Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 6/15 p. 32
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ta Hanyar Almasihu Ne Allah Zai Kawo Ceto
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Sun Jira Zuwan Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 6/15 p. 32

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Yesu ya yi wa’azi a dukan ƙasar Isra’ila. To, me ya sa manzo Bitrus ya ce mutanen Yahuda da shugabanansu sun aikata da “jahilci” sa’ad da suka kashe shi?—A. M. 3:17.

Sa’ad da yake yi wa rukunin Yahudawa magana game da hakkinsu a mutuwar Almasihu, manzo Bitrus ya ce: “Na sani cikin jahilci kuka yi wannan, kamar yadda mahukuntanku kuma suka yi.” (A. M. 3:14-17) Mai yiwuwa wasu Yahudawa ba su fahimci Yesu da koyarwarsa ba. Wasu kuma suna da jahilci na ruhaniya domin ba sa son su faranta wa Allah rai, suna nuna ƙabilanci, hassada, da ƙiyayya.

Ka yi la’akari da yadda rashin son su faranta wa Jehobah rai ya shafi ra’ayin da mutane da yawa suke da shi game da koyarwar Yesu. Sau da yawa, Yesu ya yi amfani da kwatanci a koyarwarsa, kuma yana bayyana wa dukan waɗanda suke son su ƙara koyo. Amma, wasu sun yi tafiyarsu, ba su yi ƙoƙarin su fahimci abin da ya koya musu ba. A wani lokaci, har wasu cikin almajiransa sun yi fushi game da wata fasahar magana da Yesu ya yi amfani da ita. (Yoh. 6:52-66) Irin waɗannan mutane sun kasa fahimtar cewa kwatancin Yesu yana gwada su ne ko suna shirye su canja tunaninsu da ayyukansu. (Isha. 6:9, 10; 44:18; Mat. 13:10-15) Sun kuma yi banza da annabcin da ya ce Almasihu zai yi amfani da kwatanci a koyarwarsa.—Zab. 78:2.

Wasu sun ƙi koyarwar Yesu domin bambanci. Sa’ad da ya koyar a majami’ar da ke garinsu, Nazarat, mutanen sun yi “mamaki.” Amma, maimakon su amince cewa Yesu Almasihu ne, sun yi tambayoyi game da inda ya fito: “Daga ina wannan mutum yana da waɗannan abu? . . . Wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan’uwan Yaƙub, da Yosi, da Yahuda, da Siman? Yan’uwansa mata fa ba nan su ke tare da mu ba?” (Mar. 6:1-3) Inda Yesu ya fito ya sa koyarwarsa ba ta da muhimmanci ga mutanen Nazarat.

Shugabannin addinan kuma fa? Yawancinsu ba su mai da hankali ga Yesu sosai ba don waɗannan dalilai. (Yoh. 7:47-52) Sun kuma ƙi koyarwarsa domin suna kishin Yesu, da yake mutane suna mai da masa hankali. (Mar. 15:10) Sanannu da yawa sun yi fushi sosai sa’ad da ya hukunta su domin munafuncinsu da ruɗu. (Mat. 23:13-36) Ya dace da Yesu ya hukunta jahilcinsu, yana cewa: “Kaitonku masanan shari’a! gama kuka ɗauki mabuɗin sani: ku da kanku ba ku shiga [Mulkin] ba, masu shiga kuwa kuka hana su.”—Luk 11:37-52.

Yesu ya yi wa’azin bishara na shekara uku da rabi a ƙasar. Ya kuma koya wa mutane da yawa su yi wannan aikin. (Luk 9:1, 2; 10:1, 16, 17) Yesu da almajiransa sun yi aikinsu da kyau don haka Farisawa sun kai kuka cewa: “Ga duniya ta rigaya tana binsa.” (Yoh. 12:19) Saboda haka, ba za a ce yawancin Yahudawa ba su san komi ba gabaki ɗaya. Duk da haka, suna son su kasance da “jahilci” game da Yesu a matsayinsa na Almasihu. Ya kamata a ce sun zurfafa saninsu da ƙaunarsu game da Almasihu, amma ba su yi hakan ba. Wasu sun sa hannu a mutuwar Yesu. Shi ya sa, manzo Bitrus ya gargaɗi da yawa cikinsu cewa: “Ku tuba fa, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin hakanan wokatan wartsakewa daga wurin Ubangiji su zo; domin kuma shi aiko Kristi wanda aka ƙadara maku shi, shi Yesu.” (A. M. 3:19, 20) Abu ne mai muhimmanci cewa Yahudawa da yawa sun soma mai da hankali, har da “babban taro kuma na malamai.” Sun daina yin abubuwa cikin jahilci. Maimakon haka, sun tuba kuma sun samu tagomashin Jehobah.—A. M. 2:41; 4:4; 5:14; 6:7.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba