Yadda Fansa Ta Cece mu
“Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda bai bada gaskiya ga Ɗan ba, ba zai gan rai ba, amma fushin Allah yana bisansa zaune.”—YOH. 3:36.
1, 2. Wane dalili ɗaya ne ainihi ya sa aka wallafa Zion’s Watch Tower?
“IDAN mutum ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, zai ga muhimmancin mutuwar Kristi,” in ji fitowa na huɗu na wannan mujallar a watan Oktoba na shekara ta 1879. Wannan talifin ya kammala da wannan kalami mai muhimmanci: “Dole ne mu ƙi duk wani abin da ke nuna cewa mutuwar Kristi ba hadaya ba ce da kuma fansar zunubi.”—Karanta 1 Yohanna 2:1, 2.
2 Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka wallafa Zion’s Watch Tower a watan Yuli na shekara ta 1879 shi ne don a kāre koyarwar Littafi Mai Tsarki game da fansa. Abin da aka rubuta a cikinsa ya yi tanadin ‘abinci a lotonsa,’ domin a tsakanin shekara ta 1800 da 1899, mutane da yawa da suke da’awar cewa su Kiristoci ne sun soma shakka yadda mutuwar Yesu za ta iya zama fansa ga zunubanmu. (Mat. 24:45) A wannan lokacin, mutane da yawa suka soma gaskata da koyarwar ra’ayin bayyanau, ra’ayin da ya saɓa wa gaskiya cewa ’yan Adam sun yi hasarar kamiltaccen yanayi. Masu koyar da ra’ayin bayyanau sun ce ’yan Adam suna samun ci gaba da kansu kuma ba sa bukatar fansa. Hakan ya sa shawarar manzo Bulus ga Timotawus ta dace: “Ka tsare abin da aka danƙa maka, kana kauce wa maganganu na saɓo da kuma surutai na banza irin ilimin da ake fadinsu haka nan kawai a ƙaryace; waɗansu da sun mallaki halin nan sun yi kuskure sun kuma yaudaru daga hanyan imani.”—1 Tim. 6:20, 21.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yanzu?
3 Babu shakka, ka ƙudurta cewa ba za ka kauce ‘daga hanyan imani ba.’ Saboda haka, zai dace mu tattauna waɗannan tambayoyin: Me ya sa nake bukatar fansa? Wace sadaukarwa ce aka yi? Yaya zan amfana daga wannan tanadi mai tamani da zai cece ni daga fushin Allah?
Ceto Daga Fushin Allah
4, 5. Menene ya nuna cewa fushin Allah ya kasance kan wannan mugun zamani?
4 Littafi Mai Tsarki da kuma tarihin ’yan Adam sun nuna cewa tun lokacin da Adamu ya yi zunubi, fushin Allah ‘ya kasance bisa’ ’yan Adam. (Yoh. 3:36) Hakan gaskiya ne domin mutane suna mutuwa. Sarautar Shaiɗan ta kasa kāre ’yan Adam daga waɗannan masifun, kuma babu gwamnatin ɗan Adam da ta cika bukatun dukan talakawanta. (1 Yoh. 5:19) Saboda haka, yaƙi, aikata laifi, da talauci sun ci gaba da addabar ’yan Adam.
5 A bayyane yake cewa albarkar Jehobah ba ta kan wannan mugun zamani. Bulus ya ce “fushin Allah ya bayyana daga sama bisa dukan rashin ibada.” (Rom. 1:18-20) Saboda haka, waɗanda suka ci gaba da yin rayuwa da ke ɓata wa Allah rai ba za su tsira ba daga sakamakon halinsu ba. A yau, ana sanar da fushin Allah a saƙon hukunci da ake zubowa kamar annoba a kan duniyar Shaiɗan, kuma irin waɗannan bayanan suna bayyana a cikin littattafanmu da yawa da ke bisa Littafi Mai Tsarki.—R. Yoh. 16:1.
6, 7. Wane aiki ne shafaffu Kiristoci suke ja-gora, kuma wane zarafi ne har ila waɗanda suke sashe na duniyar Shaiɗan suke da shi?
6 Hakan yana nufin cewa lokaci ya ƙure ne ainun ga mutane su samu ’yanci daga ja-gorar Shaiɗan kuma su sulhunta da Allah? A’a, har ila ƙofa a buɗe take don sulhuntawa da Jehobah. Shafaffun Kiristoci, da suke “madadin Kristi,” su ne ke ja-gora a aikin wa’azi inda ake gayyatar mutane na dukan al’ummai: Su “sulhuntu ga Allah.”—2 Kor. 5:20, 21.
7 Manzo Bulus ya ce Yesu ya “tsamar da mu daga fushi mai-zuwa.” (1 Tas. 1:10) Wannan fushin Jehobah na ƙarshe zai kawo madawwamiyar halaka ga masu zunubi da suka ƙi tuba. (2 Tas. 1:6-9) Su waye ne za su tsira? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda bai bada gaskiya ga Ɗan ba, ba zai gan rai ba, amma fushin Allah yana bisansa zaune.” (Yoh. 3:36) Hakika, ba za a halaka dukan waɗanda suke da rai kuma suka ba da gaskiya ga Yesu da kuma fansa ba, sa’ad da wannan zamanin zai zo ƙarshensa a rana ta ƙarshe na fushin Allah.
Yadda Fansa Yake Aiki
8. (a) Wane bege ne mai girma Adamu da Hauwa’u suke da shi? (b) Yaya Jehobah ya zama Allah mai cikakken adalci?
8 An halicci Adamu da Hauwa’u kamiltattu. Da a ce sun ci gaba da yin biyayya ga Allah, da duniya ta cika da ’ya’yansu masu farin ciki da suke zama tare da su a cikin Aljanna. Abin baƙin ciki, iyayenmu na farko sun yi rashin biyayya ga umurnin Allah da gangan. A sakamakon haka, an yi musu hukuncin mutuwa na dindindin kuma aka kore su daga Aljanna na asali. A lokacin da Adamu da Hauwa’u suka haifi yara, zunubi ya riga ya shafi ’yan Adam, kuma mace da namiji na farko suka tsufa kuma suka mutu. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana yin abin da ya faɗa. Bugu da ƙari, shi Allah ne na cikakken adalci. Jehobah ya riga ya gargaɗi Adamu cewa cin haramtaccen ’ya’yan itace zai jawo musu mutuwa, kuma hakan ya faru.
9, 10. (a) Me ya sa zuriyar Adamu suke mutuwa? (b) Ta yaya za mu tsira daga mutuwa na dindindin?
9 A matsayin ’ya’yan Adamu, mun gāji jiki ajizi na zunubi da mutuwa. Sa’ad da Adamu ya yi zunubi, mu ma muka zama masu zunubi, ko da yake bai haife mu tukuna ba a matsayin zuriyarsa. Saboda haka, hukuncin mutuwar ya haɗa da mu. Idan Jehobah ya kawar da tsarin tsufa da mutuwa, ba tare da biyan fansa ba, maganarsa ba za ta kasance gaskiya ba. Bulus yana magana a madadin dukanmu sa’ad da ya ce: “Mun sani shari’a mai ruhaniya ce: amma ni ba-jiki ne, sayayye ne ƙarƙashin zunubi. Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! wanene zai tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa?”—Rom. 7:14, 24.
10 Jehobah Allah ne kaɗai zai iya yin tanadin hanyar gafarta mana zunubanmu kuma ya ’yantar da mu daga hukuncin mutuwa har abada. Ya yi hakan ta wajen aiko da Ɗansa ƙaunatacce daga sama don a haife shi a matsayin kamiltaccen ɗan Adam, wanda zai iya ba da ransa fansa domin mu. Ba kamar Adamu ba, Yesu kamili ne. Hakika, “ba ya yi zunubi ba.” (1 Bit. 2:22) Da haka, Yesu yana iya zama uban tsara ’yan Adam kamiltattu. Amma, maimakon hakan, ya ƙyale magabtan Allah su kashe shi don ya karɓi ’ya’yan Adamu masu zunubi kuma ya sa ya yiwu waɗanda suka ba da gaskiya a gare shi su samu rai madawwami. Nassosi sun bayyana: “Akwai Allah ɗaya, matsakanci ɗaya kuma tsakanin Allah da mutane, shi kuwa mutum ne, Kristi Yesu, wanda ya bada kansa fansar dukan mutane.”—1 Tim. 2:5, 6.
11. (a) Ta yaya za a iya kwatanta amfanin fansa? (b) Yaya yawan amfanin fansa yake?
11 Ana iya kwatanta amfanin fansa da yanayin mutanen da banki ya damfara kuma don hakan suka ci bashi. An yanke wa masu bankin hukuncin shekaru masu yawa a kurkuku. Amma waɗanda suka ajiye kuɗinsu kuma fa? Da yake sun zama matalauta, ba su da mafita daga yanayinsu sai dai idan wani mutum mai alheri da arziki ya sayi bankin kuma ya mai da musu kuɗinsu, ya kawar musu bashin. Hakazalika, Jehobah Allah da Ɗansa ƙaunatacce sun sayi zuriyar Adamu kuma suka yafe musu bashinsu na zunubi bisa jinin da Yesu ya zubar. Shi ya sa Yohanna mai Baftisma ya ce game da Yesu: “Duba, ga Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya!” (Yoh. 1:29) ’Yan Adam da aka ɗauke zunubansu sun haɗa da masu rai har da matattu.
Sadaukarwa da Aka Yi Don Tanadin Fansa
12, 13. Menene za mu iya koya daga yadda Ibrahim ya amince ya yi hadaya da Ishaƙu?
12 Ba zai yiwu mu fahimci irin sadaukarwar da Ubanmu na samaniya da Ɗansa ƙaunatacce suka yi ba don yin tanadin fansa. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da labarai da za su iya taimaka mana mu yi bimbini a kan wannan batun. Alal misali, ka yi tunanin yadda Ibrahim ya ji sa’ad da ya yi tafiya ta kwana uku zuwa Moriah don yin biyayya da umurnin Allah: “Ka ɗauki ɗanka, tilonka, wanda ka ke ƙaunarsa, wato Ishaƙu, ka tafi ƙasar Moriah; dagacan ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a bisa ɗayan duwatsu wanda zan faɗa maka.”—Far. 22:2-4.
13 A ƙarshe Ibrahim ya isa wurin da aka gaya masa. Ka yi tunanin irin baƙin ciki da ya yi sa’ad da yake ɗaure hannayen da ƙafafun Ishaƙu kuma ya sa shi ya kwanta a kan bagadin da Ibrahim ya gina da hannunsa. Ibrahim yana cike da baƙin ciki sosai yayin da ya ɗaga wuƙar da zai kashe ɗansa da ita! Ka yi tunanin yadda Ishaƙu yake ji sa’ad da ya kwanta a kan bagadi, yana jiran zafi mai raɗaɗi da zai kai ga mutuwarsa. A daidai wannan lokacin ne mala’ikan Jehobah ya hana Ibrahim yin hakan. Abin da Ibrahim da Ishaƙu suka yi a wannan lokacin ya taimaka mana mu fahimci irin sadaukarwa da Jehobah ya yi don ya ƙyale mabiyan Shaiɗan su kashe Ɗansa. Yadda Ishaƙu ya ba da haɗin kai ga Ibrahim kwatanci ne mai kyau na yadda Yesu ya kasance da yardan rai ya sha wahala kuma ya mutu dominmu.—Ibran. 11:17-19.
14. Wane abu ne da ya faru a rayuwar Yakubu ya taimaka mana mu fahimci irin sadaukarwa da aka yi don a yi tanadin fansa?
14 Ana iya kwatanta irin sadaukarwa da aka yi don a yi tanadin fansa da wani abin da ya faru a rayuwar Yakubu. A cikin dukan ’ya’yansa maza, Yakubu ya fi ƙaunar Yusufu. Abin baƙin ciki, ’yan’uwan Yusufu suna kishinsa kuma sun tsane shi. Duk da haka, Yusufu ya yarda babansa ya aike shi don ganin yadda ’yan’uwansa suke. A wannan lokacin suna kiwon tumakin Yakubu da ke kilomita 100 arewa daga gidansu a Hebron. Ka yi tunanin yadda Yakubu ya ji sa’ad da ’ya’yansa suka dawo da rigar Yusufu cike da jini! Ya ce: “Rigar ɗana ce; wani mugun naman jeji ya cinye shi; babu shakka an yayyage Yusufu.” Dukan waɗannan sun shafi Yakubu sosai, wanda ya yi kwanaki da yawa yana makokin Yusufu. (Far. 37:33, 34) Jehobah ba ya aikatawa ga yanayi kamar yadda ’yan Adam ajizai za su yi ba. Duk da haka, yin bimbinin a kan wannan abin da ya faru a rayuwar Yakubu yana iya taimaka mana mu fahimci yadda Allah ya ji sa’ad da aka wulakanta Ɗansa ƙaunatacce kuma aka yi masa mugun kisa a duniya.
Yadda Fansa ta Amfane Mu
15, 16. (a) Yaya Jehobah ya nuna ya amince da fansar? (b) Yaya fansar ta amfane ka?
15 Jehobah Allah ya ta da Ɗansa mai aminci da jiki mai ɗaukaka na ruhu. (1 Bit. 3:18) Yesu da aka ta da daga matattu ya bayyana ga almajiransa kwanaki arba’in, yana ƙarfafa bangaskiyarsu da kuma shirya su don aikin wa’azi mai girma da za su yi. Bayan haka ya koma sama, inda ya miƙa wa Allah amfanin jininsa da ya zubar, don a yi amfani da shi a madadin mabiyansa na gaske, waɗanda suka ba da gaskiya ga amfanin hadayarsa ta fansa. Jehobah Allah ya nuna cewa ya karɓi fansar Kristi ta wajen gaya wa Yesu ya zubo ruhu mai tsarki a kan almajiransa da suka taru a Urushalima a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z.—A. M. 2:33.
16 Waɗannan mabiyan Kristi da aka shafa da ruhu nan da nan suka soma ariritar mutane su tsira daga fushin Allah ta wajen yin baftisma cikin sunan Yesu Kristi don su sami gafarar zunubansu. (Karanta A. M. 2:38-40.) Tun daga wannan rana na musamman har zuwa yau, an jawo mutane miliyoyi daga dukan al’ummai su ƙulla dangantaka da Allah bisa bangaskiyarsu ga hadayar fansa na Yesu. (Yoh. 6:44) A wannan lokacin, muna bukatan mu bincika ƙarin tambayoyi biyu: An ba wani a cikinmu begen rai madawwami ne domin nagargarun ayyukanmu? Muddin mun samu wannan bege mai ban al’ajabi, za mu iya yin hasararsa kuwa?
17. Yaya ya kamata ka ɗauki albarka mai ban al’ajabi na zama abokin Allah?
17 Ba mu cancanci samun fansar gabaki ɗaya ba. Amma ta wurin ba da gaskiya ga fansar, mutane da yawa a yau sun zama abokan Allah, kuma suna da begen rai madawwami a cikin aljanna a duniya. Amma, zama abokan Jehobah ba tabbaci ba ne cewa za mu ci gaba da kasancewa a irin wannan dangantakar da shi ba. Don mu tsira daga ranar fushi na Allah na nan gaba, dole ne mu ci gaba da nuna godiya sosai ga “fansa da ke cikin Yesu Kristi.”—Rom. 3:24; karanta Filibiyawa 2:12.
Ka Ci Gaba da Ba da Gaskiya ga Fansa
18. Menene ba da gaskiya a fansa ya ƙunsa?
18 Ayar jigo na wannan talifin, Yohanna 3:36, ta nuna cewa ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu Kristi ya ƙunshi yin biyayya a gare shi. Nuna godiya ga fansa ya kamata ya motsa mu mu yi rayuwar da ta jitu da koyarwar Yesu, har da abin da ya koyar game da ɗabi’u. (Mar. 7:21-23) “Fushin Allah yana zuwa” a kan dukan waɗanda suka ci gaba da yin ayyukan nan kamar su fasikanci, alfasha, da “dukan ƙazanta,” waɗanda suka haɗa da ci gaba da kallon hotunan batsa.—Afis. 5:3-6.
19. A waɗanne hanyoyi masu kyau ne za mu iya nuna bangaskiyarmu a fansa?
19 Nuna godiya don fansar ya kamata ya sa mu duƙufa da ayyukan “ibada.” (2 Bit. 3:11) Bari mu keɓe isashen lokaci don yin addu’a sosai a kai a kai, nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu, halartan taro, bauta ta iyali, da yin aikin wa’azin Mulki da himma. Kada mu “manta da yin alheri da zumuntar tarayya: gama da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.”—Ibran. 13:15, 16.
20. Dukan waɗanda suka ci gaba da ba da gaskiya ga fansar za su samu wace albarka nan gaba?
20 Sa’ad da Jehobah ya zubo da fushinsa a kan wannan zamani, za mu yi farin cikin cewa mun ba da gaskiya a fansar kuma mun ci gaba da nuna godiya a gare ta! A sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta, za mu ci gaba da yin godiya har abada don wannan tanadi mai ban al’ajabi da ya cece mu daga fushin Allah.—Karanta Yohanna 3:16; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 13, 14.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa muke bukatan fansa?
• Wane sadaukarwa aka yi don a yi tanadin fansa?
• Waɗanne fa’idodi aka samu don fansa?
• Yaya muke ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu?
[Hoton da ke shafi na 13]
Da akwai zarafin sulhuntawa da Jehobah
[Hotuna da ke shafi na 15]
Yin bimbini a kan waɗannan abubuwa da suka faru da Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu za su taimaka mana mu nuna godiya ga sadaukarwa mai girma na fansa