Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w20 Afrilu pp. 1-32
  • Za A Kawo Hari Daga Arewa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za A Kawo Hari Daga Arewa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILAI HUƊU NA YIN GYARA
  • ME HAKAN YAKE NUFI?
  • ZA A SAMI CANJIN YANAYI
  • WANE ƘARIN HASKE NE AKA SAMU?
  • Jimrewa Da Gwaji Ya Ƙarfafa Dogararmu Ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Joel
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Darussa Daga Littattafan Joel da Amos
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
w20 Afrilu pp. 1-32

TALIFIN NAZARI NA 14

Za A Kawo Hari Daga Arewa!

“Tulin mutane sun fāɗa wa ƙasata.”​—YOW. 1:6.

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Ta yaya ʼyan’uwa a zamanin su Russell suka yi nazari, me ya sa hakan ya dace?

FIYE da shekaru 100 da suka shige, Ɗan’uwa C. T. Russell da wani ƙaramin rukuni sun soma taro don su yi nazarin Kalmar Allah. Sun so su san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Jehobah da Yesu Kristi da abin da ke faruwa da matattu da kuma fansar da Yesu ya yi. Yadda suka yi nazarin yana da sauƙi. Wani zai yi tambaya, sai ʼyan’uwa a rukunin su tattauna kowane nassi da ke da alaƙa da batun. Daga baya, sai su rubuta abin da suka fahimta. Jehobah ya taimaka musu su fahimci gaskiya mai muhimmanci da muke darajawa har yau.

2. Mene ne zai iya sa mu kasa fahimtar wani annabcin Littafi Mai Tsarki?

2 Ba da daɗewa ba, ʼyan’uwan sun fahimci cewa gane ma’anar annabcin Littafi Mai Tsarki ya fi gane ma’anar koyarwar nassosi wuya. Me ya sa? Domin ya fi sauƙi a gane ma’anar annabci a lokacin da yake cika ko bayan ya cika. Amma akwai wasu dalilai kuma. Idan muna so mu fahimci wani annabci, muna bukatar mu fahimci annabcin gabaki ɗaya. Idan muka fi mai da hankali a kan sashe guda na annabcin kuma muka bar sauran, ba za mu fahimci annabcin sosai ba. Kamar dai abin da ya faru da wani annabcin da ke littafin Yowel ke nan. Bari mu sake bincika wannan annabcin domin mu ga dalilin da ya sa muke bukatar mu yi gyara ga yadda muka fahimce shi.

3-4. Ta yaya muka fahimci annabcin da ke Yowel 2:​7-9?

3 Karanta Yowel 2:​7-9. Yowel ya annabta cewa fāri za su yi ɓarna a ƙasar Isra’ila kuma hakan zai tayar da hankulan mutane. Fārin suna da haƙora kamar zakuna kuma za su cinye dukan shuke-shuken da ke ƙasar. (Yow. 1:​4, 6) A cikin shekaru da yawa yanzu, mun ɗauka cewa wannan annabcin yana magana ne game da yadda Shaidun Jehobah suke wa’azi a ko’ina kamar tulin fāri da ba za a iya dakatar da su ba. Mun fahimci cewa wannan wa’azin yana shafan ‘ƙasar’ ko kuma mutanen da limaman addinan ƙarya ke musu ja-goranci.b

4 Wannan bayanin daidai ne idan muka karanta littafin Yowel 2:​7-9 kaɗai. Amma idan muka yi tunani a kan annabcin gabaki ɗaya, za mu ga cewa muna bukatar mu fahimci annabcin a wata hanya dabam. Yanzu bari mu tattauna dalilai huɗu da suka sa hakan ya dace.

DALILAI HUƊU NA YIN GYARA

5-6. Wace tambaya ce muke yi sa’ad da muka karanta (a) Yowel 2:20? (b) Yowel 2:25?

5 Da farko, ku lura da alkawarin da Jehobah ya yi game da harin fāri: ‘Zan kawar da fāri nesa da ku, sojojin arewa waɗanda suka fāɗo muku.’ (Yow. 2:20) Idan fārin na wakiltar Shaidun Jehobah da ke yin biyayya ga umurnin da Yesu ya bayar cewa mu riƙa wa’azi, me ya sa Jehobah zai yi alkawari cewa zai kawar da su? (Ezek. 33:​7-9; Mat. 28:​19, 20) A bayyane yake cewa Jehobah ba ya so ya kawar da bayinsa, amma yana so ya kawar da wani abu ko kuma wani mutum da ke gāba da bayinsa.

6 Dalili na biyu shi ne abin da ke Yowel 2:25. A nan Jehobah ya ce: ‘Zan mayar da duk abin da fāri suka ci cikin shekarun nan, ko manyan fāri ne ko fāri masu rarrafe ko wata ƙungiyar fāri, ko kuwa fāri masu yawo, wato babbar ƙungiyar soja da na aiko muku.’ Ka lura cewa Jehobah ya yi alkawari cewa zai “mayar da” dukan abubuwan da fārin suka ɓata. Idan fārin suna wakiltar bayin Jehobah da ke wa’azi, hakan zai nuna cewa saƙon da suke yaɗawa yana jawo lahani. Amma a bayyane yake cewa saƙon yana sa wasu mugayen mutane su tuba. (Ezek. 33:​8, 19) Wannan albarka ce sosai a gare su!

7. Mene ne ma’anar kalmomin nan “bayan abubuwan nan” da ke Yowel 2:​28, 29?

7 Karanta Yowel 2:​28, 29. Dalili na uku ya shafi yadda aka tsara abubuwan da aka annabta. Ku lura cewa Jehobah ya ce: ‘Bayan abubuwan nan, zan zuba ruhuna,’ wato bayan fārin sun kammala aikin da aka ba su. Idan fārin suna wakiltar masu shela, me ya sa Jehobah zai zuba musu ruhunsa bayan sun kammala wa’azin da ya ce su yi? Gaskiyar ita ce, idan Jehobah bai taimaka musu da ruhunsa ba, ba za su iya yin shekaru suna wa’azi duk da tsanantawa da kuma takunkumin da aka saka wa aikinsu ba.

Hotuna: Hotunan yadda ake wa’azi a dā. 1. Wata ’yar’uwa kusa da mota kuma tana rike da jaka da littattafai a ciki. 2. Wasu ’yan’uwa sanye da fosta. 3. Mota mai lasifika. 4. Wani dan’uwa rike da mujalla. 5. Dan’uwa Joseph F. Rutherford yana ba da jawabi a taron yanki. 6. Wani dan’uwa ya saka jawabai da garmaho a wa’azi kuma mutane biyu suna saurara.

Ɗan’uwa J. F. Rutherford da wasu ’yan’uwa shafaffu da suka yi ja-goranci a ƙungiyar Jehobah sun yi shela da gaba gaɗi a kan yadda Jehobah zai hallaka duniyar Shaiɗan (Ka duba sakin layi na 8)

8. Su waye ne fārin da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 9:​1-11 suke wakilta? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

8 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 9:​1-11. Yanzu bari mu tattauna dalili na huɗu. A dā, mun ce tulin fārin da aka ambata a littafin Yowel na da alaƙa da wa’azin da muke yi domin an yi irin wannan annabcin a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. A annabcin, an ambata tulin fārin da ke da fuskokin ʼyan Adam kuma suna sanye da “wani abu kamar hulunan mulki na zinariya” a kawunansu. (R. Yar. 9:7) Suna azabtar da “mutane [maƙiyan Allah] waɗanda ba su da hatimi na Allah a goshinsu” har tsawon watanni biyar, wato tsawon rayuwar fāri. (R. Yar. 9:​4, 5) Babu shakka, ana kwatanta shafaffun bayin Jehobah ne a wannan annabcin. Suna sanar da saƙon hukuncin Allah a kan mugayen mutane kuma saƙon yana tayar musu da hankali sosai.

