” (Ayukan Manzanni 28:13-15) Ya samu ƙarfi ta wajen zama tare da Kiristoci ’yan’uwansa. Mu ma muna samun ƙarfi daga cuɗanya tare da Kiristoci ’yan’uwa. Muddin muna da ’yanci kuma iya yin tarayya da juna, tilas ne kada mu yi ƙoƙari mu yi tafiya mu kaɗai a matsatsiyar hanya wadda take nufa wajen rai.—Misalai 18:1; Matta 7:14.
11. Ka ambata wasu yanayi inda musamman ake bukatar “mafificin girman iko.”
11 Ta wajen addu’a na kullum, nazarin Kalmar Allah, da cuɗanya tare da ’yan’uwa masu-bi, muna “ƙarfafa cikin Ubangiji, cikin ƙarfin ikonsa kuma.” (Afisawa 6:10) Babu shakka dukan mu muna bukatar “ƙarfafa cikin Ubangiji.” Wasu suna shan wahala daga ciwo da ke raunana su, wasu daga wahalar da tsufa ke kawowa ko kuma rashin abokan aure. (Zabura 41:3) Wasu suna jimre hamayyar uwargida ko maigida da ba mai-bi ba. Iyaye, musamman iyaye gwauraye, suna iya iske cewa yin aiki na cikakken lokaci yayin da suke lura da iyali nawaya ce mai girma ƙwarai. Matasa Kiristoci suna bukatar ƙarfi don su jimre da matsi na tsara kuma ƙi da miyagun ƙwayoyi da lalata. Ya kamata kada kowa ya yi shakkar biɗan “mafificin girman iko” wurin Jehovah don mu jure wa irin kaluɓale nan.—2 Korinthiyawa 4:7.
“Bada Ƙarfi ga Masu-Kasala”
12. Ta yaya Jehovah yake kiyaye mu cikin hidimar Kirista?
12 Ƙari ga haka, Jehovah yana ba bayinsa ƙarfi lokacin da suke tafiyar da hidimarsu. Mun karanta cikin annabcin Ishaya: “Yana bada ƙarfi ga masu-kasala: ga wanda ba shi da iko kuma yana ƙara ƙarfi. . . . Waɗanda ke sauraro ga Ubangiji za su sabonta ƙarfinsu; da fukafukai kamar gaggafa za su tashi sama; za su yi gudu, ba za su gaji ba; za su kama tafiya, ba za su yi suwu ba.” (Ishaya 40:29-31) Manzo Bulus da kansa ya karɓi ƙarfi don ya tafiyar da hidimarsa. A sakamakon haka, hidimarsa ta yi nasara. Ga Kiristoci a Tassaluniki, ya rubuta: “Da shi ke bisharammu ba da magana kaɗai ba ta zo wurinku, amma da iko kuma, cikin ruhu mai-tsarki.” (1 Tassalunikawa 1:5) Aikin wa’azinsa da koyarwa yana da ikon kawo canje-canje mai girma a rayukan waɗanda suka saurare shi.
13. Menene ya ba Irmiya ƙarfi ya nace duk da hamayya?
13 Yayin da muka fuskanci halin rashin marmari a yankinmu—yanki da ƙila mun yi wa’azi a kai a kai na shekaru da yawa yanzu—za mu iya fid da zuciya. Hakanan ne ma Irmiya ya yi sanyin gwiwa don hamayya, ba’a, da rashin marmari da ya gamu da su. Sai ya gaya ma kansa: “Ba ni ambatonsa [Allah], ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.” Amma ya kasa yin shuru. Saƙonsa “kamar wuta mai-ƙonewa a kuble cikin ƙasusuwan[sa].” (Irmiya 20:9) Menene ya ba shi sabon ƙarfin a fuskar wahala da yawa? Irmiya ya ce: “Ubangiji yana tare da ni, ƙaƙarfa ne mai-ban tsoro.” (Irmiya 20:11) Godiyar Irmiya ga muhimmancin saƙonsa da aiki wanda Allah ya ba shi ya sa ya ji ƙarfafawa na Jehovah.
Ikon Baƙantawa da Kuma Ikon Warkarwa
14. (a) Ta yaya harshe ya zama kayan aiki mai iko sosai? (b) Ka ba da misalai da za su nuna ɓarna da harshe zai iya yi.
14 Ba dukan ƙarfi da muke da shi ba ne ya zo car daga wurin Allah. Alal misali, harshe yana da ikon baƙantawa da kuma warkarwa. “Mutuwa da rai suna cikin ikon harshe,” Sulemanu ya yi kashedi. (Misalai 18:21) Sakamakon ɗan taɗi da Shaiɗan ya yi da Hawa’u ya nuna yadda maganganu suke ɓarna. (Farawa 3:1-5; Yaƙub 3:5) Mu ma za mu iya yin ɓarna mai yawa da harshe. Baƙar magana game da ƙibar wata yarinya zai sa ta ta yi rashin marmarin cin abinci. Mai yiwuwa yin tsegumi ba tare da tunani ba zai ɓata abokantaka da ta daɗe. I, ya kamata a kame harshe.
15. Ta yaya za mu yi amfani da harshenmu mu gina kuma mu warkar?
15 Amma, harshe zai iya gina da kuma rushe. Karin magana na Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Akwai wanda ya kan yi magana da garaje kamar sussukan takobi: amma harshen mai-hikima lafiya ne.” (Misalai 12:18) Kiristoci masu hikima suna yin amfani da ikon harshe su ta’azantar da waɗanda suke baƙin ciki da waɗanda aka yi masu rasuwa. Kalmomin juyayi zai ƙarfafa ballagai da suke fama da matsi na tsara mai ɓarna. Harshen mai tunani zai tabbatar wa ’yan’uwa maza da mata tsofaffi cewa har ila yau, ana bukatarsu kuma ana ƙaunarsu. Kalmomi masu daɗi za su sa masu rashin lafiya su sami ɗan sauƙi. Ban da haka ma, za mu iya yin amfani da harshenmu a yin saƙon Mulki mai iko ma dukan waɗanda za su saurara. Muna da ikon shelar Kalmar Allah idan zuciyarmu tana ɗaukanta haka. Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Kada ka hana alheri ga waɗanda ya wajibce su, lokacin da yana cikin ikon hannunka da za ka aika.”—Misalai 3:27.
Yin Amfani da Ya Dace da Iko
16, 17. Lokacin da suke nuna ikon da Allah ya ba su, yaya dattiɓai, iyaye, magidanta, da kuma mata za su yi koyi da Jehovah?
16 Ko da shi ke shi Mai Iko Duka ne, Jehovah yana sarautar ikklisiya da ƙauna. (1 Yohanna 4:8) A yin koyi da shi, masu kula Kirista suna kulawa da garken Allah cikin ƙauna—suna yin amfani da ikonsu, ba ta ɓatawa ba. Da gaske, ana bukatar masu kula a wasu lokutta su “tsautas, kwaɓa, gargaɗas,” amma suna yin wannan da “iyakacin jimrewa da koyaswa.” (2 Timothawus 4:2) Saboda haka, dattiɓai suna bimbini koyaushe akan kalmomin da manzo Bitrus ya rubuta ga waɗanda suke da iko cikin ikklisiya: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.”—1 Bitrus 5:2, 3; 1 Tassalunikawa 2:7, 8.
17 Iyaye da magidanta kuma, suna da iko da Jehovah ya ba su, amma ya kamata a yi amfani da wannan iko wajen taimakawa, yin reno, da kuma yin ƙauna. (Afisawa 5:22, 28-30; 6:4) Misalin Yesu ya nuna cewa za a iya yin amfani da iko sosai a hanya mai kyau. Idan yin horo ya daidaita kuma an ci gaba da yin haka, ran yara ba zai yi suwu ba. (Kolossiyawa 3:21) Aure yakan yi ƙarfi yayin da magidanta Kirista suna nuna ikonsu na kan gida da ƙauna kuma mata suna daraja maigidansu sosai maimakon neman wuce matsayin da Allah ya sa su, don su mallake ko sami iko da suke so.—Afisawa 5:28, 33; 1 Bitrus 3:7.
18. (a) Ta yaya ya kamata mu yi koyi da misalin Jehovah a kame fushinmu? (b) Me ya kamata waɗanda suke da iko su yi ƙoƙari, su shuka a cikin waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsu?
18 Ya kamata waɗanda suke da iko cikin iyali da kuma cikin ikklisiya su mai da hankali musamman ma wajen kame fushinsu, tun da shi ke fushi yana tsoratarwa maimakon sa a yi ƙauna. Annabi Nahum ya ce: “Ubangiji mai-jinkirin fushi ne, mai-girma ne cikin iko.” (Nahum 1:3; Kolossiyawa 3:19) Kame fushinmu alamar ƙarfi ne, yayin nan yin fushi sosai yana nuna kumamanci. (Misalai 16:32) A cikin iyali da kuma a cikin ikklisiya, burin shi ne a shuka ƙauna—ƙaunar Jehovah, ƙaunar juna, da kuma ƙaunar ƙa’idodi da ke daidai. Ƙauna ita ce gami mafi ƙarfi na haɗin kai da kuma abin motsawa mafi ƙarfi a yin abin da ke daidai.—1 Korinthiyawa 13:8, 13; Kolossiyawa 3:14.
19. Wane tabbaci na ta’azantarwa ne Jehovah ya ba mu, kuma yaya ya kamata mu mayar da martani?
19 A san Jehovah shi ne a gane ikonsa. Ta bakin Ishaya, Jehovah ya ce: “Ba ka rigaya ka sani ba? ba ka ji ba? madawamin Allah, Ubangiji, Mahalicin matuƙan duniya, ba ya kan suma ba, ba ya kan gaji ba.” (Ishaya 40:28) Ikon Jehovah ba ya ƙarewa. Idan mun dogara gareshi ba ga kanmu ba, ba zai yashe mu ba. Ya tabbatar mana: “Kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai: kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka: ni taimake ka, i, ni riƙe ka da hannun dama na adilcina.” (Ishaya 41:10) Ta yaya ya kamata mu mayar da martani ga kulawarsa na ƙauna? Kamar Yesu, bari koyaushe mu yi amfani da kowane ƙarfi da Jehovah ya ba mu don mu taimaka kuma mu gina wasu. Mu kame harshenmu domin ya warkar maimako ya yi ɓarna. Kuma bari koyaushe mu yi tsaro a ruhaniya, mu tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya, mu ƙarfafa cikin ikon Mahaliccinmu Mai Girma, Jehovah Allah.—1 Korinthiyawa 16:13.
[Hasiya]
a Babu shakka, Yahudawan sun samo kofi na asalin Dokar Musa, wadda aka ajiye cikin haikalin ƙarnuka da sun gabata.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya Jehovah yake yin amfani da ikonsa?
• A waɗanne hanyoyi za mu iya samun ikon Jehovah?
• Ta yaya ya kamata a yi amfani da ikon harshe?
• Ta yaya iko da Allah yake bayarwa zai zama albarka?
[Hoto a shafi na 26]
Yesu ya yi amfani da ikon Jehovah don ya taimake wasu
[Hotuna a shafi na 28]
Muna da ikon shelar Kalmar Allah idan zuciyarmu tana ɗaukanta haka