“Za Ku Zama Shaiduna”
“[Yesu] ya ce masu, . . . Za ku zama shaiduna . . . har kuma iyakan duniya.”—A. M. 1:7, 8.
1, 2. (a) Wane ne “amintaccen mashaidi mai-gaskiya”? (b) Mene ne ma’anar sunan nan Yesu, kuma mene ne ya yi don ya taimaka wa Yahudawa su komo ga Jehobah?
SA’AD DA ake yi wa Yesu shari’a, ya gaya wa Bilatus Babunti wanda shi ne gwamnan Yahuda cewa: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in ba da shaida ga gaskiya.” (Karanta Yohanna 18:33-37.) Shekaru da yawa bayan haka, manzo Bulus ya kira Yesu Mashaidi “wanda ya shaida kyakkyawan furci a gaban Bunti Bilatus.” (1 Tim. 6:13) Muna rayuwa a duniyar da ke cike da ƙiyayya kuma Shaiɗan ne yake mulki. Idan muna so mu ci gaba da ba da shaida, dole mu kasance da gaba gaɗi sosai kamar Yesu wanda shi ne “amintaccen mashaidi mai-gaskiya.”—R. Yoh. 3:14.
2 Dukan Yahudawa shaidun Jehobah ne, amma Yesu ne mafi girma cikinsu. (Isha. 43:10) Kafin a haifi Yesu, wani mala’ika ya gaya wa Yusufu wanda ya yi rainonsa game da Maryamu cewa: “Za ta haifi ɗa; kuma za ka kira sunansa Yesu; gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” (Mat. 1:20, 21) A Ibrananci, Yesu yana nufin “Jehobah Mai-ceto Ne.” Jehobah zai yi amfani da Yesu don ya ceci mutane daga zunubi da mutuwa. Yesu ya gaya wa Yahudawa cewa suna bukata su tuba daga zunubansu domin Jehobah ya sake amincewa da su. (Mat. 10:6; 15:24; Luk 19:10) Ya yi wa’azi game da Mulkin Allah. Littafin Markus ya ce: “Yesu ya taho cikin Galili, yana wa’azin bishara ta Allah, ya ce, Zamani ya cika, gashi lokacin bayyanan mulkin Allah ya zo: ku tuba ku ba da gaskiya ga bisharar nan.” (Mar. 1:14, 15) Yesu ya kasance da ƙwazo da kuma gaba gaɗi sa’ad da yake wa’azi. Ya ma tsauta wa limaman Yahudawa, kuma hakan yana cikin dalilan da suka sa aka kashe shi.—Mar. 11:17, 18; 15:1-15.
“AYYUKA MASU GIRMA NA ALLAH”
3. Mene ne ya faru kwanaki uku bayan Yesu ya mutu?
3 Kwanaki uku bayan da aka kashe Yesu, wani abu mai ban mamaki ya faru. Jehobah ya ta da Yesu daga mutuwa. Shin an ta da Yesu ne da jikin mutum? A’a. An ta da shi cikin ruhu. (1 Bit. 3:18) Sa’ad da Yesu ya bayyana ga almajiransa da jikin mutum, ya nuna musu cewa an ta da shi daga mutuwa. Washegari bayan an ta da shi, ya bayyana ga almajiransa dabam-dabam wajen sau biyar.—Mat. 28:8-10; Luk 24:13-16, 30-36; Yoh. 20:11-18.
4. Mene ne ya faru sa’ad da Yesu ya bayyana ga almajiransa, kuma wane umurni ya ba su?
4 Yesu ya bayyana a ƙaro na biyar domin almajiransa da kuma wasu da suka taru wuri ɗaya su gan shi. Sa’an nan, ya taimaka musu su fahimci cewa an annabta mutuwarsa da kuma tashinsa a cikin Nassosi. A ƙarshen wannan muhimmiyar taron, Yesu ya gaya wa almajiransa abin da suke bukatar su yi. Ya ce “za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai cikin sunansa ga dukan al’ummai, ana farawa daga Urushalima.” Sai Yesu ya umurce su: ‘Ku shaidu ne ga waɗannan abubuwa.’—Luk 24:44-48.
5, 6. (a) Almajiran Yesu za su zama shaidun waye? (b) Mene ne almajiran Yesu za su ba da shaida a kai?
5 Saboda haka, shekaru 40 bayan haka, sa’ad da Yesu ya bayyana wa almajiransa a karo na ƙarshe, babu shakka, sun fahimci umurnin da ya bayar. Ya ce: “Za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Almajiran Isra’ilawa ne kuma su Shaidun Jehobah ne. Amma yanzu, za su zama shaidun Yesu. Mene ne Yesu yake nufi?
6 Za su fara sanar da mutane cewa Jehobah ya soma yin amfani da Yesu don ya ceci ’yan Adam. Yadda Jehobah zai cece su a wannan lokacin ya fi yadda ya ceci Isra’ilawa a zamanin dā. Mutuwar Yesu da tashiwarsa ya ceci mutane daga zunubi da kuma mutuwa. Sa’ad da aka shafe almajiran Yesu da ruhu mai tsarki a ranar Fentakos na shekara ta 33, sun soma shaida “ayyuka masu-girma na Allah.” Mutane da yawa da suka ji wannan saƙon sun tuba kuma sun yi imani ga hadayar Yesu. An ƙara wa Yesu mukami a cikin sama, kuma Jehobah ya soma amfani da shi don ya ceci dubban mutane a duniya.—A. M. 2:5, 11, 37-41.
“ABIN FANSAR MUTANE DA YAWA”
7. Mene ne abin da ya faru a ranar Fentakos na shekara ta 33 ya nuna?
7 Abin da ya faru a ranar Fentakos na shekara ta 33 ya nuna cewa Jehobah ya amince da hadayar da Yesu ya yi don ya fanshe mutane daga zunubi. (Ibran. 9:11, 12, 24) Yesu ya bayyana cewa ya zo domin ya “ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Shin Yahudawa ne kawai za su amfana daga wannan fansar? A’a. Fansar ta ‘ɗauke zunubin duniya!’—1 Tim. 2:4-6; Yoh. 1:29, Littafi Mai Tsarki.
8. Mene ne ya taimaka wa almajiran Yesu su ci gaba da ba da shaida game da shi, kuma me suka cim ma?
8 Almajiran Yesu na dā sun ci gaba da ba da shaida game da shi da gaba gaɗi. Amma wane ne ya ba su ikon yin hakan? Ba su yi hakan da ikonsu ba, amma ruhu mai tsarki na Jehobah ne ya ƙarfafa su su ci gaba da ba da shaida. (Karanta Ayyukan Manzanni 5:30-32.) Bayan almajiran Yesu sun yi wa’azi kusan shekara 27, sun yi “jawabin gaskiya ta bishara” ga Yahudawa da ’Yan Al’ummai “da ke ƙarƙashin sama.”—Kol. 1:5, 23.
9. Kamar yadda aka annabta, mene ne ya faru a ikilisiyar Kirista?
9 Abin baƙin ciki, wasu cikin ikilisiyar sun soma koyar da ƙarya da shigewar lokaci. (A. M. 20:29, 30; 2 Bit. 2:2, 3; Yahu. 3, 4) Da sannu-sannu, waɗannan limaman ƙarya sun gurɓata ikilisiyar baƙi ɗaya. Yesu ya annabta cewa waɗannan ’yan ridda za su bunƙasa har “matuƙar zamani.” (Mat. 13:37-43) Jehobah ya naɗa Yesu a matsayin sarki bisa ’yan Adam a shekara ta 1914. A lokacin ne aka shiga “kwanaki na ƙarshe” na duniyar Shaiɗan.—2 Tim. 3:1.
10. (a) Kiristoci shafaffu sun yi wa’azi game da wane kwanan wata? (b) Mene ne ya faru a watan Oktoba na 1914, kuma yaya muka sani?
10 Fiye da shekara 30 kafin watan Oktoba na 1914, Kiristoci shafaffu sun soma yin wa’azi suna sanar da mutane cewa Mulki Allah zai soma sarauta a wannan kwanan watan. Annabcin Daniyel game da wani babban itace da aka sare kuma zai sake girma ne ya taimaka musu su sami wannan fahimtar. (Dan. 4:16) Yesu ya bayyana wata alamar da za ta taimaka wa almajiransa su san cewa ya soma sarauta kuma an shiga kwanaki na ƙarshe. Abubuwan da suke faruwa tun shekara ta 1914 sun bayyana sarai cewa an naɗa Yesu Sarki. (Mat. 24:3, 7, 14; Luk 21:24) A yau, “ayyuka masu girma na Allah” da muke wa’azinsu sun haɗa da gaskiyar nan cewa Jehobah ya naɗa Yesu Sarkin Mulkinsa.
11, 12. (a) Mene ne ya faru a shekara ta 1919? (b) Mene ne ya kasance a bayyane a shekara ta 1935? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)
11 Sa’ad da Yesu ya zama Sarki a shekara ta 1914, ya soma ’yantar da mabiyansa shafaffu daga “Babila babba,” wato addinin ƙarya. (R. Yoh. 18:2, 4) A shekara ta 1919, sa’ad da ake dab da kammala Yaƙin Duniya na Ɗaya, shafaffu sun sami ’yancin yin wa’azi a duniya sosai. Sun ba da shaida game da hadayar fansar Yesu kuma sun yi bishara game da Mulkin Allah. A sakamakon haka, dubban mutane sun koyi gaskiya kuma an shafe su su yi sarauta tare da Kristi a sama.
12 A shekara ta 1935, ya kasance a bayyane cewa Kristi ya soma tattara “waɗansu tumaki.” A yau, akwai miliyoyin waɗansu tumaki daga dukan ɓangarori na duniya. Shafaffu da waɗansu tumaki suna bin misalin Yesu ta wajen ba da shaida da gaba gaɗi. Waɗansu tumaki ma sun yi imani cewa hadayar fansar Yesu ce kawai hanyar samun ceto. Sun san cewa idan sun ci gaba da ba da shaida kuma sun faranta wa Jehobah rai, za su iya tsira daga “babban tsananin” kuma su yi rayuwa cikin sabuwar duniya.—Yoh. 10:16; R. Yoh. 7:9, 10, 14.
KA “YI ƘARFIN HALI” DON SANAR DA BISHARA
13. Mene ne muka ƙuduri niyyar yi a matsayin Shaidun Jehobah, kuma me ya sa muka tabbata cewa za mu yi nasara?
13 Shaida wa mutane game da “ayyuka masu girma” da Jehobah ya yi da kuma waɗanda zai yi a nan gaba babban gata ne. Ko da yake ci gaba da yin hakan ba shi da sauƙi. Me ya sa? Domin mutane za su iya ƙin saƙonmu ko kuma su tsananta mana. Idan hakan ya faru da mu, za mu iya yin koyi da manzo Bulus da kuma abokan aikinsa. Bulus ya ce: “Muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin husuma mai-yawa.” (1 Tas. 2:2) Wajibi ne mu cika wa’adin da muka yi sa’ad da muka yi wa Jehobah alkawari cewa za mu bauta masa. Muna so mu ci gaba da zama Shaidun Jehobah yayin da wannan muguwar duniyar Shaiɗan take ƙara taɓarɓarewa har sai ta halaka. (Isha. 6:11) Ba za mu iya cim ma wannan da ƙarfinmu ba. Amma za mu iya yin koyi da Kiristoci na ƙarni na farko, kuma mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki domin mu kasance da “mafificin girman iko.”—Karanta 2 Korintiyawa 4:1, 7; Luk 11:13.
14, 15. (a) Yaya aka bi da Kiristoci a ƙarni na farko, kuma ta yaya Bitrus ya ƙarfafa su? (b) Mene ne ya kamata mu tuna idan ana tsananta mana domin mu Shaidun Jehobah ne?
14 A yau, miliyoyin mutane suna da’awar cewa su Kiristoci ne, “amma suna saɓa masa [Allah] ta ayyukansu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani wajen yin aiki nagari.” (Tit. 1:16, LMT) A ƙarni na farko, yawancin mutane ba su bauta wa Allah a hanyar da ta dace ba. Mutane da yawa sun tsani Kiristoci na gaske a lokacin. Shi ya sa manzo Bitrus ya rubuta kalmomi na gaba domin ya ƙarfafa su. Ya ce: “Idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku; domin Ruhu na daraja da Ruhu na Allah yana zaune a kanku.”—1 Bit. 4:14.
15 Shin Shaidun Jehobah suna “shan zargi sabili da sunan Kristi” kuwa a yau? Ƙwarai kuwa. Me ya sa? Domin ba sa ba da shaida game da Jehobah kaɗai, amma suna gaya wa mutane game da Yesu kuma suna yin wa’azi cewa shi Sarkin Mulkin Allah ne. An tsananta wa Yesu domin shi ma mashaidin Jehobah ne. Yesu ya gaya wa maƙiyansa: “Ni na zo cikin sunan Ubana, ba ku karɓe ni ba.” (Yoh. 5:43) Saboda haka, idan wani ya sake tsananta maka domin kai Mashaidi ne, ka tuna cewa Allah ya amince da kai kuma ruhu mai tsarki nasa yana tare da kai.
16, 17. (a) Ta yaya Shaidun Jehobah a faɗin duniya suke ji game da yin wa’azi? (b) Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?
16 Ka kuma tuna cewa mutane da yawa a faɗin duniya suna koyon gaskiya kuma suna soma bauta wa Jehobah. Ko ma a yankunan da ake yawan wa’azi a ciki, akwai mutanen da suke a shirye su saurari saƙonmu. Saboda haka, duk sa’ad da muka tarar da mutanen da suke son saƙonmu, ya kamata mu tabbata cewa mun koma ziyara wurinsu kuma mun yi ƙoƙari don mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Idan muka yi haka, za mu iya taimaka musu su san Jehobah domin su soma bauta wa Jehobah kuma su yi baftisma. Yaya muke ji sa’ad da muka yi wannan aikin? Wata mata mai suna Sarie a Afirka ta Kudu wadda ta kwashi sama da shekara 60 tana bauta wa Jehobah ta ce: “Ina matuƙar farin ciki domin hadayar fansar Yesu ta sa na sami zarafin more dangantaka mai kyau da Jehobah, Maɗaukakin Sarki kuma ina farin ciki cewa ina iya yin shelar sunansa mai girma.” Ita da mijinta, Martinus sun taimaka wa yaransu guda uku da kuma mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah. Ya daɗa cewa: “Babu wani aiki da ke sa mutum wadar zuci kamar wannan. Kuma Jehobah yana yin amfani da ruhunsa don ya ƙarfafa mu mu ci gaba da wannan aikin da ke sa mutane su sami ceto.”
17 Ko da mun yi baftisma ko a’a, ya kamata mu yi farin ciki domin muna tarayya da ikilisiyar Shaidun Jehobah a faɗin duniya. Saboda haka, bari mu ci gaba da ba da shaida sosai tare da sauran bayin Jehobah a faɗin duniya, kuma mu tsarkake kanmu daga duniyar Shaiɗan. Idan muka yi haka, za mu ɗaukaka Ubanmu da ke sama, Jehobah, wanda muke shaidarsa.