Markus ‘Yana da Amfani Wajen Hidima’
IKILISIYAR Antakiya ta taɓa ganin matsaloli dabam-dabam, amma rashin jituwar da ke tsakanin manzanni Bulus da Barnaba ta bambanta da wadda suka taɓa gani. Mazan suna shirin yin tafiya na wa’azi, amma, sa’ad da ya zo ga tsai da shawara game da wanda zai yi tafiyar tare da su, “jayayya ta tashi” tsakaninsu. (A. M. 15:39) Mazan biyu suka rabu, kowa ya kama hanyarsa. Markus, mai wa’azi na uku shi ne dalilin jayayyarsu.
Wanene Markus? Me ya sa manzannin biyu suka yi gardama saboda shi? Me ya sa suke da irin waɗannan ra’ayoyi masu ƙarfi? Waɗannan ra’ayoyin sun canja kuwa? Menene za ka iya koya daga labarin Markus?
A Gida a Urushalima
Markus, wanda wataƙila ya fito daga iyalin Yahudawa mai arziki, ya yi girma a Urushalima. Abu na farko da muka sani game da shi ya shafi tarihin ikilisiyar Kirista na farko. A wajen shekara ta 44 A.Z., sa’ad da mala’ikan Jehobah ta hanyar mu’ujiza ya ’yantar da manzo Bitrus daga fursuna na Hirudus Agaribas na ɗaya, Bitrus ya tafi “gidan Maryamu uwar Yohanna wanda ana ce da shi Markus; can fa mutane da yawa suke a tattare, suna addu’a.”—A. M. 12:12.a
Kamar dai, ikilisiyar Urushalima tana amfani da gidan mamar Markus don taro. Da yake “mutane da yawa” sun taru a wajen ya nuna cewa babban gida ne. Maryamu tana da baiwa mai suna Roda wadda ta je ta ga kowanene ke bakin ƙofa sa’ad da Bitrus ya ƙwanƙwasa “ƙyamren ƙofa.” Waɗannan abubuwa sun nuna cewa Maryamu mace ce mai ɗan arziki. Kuma an ce gidan nata ne maimako na mijinta, saboda haka, wataƙila gwauruwa ce kuma Markus yaro ne ƙarami.—A. M. 12:13.
Wataƙila Markus yana cikin waɗanda suka taru su yi addu’a. Ya san almajiran Yesu sosai kuma yana cikin waɗanda suka ga aukuwa na hidimar Yesu. Mai yiwuwa, Markus ne saurayin da ke yafe da mayafi wanda ya yi ƙoƙari ya bi Yesu sa’ad da aka kama shi da farko amma ya gudu sa’ad da suke ƙoƙari su kama Yesu.—Mar. 14:51, 52.
Gata a Cikin Ikilisiya
Yin tarayya da Kiristoci da suka manyanta babu shakka ya yi tasiri a kan Markus sosai. Ya manyanta a ruhaniya kuma hakan ya jawo hankalin ’yan’uwa masu hakki a gare shi. A wajen shekara ta 46 A.Z., sa’ad da Bulus da Barnaba suka aika “gudunmuwa” daga Antakiya zuwa Urushalima don su rage sakamakon yunwa, kuma sun so Markus. Sa’ad da Bulus da Barnaba suka koma Antakiya, sun tafi tare da Markus.—A. M. 11:27-30; 12:25.
Wani da ke karanta wannan labarin sama-sama zai yi tunani cewa ba abin da ya haɗa waɗannan maza uku, ban da cewa su Kiristoci ne, kuma zai iya yin tunani cewa Bulus da Barnaba sun ɗauki Markus ne kawai domin iyawarsa. Amma ɗaya daga cikin wasiƙun Bulus ta nuna cewa kakan Markus ɗaya ne da na Barnaba. (Kol. 4:10; Littafi Mai Tsarki) Hakan zai iya taimakawa wajen bayyana abubuwan da suka faru da suka shafi Markus.
Shekara guda ko fiye da haka ta wuce, kuma ruhu mai tsarki ya ja-goranci Bulus da Barnaba su yi tafiya zuwa wasu ƙasashe don yin wa’azi. Suka tashi daga Antakiya zuwa Ƙubrus. Yohanna Markus ya tafi da su “yana yi masu hidima.” (A. M. 13:2-5) Wataƙila Markus yana kula da bukatu masu muhimmanci ne a lokacin tafiyar domin manzannin sun mai da hankali ga al’amura na ruhaniya.
Bulus, Barnaba, da Markus suka yi tafiya zuwa Ƙubrus, suna wa’azi sa’ad da suke tafiya; sai suka kama tafiya zuwa Asiya Ƙarama. A can, Yohanna Markus ya tsai da shawara da ta sa Bulus baƙin ciki. Labarin ya ce sa’ad da suka isa Barjata, “Yohanna ya rabu da su, ya koma Urushalima.” (A. M. 13:13) Ba a faɗi dalilin da ya sa ya yi hakan ba.
Shekaru bayan haka, Bulus, Barnaba da Markus sun riga sun koma Antakiya. Manzannin biyu suna tattauna tafiya ta biyu na yin wa’azi a ƙasashen waje don su ƙarfafa abin da suka cim ma a tafiyarsu ta farko. Barnaba yana son ya ɗauki ɗan kakansa, amma Bulus ba ya son su tafi da shi domin Markus ya bar su a dā. Wannan shi ne ya jawo gardamar da aka kwatanta a gabatarwa. Barnaba ya ɗauki Markus kuma suka tafi garinsa Ƙubrus, yayin da Bulus kuma ya tafi Suriya. (A. M. 15:36-41) A bayyane yake cewa Bulus da Barnaba suna da ra’ayi dabam-dabam game da abin da Markus ya yi a dā.
Sulhuntawa
Babu shakka Markus ya yi baƙin ciki don abin da ya faru. Duk da haka, ya ci gaba da zama mai hidima da aminci. Shekaru goma sha ɗaya ko biyu bayan wannan matsala da Bulus, Markus ya sake bayyana a tarihin Kiristanci na farko. A ina? Inda ba za ka yi tsammanin ganinsa ba, wato, tare da Bulus!
A shekara ta 60 zuwa 61 A.Z., sa’ad da Bulus yake kurkuku a ƙasar Roma, ya aika wasiƙu da yawa da yanzu sashe ne na Nassosi Masu Tsarki. A cikin wadda ya rubuta zuwa ga Kolosiyawa, ya rubuta: “Aristarkus abokin sarƙana yana gaishe ku, da Markus kuma, [wanda kakansa ɗaya ne da] Barnaba (wanda kuka karɓi umurni a kansa; idan ya zo gare ku, ku karɓe shi) . . . waɗannan su ne kaɗai abokan aikina zuwa mulkin Allah, mutane waɗanda suka yi mini ta’aziyya.”—Kol. 4:10, 11.
Wannan canji ne gabaki ɗaya! Ko da yake a dā Bulus ya ƙi jinin Markus, amma a yanzu ya sake ɗaukansa abokin aiki mai tamani. Babu shakka, Bulus ya gaya wa Kolosiyawa cewa Markus yana iya ziyartarsu. Idan ya zama hakan, Markus zai zama wakilin Bulus.
Shin Bulus ya yi yawan sūkan Markus cikin shekaru da suka shige ne? Markus ya amfana ne daga wannan horon? Ko kuwa waɗannan yanayin biyu sun faru da gaske? Ko yaya dai, sulhuntawar da suka yi ta nuna cewa Bulus da Markus sun manyanta. Ba su ƙyale jayayyarsu ta shafe su har dindindin ba, kuma hakan ya taimaka musu su yi aiki tare. Wannan misali ne mafi kyau ga duk wanda yake da matsala da ɗan’uwansa Kirista!
Markus Matafiyi
Yayin da ka karanta game da tafiye-tafiyen da Markus ya yi, za ka fahimci cewa ya yi tafiya sosai. Ya fito daga Urushalima, ya tafi Antakiya, kuma daga wajen ya tafi Ƙubrus da Barjata. Sai ya tafi Roma. Daga wajen Bulus, yana son ya aika shi zuwa Kolosi. Kuma da ƙari!
Manzo Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko, a wajen shekara ta 62 zuwa 64 A.Z. Ya rubuta: “Ita wadda ta ke cikin Babila, . . . tana gaishe ku; haka nan kuma Markus ɗana.” (1 Bit. 5:13) Hakan ya nuna cewa Markus ya yi tafiya zuwa Babila don ya yi hidima tare da manzo wanda shekaru da suka shige ya halarci taron Kirista a gidan mamarsa.
Sa’ad da aka riƙe Bulus a kurkuku a Roma a lokaci na biyu a misalin shekara ta 65 A.Z., ya rubuta a kira Timotawus daga Afisa, Bulus ya daɗa: “Ka ɗauko Markus, ka kawo shi tare da kai.” (2 Tim. 4:11) Wannan ya nuna cewa Markus yana Afisa a lokacin. Mai yiwuwa ya yarda ya koma Roma tare da Timotawus yadda Bulus ya faɗa. Yin tafiya ba shi da sauƙi a lokacin, amma Markus ya yi waɗannan tafiye-tafiye da yardan rai.
Wani Gata Mai Girma
Wani gata mai girma da Markus ya more shi ne zama wanda Jehobah ya hure ya rubuta littafi ɗaya cikin Linjila. Ko da yake Linjila ta biyu ba ta ambata sunan wanda ya rubuta ta ba, al’adu na farko sun faɗi cewa Markus ne ya rubutata kuma ya samu bayaninsa daga Bitrus ne. Hakika, Bitrus ya shaida dukan abubuwan da Markus ya rubuta.
Masu binciken Linjilar Markus sun gaskata cewa ya rubuta ta don masu karatu na ’yan Al’umma ne; ya ba da bayani masu kyau game da al’adun Yahudawa. (Mar. 7:3; 14:12; 15:42) Markus ya fassara kalaman Aramaic don waɗanda ba Yahudawa ba su fahimta. (Mar. 3:17; 5:41; 7:11, 34; 15:22, 34) Ya yi amfani da kalaman yaren Latin da yawa kuma ya bayyana kalaman Helenanci masu sauƙi ta wajen yin amfani da yaren Latin. Dukan waɗannan abubuwa sun jitu da tsohuwar al’adar da ta ce Markus ya rubuta Linjilarsa a Roma.
“Yana da Amfani Gare ni Wajen Hidima”
Rubuta Linjilarsa ba ita ba ce kawai aikin da Markus ya yi a Roma ba. Ka tuna abin da Bulus ya gaya wa Timotawus: “Ka ɗauko Markus, ka kawo shi tare da kai.” Menene dalilin da ya sa Bulus ya ce hakan? “Gama yana da amfani gare ni wajen hidima.”—2 Tim. 4:11.
Da yake an ambata Markus a tsari na ƙarshe a cikin Nassosi, hakan ya bayyana abubuwa da yawa game da shi. A cikin ayyukansa da yake da ikilisiya, babu inda aka kira Markus cewa shi manzo ne, shugaba, ko annabi. Shi mai hidima ne, wato, wanda yake yi wa mutane hidima. Kuma a wannan lokacin, ba da daɗewa ba kafin mutuwar Bulus, babu shakka manzon ya amfana daga taimakon Markus.
Idan aka tara bayanai dabam-dabam da muke da su game da Markus, za mu ga cewa shi mutum ne mai himma da ke faɗaɗa wa’azin bishara a wurare dabam-dabam a dukan duniya, mutum mai farin cikin yi wa wasu hidima. Hakika, Markus ya more gata masu kyau domin bai yi kasala ba!
Kamar Markus, mu a matsayin bayin Allah a yau muna nuna irin wannan himmar yin wa’azin bisharar Mulki. Kamar Markus, wasu a cikinmu mun ƙaura zuwa wasu wurare, har da ƙasar waje, don mu yaɗa wa’azin bishara a wajen. Ko da yake yawancinmu ba za mu iya yin irin wannan ƙauran ba, dukanmu muna iya yin koyi da Markus a wata hanya mai muhimmanci. Kamar yadda ya ƙoƙarta ya yi hidima ga ’yan’uwansa Kiristoci, mu kasance a shirye mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu taimaka wa ’yan’uwanmu masu bi a hanyoyi masu kyau don su yi hidimarsu ga Allah. Yayin da muke yin hakan, mu kasance da tabbaci cewa za mu ci gaba da samun albarkar Jehobah.—Mis. 3:27; 10:22; Gal. 6:2.
[Hasiya]
a Ba sabon abu ba ne tsararrakin Markus su ɗauki sunan Ibrananci na biyu ko kuwa baƙon suna. Sunan Markus na Yahudanci shi ne Yohanan, wato, Yohanna a Hausa. Sunan babansa na yaren Latin shi ne Marcus ko kuma Markus.—A. M. 12:25.
[Taswira/Hoton da ke shafi na 8, 9]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Wasu Birane da Markus ya Kai Ziyara
Roma
Afisa
Kolosi
Barjata
Antakiya (na Suriya)
Ƙubrus
BAHAR RUMA
Urushalima
Babila