9. Wane bambanci ne ke tsakanin fārin da Yowel ya gani da wanda Yohanna ya ambata?

9 Babu shakka, akwai alaƙa tsakanin annabcin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna da kuma wanda Yowel ya rubuta. Duk da haka, suna da bambanci sosai. Alal misali: A annabcin Yowel, fārin sun cinye itatuwa da ganyaye. (Yow. 1:​4, 6, 7) Amma a annabcin Yohanna, an gaya wa fārin cewa “kada su yi wa ciyawar ƙasa ɓarna.” (R. Yar. 9:4) Fārin da Yowel ya gani sun zo ne daga arewa. (Yow. 2:20) Amma fārin da Yohanna ya gani sun fito ne daga wani rami mai zurfi. (R. Yar. 9:​2, 3) An kawar da fārin da Yowel ya gani. A wanda Yohanna ya ambata, ba a kawar da su ba amma an bar su su kammala aikinsu. Babu wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa Jehobah ya yi fushi da su.​—Ka duba akwatin nan “Annabci Game da Fāri, Sun Yi Kama Amma Sun Bambanta.”

Annabci Game da Fāri, Sun Yi Kama Amma Sun Bambanta

Yowel 1:4; 2:​7-9, 20

  • Sojojin Babiloniyawa rike da takobi da kuma mashi. Fāri da yawa a bayansu.

    Sun fito daga arewa

  • Sun cinye itatuwa da ganyaye

  • An kore su

  • Suna wakiltar sojojin Babila da suka kai wa Urushalima hari a shekara ta 607

Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 9:​1-11

  • ’Yan’uwa suna wa’azi rataye da fosta a wuyansu. Fāri da yawa a karkashin hoton.

    Sun fito daga rami mai zurfi

  • Ba a yarda su cinye itatuwa da ganyaye ba

  • Sun kammala aikinsu

  • Suna wakiltar bayin Jehobah shafaffu da suke wa’azi da ƙarfin zuciya game da hukuncin Allah a kan miyagu

10. Ka ba da misali a Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa fārin da Yowel ya gani da kuma na Yohanna sun bambanta.

10 Bambancin da ke tsakanin waɗannan annabci biyu sun sa mu san cewa ba su da alaƙa. Shin muna nufi ne cewa fārin da Yowel ya gani da kuma wanda Yohanna ya ambata ba su da alaƙa? Ƙwarai kuwa. A wasu lokuta a cikin Littafi Mai Tsarki, ana yin amfani da abu guda domin kwatanta abubuwa dabam-dabam. Alal misali, a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:​5, an kira Yesu “Zakin nan daga zuriyar Yahuda” amma a littafin 1 Bitrus 5:​8, an kira Shaiɗan “zaki mai jin yunwa.” Dalilan nan huɗu da muka tattauna da wasu abubuwa sun sa ya dace mu yi gyara ga yadda muka fahimci annabcin Yowel. Wane ƙarin haske ne aka samu?

ME HAKAN YAKE NUFI?

11. Ta yaya Yowel 1:6 da 2:​1, 8, 11 suka taimaka mana mu fahimci ma’anar tulin fārin?

11 Idan mun sake duba annabcin Yowel sosai, za mu lura cewa yana magana ne game da harin da sojoji za su kai. (Yow. 1:6; 2:​1, 8, 11) Jehobah ya ce zai yi amfani da “babbar ƙungiyar soja,” wato sojojin Babila wajen hukunta Isra’ilawa masu taurin kai. (Yow. 2:25) Ya dace da aka kira su “sojojin arewa” domin Babiloniyawa za su kawo wa Isra’ilawa hari daga arewa. (Yow. 2:20) An kwatanta sojojin nan da tulin fāri da aka tsara su da kyau. Yowel ya yi furucin nan game da su: Kowane soja “yana bin layinsa. . . . Sukan kai da kawowa a birnin, sukan gudu a kan katanga. Sukan hau su shiga gidaje, sukan shiga tagogi kamar ɓarayi.” (Yow. 2:​8, 9) Ka yi tunani a kan abin da aka kwatanta a ayar nan. Akwai sojoji a ko’ina kuma babu wurin ɓuya. Babu wani da zai iya tsira daga sojojin Babila!

12. Ta yaya annabcin Yowel game da fāri ya cika?

12 Babiloniyawa (ko Kaldiyawa) sun kai wa birnin Urushalima hari kamar fāri a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Sarkin [Kaldiyawa] ya kakkashe samarin Yahuda da takobi . . . . Bai ji tausayin kowa ba, babba da ƙarami, saurayi ko budurwa, mai lafiya ko marar lafiya. Dukansu Allah ya bashe su a hannun sarkin Babila mutumin Kaldiya. Sojojinsa suka ƙone Gidan Allah, suka rushe katangar birnin Urushalima, suka ƙone dukan gidajen sarki, da kowane abu mai daraja wanda yake a ciki.’ (2 Tar. 36:​17, 19) Bayan Babiloniyawa sun yi kaca-kaca da ƙasar, sai mutane suka ce: “Ta zama kufai, babu mutum ko dabba a ciki, gama an ba da ita a hannun Kaldiyawa.”​—Irm. 32:43.

13. Ka bayyana ma’anar littafin Irmiya 16:​16, 18.

13 Wajen shekara 200 bayan Yowel ya yi annabcin nan, Jehobah ya yi amfani da Irmiya don ya annabta wani abu dabam game da wannan harin. Jehobah ya ce mahara za su nemi Isra’ilawa da ke miyagun ayyuka kuma za su kama dukansu. Jehobah ya ce: “Duk da haka, yanzu ga shi, ina shirin kirawo mutane masu kamun kifi da yawa, su kama mutanen nan. Daga baya kuma zan kirawo mutane masu farauta da yawa, su farauci mutanen nan. Za a yi farautarsu a kowane babban tudu da kuma a kowane tudu, har ma a cikin kogon duwatsu. Zan hukunta su da cikakken hukunci gwargwadon laifofinsu da zunubansu.” Koguna ko kuma daji ba za su iya kāre Isra’ilawa da ba su tuba ba daga harin Babiloniyawa.​—Irm. 16:​16, 18.

ZA A SAMI CANJIN YANAYI

14. A wane lokaci ne annabcin da ke Yowel 2:​28, 29 ya cika?

14 Bayan haka, sai Yowel ya faɗi wani albishiri. Ya ce ƙasar za ta sake ba da amfani. (Yow. 2:​23-26) Kuma a nan gaba, abubuwa na ibada za su yalwata. Jehobah ya ce: “Zan zuba ruhuna a kan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, . . . bayinku maza da mata zan zuba musu ruhuna.” (Yow. 2:​28, 29) Jehobah bai zuba wa Isra’ilawa ruhunsa nan da nan da suka dawo daga ƙasar Babila ba. Amma hakan ya faru bayan shekaru da yawa, wato a ranar Fentakos ta 33. Ta yaya muka san hakan?

15. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 2:​16, 17 suka nuna, wane gyara ne Bitrus ya yi ga littafin Yowel 2:​28, kuma me hakan ya nuna?

15 Manzo Bitrus ya faɗi cewa annabcin da ke littafin Yowel 2:​28, 29 ya cika a ranar Fentakos. A wajen ƙarfe tara na safe, sai Allah ya zubo da ruhunsa kuma mutanen da suka sami ruhun suka soma magana cikin harsuna dabam-dabam game da “manyan abubuwan da Allah ya yi.” (A. M. 2:11) Allah ya hure Bitrus ya yi amfani da kalmomi dabam sa’ad da yake yin ƙaulin annabcin Yowel. Shin ka lura da canjin da ya yi? (Karanta Ayyukan Manzanni 2:​16, 17.) Maimakon Bitrus ya soma ƙaulinsa da kalmomin nan “bayan abubuwan nan,” ya ce: “A kwanakin ƙarshe.” Kwanaki na ƙarshe da ya ambata a ayar tana nufin ƙarshen zamanin Yahudawa kuma a lokacin ne Allah zai zubo ruhunsa a kan “dukan ’yan Adam.” Hakan ya nuna cewa an jima sosai kafin annabcin Yowel ya cika.

16. Ta yaya ruhun Allah ya taimaka wa Kiristoci su yaɗa bishara a ƙarni na farko, kuma ta yaya yake taimaka mana a yau?

16 Sai bayan da Allah ya zuba ruhunsa a kan almajiran Yesu a ƙarni na farko ne aka soma samun ci gaba sosai a wa’azi a faɗin duniya. A lokacin da manzo Bulus ya rubuta wasiƙa ga Kolosiyawa a wajen shekara ta 61, ya ce an riga an yi wa’azin bishara ga “kowace halitta a ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Sa’ad da manzo Bulus ya ce “kowace halitta,” yana nufin wuraren da shi da abokan aikinsa suka yi wa’azi. A zamaninmu, Jehobah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki wajen taimaka wa bayinsa su yi wa’azi “har zuwa iyakar duniya”!​—A. M. 13:47; ka duba akwatin nan “Zan Zuba Ruhuna” a Kan Bayina.

“Zan Zuba Ruhuna” a Kan Bayina

A ranar Fentakos ta 33, maza da mata wajen 3,000 sun yi baftisma kuma sun zama almajiran Yesu Kristi. Ba tare da ɓata lokaci ba, sun soma yi wa mutane wa’azi game da Yesu. Jehobah ya albarkace su kuwa? Ƙwarai kuwa! “Dubban mutane” sun zama almajiran Yesu.​—A. M. 2:41; 21:20.

Mutane nawa ne suka zama Kiristoci? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba, amma har ƙarshen ƙarni na farko, adadin Kiristoci bai kai 144,000 ba. A lokacin, Jehobah yana zaɓan maza da mata da za su yi sarauta da Yesu a sama, amma a zamaninmu ne Jehobah ya zaɓi yawancin shafaffu. Duk da haka, mutanen da suka zama Kiristoci a lokacin ya nuna cewa Jehobah ya zuba ruhunsa a kan almajiran Yesu.​—A. M. 2:​16-18.

Shin da akwai alamar da ta nuna cewa Jehobah ya zuba ruhunsa a kan bayinsa a yau? Ƙwarai kuwa! Ka yi la’akari da waɗannan misalai: A shekara ta 1919, adadin masu shela bai kai 6,000 ba. Duk da haka, Jehobah ya albarkaci wa’azin da muke yi. Tun shekara ta 1983, mutane fiye da 144,000 ne suke yin baftisma a kowace shekara! Babu shakka, hakan ya nuna cewa Jehobah yana cika alkawarin da ya yi wa bayinsa cewa “zan zuba ruhuna” a kanku.​—Yow. 2:​28, 29.

WANE ƘARIN HASKE NE AKA SAMU?

17. Wane ƙarin haske ne aka samu game da annabcin fāri da Yowel ya yi?

17 Wane ƙarin haske ne aka samu? A yanzu muka fi fahimtar annabcin da ke littafin Yowel 2:​7-9. A taƙaice, ayoyin nan suna magana ne game da harin da sojojin Babila suka kai wa Urushalima a shekara ta 607, ba wa’azin da muke yi da ƙwazo a yau ba.

18. Mene ne bai canja ba a fahimtarmu?

18 Mene ne bai canja ba a fahimtarmu? Bayin Jehobah za su ci gaba da yin amfani da kowane zarafin da suka samu don yin wa’azi a ko’ina. (Mat. 24:14) Babu gwamnatin ʼyan Adam da ta isa ta hana mu yin wa’azi. Jehobah yana taimaka mana mu yi wa’azi game da Mulkin Allah da ƙwazo a yau fiye da dā! Muna ci gaba da dogara ga Jehobah don ya taimaka mana mu fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki. Kuma muna da tabbaci cewa zai sa mu fahimci “dukan gaskiya” a lokacin da ya dace!​—Yoh. 16:13.

ZA KA IYA BAYYANAWA?

  • A wasu lokuta, me ya sa muke bukatar gyara ga yadda muka fahimci wasu annabcin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne aka annabta a littafin Yowel 2:​7-9?

  • Me ya sa kake ganin cewa yin gyara ga yadda muka fahimci Nassosi suna ƙarfafa bangaskiyarmu?

WAƘA TA 97 Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu

a Shekaru da yawa yanzu, mun gaskata cewa annabcin da ke littafin Yowel surori 1 da 2 na magana ne game da wa’azin da muke yi a yau. Amma akwai dalilai huɗu da suka sa ya wajaba mu yi gyara ga yadda muka fahimci wannan annabcin. Waɗanne dalilai ke nan?

b Alal misali, ka duba talifin nan “Hikimar Jehobah Ta Bayyana A Halittarsa” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2009, sakin layi na 14-16.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba