Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/15 pp. 21-25
  • Ka Yi Biyayya ga Makiyayan da Jehobah Ya Naɗa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Biyayya ga Makiyayan da Jehobah Ya Naɗa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MAKIYAYI MAI KYAU YA NAƊA WASU DON SU TAIMAKE SHI
  • MAKIYAYI MAI-KYAU YANA CIYAR DA KUMA KĀRE TUMAKIN
  • TA YAYA YA KAMATA MU ƊAUKI KASAWAR DATTAWA?
  • “GARKE ƊAYA, MAKIYAYI ƊAYA”
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Ku Yi Kiwon Garken Allah Wanda Ke Wurinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ku Taimaki Waɗanda Suka Bar Garken
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/15 pp. 21-25

Ka Yi Biyayya Ga Makiyayan Da Jehobah Ya Naɗa

“Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku.”—IBRAN. 13:17.

YAYA ZA KA AMSA?

  • Ta yaya dattawan ikilisiya suke kula da garken Allah?

  • Me ya sa ya kamata mu yi biyayya ga dattawan ikilisiya?

  • Me ya sa ba zai dace mu riƙa yi wa dattawa gunaguni ko mu ƙi bin ja-gorarsu don ajizancinsu ko kuma kasawarsu ba?

1, 2. Me ya sa Jehobah ya misalta kansa da makiyayi?

JEHOBAH ya misalta kansa da makiyayi. (Ezek. 34:11-14) Hakan yana da muhimmanci don ya taimaka mana mu san yadda Jehobah yake. Makiyayi mai ƙauna yana da hakkin kula da rayukan tumakin da aka danƙa masa. Yana kai su kiwo inda akwai ciyayi da kuma ruwa (Zab. 23:1, 2), yana tsaronsu dare da rana (Luk 2:8), yana kāre su daga mugayen dabbobi (1 Sam. 17:34, 35), yana kula da ’ya’yan da tumakin suka haifa (Isha. 40:11), yana kuma neman waɗanda suka ɓace kuma ya kula da waɗanda suka ji rauni.—Ezek. 34:16.

2 Da yake yawancin mutanen Allah a zamanin dā makiyaya ne da kuma manoma, sun fahimci abin da ya sa Jehobah ya misalta kansa da makiyayi. Sun san cewa tumaki suna bukatar kula don su rayu kuma su kasance da ƙoshin lafiya. Hakazalika, abin da mutane ma suke bukata ke nan. (Mar. 6:34) Mutane za su sha wuya idan Jehobah bai kula da kuma ja-gorance su ba. Ba za su san abu mai kyau da marar kyau ba, kuma ba wanda zai kāre su. Za su zama kamar “tumakin da ba su da makiyayi.” (1 Sar. 22:17) Amma, Jehobah yana tanadar wa mutanensa bukatunsu.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A yau ma mun fahimci yadda Jehobah ya misalta kansa da makiyayi. Muna ganin yadda yake kula da mutanensa sosai a yau. Bari mu ga yadda yake yi mana ja-gora da kuma biyan bukatunmu. Za mu kuma tattauna abin da ya wajaba mu yi don mu amfana daga ja-gora da kuma kula da muke samu daga Jehobah.

MAKIYAYI MAI KYAU YA NAƊA WASU DON SU TAIMAKE SHI

4. Ta yaya Yesu yake kula da tumakin Jehobah?

4 Jehobah ya naɗa Yesu a matsayin Shugaban ikilisiyar Kirista. (Afis. 1:22, 23) Yesu wanda shi ne “makiyayi mai-kyau,” yana koyi da Ubansa ta wajen kula da kuma ƙaunar tumakinsa. Har ya ‘ba da ransa domin tumakin.’ (Yoh. 10:11, 15) Babu shakka, fansar hadayar Kristi albarkar ce ga ’yan Adam! (Mat. 20:28) Nufin Jehobah shi ne duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu, “kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”—Yoh. 3:16.

5, 6. (a) Su wane ne Yesu ya zaɓa don su kula da tumakinsa, kuma me ya wajaba tumakin su yi don su amfana daga wannan tanadin? (b) Wane dalili ne musamman ya sa za mu bi ja-gorar dattawa?

5 Ta yaya tumakin suka nuna cewa Yesu ne makiyayinsu? Yesu ya ce: “Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma.” (Yoh. 10:27) Tumakin suna jin muryar Makiyayi Mai-kyau ta wurin bin ja-gorarsa. Hakan ya ƙunshi yin biyayya ga waɗanda ya naɗa don su taimaka masa. Yesu ya nuna cewa manzanninsa da kuma almajiransa za su ci gaba da yin aikin da ya soma. Za su ‘koyar’ da kuma ‘yi kiwon ’ya’yan tumakin Yesu.’ (Mat. 28:20; karanta Yohanna 21:15-17.) Yayin da ake yaɗa bishara kuma almajirai suna ƙaruwa, Yesu ya sanya Kiristoci makiyaya da za su riƙa kula da ikilisiyoyi.—Afis. 4:11, 12.

6 Daga baya, Bulus ya gaya wa dattawan da ke ikilisiyar Afisawa cewa: “Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki, garin ku yi kiwon ikilisiyar Allah.” (A. M. 20:28) Haka ma yake a yau, ana naɗa dattawa da taimakon ruhu mai tsarki ne. Me ya sa muka ce hakan? Domin an naɗa su ne bisa ga ja-gorar da ke cikin hurarriyar Kalmar Allah. Saboda haka, idan muka yi biyayya ga dattawa, muna girmama Jehobah da kuma Yesu, waɗanda su ne Makiyayanmu mafi girma. (Luk 10:16) Hakika, wannan ne asalin dalilin da ya sa ya kamata mu yi biyayya ga dattawa. Amma, akwai wasu dalilai suka sa ya kamata mu bi ja-gorancin dattawa.

7. Ta yaya dattawa suke taimaka maka ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah?

7 Dattawa suna ƙarfafa ’yan’uwa ta wajen yin amfani da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Dattawa ba sa gaya wa ’yan’uwa yadda ya kamata su yi rayuwarsu. (2 Kor. 1:24) Maimakon haka, suna so su taimaka musu su iya tsai da shawara da kansu bisa mizanan Littafi Mai Tsarki. Ta hakan, dattawa suna sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai da kuma zaman lafiya. (1 Kor. 14:33, 40) Dattawa ‘suna yin tsaro sabili da rayuka,’ wato suna taimaka wa kowa a cikin ikilisiya ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Saboda haka, da gaggawa suke taimaka wa ’yar’uwa ko kuma ɗan’uwa da ke so ya ɗauki matakin da bai dace ba, ko wanda ya riga ya yi hakan. (Gal. 6:1, 2; Yahu. 22) Hakika, waɗannan dalilai ne masu kyau na yin ‘biyayya da waɗanda ke shugabanninmu.’—Karanta Ibraniyawa 13:17.

8. Ta yaya dattawa suke kāre ikilisiya?

8 Manzo Bulus dattijo ne mai kula sosai, kuma ya gargaɗi ’yan’uwan da ke Kolosi cewa: “Ku yi hankali kada kowa ya cuceku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga ta’adar mutane, bisa ga rukunai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.” (Kol. 2:8) Wannan gargaɗin ya taimaka mana mu san wani dalili kuma da ya sa ya kamata mu bi ja-gorar da dattawa suke yi mana. Suna kāre ’yan’uwa daga waɗanda suke so su nisanta su da Jehobah. Manzo Bitrus ya yi gargaɗi cewa “annabawan ƙarya” da kuma “malaman ƙarya” za su ƙoƙarta su yaudari “marasa kintsuwa” don su yi abin da bai dace ba. (2 Bit. 2:1, 14, Littafi Mai Tsarki) Hakazalika, a yau dattawa suna bukata su ba da irin wannan gargaɗin idan bukata ta taso. Dattawa Kiristoci ne masu hikima da kuma ƙwarewa. An naɗa su a matsayin dattawa domin sun nuna cewa sun fahimci Littafi Mai Tsarki sosai kuma sun ƙware wajen koyar da gaskiyar da ke cikinsa. (1 Tim. 3:2; Tit. 1:9) Ƙwarewa da sanin ya kamata da kuma hikima da suke nunawa sun taimake su su yi ja-gorar garken da kyau.

MAKIYAYI MAI-KYAU YANA CIYAR DA KUMA KĀRE TUMAKIN

9. Ta yaya Yesu yake ja-gorar da kuma kiwon ikilisiya a yau?

9 Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa wajen koyar da kuma ja-gorar Kiristoci shafaffu har da sauran ’yan’uwa a duniya baƙi ɗaya. Muna samun shawarar Nassi daga littattafanmu. A wasu lokatai, ƙungiyar tana ja-gorarmu ta wasiƙun da ake aika wa dattawan ikilisiya da kuma ta umurnin da masu kula masu ziyara suke bayarwa. Ta waɗannan hanyoyin ne ake ja-gorar tumakin.

10. Wane hakki ne dattawa suke da shi game da waɗanda suka daina halartar taro?

10 Makiyaya na zahiri suna da hakkin kāre da kuma kula da tumakinsu. Dattawa ma suna mai da hankali sosai ga waɗanda suke yin sanyin gwiwa ko kuma waɗanda suka yi kurakure masu tsanani. (Karanta Yaƙub 5:14, 15.) Wataƙila wasu ma sun daina halartar taro kuma sun daina bauta wa Jehobah. A wannan yanayin, mene ne dattijo ya kamata ya yi? Zai ƙoƙarta ya neme su kuma ya ƙarfafa su don su soma halartar taro kuma. Yesu ya ce: ‘Ba nufin Ubanna wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.’—Mat. 18:12-14.

TA YAYA YA KAMATA MU ƊAUKI KASAWAR DATTAWA?

11. Me ya sa wasu suke jinkirin bin ja-gorar dattawa?

11 Jehobah da kuma Yesu kamiltattun Makiyaya ne. Amma, waɗanda aka danƙa wa hakkin kula da ikilisiya, wato dattawa, ajizai ne. Hakan yana sa wasu su yi jinkirin bin ja-gorar dattawa. Za su iya yin tunani cewa: ‘Dattawa ajizai ne kamar mu, me ya sa za mu bi ja-gorarsu?’ Hakika, dattawa ajizai ne, amma ba zai dace mu mai da hankali ga ajizancinsu da kuma kurakurensu ba.

12, 13. (a) Wane irin kurakurai ne wasu bayin Allah da ke da hakki suka yi a dā? (b) Me ya sa Jehobah ya sa aka rubuta kurakuren mazaje masu hakki a cikin Littafi Mai Tsarki?

12 Nassosi sun bayyana cewa wasu da Jehobah ya yi amfani da su don ya ja-goranci mutanensa a dā sun yi kurakurai. Alal misali, an naɗa Dauda a matsayin sarki da kuma shugaban Isra’ilawa. Amma ya kwana da matar da ba nasa ba kuma ya kashe mijinta. (2 Sam. 12:7-9) Bitrus ma wanda aka danƙa wa gata mai girma a ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko, ya yi kurakurai masu tsanani. (Mat. 16:18, 19; Yoh. 13:38; 18:27; Gal. 2:11-14) Ban da Yesu, ba a taɓa yin ɗan Adam kamiltacce ba bayan su Adamu da Hawwa’u.

13 Jehobah ya ƙyale a rubuta kurakuren wasu bayinsa da ya danƙa wa hakki a zamanin dā cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Wani dalili shi ne, yana so ya nuna cewa zai iya yin amfani da mazaje ajizai don ya ja-goranci mutanensa. Babu shakka ya yi hakan sau da sau. Saboda haka, kada mu riƙa yi wa dattawa gunaguni ko mu ƙi bin ja-gorarsu don ajizancinsu ko kuma kasawarsu. Jehobah yana so mu girmama su kuma mu yi musu biyayya.—Karanta Fitowa 16:2, 8.

14, 15. Mene ne za mu iya koya daga yadda Jehobah ya umurci mutanensa a dā?

14 Yana da muhimmanci sosai mu yi biyayya ga dattawa. Ka yi tunanin yadda Jehobah yake ba mutanensa umurni don su jimre a mawuyacin yanayi a dā. Alal misali, sa’ad da Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar, Allah ya yi amfani da Musa da kuma Haruna don ya umurce su. Don kada annoba ta goma ta shafe su, Isra’ilawa suna bukatar su bi umurnin da aka ba su cewa, su ci abinci na musamman, su yanka tunkiya kuma su shafa jinin a saman ƙofarsu. Shin Jehobah ya yi musu magana ne daga sama? A’a, suna bukata ne su saurari mazaje Isra’ilawa tsofaffi waɗanda suka sami umurnin daga wurin Musa. (Fit. 12:1-7, 21-23, 29) A waɗannan yanayin, Jehobah ya yi amfani da Musa da kuma mazaje tsofaffi don ya ja-goranci mutanensa. A yau ma, Jehobah yana amfani da dattawa don yin hakan.

15 Wataƙila za ka iya tuna wasu yanayi a Littafi Mai Tsarki da Jehobah ya yi amfani da ’yan Adam ko kuma mala’iku wajen ja-gorar mutanensa. A yanayi da yawa, waɗannan ja-gorar sun ceci rayuka. A irin waɗannan yanayin, Jehobah yana ba wasu iko don su yi magana a madadinsa kuma su gaya wa mutanensa abin da suke bukata su yi a mawuyacin yanayi. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai yi hakan ga mutanensa a Armageddon. Kowane dattijon da yake da gatan wakiltar Jehobah ko kuma ƙungiyarsa a yau, yana bukata ya mai da hankali don kada ya yi amfani da ikon da aka ba shi a hanyar da ba ta dace ba.

“GARKE ƊAYA, MAKIYAYI ƊAYA”

16. Wace “magana” ce muke bukata mu saurara?

16 Mutanen Jehobah “garke ɗaya” ne, kuma suna ƙarƙashin “makiyayi ɗaya,” wato Yesu. (Yoh. 10:16) Yesu ya ce zai kasance da almajiransa “kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:20) A matsayin Sarki a sama, yana da iko ya sa waɗannan abubuwan su auku kafin ya zo ya halaka duniyar Shaiɗan. Don mu kasance da haɗin kai kuma mu more kāriya a matsayin garken Allah, muna bukatar mu saurari ‘magana daga bayanmu’ da ke gaya mana hanyar da za mu bi. Wannan ‘maganar’ ta ƙunshi abin da Jehobah yake koya mana ta Littafi Mai Tsarki da kuma abin da shi da Yesu suka ce ta makiyayan da suka naɗa.—Karanta Ishaya 30:21; Ru’ya ta Yohanna 3:22.

17, 18. (a) Wace barazana ce ake yi wa mutanen Allah, amma wane tabbaci ne muke da shi? (b) Mene ne za mu koya a talifi na gaba?

17 Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan yana “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8) Kamar mugun naman daji mai jin yunwa, Shaiɗan yana fakon garken, yana jiran lokacin da zai kai hari ga wanda ke sanyin gwiwa ko kuma wanda ya bar garken. Saboda wannan barazanar, yana da kyau mu riƙa kasancewa kusa da ikilisiya da kuma ‘Makiyayi da Mai-tsaron rayukanmu.’ (1 Bit. 2:25) Game da waɗanda za su tsira daga ƙunci mai girma, Ru’ya ta Yohanna 7:17 ta ce: “Ɗan rago [Yesu] . . . za ya zama makiyayinsu, za ya bishe su kuma wurin maɓulɓulan ruwaye na rai: Allah kuma za ya share dukan hawaye daga idanunsu.” Babu shakka, wannan alkawari mai ban sha’awa ne!

18 Hakkin da aka danƙa wa dattawa na kula da ikilisiya yana da muhimmanci sosai. Ta yaya waɗannan mazajen da aka naɗa za su tabbata cewa suna kula da garken Yesu yadda ya kamata? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba