Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w20 Maris p. 31
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
w20 Maris p. 31
’Yan sandan haikalin Yahudawa sun kama maza biyu da masu adawa suka nuna musu.

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Su waye ne ’yan sandan haikalin Yahudawa? Mene ne aikinsu?

A dā, wasu daga cikin Lawiyawa da ba firistoci ba suna aikin ’yan sanda a haikali. Shugaban masu gadin haikalin ne yake ja-goranci a wannan aikin. Wani marubuci Bayahude mai suna Philo ya bayyana aikin da ’yan sandan suke yi, ya ce: “Wasu daga cikin waɗannan [Lawiyawa] suna zama a ƙofofin haikalin don yin gadi. Wasu kuma suna zama a [cikin haikalin] a gaban mazauni don su hana mutane shiga wurin da bai kamata ba. Suna yawo a cikin haikalin don yin gadi, wasu suna aiki daddare wasu kuma sa’ad da gari ya waye.”

Ƙari ga haka, waɗannan ’yan sanda suna taimakawa a Majalisa. ’Yan sandan ne kaɗai Romawa suka amince da su.

Wani masani mai suna Joachim Jeremias ya ce: “Abin da Yesu ya ce sa’ad da ’yan sanda suka kama shi cewa kowace rana ina zama a Haikali ina yin koyarwa ba ku kama ni ba (Mat. 26:55), ya nuna cewa ’yan sandan haikali ne suka kama shi.” Marubucin ya gaskata cewa mutanen da suka so su kama Yesu kafin wannan lokacin ma ’yan sandan haikali ne. (Yoh. 7:​32, 45, 46) Bayan haka, an tura ’yan sanda da shugabansu su kawo Yesu gaban Majalisa. Daga baya, ’yan Majalisa sun tura ’yan sandan su kamo manzannin Yesu, kuma wataƙila su ne suka fitar da Bulus daga haikali.​—A. M. 4:​1-3; 5:​17-27; 21:​27-30.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba