Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 4 pp. 32-40
  • Wanda Dukan Annabawa Suka Yi Shaidarsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wanda Dukan Annabawa Suka Yi Shaidarsa
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Annabce-Annabcen Suke Bayyanawa
  • Ka Nuna Bangaskiya ga Kristi
  • Ka Kasance Da Bangaskiya Cikin Kalmomin Annabci Na Allah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 4 pp. 32-40

Babi Na Huɗu

Wanda Dukan Annabawa Suka Yi Shaidarsa

1. Mecece gaskiya game da Yesu kafin ya zama mutum ta nuna game da dangantakarsa da Jehovah?

“UBAN yana ƙaunar Ɗan, kuma yana nuna masa dukan abin da yana yi da kansa.” (Yohanna 5:20) Dangantaka mai kyau ne Ɗan ya mora da Ubansa, Jehovah! Kusanci na wannan dangantakar ta fara ne a lokacin da aka halicce shi, shekaru aru aru kafin a haife shi. Shi ne makaɗaici Ɗan Allah, wanda Jehovah ne ya halicce shi da kansa. Kome a sama da ƙasa ya halitta ta wurin Ɗan farinsa ne da yake ƙauna sosai. (Kolossiyawa 1:15, 16) Ya kuma zama Kalmar Allah, ko Kakaki, Wanda ta wurinsa aka sanar da nufin Allah ga wasu. Wannan, Ɗan da Allah yake so sosai, shi ya zama Yesu Kristi.—Misalai 8:22-30; Yohanna 1:14, 18; 12:49, 50.

2. Har yaya annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun yi nuni da Yesu?

2 Kafin a yi cikin Ɗan fari na Allah irin na mutum, akwai annabce-annabce hurarru game da shi da aka rubuta. Manzo Bitrus ya tabbatar wa Karniliyus: “Dukan annabawa kuma suna shaidarsa.” (Ayukan Manzanni 10:43) An nuna matsayin Yesu cikin Littafi Mai Tsarki da girma har da mala’ika ya gaya wa manzo Yohanna: “Shaidar Yesu ruhun annabci ne.” (Ru’ya ta Yohanna 19:10) Waɗannan annabce-annabce sun bayyana shi sarai cewa shi ne Almasihu. Sun mai da hankali ga matsayi dabam dabam da zai kasance a cika ƙudurin Allah. Ya kamata mu so dukan waɗannan a yau sosai.

Abin da Annabce-Annabcen Suke Bayyanawa

3. (a) A cikin annabci da ke Farawa 3:15, wanene ke wakilta macijin, “macen,” da kuma ‘zuriyar macijin’? (b) Me ya sa ‘ƙuje kan macijin’ zai zama abin da bayin Jehovah za su so sosai?

3 Na farko cikin waɗannan annabce-annabcen an faɗe su bayan tawaye ne a Adnin. Jehovah ya gaya wa macijin: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Farawa 3:15) Annabcin nan Shaiɗan aka yi wa, wanda macijin yake wakilta. “Macen” ƙungiyar Jehovah ce ta sama, wadda take kama da mace mai aminci gare shi. ‘Zuriyar macijin’ ta ƙunshi dukan mala’iku da kuma mutane da suke da ruhun Shaiɗan, waɗanda suke hamayya da Jehovah da kuma mutanensa. ‘Ƙuje kan macijin’ yana nufin halaka ɗan tawaye a ƙarshe, Shaiɗan, wanda ya yi wa Jehovah tsegumi kuma ya kawo baƙin ciki mai yawa ga mutane. Amma wanene asali cikin ‘zuriyar’ da zai yi ƙujewar? Wannan ya kasance “asirin da ke ɓoye” na ƙarnuka.—Romawa 16:20, 25, 26.

4. Ta yaya zuriyar Yesu ya taimaka wajen nuna cewa shi ne Ɗa na alkawarin?

4 Bayan shekaru 2,000 na tarihin bil Adam, Jehovah ya yi tanadin bayani daki-daki. Ya nuna cewa wannan Ɗa zai fito ne daga zuriyar Ibrahim. (Farawa 22:15-18) Amma, iyalin da Ɗan zai fito zai dangana a kan zaɓen Allah ne, ba wata zuriya ta jiki ba ce. Duk da yadda Ibrahim yake ƙaunar ɗansa Isma’ila, wanda Hajaratu ta haifa masa, Jehovah ya ce: “Alkawarina zan tsayarda shi a wurin Ishaƙu, wanda Saratu za ta haifa maka.” (Farawa 17:18-21) Daga baya aka tabbatar da alkawarin, ba ga ɗan fari na Ishaƙu ba, Isuwa, amma wa Yakubu wanda ta wurinsa aka sami ƙabilai 12 na Isra’ila. (Farawa 28:10-14) A kwana a tashi, an nuna cewa za a haifi Ɗan nan cikin ƙabilar Yahuda, ta iyalin Dauda.—Farawa 49:10; 1 Labarbaru 17:3, 4, 11-14.

5. Lokacin da Yesu ya fara hidimarsa a duniya, menene ya tabbatar da cewa shi ne Almasihu?

5 Waɗanne alamu kuma aka bayar game da sanin Ɗan? Fiye da shekaru 700, Littafi Mai Tsarki ya ce Bai’talahmi ne wurin da za a haifi Ɗa na alkawarin. Ya kuma bayyana cewa Ɗan ya wanzu “tun fil’azal,” tun lokacin da aka halicce shi a sama. (Mikah 5:2) An kuma faɗi daidai lokacin da zai bayyana a duniya ya zama Almasihu, ta bakin annabi Daniel. (Daniel 9:24-26) Kuma sa’ad da aka shafa Yesu da ruhu mai tsarki, lalle ya zama Almasihu na Jehovah, muryar Allah daga sama ta ambata shi a fili cewa Ɗansa ne. (Matta 3:16, 17) An bayyana Ɗan! Domin haka ne, Filibbus ya faɗa da tabbaci: “Mun same shi wanda Musa a cikin Attaura, da Annabawa kuma suka rubuta labarinsa, Yesu.”—Yohanna 1:45.

6. (a) Bayan mutuwar Yesu, menene mabiyansa suka fahimta? (b) Wanene musamman ‘ɗa na zuriyar macen,’ kuma menene ake nufi da ƙuje kan macijin da zai yi?

6 Daga baya mabiyan Yesu suka fahimci cewa a zahiri yawancin annabce-annabce game da shi suka zama sashen hurarren Nassosi. (Luka 24:27) Ya daɗa yin bayani sarai cewa Yesu shi ne ‘ɗa’ na musamman ‘na zuriyar macen,’ wanda shi zai ƙuje kan macijin, ya ƙuje Shaiɗan daga rayuwa. Ta wurin Yesu, dukan alkawuran Allah ga bil Adam, dukan abubuwan da muke sha’awa da daɗewa, za su cika.—2 Korinthiyawa 1:20.

7. Ƙari ga sanin Wanda aka yi zancensa cikin annabce-annabce, me ya zama da amfani mu fahimta?

7 Yaya ya kamata sanin wannan ya shafe mu? Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da bābā Bakushi wanda ya karanta wasu cikin annabce-annabcen nan game da Mai Fansa mai zuwa kuma Almasihu. Da ya ɗimauce, ya tambayi mai bishara Filibbus: “Annabi yana ambaton wanene?” Amma Bakushin bai bar magana ba bayan ya sami amsa. Bayan ya saurari bayanin Filibbus da kyau, mutumin ya fahimci cewa fahimtar wannan annabcin da ya cika na bukatar ya yi wani abu. Ya fahimci cewa yana bukatar ya yi baftisma. (Ayukan Manzanni 8:32-38; Ishaya 53:3-9) Mu ma muna yin haka kuwa?

8. (a) Menene kusan hadayar da Ishaƙu da Ibrahim ya yi yake hotonsa? (b) Me ya sa Jehovah ya gaya wa Ibrahim cewa dukan al’ummai za su sami albarka ta wurin Ɗan, kuma yaya wannan yake a gare mu a yau?

8 Ka kuma yi la’akari da labari mai taɓa zuciya na yadda Ibrahim ya yi kusa ya yi hadaya da Ishaƙu, ɗansa kaɗai ta wajen Saratu. (Farawa 22:1-18) Wannan ya nuna hoton abin da Jehovah zai yi—yin hadaya da makaɗaicin Ɗansa: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Wannan yana ba mu tabbacin cewa yadda Jehovah ya ba da makaɗaicin Ɗansa ya cika Ƙudurinsa, haka kuma zai “ba mu abu duka.” (Romawa 8:32) Me ake bukata a gare mu? Yadda yake a rubuce a Farawa 22:18, Jehovah ya gaya wa Ibrahim cewa dukan al’ummai za su sami albarka ta wurin Ɗan, “domin [Ibrahim ya] yi biyayya da maganata [Allah].” Mu ma muna bukatar mu saurari Jehovah da Ɗansa: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda ba ya yi biyayya ga Ɗan ba, ba za shi ganin rai ba, amma fushin Allah yana bisansa zaune.”—Yohanna 3:36.

9. Idan muna nuna godiya ga begen rai madawwami da hadayar Yesu ya sa ya yiwu, me za mu yi?

9 Idan muna nuna godiya ga begen rai madawwami da ya yiwu ta wurin hadayar Yesu, za mu so mu yi abubuwa da Jehovah ya faɗa ta bakin Yesu. Waɗannan na kewaye da ƙaunarmu ga Allah da kuma ga maƙwabta. (Matta 22:37-39) Yesu ya nuna cewa ƙaunar Jehovah za ta motsa mu mu koyar da wasu su “kiyaye dukan iyakar abin da [Yesu ya] umurce [mu].” (Matta 28:19, 20) Kuma muna son mu raba wannan ƙauna tare da ’yan’uwa bayin Jehovah ta wurin “tattaruwanmu,” a kai a kai tare da su. (Ibraniyawa 10:25; Galatiyawa 6:10) Haka kuma, ta sauraron Allah da Ɗansa, kada mu yi tunanin wai suna bukatar kamilci ne a gare mu. Ibraniyawa 4:15 ta ce Yesu, wanda Babban Firist namu, yana “taɓuwa da tarayyar kumamancinmu.” Abar ta’aziyya ce wannan, musamman yayin da muka kusaci Allah cikin addu’a ta wurin Kristi don taimako mu sha kan kumamancinmu!—Matta 6:12.

Ka Nuna Bangaskiya ga Kristi

10. Me ya sa ba ceto idan ba Yesu Kristi ba?

10 Bayan ba da bayani wa majalisar Yahudawa a Urushalima cewa annabcin Littafi Mai Tsarki ya cika a kan Yesu, manzo Bitrus ya kammala da ƙarfi haka: “Babu ceto ga waninsa: gama babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (Ayukan Manzanni 4:12) Tun da yake dukan ’ya’yan Adamu masu zunubi ne, mutuwarsu ba ta da daraja da za a yi amfani da ita don fansa ga wani. Amma Yesu kamiltacce ne, ransa yana da darajar hadaya. (Zabura 49:6-9; Ibraniyawa 2:9) Ya ba Allah fansa da ta daidaita da kamiltaccen rai da Adamu ya ɓatar. (1 Timothawus 2:5, 6) Wannan ya buɗe mana hanyar samun rai madawwami cikin sabuwar duniyar Allah.

11. Ka yi bayanin yadda hadayar Yesu zai amfane mu ƙwarai.

11 Fansar ta kuma buɗe mana hanyar samun wasu fa’idodi, ko a yanzu ma. Alal misali, ko da mu masu zunubi ne, hadayar Yesu ta sa ya yiwu mu sami lamiri mai tsabta domin gafarar zunubai. Wannan ya fi wanda Isra’ilawa suka samu ta wurin hadayar dabbobi da Dokar Musa ke bukata. (Ayukan Manzanni 13:38, 39; Ibraniyawa 9:13, 14; 10:22) Amma, samun irin gafarar nan tana bukatar mu nuna yarda ga bukatar hadayar Kristi: “Idan mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu mu ke yi, gaskiya kuwa ba ta cikinmu ba. Idan mun faɗi zunubanmu, shi mai-alkawari ne, mai-adalci kuma, da za shi gafarta mamu zunubanmu, shi tsarkake mu daga dukan rashin adalci.”—1 Yohanna 1:8, 9.

12. Me ya sa nutsewa a ruwa muhimmin abu ne a samun lamiri mai kyau a gaban Allah?

12 Ta yaya masu zunubi za su iya nuna bangaskiya cikin Kristi da hadayarsa? Yayin da mutane a ƙarni na farko suka zama masu bi, sun nuna wannan a fili. Ta yaya? Sun yi baftisma. Me ya sa? Domin Yesu ya umurta cewa dukan almajiransa su yi baftisma. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 8:12; 18:8) Mutum ba zai iya jan baya ba idan zuciyarsa ta motsa saboda kyauta ta ƙauna da Jehovah ya bayar ta wurin Yesu. Zai yi gyaran da ake bukata a rayuwarsa, keɓe kansa ga Allah cikin addu’a, kuma ya nuna wannan keɓewar kai ta wurin nutsewa a ruwa. Ta wurin nuna bangaskiya a hanyar nan ne yake ‘biɗan lamiri mai kyau daga wurin Allah.’—1 Bitrus 3:21.

13. Idan muka san mun yi zunubi, menene ya kamata mu yi game da shi, kuma me ya sa?

13 Amma, ko bayan haka, halayen zunubi sa bayyana. To me zai faru? Manzo Yohanna ya ce: “Waɗannan abu ni ke rubuta muku domin kada ku yi zunubi. Idan kowa ya yi zunubi, muna da Mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai-adalci: shi ne kuwa fansar zunubanmu.” (1 Yohanna 2:1, 2) Wannan yana nufin cewa kowane irin zunubi da muka yi, idan muka yi addu’a ga Allah don gafara, sai ya yi hakanan ne? Ba haka ba. Mabuɗin sahihiyar gafara tuba ce. Za a bukaci taimako daga dattawa, da suka ƙware cikin ikilisiyar Kirista. Dole ne mu tabbata cewa abin da muka yi mummuna ne kuma mu yi baƙin ciki daga zuciya a kansa domin mu yi ƙoƙarin gaske a guje maimaita shi. (Ayukan Manzanni 3:19; Yaƙub 5:13-16) Idan muka yi haka, lallai za mu iya samun taimakon Yesu da kuma sake samun tagomashin Jehovah.

14. (a) Ka bayyana muhimmiyar hanya da hadayar Yesu ta amfane mu. (b) Idan muna da bangaskiya da gaske, me za mu yi?

14 Hadayar Yesu ta buɗe hanyar rai madawwami a sama don “ƙaramin garke,” sashe na biyu na zuriyar da aka ambata a Farawa 3:15. (Farawa 3:15; Luka 12:32; Galatiyawa 3:26-29) Ya kuma buɗe hanya don rai madawwami a aljanna a duniya don biliyoyin mutane. (Zabura 37:29; Ru’ya ta Yohanna 20:11, 12; 21:3, 4) Rai madawwami “kyautar Allah . . . ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23; Afisawa 2:8-10) Idan muna da bangaskiya da kuma godiya ga kyautar nan yadda ya yiwu, za mu nuna wannan. Fahimtar yadda Jehovah cikin mu’ujiza ya yi amfani da Yesu a cika Nufinsa da kuma yadda haka yake da muhimmanci cewa dukanmu mu bi sawun Yesu da kyau, za mu mai da hidimar Kirista ɗaya cikin muhimman ayyuka na rayuwarmu. Bangaskiyarmu za ta bayyana ta yadda muke gaya wa wasu da gaba gaɗi game da kyauta mai girma daga Allah.—Ayukan Manzanni 20:24.

15. Ta yaya bangaskiya cikin Yesu Kristi yake kawo haɗin kai?

15 Dubi yadda bangaskiyar nan take kawo haɗin kai! Ta wurinta, muka kusaci Jehovah, Ɗansa, da kuma juna cikin ikilisiya ta Kirista. (1 Yohanna 3:23, 24) Tana sa mu yi farin ciki cewa Jehovah cikin alheri ya ba Ɗansa “suna wanda ke bisa kowane suna [ban da sunan Allah]; domin cikin sunan Yesu kowacce gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya da ta ƙarƙashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba.”—Filibbiyawa 2:9-11.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Yayin da Almasihu ya bayyana, me ya sa waɗanda suka gaskata da Kalmar Allah da gaske suka san shi?

• Waɗanne abubuwa ya kamata mu yi a nuna godiyarmu ga hadayar Yesu?

• A waɗanne hanyoyi ne hadayar Yesu ta amfane mu? Ta yaya wannan yake taimakonmu sa’ad da muke addu’a ga Jehovah don gafarar zunubanmu?

[Hoto a shafi na 36]

Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su koya wa wasu su kiyaye umurnan Allah

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba