-
Yesu Yana Ciyar da Jama’a ta Hannun Mutane ƘalilanHasumiyar Tsaro—2013 | 15 Yuli
-
-
8. Shin sababbin Kiristoci sun san waɗanda za su koyar da su kuwa? Ka bayyana.
8 Tun daga ranar Fentakos ta shekara ta 33, Yesu ya ci gaba da yin amfani da manzanninsa don koyar da sauran almajiransa shafaffu. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:41, 42.) Yahudawa da kuma sauran ’yan al’ummai da suka zama shafaffun Kiristoci a ranar sun fahimci cewa Yesu yana amfani da waɗannan manzannin. Saboda haka, sun ci gaba da “lizima a cikin koyarwar manzanni.” Hakan yana nufi cewa sun ci gaba da bin koyarwar da aminci. Sababbin Kiristocin sun san cewa suna bukatar su ci gaba da koyon gaskiya, kuma sun san waɗanda za su iya koyar da su. Sun amince da manzannin sosai, kuma sun ci gaba da neman bayani game da ayyukan Yesu da kuma annabcin da aka yi a kansa.c—A. M. 2:22-36.
-
-
Yesu Yana Ciyar da Jama’a ta Hannun Mutane ƘalilanHasumiyar Tsaro—2013 | 15 Yuli
-
-
c Sakin layi na 8: Da yake sababbin almajirai sun ci gaba da “lizima a cikin koyarwar manzanni,” hakan ya nuna cewa manzannin suna koyarwa a kai a kai. A yanzu, wasu koyarwa da manzannin suka yi yana rubuce a cikin hurarrun littattafan Nassosin Helenanci na Kirista.
-