Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/15 pp. 4-8
  • Kiristoci na Gaskiya Suna Daraja Kalmar Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kiristoci na Gaskiya Suna Daraja Kalmar Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AN WARWARE MATSALA MAI WUYA
  • BAMBANCIN YA KASANCE A BAYYANE
  • “ALKAMA” DA “ZAWA” SUN YI GIRMA TARE
  • “BA A ƊAURE MAGANAR ALLAH BA”
  • Kiristoci Na Farko Da Dokar Musa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Sun Fito Daga Duhu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/15 pp. 4-8

Kiristoci na Gaskiya Suna Daraja Kalmar Allah

“Maganarka ita ce gaskiya.”—YOH. 17:17.

1. Mene ne kake gani ya sa Shaidun Jehobah suka yi dabam da sauran addinai?

KA TUNA lokaci na farko da ka tattauna da Shaidun Jehobah? Mutane da yawa za su ce, ‘Abin da ya fi burge ni shi ne cewa Shaidu suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ba da amsa.’ Mun yi farin ciki sosai sa’ad da muka san nufin Allah ga duniya da abin da ke faruwa sa’ad da muka mutu da begen da ƙaunatattunmu da suka rasu suke da shi.

2. Waɗanne dalilai ne suke sa kake daraja Littafi Mai Tsarki?

2 Sa’ad da muka ci gaba da yin nazari, mun fahimci cewa za mu koya abubuwa da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki fiye da amsoshi ga tambayoyinmu game da rayuwa da mutuwa da kuma rayuwarmu ta nan gaba. Mun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki ne littafin da ya fi ba da taimako a duniya baki ɗaya. Shawarwarin da ke ciki suna taimaka wa mutane a koyaushe, kuma waɗanda suka bi su za su yi rayuwa mai farin ciki. (Karanta Zabura 1:1-3.) A ko yaushe, Kiristoci na gaskiya suna ɗaukan Littafi Mai Tsarki “ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah.” (1 Tas. 2:13) Tattauna wasu abubuwa da suka faru a dā za su sa mu fahimci bambancin da ke tsakanin waɗanda suke daraja Kalmar Allah sosai da kuma waɗanda ba su yin hakan.

AN WARWARE MATSALA MAI WUYA

3. Mene ne ya jawo matsala a ikilisiyar Kiristoci na ƙarni na farko kuma me ya sa wannan babbar matsala ce?

3 Shekara 13 bayan an shafa Ɗan Al’umma na farko, wato, Karniliyus, wani batu ya taso da ya kawo rashin haɗin kai a cikin ikilisiyar Kiristoci. ’Yan Al’ummai da yawa suna zama Kiristoci. Amma tambayar ita ce, Shin ya kamata a yi wa mazan kaciya bisa al’adar Yahudawa kafin a yi musu baftisma? Wannan tambaya mai wuya ce sosai ga Bayahude. Yahudawa da suke bin Dokar sosai ba za su ma shiga cikin gidan ’Yan Al’ummai ba, barin ma su zama abokansu. Kuma an riga an tsananta wa Yahudawa da Kiristoci ne sosai domin sun bar addininsu na dā. Idan sun zama abokan ’Yan Al’umma da ba su yi kaciya ba, hakan zai daɗa sa magabtakarsu da Yahudawa da kuma Kiristoci ya yi tsanani sosai kuma ya sa a daɗa tsananta wa ’Yan Al’umma.—Gal. 2:11-14.

4. Su waye ne suka hallara don a yi maganin matsalar kuma wataƙila waɗanne tambayoyi ne mutane suka yi?

4 A shekara ta 49 A.Z., manzanni da kuma dattawa na Urushalima da Yahudawa da suka yi kaciya, “suka tattaru garin su duba wannan al’amari.” (A. M. 15:6) Ba su yi musu a kan abubuwan da ba su da amfani a wannan taron ba, amma sun yi tattaunawa mai daɗi game da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Dukan waɗanda suka halarci wannan taron sun ba da nasu shawara. Ta yaya za su yi maganin matsalolin? Shin za su ƙyale ra’ayin wani ko wariya ya shafi shawarar da za su tsai da? Shin dattawan za su jira ne tukun sai abubuwa sun daidaita a Isra’ila kafin su tsai da shawara? Ko kuwa za su yi abin da ba su amince cewa yana da kyau ba?

5. A waɗanne hanyoyi masu muhimmanci ne taron da aka yi a Urushalima a shekara ta 49 A.Z. ya bambanta da taron da ake yi a coci?

5 A tarurrukan da limaman coci suke yi, sun amince da ra’ayin da ba su yarda ba kuma wasu shugabannin suna ƙoƙarin sa mutane su amince da nasu ra’ayin. Amma dai, a wannan taron da aka yi a Urushalima, ba a yi zaɓe ba, duk da haka, an tsai da shawara guda. Ta yaya hakan ya faru? Ko da suna da ra’ayi dabam-dabam, dukansu sun daraja Kalmar Allah, kuma sun yi amfani da Nassosi don su warware matsalar.—Karanta Zabura 119:97-101.

6, 7. Ta yaya aka yi amfani da Nassosi don daidaita batun kaciya da ya taso?

6 Kalmomin da suke cikin Amos 9:11, 12 ne suka taimaka wajen yin maganin wannan matsalar. An yi ƙaulin waɗannan kalmomi daga littafin Ayyukan Manzanni 15:16, 17, kuma wurin ya ce: ‘Zan komo, in sake gina mazaunin Dauda, wanda ya rushe; in sake gina kufansa kuma, in tashe shi: domin sauran mutanen duniya su nemi Ubangiji, da dukan Al’ummai, waɗanda an kira sunana a bisansu.’

7 Amma wani yana iya yin musu cewa wannan ayar ba ta ce ’Yan Al’ummai da suka zama Kiristoci su yi kaciya ba. Hakan gaskiya ne, amma dai, sun fahimci abin da hakan yake nufi. Ba sa ɗaukan ’Yan Al’ummai da suka yi kaciya a matsayin “mutanen duniya” amma a matsayin ’yan’uwa. (Fit. 12:48, 49) Alal misali, juyin Septuagint na Bagster ya fassara littafin Esther 8:17 haka: “’Yan Al’ummai da yawa sun yi kaciya, kuma sun zama Yahudawa.” Saboda haka, an fahimci bayanin sarai sa’ad da Nassosi sun annabta cewa Isra’ilawa da suka rage (Yahudawa da Yahudawa shigaggu da suka yi kaciya) tare da “mutanen duniya” (’Yan Al’ummai da ba su yi kaciya ba) za su zama mutane ɗaya don sunan Allah. Ba tilas ba ne ’Yan Al’ummai da suke son su zama Kiristoci su yi kaciya ba.

8. Me ya sa waɗannan Kiristoci Yahudawa suke bukatar gaba gaɗi don su tsai da shawara?

8 Kalmar Allah da kuma ruhunsa sun taimaki waɗannan Kiristoci su tsai da shawara. (A. M. 15:25) Ko da shawarar za ta sa a daɗa tsananta wa Kiristoci Yahudawa, waɗannan amintattu sun goyi bayan wannan shawarar daga Littafi Mai Tsarki.—A. M. 16:4, 5.

BAMBANCIN YA KASANCE A BAYYANE

9. Wane dalili ɗaya ne ya sa koyarwar ƙarya ta gurɓatar da ta gaskiya, kuma wacce koyarwa ta musamman ta Kirista ce aka gurɓata?

9 Manzo Bulus ya annabta cewa bayan manzannin sun rasu, za a gurɓata bangaskiyar Kiristoci da koyarwar ƙarya. (Karanta 2 Tasalonikawa 2:3, 7.) Wasu cikin waɗanda ba za su daure da “koyarwa mai-lafiya ba” sun haɗa da waɗanda suke aikin kula. (2 Tim. 4:3) Bulus ya yi wa dattawa a zamaninsa kashedi: ‘Daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.’ (A. M. 20:30) Littafin nan The New Encyclopædia Britannica ya bayyana wani dalilin da ya sa wannan tunani marar kyau ya taso: “Kiristocin da aka ɗan koyar da su a kan ilimin falsafa na Hellanawa suka soma yin amfani da falsafa wajen bayyana imanin Kirista. Hakan ya sa suka yi farin ciki domin iliminsu kuma suka yi tunani cewa za a iya yin amfani da shi wajen ilimantar da kafirai.” Koyarwa ta musamman da suke wa kafiri ita ce ko Yesu Kristi wane irin mutum ne. Littafi Mai Tsarki ya kira shi Ɗan Allah, amma waɗannan ’yan Falsafa na Hellenanci sun ce shi Allah ne.

10. A ina ne limaman coci za su samu amsa ga tambayar da suke yi game da Kristi?

10 Daga baya, limaman coci da yawa sun yi musu game da wannan koyarwar a tarurrukan da suka yi. Da sun yi maganin matsalar da sauƙi, da a ce sun bi abin da ke cikin Nassi, amma yawancinsu ba su yi hakan ba. Hakika, yawancinsu sun riga su tsai da shawara kafin ma su halarci taron, kuma babu abin da ya isa ya canja imaninsu. Shawarar da suka tsai da ba ta jitu da Littafi Mai Tsarki ba.

11. Bisa mene ne limaman coci suke tsai da shawara kuma me ya sa?

11 Me ya sa ba su bincika Littafi Mai Tsarki sosai ba? Masani Charles Freeman ya ce ya yi wa waɗanda suka amince cewa Yesu Allah ne “wuya su ƙi amincewa da koyarwar da Yesu ya yi cewa Allah ya fi shi iko.” A sakamako, al’adun coci da ra’ayin limamai ya fi abin da Linjila ta ce muhimmanci. Har wa yau, limamai da yawa suna zato cewa koyarwar waɗanda suke kiran Ubanni na Coci ya fi Kalmar Allah muhimmanci! Idan ka taɓa tattauna koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya da ɗaliban addini, wataƙila ka lura da hakan.

12. Ta yaya sarkin ya yi rinjaya da ba ta dace ba?

12 Masu sarautar ƙasar Roma suna da iko sosai bisa wannan taron. Alal misali, Farfesa Richard E. Rubenstein ya rubuta game da abin da ya faru a taron da aka yi a birnin Nicaea: “Constantine ya sa limaman wadata sosai. Kafin shekara guda, wannan sabon sarkin ya mayar musu da dukan abubuwan da aka karɓi a hannunsu, kamar cocinsu da sana’o’insu da kuma mukamansu . . . Ya ba limaman Kirista gatan da ake ba firistoci kafirai a dā.” A sakamako, “Constantine ya samu damar rinjayar shawarar da aka tsai da a taron da aka yi a birnin Nicaea, wataƙila ya ma canja kome.” Charles Freeman ya daɗa: “Bayan taron, sarkin ya soma samun iko sosai a cocin. Ya ba cocin iko kuma ya rinjayi koyarwarta.”—Karanta Yaƙub 4:4.

13. Me kake tsammani ya sa shugabannin coci suka yi banza da koyarwar Littafi Mai Tsarki?

13 Ko da yake ya yi wa limaman coci wuya su amince cewa Yesu Kristi Ɗan Allah ne, amma wasu da ba limamai ba ne ba su da irin wannan ra’ayin. Waɗanda ba limaman cocin ba ne sun fahimci da kuma amince da abin da suka karanta a cikin Nassosi. Amma limaman suna son kuɗi da kuma ikon da sarkin yake ba su, saboda haka, suka yi banza da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Gregory na Nyssa, wanda shugaban addini ne a lokacin, ya yi baƙar magana game da yadda mutane, kamar masu sayar da tufafi da masu canja kuɗaɗe da masu sayar da kayayyaki da bayi suka yi magana game da addini. Gregory bai yi farin ciki ba cewa mutane da yawa sun ce Ɗan ya bambanta da Uban, Uban kuma ya fi Ɗan girma kuma ba a yi amfani da kome wajen halittar Ɗan ba. Mutanen sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen bayyana wannan gaskiyar. Wannan abu ne da Gregory na Nyssa da kuma limaman cocin ba sa yi. Da ya fi dacewa su saurari mutanen.

“ALKAMA” DA “ZAWA” SUN YI GIRMA TARE

14. Yaya muka san cewa akwai Kiristoci shafaffu na gaske a duniya tun daga ƙarni na farko zuwa yanzu?

14 Yesu ya bayyana a almararsa cewa daga ƙarni na farko zuwa gaba, za a ci gaba da samun shafaffu Kiristoci masu aminci a duniya. Ya kwatanta su da “alkama” da suke girma cikin “zawan.” (Mat. 13:30) Ko da yake ba za mu iya faɗa da tabbaci mutane ko rukunin da ke cikin rukunin alkama shafaffe ba, amma za mu iya tabbata cewa akwai mutanen da suke kāre Kalmar Allah da gaba gaɗi kuma suke fallasa koyarwar ƙarya na cocin. Bari mu tattauna wasu misalai.

15, 16. Ka ambata sunayen wasu da suka daraja Kalmar Allah?

15 Wani shugaban coci mai suna Agobard na Lyons a ƙasar Faransa daga shekara ta 779 zuwa 840 A.Z., ya nuna rashi yarda game da bautar gumaka da keɓe coci ga waliyai da kuma ayyuka da kuma bautar da cocin suke yi. Wani limami mai suna Claudius, da ya wanzu a zamanin Agobard ma ya ƙi da al’adar cocin da yi wa waliyai sujada da kuma bauta wa gumaka. A ƙarni na 11, an yi wa deacon Berengarius na birnin Tours, a ƙasar Faransa yankan zumunci domin bai amince da koyarwar cewa gurasa da kuma ruwan inabin da Yesu ya bayar kafin ya mutu ya zuma ainihin jikinsa da kuma jininsa ba. Ya kuma koyar cewa Littafi Mai Tsarki ya fi al’adar cocin iko.

16 Akwai mutane biyu a ƙarni na 12, wato, Peter Bruys da Henry Lausanne da suke son koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai. Peter ya yi murabus daga coci domin bai amince da Nassosin da Katolika suka ce sun goyi bayan yi wa jarirai baftisma da cewa gurasa da ruwan inabin da Yesu ya yi jibin maraice da su sun zama ainihin jiki da kuma jininsa da yi wa matattu addu’a da kuma yin amfani da giciye a bauta ba. A shekara ta 1140, aka kashe Peter saboda imaninsa. Henry, wanda shi sufi ne ya nuna rashin yardarsa game da ayyuka da kuma bauta marasa kyau da ake yi a coci. Sai aka kama shi a shekara ta 1148 kuma aka masa ɗaurin rai da rai a cikin kurkuku.

17. Waɗanne matakai masu muhimmanci ne Waldo da mabiyansa suka ɗauka?

17 A lokacin da aka ƙona Peter Bruys domin ya yi musun abin da aka koyar a coci, an haifi wani kuma wanda daga baya ya sa aka yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Sunan mahaifinsa shi ne, Valdès, ko Waldo.a Ba shi da ilimin addini kamar su Peter Bruys da Henry na Lausanne, amma ya daraja Kalmar Allah sosai har ya yi watsi da dukiyarsa kuma ya sa aka fassara ɓangarori na Littafi Mai Tsarki a harshen da mutane da yawa suke yi a kudu matso gabas na ƙasar Faransa. Wasu sun yi farin ciki sosai don jin saƙon Littafi Mai Tsarki a nasu harshe har su ma suka rarraba wa mutane dukiyoyinsu kuma suka yi amfani da rayuwarsu don su tattauna gaskiyar Littafi Mai Tsarki da mutane. Limaman cocin ba su yi farin ciki ba sam. A shekara ta 1184, fafaruma ya yi wa waɗannan maza da mata masu ƙwazo da aka kira su daga baya Waldenses yankan zumunci, kuma limamin cocin ya kore su daga gidajensu. Hakan ya sa an yaɗa saƙon Littafi Mai Tsarki a wasu wurare. Daga baya, mabiyan Waldo da Peter Bruys da Henry na Lausanne da kuma wasu da suka bar cocin sun kasance a wurare da yawa a ƙasar Turai. A ƙarni na gaba, wasu da suka goyi bayan gaskiyar Littafi Mai Tsarki su ne: John Wycliffe (daga shekara ta 1330-1384) da William Tyndale (daga shekara ta 1494-1536) da Henry Grew (daga shekara ta 1781-1862) da George Storrs (daga shekara ta 1796-1879).

“BA A ƊAURE MAGANAR ALLAH BA”

18. Ta yaya ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu zukatan kirki a ƙarni na 19 suka yi nazarin Littafi Mai Tsari kuma yaya hakan ya yi nasara?

18 Maƙiyan Littafi Mai Tsarki ba su iya hana mutane yaɗa gaskiya ba. Littafin 2 Timotawus 2:9 ya ce, “Ba a ɗaure maganar Allah ba.” A shekara ta 1870, wani rukunin mai son gaskiya, ya soma bincika Littafi Mai Tsarki. Yaya suka yi nazarinsu? Da farko, wani zai yi tambaya game da wani batu. Sai su tattauna batun tare. Za su bincika dukan nassosin da suka yi magana game da batun, bayan hakan idan suka gamsu da amsar, sai su tsai da shawara kuma su rubuta shawarar da suka tsai da. Wannan hanya ce mai kyau na yin nazari domin sun bi misalin manzanni da kuma dattawa na ƙarni na farko. Yana da ban ƙarfafa sanin cewa waɗannan Shaidun Jehobah amintattu a ƙarni na 19 sun tabbata cewa sun yi imani gabaki ɗaya ga Kalmar Allah.

19. Mene ne jigon nassi na shekara ta 2012, kuma me ya sa ya dace?

19 Har yau, Littafi Mai Tsarki ne tushen imaninmu. Saboda haka, Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah ta zaɓi kalamin Yesu don jigo na shekara ta 2012: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yoh. 17:17) Tun da wajibi ne duk wanda yake son ya yi tafiya bisa gaskiya ya samu amincewar Allah, bari dukanmu mu ci gaba da yin ƙoƙari don Kalmar Allah ta yi mana ja-gora.

[Hasiya]

a A wasu lokatai ana kiran Valdès, Pierre Valdès ko Peter Waldo, amma ba a san ainihin sunansa na farko ba.

KA NEMI WAƊANNAN BAYANAN:

․․․․․

Mene ne bambancin taron da aka yi a Urushalima a shekara ta 49 A.Z., da na cocin da aka yi?

․․․․․

Mene ne sunayen wasu da suka kāre Kalmar Allah bayan zamanin manzanni?

․․․․․

Ta yaya Kiristoci amintattu suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki a ƙarni na 19 kuma me ya sa hakan yake da kyau?

[Bayanin da ke shafi na 8]

Jigo na shekara ta 2012 shi ne: “Maganarka ita ce gaskiya.”—Yoh. 17:17

[Hoton da ke shafi na 7]

Waldo

[Hoton da ke shafi na 7]

Wycliffe

[Hoton da ke shafi na 7]

Tyndale

[Hoton da ke shafi na 7]

Grew

[Hoton da ke shafi na 7]

Storrs

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba