Matsayin Ruhu Mai Tsarki Wajen Cika Nufin Jehobah
“Maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina . . . za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.”—ISHA. 55:11.
1. Ka kwatanta bambancin da ke tsakanin tsari da nufi.
A CE mutane biyu kowanne yana shirin yin tafiya a cikin motarsa. Ɗaya a cikinsu ya ƙaga hanyar da zai bi. Ɗayan kuma ya zana hanyar da zai bi a cikin zuciyarsa, amma ya san wasu hanyoyi da za a iya bi. Ya yi shiri ya canja hanya idan bukata ta kama. A wani azancin, hanyoyi dabam-dabam da mutane biyun nan suka yi amfani da su ya kwatanta bambancin da ke tsakanin tsari da nufi. Za a iya kwatanta tsari da taswirar hanya don a isa wani waje, amma nufi ta ƙunshi sanin wajen da za a je ba tare da sanin ainihin hanyar da za a bi ba.
2, 3. (a) Menene nufin Jehobah ya ƙunsa, kuma yaya ya bi da yanayin da ya taso sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi? (b) Me ya sa ya kamata mu aikata bisa ga cikawar nufin Jehobah?
2 Idan ya zo ga cika nufinsa, Jehobah bai shirya wani tsari ba, amma yana da manufa da zai cika da shigewar lokaci. (Afis. 3:11) Wannan nufin ya ƙunshi ainihin shirin da ya yi game da ’yan Adam da kuma duniya, wato, wannan duniyar ta zama aljanna inda ’yan Adam kamiltattu za su iya rayuwa a cikin salama da farin ciki har abada. (Far. 1:28) Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, nan da nan Jehobah ya yi shirye-shirye don ya tabbata cewa nufinsa ya cika. (Karanta Farawa 3:15.) Jehobah ya ƙudurta cewa macensa ta alama za ta haifi ‘zuriya,’ ko kuma Ɗa, wanda zai halaka Shaiɗan, kuma ya gyara ɓarnar da ya yi.—Ibran. 2:14; 1 Yoh. 3:8.
3 Babu wani iko a sama ko a duniya da zai iya hana nufin Allah ya cika. (Isha. 46:9-11) Me ya sa za mu iya ce hakan? Domin ya shafi ruhu mai tsarki na Jehobah. Wannan ikon da ba za a iya ƙi ba ya tabbata cewa nufin Allah zai “yi albarka.” (Isha. 55:10, 11) Muna bukatar mu ci gaba da fahimtar yadda Allah yake cika nufinsa. Rayuwarmu ta nan gaba ta dangana ne ga cikawarsa. Ƙari ga hakan, abin ƙarfafa bangaskiya ne mu ga yadda Jehobah yake amfani da ruhu mai tsarki. Bari mu yi la’akari da matsayin ruhun a dā, a yanzu, da kuma a nan gaba wajen cika nufin Jehobah.
Aikin da Ruhu Mai Tsarki Ya Yi a Dā
4. Ta yaya Jehobah ya bayyana nufinsa da sannu-sannu?
4 A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya bayyana nufinsa da sannu-sannu. A farko, zuriyar da aka yi alkawarinsa “asiri” ne. (1 Kor. 2:7) Sai bayan shekaru dubu biyu ne Jehobah ya yi magana kuma game da zuriyar. (Karanta Farawa 12:7; 22:15-18.) Jehobah ya yi wa Ibrahim ƙarin alkawari. Kalmomin nan “ta wurin zuriyarka” tabbaci ne cewa Zuriyar za ta zo a matsayin ɗan Adam, wato, zuriyar Ibrahim. Mun tabbata cewa Shaiɗan ya yi farin ciki sa’ad da aka bayyana wannan. Wannan Maƙiyin babu shakka yana so ya halaka ko kuma ya ɓata zuriyar Ibrahim kuma ta hakan ya hana ƙudurin Jehobah cika. Amma irin wannan sakamakon ba za ta yiwu ba, domin ruhun Allah da ba a gani yana kan aiki. A waɗanne hanyoyi?
5, 6. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ruhunsa don ya kāre mutanen da za su kai ga zuwan Zuriyar?
5 Jehobah ya yi amfani da ruhunsa don kāre mutanen da za su kai ga zuwan Zuriyar. Ga Abram, wato Ibrahim, Jehobah ya ce: “Ni ne garkuwarka.” (Far. 15:1) Waɗannan ba zance ba ne kawai. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru a kusan shekara ta 1919 K.Z., sa’ad da Ibrahim da Saratu suka soma zama a ƙasar Gerar na ɗan lokaci. Ba tare da sanin cewa Saratu matar Ibrahim ba ce, Abimelech, sarkin Gerar ya ɗauki Saratu da nufin mai da ta matarsa. Shin Shaiɗan yana neman ɓata shirin ne, don kada Saratu ta haifi zuriyar Ibrahim? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Amma abin da ya faɗa mana shi ne Jehobah ya ɗauki mataki. A cikin mafarki Jehobah ya gargaɗi Abimelech kada ya taɓa Saratu.—Far. 20:1-18.
6 Ba a wannan lokacin ba ne kaɗai Jehobah ya kāre su. Jehobah ya ceci Ibrahim da iyalinsa sau da yawa. (Far. 12:14-20; 14:13-20; 26:26-29) Game da Ibrahim da zuriyarsa, mai zabura ya ce: Shi “[Jehobah] ba ya bar wani mutum shi zalumce su ba; I, ya tsauta wa sarakuna sabili da su; Ya ce, kada ku taɓa shafaffuna, Kada ku cuci annabawana.”—Zab. 105:14, 15.
7. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya kāre al’ummar Isra’ila?
7 Ta wurin ruhunsa, Jehobah ya kāre al’ummar Isra’ila na dā, inda za a haifi Zuriya da aka yi alkawarinta. Ta ruhunsa, Jehobah ya ba Isra’ilawa Dokarsa, wadda ta kāre bauta ta gaskiya da kuma Yahudawa daga lalata na ruhaniya, ɗabi’a, da kuma na zahiri. (Fit. 31:18; 2 Kor. 3:3) A zamanin Alƙalawa, ruhun Jehobah ya ƙarfafa wasu mutane su ceci Isra’ilawa daga maƙiyinsu. (Alƙa. 3:9, 10) A zamanin da aka haifi Yesu, ainihin zuriyar Ibrahim, ruhu mai tsarki ya kāre Urushalima, Bai’talami, da kuma haikali, don waɗannan za su taimaka wajen cika annabce-annabce game da Yesu.
8. Menene ya nuna cewa ruhu mai tsarki yana da matsayi na kai tsaye a rayuwa da kuma hidimar Ɗan Allah?
8 Ruhu mai tsarki ya taimaki Yesu a rayuwarsa da kuma hidimarsa. Da yake aiki a cikin Maryamu, ruhu mai tsarki ya cim ma abin da bai taɓa yi ba a dā kuma bai ƙara yi tun lokacin ba. Ya sa mace ajiza ta samu ciki kuma ta haifi Ɗa kamiltacce, wanda ba ya ƙarƙashin hukuncin mutuwa. (Luk 1:26-31, 34, 35) Ruhun daga baya ya kāre Yesu daga mutuwa sa’ad da yake jariri. (Mat. 2:7, 8, 12, 13) Sa’ad da Yesu ya kusan shekara talatin, Allah ya shafa shi da ruhu mai tsarki ya zama magajin kursiyin Dauda kuma ya aike shi ya yi wa’azi. (Luk 1:32, 33; 4:16-21) Ruhu mai tsarki ya ba Yesu ikon yin mu’ujizai, haɗe da warkar da marasa lafiya, ciyar da taron mutane, da ta da matattu. Irin waɗannan ayyuka masu ban al’ajabi suna nuna albarka da za mu samu a ƙarƙashin sarautar Yesu ne.
9, 10. (a) Ta yaya aka san cewa almajiran Yesu na ƙarni na farko suna da ruhu mai tsarki? (b) Wane aukuwa na cika nufin Jehobah ne aka bayyana a ƙarni na farko A.Z.?
9 Somawa daga Fentakos na 33 A.Z., Jehobah ya yi amfani da ruhunsa don ya naɗa zuriyar Ibrahim ta biyu, waɗanda da yawa a cikinsu ba zuriyar Ibrahim ba ne. (Rom. 8:15-17; Gal. 3:29) Da tabbaci cewa ruhu mai tsarki ya taimaki almajiran Yesu na ƙarni na farko, ya taimaka musu su yi wa’azi da ƙwazo kuma ya ƙarfafa su su yi ayyuka masu ban al’ajabi. (A. M. 1:8; 2:1-4; 1 Kor. 12:7-11) Ta wajen waɗannan kyauta ta mu’ujiza, ruhu mai tsarki ya bayyana sabuwar hanya da Jehobah zai cika ƙudurinsa. Jehobah ya daina yin amfani da shirin da ya yi a zamanin dā, wato, bauta masa a haikali a Urushalima. Tagomashinsa ya koma ga sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa. Tun lokacin, Jehobah yana amfani da ikilisiyar shafaffu don ya cika ƙudurinsa.
10 Kārewa, ƙarfafawa, naɗawa, ƙalilan ne kawai cikin hanyoyin da Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki don ya sa nufinsa ta kai ga cikawa. Zamaninmu kuma fa? Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhunsa a yanzu don ya tallafa wa nufinsa? Muna bukatar mu sani, domin muna son mu yi aiki cikin jituwa da ruhun. Bari mu yi la’akari da hanyoyi huɗu da Jehobah yake amfani da ruhunsa a zamanin nan.
Aikin da Ruhu Mai Tsarki Yake Yi a Yanzu
11. Menene ya nuna cewa ruhu mai tsarki iko ne mai sa mutanen Allah su kasance da tsarki, kuma yaya za ka nuna cewa kana ba da haɗin kai ga ruhun?
11 Na farko, ruhu mai tsarki iko ne da ke tabbatar cewa mutanen Allah suna da tsarki. Dole ne waɗanda suke da matsayi wajen cika nufin Jehobah su kasance da tsabtar ɗabi’a. (Karanta 1 Korintiyawa 6:9-11.) A dā, wasu da suka zama Kiristoci na gaskiya suna aikata ayyukan lalata kamar su fasikanci, zina, da luwaɗi a dā. Sha’awar da take haifan zunubi tana da ƙarfi sosai. (Yaƙ. 1:14, 15) Duk da haka, waɗannan sun “tsarkake,” hakan ya nuna cewa sun yi canje-canje da ake bukata a rayuwarsu don su faranta wa Allah rai. Menene yake motsa wanda yake ƙaunar Allah ya yi nasara wajen yin tsayayya da sha’awoyi marar kyau? “Ruhun Allahnmu” ne, in ji 1 Korintiyawa 6:11. Ta kasancewa da tsabta na ɗabi’a, ka nuna cewa kana barin ruhun ya yi tasiri a rayuwarka.
12. (a) Bisa ga wahayin Ezekiyel, yaya Jehobah yake wa ƙungiyarsa ja-gora? (b) Ta yaya za ka nuna cewa kana aikata cikin jituwa da ruhun?
12 Na biyu, Jehobah yana yin amfani da ruhunsa wajen ja-gorar ƙungiyarsa bisa ga hanyar da yake son ta nufa. A wahayin Ezekiyel, an kwatanta sashen ƙungiyar Jehobah na sama a matsayin karusa na samaniya da ke nufa wajen cika ƙudurin Jehobah. Menene ya motsa karusar ta bi hanyar da ta dace? Ruhu mai tsarki. (Ezek. 1:20, 21) Bari mu tuna cewa ƙungiyar Jehobah na da sashe biyu, ɗaya a sama na biyu kuma a duniya. Idan ruhu mai tsarki yana yi wa na saman ja-gora, babu shakka shi ne ma yake ja-gorar na duniya. Ta wajen yin biyayya da kuma kasancewa da aminci ga ja-gorar da muke samu daga sashen ƙungiyar Allah na duniya, kana nuna cewa kana tafiya tare da karusar Jehobah na sama kuma kana aikatawa cikin jituwa da ruhu mai tsarki.—Ibran. 13:17.
13, 14. (a) Su wanene suke cikin “wannan tsarar” da Yesu ya ambata? (b) Ka ba da misali da ya nuna cewa ruhu mai tsarki yana aiki wajen haskaka gaskiya na Littafi Mai Tsarki. (Duba akwatin nan “Kana Bin Ƙarin Haske Kuwa?”)
13 Na uku, Jehobah yana amfani da ruhunsa don ya taimaka mana mu fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Mis. 4:18) Da daɗewa “bawa mai-aminci, mai-hikima” yana amfani da mujallar nan a matsayin hanya ta musamman don ya bayyana gaskiyar Littafi Mai Tsarki da sannu-sannu. (Mat. 24:45) Alal misali, ka yi la’akari da yadda muka fahimci “wannan tsara” da Yesu ya faɗa. (Karanta Matta 24:32-34.) Wane tsara ne Yesu yake maganarsa? Talifin nan “Mecece Bayyanuwar Kristi Take Nufi A Gare Ka?” ya bayyana cewa Yesu yana magana ne ba game da miyagu ba, amma ga almajiransa, waɗanda ba da daɗewa ba za a naɗa su da ruhu mai tsarki.a Mabiyan Yesu shafaffu, a ƙarni na farko da zamanin mu, za su zama waɗanda za su ga alamun, su kuma fahimci manufarta, cewa Yesu “ya yi kusa, har bakin ƙofa.”
14 Menene wannan bayanin yake nufi a gare mu? Ko da yake ba za mu iya auna daidai tsawon ‘wannan tsarar’ ba, ya dace mu san abubuwa da yawa game da kalmar nan “tsara,” a yawancin lokaci tana nufin mutane masu shekaru dabam dabam waɗanda suka rayu a wani lokaci, ba ta da tsawo sosai kuma tana da iyaka. (Fit. 1:6) To, yaya za mu fahimci kalaman Yesu game da ‘wannan tsarar’? Babu shakka, yana nufin cewa kafin shafaffun da suke raye sa’ad da alama ta soma bayyana a shekara ta 1914 su gama mutuwa, sauran shafaffun da za su ga somawar ƙunci mai girma za su soma rayuwa. Wannan tsarar tana da mafari, kuma babu shakka za ta samu ƙarshe. Cikawar fannoni dabam dabam na alamar babu shakka ya nuna cewa ƙuncin ya yi kusa. Ta wajen kasancewa da azancin gaggawa da kuma yin tsaro, kana nuna cewa kana bin gyara da ake yi ga fahiminmu na gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma ja-gorar ruhu mai tsarki.—Mar. 13:37.
15. Menene ya nuna cewa ruhu mai tsarki ne yake ƙarfafa mu mu yaɗa bishara?
15 Na huɗu, ruhu mai tsarki yana ƙarfafa mu mu yaɗa bishara. (A. M. 1:8) Menene kuma zai iya bayyana yadda aka yi wa’azin bishara a dukan duniya? Ka yi tunani a kan wannan. Za ka iya kasancewa cikin waɗanda wataƙila domin yawan kunya ko kuwa tsoro, a dā suna tunani cewa, ‘Ba zan taɓa iya yin wa’azi gida gida ba!’ Duk da haka, kana ƙwazo sosai yanzu a wannan aikin.b Amintattun Shaidun Jehobah da yawa sun ci gaba da yin wa’azi ko da hamayya ko tsanantawa. Ruhu mai tsarki na Allah ne kawai zai iya ƙarfafa mu mu sha kan mahani kuma mu yi abubuwa da ba za mu iya aikatawa ba da ƙarfinmu. (Mi. 3:8; Mat. 17:20) Ta wajen sa hannu sosai a aikin wa’azi, kana nuna cewa kana ba da haɗin kai ga ruhun.
Aikin da Ruhu Mai Tsarki Zai Yi a Nan Gaba
16. Me ya sa za mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai kāre mutanensa a lokacin babban tsanani?
16 A nan gaba, Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki a hanya mai ban al’ajabi don cika ƙudurinsa. Ka fara yin la’akari da batun kāriya. Kamar yadda muka gani, Jehobah ya yi amfani da ruhunsa a dā don ya kāre mutane ɗaɗɗaya da kuma al’ummar Isra’ila gabaki ɗaya. Don hakan, muna da dalilin amince cewa zai yi amfani da ruhunsa mai iko don ya kāre mutanensa a lokacin babban tsanani. Ba ma bukata mu yi hasashe game da yadda ainihi Jehobah zai kula da mu a lokacin. Maimakon haka, za mu iya duba gaba da tabbaci, da sanin cewa masu ƙaunar Jehobah ba za su taɓa ɓacewa ba daga idanunsa ko kuwa daga ikon ruhunsa mai tsarki.—2 Laba. 16:9; Zab. 139:7-12.
17. Ta yaya Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki a cikin sabuwar duniya?
17 Ta yaya Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki a sabuwar duniya mai zuwa? Wannan ruhun zai zama ikon da za a yi amfani da shi ga sababbin littattafai da za a buɗe a lokacin. (R. Yoh. 20:12) Menene zai kasance cikinsa? Babu shakka, abubuwan da Jehobah yake bukata a gare mu dalla-dalla a shekaru dubun. Kana ɗokin bincika abin da ke cikin littattafan kuwa? Muna ɗokin jiran sabuwar duniya. Ba za mu iya kwatanta yadda zai zama a yi rayuwa a wannan lokaci mai albarka da Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya cika nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam da ke cikinta ba.
18. Menene ka ƙuduri aniya za ka yi?
18 Kada mu taɓa manta cewa nufin Jehobah da yake cika da sannu-sannu tabbas zai yi nasara, domin yana amfani da ruhunsa mai tsarki, wato, iko mafi ƙarfi a sararin samaniya don ya aikata shi. Wannan ƙudurin ya shafe ka ma. Saboda haka, bari mu ƙuduri aniya mu roƙi Jehobah don ya ba mu ruhunsa kuma mu aikata bisa ga ja-gorarsa. (Luk 11:13) Ta yin haka wataƙila za ka samu gatan yin rayuwa kamar yadda Jehobah ya ƙudurta wa ’yan Adam, wato, har abada cikin aljanna a duniya.
[Hasiya]
a Duba Hasumiyar Tsaro, na 15 ga Fabrairu, 2008, shafuffuka na 21 zuwa 25.
b Don misalin wadda ta sha kan jin kunya sosai kuma ta zama mai ƙwazo a hidima, ka duba Hasumiyar Tsaro, na 1 ga Mayu, 1994, shafi na 19.
Ka Tuna?
• A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki domin ya sa nufinsa ya ci gaba?
• Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhunsa a yanzu?
• Ta yaya Jehobah zai yi amfani da ruhunsa a nan gaba don ya cika nufinsa?
[Akwati da ke shafi na 10]
Kana Bin Ƙarin Haske Kuwa?
Jehobah yana ci gaba da bayyana gaskiyar Littafi Mai Tsarki ga mutanensa. Waɗannene wasu cikin gyare-gyare da aka wallafa cikin Hasumiyar Tsaro?
▪ Menene kwatancin Yesu na yisti ya nuna game da girma na ruhaniya? (Mat. 13:33)—15 ga Yuli, 2008, shafuffuka na 19-20.
▪ A wane lokaci ne za a daina kiran Kiristoci zuwa bege na samaniya?—1 ga Janairu, 2008, shafi na 23, sakin layi na 15-16.
▪ Menene yake nufi a yi wa Allah sujjada “cikin ruhu”? (Yoh. 4:24)—1 ga Agusta , 2002, shafi na 9.
▪ A cikin wace farfajiya ce taro mai girma suke hidima? (R. Yoh. 7:15)—1 ga Yuni, 2006, shafi na 21, sakin layi na 15.
▪ A wane lokaci ne aka ware tumaki da awaki? (Mat. 25:31-33)—1 ga Nuwamba , 1995, shafuffuka na 8-24.