Me Ya Sa Hidimar Gida Gida Take Da Muhimmanci Yanzu?
“Kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fāsa koyaswa da yin wa’azi [game da] Yesu Kristi.”—A. M. 5:42.
1, 2. (a) Wace hanyar wa’azi ce aka san Shaidun Jehobah da ita? (b) Menene za mu tattauna a wannan talifin?
AN SABA ganin haka a kusan kowace ƙasa a duniya. Mutane biyu da suka yi ado da kyau sun isa wani gida da niyyar yi wa mai gidan wa’azi daga cikin Littafi Mai Tsarki game da Mulkin Allah. Idan mutumin ya nuna yana so ya ji wa’azin, masu bisharar za su ba shi littatafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki kuma su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kyauta. Sai su wuce zuwa gida na gaba. Idan kana yin irin wannan aiki, za ka ga cewa mutane da yawa sun fahimci cewa kai ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah ne kafin ma ka yi magana. Hakika, an san Shaidun Jehobah da wa’azi na gida da gida.
2 Muna amfani da hanyoyi dabam dabam don mu cim ma aikin wa’azi da almajirantarwa da Yesu ya ce a yi. (Mat. 28:19, 20) Muna yin wa’azi a kasuwa, a kan titi, da kuma wuraren da ake samun mutane. (A. M. 17:17) Muna yi wa wasu wa’azi ta hanyar tarho da kuma wasiƙa. Muna shelar gaskiyar Littafi Mai Tsarki da waɗanda muke saduwa da su a aikinmu na yau da kullum. Muna da dandalin Duniyar Gizo da ke ba da hanyar samun bayani game da Littafi Mai Tsarki a fiye da harsuna 300.a Duka hanyoyin suna ba da albarka. Duk da haka, a wurare da yawa, ainihin hanyar da muke shelar bishara shi ne ta yin wa’azi na gida gida. Menene tushin wannan hanyar wa’azi? Ta yaya ne mutanen Allah a zamanin nan suke amfani da wannan hanya sosai? Kuma me ya sa yake da muhimmanci yanzu?
Yadda Manzanni Suka Yi Wa’azi
3. Wane umurni ne Yesu ya ba manzanninsa game da wa’azi, kuma menene hakan ya nuna game da yadda ya kamata su yi wa’azi?
3 Yin wa’azi na gida gida yana da tushe a cikin Nassi. Sa’ad da Yesu ya aika manzaninsa su yi wa’azi, ya umurce su: “Kowane birni ko ƙauye inda kuka shiga, a cikinsa ku nemi wanda ya cancanta.” Ta yaya za su nemi waɗanda suka cancanta? Yesu ya ce su je gidajen mutanen: ‘Da shigarku cikin gida kuma, ku gaishe shi. Idan gidan ya cancanta, salamarku ta sauka bisansa.’ Za su jira sai wani ya gayyace su ne kafin su shiga gidansa? Ka lura da abin da Yesu ya sake cewa: “Kuma dukan wanda ba ya karɓe ku ba, ba ya kuwa ji maganarku ba, lokacin da ku ke fita gidan nan ko birnin nan, sai ku karƙaɗe ƙurar ƙafafunku.” (Mat. 10:11-14) Umurnin ya nuna sarai cewa sa’ad da manzannin “suka tashi, suka bibbiya ƙauyuka, suna bishara,” ya kamata su ɗauki mataki su ziyarci mutane a gidajensu.—Luka 9:6.
4. A ina ne aka ambata wa’azi na gida gida a Littafi Mai Tsarki?
4 Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa manzannin sun yi wa’azi gida gida. Alal misali, A. M. 5:42 ya ce game da su: ‘Kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fāsa koyaswa da yin wa’azi [game da] Yesu Kristi.’ A wasu shekaru 20 bayan haka, manzo Bulus ya tuna wa dattawa na ikilisiyar Afisa: ‘Ban ji nauyin bayyana muku kowane abu mai-amfani, gida gida ni ke bin ku, ina koya muku a sarari.’ Bulus ya ziyarci waɗannan dattawa kafin su zama masu bi ne? Hakika, saboda a cikin abubuwan da ya koya musu, ya ce su “tuba zuwa ga Allah, da bangaskiya ga Ubangijinmu Yesu Kristi.” (A. M. 20:20, 21) Littafin nan Robertson’s Word Pictures in the New Testament ya yi magana a kan A. M. 20:20, ya ce: “Yana da kyau a lura cewa waɗannan da suka yi wa’azi sosai sun yi wa’azi gida gida.”
Rundunar Fari a Zamanin Nan
5. Yaya ne aka kwatanta aikin wa’azi a annabcin Joel?
5 Aikin wa’azi da aka yi a ƙarni na farko yana nuni ne ga irin aiki mai girma da za a yi a zamaninmu. Annabi Joel ya kwatanta aikin wa’azin na shafaffun Kiristoci da irin ɓarnar da ƙwari, har da fari suka yi. (Joel 1:4) Kamar rundunar soja, da gabagaɗi farin suka sha kan tangarɗa, suka shiga cikin gidaje, kuma suka cinye dukan abubuwan da suka gani. (Ka karanta Joel 2:2, 7-9.) Wannan ya kwatanta yadda mutanen Allah suke nacewa kuma suke yin wa’azi sosai a zamanin nan. Hanya mafi muhimmanci da shafaffun Kiristoci da abokanansu “waɗansu tumaki” suke amfani da shi a wajen cika wannan annabci shi ne wa’azi na gida gida. (Yoh. 10:16) Yaya ne mu Shaidun Jehobah muka soma bin wannan hanyar wa’azi na manzanni?
6. A shekara ta 1922, wane umurni ne aka ba da na yin wa’azi gida gida, amma yaya wasu suka ɗauki umurnin?
6 Daga shekara ta 1919, an nanata cewa kowane Kirista yana da hakkin yin wa’azi. Alal misali, wani talifi a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Agusta, 1922, mai jigo “Service Essential,” ya tuna wa shafaffun Kiristoci muhimmancin “kai wa mutane littatafai da ke ɗauke da saƙo, su yi musu magana a gidajensu cewa mulkin sama ya kusa.” An kwatanta dalla-dalla yadda za a yi wa’azi a ƙasidar nan Bulletin (yanzu ana ce da ita Our Kingdom Ministry). Duk da haka, da farko waɗanda suke zuwa wa’azi gida gida ba su da yawa. Wasu sun ƙi yi. Sun ba da dalilai dabam dabam, amma ainihin dalilin shi ne wasu suna ganin cewa wa’azi gida gida zai rage musu mutunci. Da aka ci gaba da nanata muhimmancin hidima na fage, yawancin waɗannan mutanen sun daina tarayya da ƙungiyar Jehobah.
7. Wace bukata ce ta kasance da muhimmanci a shekara ta 1950?
7 A ƙarnuka da suka biyo baya, mutane da yawa sun sa hannu a aikin wa’azi. Hakan ya sa aka ga cewa ana bukatar koyarwa a kan aikin wa’azi na gida gida. Alal misali, ka yi la’akari da yanayi da ke ƙasar Amirka. A farkon shekara ta 1950, kashi 28 na Shaidu a wannan ƙasar sun rage aikin wa’azi zuwa rarraba warƙa ko kuma tsaya a tituna da mujallu. Mutane fiye da kashi 40 ba sa fita wa’azi a kai a kai, har watanni su shige ba sa fita wa’azi ko sau ɗaya. Me za a yi don a taimaki dukan Kiristoci da suka keɓe kai su yi wa’azi na gida gida?
8, 9. Wane tsarin koyarwa ne aka soma a shekara ta 1953, kuma da wani sakamako?
8 A wani taro na ƙasashe da aka yi a New York a shekara ta 1953, an mai da hankali a kan hidima na gida gida. Ɗan’uwa Nathan H. Knorr ya sanar cewa ainihin aikin duka dattawa Kiristoci shi ne su taimaki kowane Mashaidi ya zama mai wa’azi na gida gida a kai a kai. Ya ce “ya kamata kowane mutum ya yi shelar bishara na gida gida.” Aka soma wani tsarin koyarwa a kowace ƙasa don a cim ma wannan burin. An koya wa waɗanda ba su soma wa’azi na gida gida ba yadda za su je gidajen mutane, su gaya musu saƙo daga Littafi Mai Tsarki, kuma su amsa tambayoyinsu.
9 Sakamakon wannan koyarwa fitacce ne. Bayan shekaru goma, adadin masu shela a dukan duniya ya ƙaru da kashi 100, adadin waɗanda aka koma a ziyarce su ya ƙaru da kashi 126, kuma adadin nazari na Littafi Mai Tsarki ya ƙaru da kashi 150. A yau, kusan mutane miliyan bakwai masu shelar Mulki suna shelar bishara a dukan duniya. Wannan ƙaruwa na ban mamaki ya nuna cewa Jehobah ya taimaki mutanensa da suke wa’azi na gida gida.—Isha. 60:22.
Zaɓan Mutane Don Ceto
10, 11. (a) Wane wahayi ne Ezekiel ya gani, kamar yadda aka ambata a Ezekiel sura 9? (b) Ta yaya wannan wahayi yake cika a zamaninmu?
10 Za a iya fahimta muhimmancin hidima na gida gida a wahayin da aka nuna wa annabi Ezekiel. A wannan wahayi, Ezekiel ya ga mutane shida da makamai a hannunsu kuma mutum na bakwan yana sanye da tufafi na lilin da ƙaho na ajiyar tadawa a gefensa. An ce mutum na bakwan ya “ratsa ta tsakiyar birni” kuma ya “sa shaida a goshin mutanen da ke ajiyar zuci, suna kuwa kuka saboda dukan ƙazanta da a ke yi a cikinta.” Bisa ga umurnin wannan aiki na sa shaida, an umurci mutane shida da ke ɗauke da makaman kisa su kashe dukan waɗanda ba su da shaida.—Ka karanta Ezekiel 9:1-6.
11 Mun fahimci cewa a cikar wannan annabci, mutumin da ke sanye da ‘tufafi na linin’ yana wakilta shafaffun Kiristoci da suka rage. Ta wajen aikin wa’azi da almajirantarwa, shafaffun suna sa wa waɗanda suka zama “waɗansu tumaki” na Kristi shaida ta alama. (Yoh. 10:16) Mecece shaidar? Tabbaci ne da kamar yana goshinsu, cewa waɗannan tumaki almajiran Yesu Kristi ne da suka keɓe kai, suka yi baftisma kuma sun ɗauki sabon hali irin na Kristi. (Afis. 4:20-24) Waɗannan tumaki sun zama garke ɗaya da shafaffun Kiristoci kuma suna taimakonsu a aikinsu na sa wa mutane shaida.—R. Yoh. 22:17.
12. Ta yaya ne wahayin Ezekiel game da sa shaida a goshi ya nanata muhimmancin aikinmu na neman masu kama da tumaki?
12 Wahayin Ezekiel ya nanata dalili ɗaya da ya sa aikinmu na neman mutane da ke “ajiyar zuci” yake da gaggawa. Ya ƙunshi rayukan mutane. Ba da daɗewa ba, mala’ikun Jehobah na samaniya masu zartar da hukunci, da suke wakilta mutane shida masu makamai, za su halaka waɗanda ba su da wannan shaida ta alama. Game da wannan hukunci, manzo Bulus ya rubuta cewa Ubangiji Yesu tare da “mala’iku na ikonsa,” zai yi “ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tas. 1:7, 8) Wannan ya nuna cewa za a hukunta mutane bisa ga yadda suka karɓi bishara. Hakika, za a ci gaba da shelar saƙon Allah har ƙarshe. (R. Yoh. 14:6, 7) Wannan ya ba dukan bayin Jehobah da suka keɓe kai hakki mai girma.—Ka karanta Ezekiel 3:17-19.
13. (a) Wane hakki ne manzo Bulus ya ɗauka, kuma me ya sa? (b) Wane hakki ne kake da shi game da mutanen yankinku?
13 Manzo Bulus ya san yana da hakkin yin shelar bishara ga wasu. Ya rubuta: “Ni mabarci ne ga Hellenawa duk da Baibayi, ga masu-hikima duk da marasa-hikima. Domin wannan fa, gwargwadon ƙarfina, a shirye ni ke in yi wa’azin bishara a gareku waɗanda ke cikin Roma kuma.” (Rom. 1:14, 15) Don ya nuna godiya ga alherin da aka yi masa, Bulus ya ga cewa dole ne ya yi ƙoƙari ya taimaki wasu don su amfana daga alherin Allah kamar yadda ya amfana. (1 Tim. 1:12-16) Yana gani kamar kowane mutum da ya haɗu da shi yana bin sa bashi, bashin da zai iya biya ta wajen yi wa wannan mutumin shelar bishara. Ka fahimci cewa mutanen da ke yankinku suna bin ka bashi kuwa?—Ka karanta A. M. 20:26, 27.
14. Wane dalili ne mafi muhimmanci ya sa muke wa’azi na fili da kuma na gida gida?
14 Ko da yake ceton ’yan adam yana da muhimmanci, akwai dalilin da ya fi muhimmanci na yin wa’azi gida gida. A cikin annabci da aka ambata a Malachi 1:11, Jehobah ya ce: “Tun daga fitowar rana har faɗuwanta sunana ya ɗaukaka a wurin al’ummai; . . . ana miƙa ma sunana turare, da hadaya mai-tsarki; gama sunana yana da girma a wurin al’ummai.” A cikar wannan annabcin, bayin Jehobah da suka keɓe kai suna yabon sunansa a dukan duniya sa’ad da suke yin hidimarsu da tawa’ilu. (Zab. 109:30; Mat. 24:14) Yin “hadaya ta yabo” ga Jehobah ita ce dalilinmu mafi girma na yin wa’azi na gida gida.—Ibran. 13:15.
Aukuwa Mai Muhimmanci a Nan Gaba
15. (a) Ta yaya Isra’ilawa suka daɗa ayyukansu yayin da suke kewaye Yariko a rana ta bakwai? (b) Menene hakan ya nuna game da aikin wa’azi?
15 Waɗanne abubuwa ne game da aikin wa’azi za su auku a nan gaba? Mun ga misalin hakan a harin da aka kai wa Yariko da ke rubuce a littafin Joshua. Ka tuna cewa kafin Allah ya halaka Yariko, ya ba Isra’ilawa umurni su kewaye birnin sau ɗaya a rana na kwanaki shida. Amma a rana ta bakwai za a ga cewa sun ƙara ayyukansu. Jehobah ya gaya wa Joshua: “Za ku zaga birni so bakwai, priestdin za su yi busa da ƙafonin. Za ya zama kuwa sa’anda suka tsawaita busa da ƙafonin rago, . . . dukan jama’a za su tada murya suna ihu mai-ƙarfi; ganuwar birni kuma za ya abka.” (Josh. 6:2-5) Haka nan ma za a faɗaɗa aikinmu na wa’azi. Babu shakka, a lokacin da za a halaka wannan zamani, za mu ga cewa za a ba da shaida sosai game da sunan Allah da Mulkinsa a tarihi na wannan duniya.
16, 17. (a) Menene za a cim ma kafin ƙarshen “babban tsanani”? (b) Menene za mu tattauna a talifi na gaba?
16 Lokaci zai kai sa’ad da saƙon da muke shelarsa zai zama kamar “ihu mai-ƙarfi.” A littafin Ru’ya ta Yohanna, an kwatanta saƙon hukunci mai ƙarfi da “ƙanƙara kuma manya manya . . . kowane guda nauyinsa ya yi wajen talent ɗaya.”b Kuma Ru’ya ta Yohanna 16:21 ta ce: “Alobar ƙanƙara, gama tsananinta da girma ne ƙwarai.” Har ila, ba mu san hakkin hidima ta gida gida wajen shelar saƙon hukuncin Allah na ƙarshe ba. Amma mun tabbata cewa kafin a ƙare “babban tsananin” za a sanar da sunan Jehobah yadda ba a taɓa yi a tarihin ’yan adam ba.—R. Yoh. 7:14; Ezek. 38:23.
17 Yayin da muke jiran aukuwa mai muhimmanci a nan gaba, bari mu ci gaba da shelar bisharar Mulki da himma. Wajen cika wannan aikin, waɗanne kaluɓale ne muke fuskanta a hidima ta gida gida, kuma ta yaya za mu magance waɗannan matsaloli? Za a tattauna waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Dandalinmu a Duniyar Gizo www.watchtower.org.
b Idan ana yin maganar talanti na Helas, kowace ƙanƙara za ta kai nauyin 45.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Menene tushe na Nassi na wa’azi gida gida?
• Ta yaya aka nanata hidima ta gida gida a zamani?
• Me ya sa bayin Jehobah da suka keɓe kansu suke da hakkin yin wa’azi?
• Wane aukuwa mai muhimmanci muke jira a nan gaba?
[Hoto a shafi na 5]
Dan’uwa Knorr, a shekara ta 1953