Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 p. 30-p. 32 par. 16
  • Darussa Daga Littafin Ayukan Manzanni

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Ayukan Manzanni
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • BITRUS YA YI AMFANI DA ‘MAƘULLAN MULKI’
  • (Ayukan Manzanni 1:1–11:18)
  • BULUS YA YI HIDIMA DA HIMMA
  • (A. M. 11:19–28:31)
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 p. 30-p. 32 par. 16

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Ayukan Manzanni

LITTAFIN Ayukan Manzanni ya ba da cikakken tarihi na yadda aka kafa ikilisiyar Kirista da kuma yadda ta yaɗu. Luka, wanda likita ne ya rubuta littafin, kuma ya ba da labarin ayyukan Kirista na kusan shekaru 28 daga shekara ta 33 A.Z., zuwa 61 A.Z.

Sashe na farko na littafin Ayukan Manzanni yana ɗauke ne da ayyukan manzo Bitrus, kuma sauran suna ɗauke ne da na manzo Bulus. Ta wajen yin amfani da wakilin suna “mu,” Luka ya nuna cewa yana wajen a lokacin da wasu abubuwa suka faru. Mai da hankali ga saƙon da ke cikin littafin Ayukan Manzanni zai taimake mu mu ɗauki ikon rubutacciyar Kalmar Allah da ruhunsa mai tsarki da tamani. (Ibran. 4:12) Zai motsa mu mu saɗaukar da kanmu kuma zai ƙarfafa bangaskiyarmu ga begen Mulki.

BITRUS YA YI AMFANI DA ‘MAƘULLAN MULKI’

(Ayukan Manzanni 1:1–11:18)

Bayan sun samu ruhu mai tsarki, manzannin sun yi wa’azi da gaba gaɗi. Bitrus ya yi amfani da “muƙublai na mulkin sama” ya buɗe wa Yahudawa da shigaggu waɗanda suka “karɓi maganatasa” ƙofar samun ilimi da kuma zarafin shiga Mulkin. (Mat. 16:19; A. M. 2:5, 41) Tsanantawa mai tsanani ya watsa almajiran, amma hakan ya faɗaɗa aikin wa’azin.

Da suka ji cewa mutanen Samariya sun karɓi maganar Allah, manzannin da ke Urushalima sun aika Bitrus da Yohanna zuwa wajensu. Ta wajen ba Samariyawa zarafin shiga Mulki, Bitrus ya yi amfani da makulli na biyu. (A. M. 8:14-17) Wataƙila cikin shekara ɗaya na tashin Yesu daga matattu, Shawulu na garin Tarsus ya canja halinsa ya zama Kirista. A shekara ta 36 A.Z., Bitrus ya yi amfani da makulli na uku, kuma aka zuba ruhu mai tsarki a kan mutanen al’ummai da ba su yi kaciya ba.—A. M. 10:45.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

2:44-47; 4:34, 35—Me ya sa masu bi suka sayar da dukiyarsu kuma suka rarrabar da kuɗin? Yawancin mutanen da suka zama masu bi sun zo ne daga wurare masu nisa kuma ba su da isashen guzurin da zai sa su ɗan daɗe a Urushalima. Duk da haka, sun so su jima a wajen domin su ƙara koyo game da sabon imaninsu kuma su yi wa mutane wa’azi. Domin su taimaka wa irin waɗannan mutanen, wasu Kiristoci sun sayar da kayansu, kuma aka rarraba wa mabukata kuɗin.

4:13—Bitrus da Yohanna jahilai ne ko kuma marasa karatu? A’a. An kira su ‘marasa karatu da talakawa’ ne domin ba su je makarantu na malamai don samun koyarwa na addini ba.

5:34-39—Ta yaya Luka ya san abin da Gamaliel ya faɗa a taron ’yan Majalisa? Wataƙila ɗaya daga cikin abubuwa uku na gaba ya faru: (1) Bulus, ɗalibin Gamaliel na ɗa ya gaya wa Luka; (2) Luka ya tambayi mai sauƙin kai da yake cikin ’yan Majalisa, kamar Nikodimu; (3) Allah ya hure Luka ya samu wannan labarin.

7:59—Istifanus yana yin addu’a ne ga Yesu? A’a, ba haka ba ne. Ya kamata mutum ya bauta wa Jehobah Allah kaɗai kuma ya yi addu’a a gare shi. (Luka 4:8; 6:12) Ko a yanayi mai kyau ma, Istafanus zai yi wa Jehobah addu’a cikin sunan Yesu. (Yoh. 15:16) Amma a wannan yanayin, Istafanus ya ga wahayin “Ɗan mutum a tsaye ga hannun dama na Allah.” (A. M. 7:56) Domin ya san cewa an ba shi ikon ta da matattu, Istafanus ya yi magana ne kai tsaye ga Yesu yana gaya masa ya kāre ruhunsa amma bai yi addu’a ga Yesu ba.—Yoh. 5:27-29.

Darussa Dominmu:

1:8. Ba za a iya cim ma aikin da masu bauta wa Jehobah suke yi a dukan duniya ba, ba tare da taimakon ruhu mai tsarki ba.

4:36–5:11. An canja sunan mahaifin Yusufu mutumin Ƙubrus zuwa Barnaba, wato, “Ɗan ƙarfafawar zuciya.” Mai yiwuwa manzannin suna kiransa Barnaba ne domin yana faranta zuciyar mutane, yana yi musu alheri kuma yana taimakonsu. Ya kamata mu zama kamarsa ba kamar Hananiya da Safiratu ba, waɗanda suka nuna kamar su masu alheri ne, amma masu riya ne da cuku-cuku.

9:23-25. Guje wa magabtanmu domin mu ci gaba da wa’azi ba wawanci ba ne.

9:28-30. Idan yin wa’azi a wasu unguwanni ko ga wasu mutane ya zama da lahani a zahiri, ga ɗabi’a, ko kuma ruhaniya, muna bukatar mu aikata da wayo kuma mu zaɓi wurare da lokacin da za mu yi wa’azi.

9:31. A lokacin salama, ya kamata mu yi ƙoƙari mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta wurin yin nazari da bimbini. Wannan zai taimake mu mu yi tafiya cikin tsoron Jehobah ta wurin yin amfani da abin da muka koya kuma mu kasance da himma a hidima.

BULUS YA YI HIDIMA DA HIMMA

(A. M. 11:19–28:31)

A shekara ta 44 A.Z., Agabus ya tafi Antakiya, inda Barnaba da Sila suka yi koyarwa “har shekara guda.” Agabus ya annabta cewa za a yi “babbar yunwa,” kuma hakan ya faru bayan shekaru biyu. (A. M. 11:26-28) “Bayanda suka cika hidimassu” na gudanar da kayan agaji a Urushalima, Barnaba da Shawulu suka koma Antakiya. (A. M. 12:25) A shekara ta 47 A.Z., misalin shekaru 12 bayan Shawulu ya zama Kirista, ruhu mai tsaki ya tura Barnaba da Shawulu su yi tafiye-tafiye na wa’azi. (A. M. 13:1-4) A shekara ta 48 A.Z., suka koma Antakiya, “wurinda aka danƙa su ga alherin Allah.”—A. M. 14:26.

Bayan watanni tara, Bulus (wanda ake kira Shawulu) ya zaɓi Sila ya zama abokin tafiyarsa kuma ya soma tafiyarsa ta biyu na yin wa’azi a ƙasashen waje. (A. M. 15:40) Timothawus da Luka sun sami Bulus a kan hanya. Luka ya tsaya a Filibbi, Bulus kuma ya ci gaba zuwa Atina da kuma Koranti, inda ya sadu da Akila da Biriskilla kuma ya yi shekara guda da watanni shida. (A. M. 18:11) Bulus ya bar Timothawus da Sila a Koranti kuma ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Biriskilla da Akila a farkon shekara ta 52 A.Z. (A. M. 18:18) Akila da Biriskilla sun bi shi har zuwa Afisa inda suka ci gaba da zama.

Bayan ya ɗan jima a Suriya ta Antakiya, Bulus ya soma tafiyarsa ta uku ta yin wa’azi a shekara ta 52 A.Z. (A. M. 18:23) A Afisa, “maganar Ubangiji ta [ci gaba da] yawaita da iko ƙwarai, ta yi nasara.” (A. M. 19:20) Bulus ya yi shekaru uku a wajen. (A. M. 20:31) Bulus yana Urushalima a lokacin Fentakos na shekara ta 56 A.Z. Bayan da aka kama shi, ya yi wa’azi babu tsoro a gaban masu mulki. A Roma an tsare Bulus a cikin gida na shekara biyu (shekara ta 59 zuwa 61 A.Z.), a wajen ya nemi hanyoyin da zai yi wa’azi game da Mulkin kuma ya koyar “da al’amura na wajen Ubangiji Yesu Kristi.”—A. M. 28:31.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

14:8-13—Me ya sa mutanen Listra suka kira “Barnaba, Zafsa, Bulus kuwa . . . Harmasa”? Zafsa sarkin allolin almara na Helenawa ne, kuma an san ɗansa Harmasa da iya magana mai rinjayar mutane. Tun da yake Bulus ne ke ja-gora wajen magana, mutanen Listra suka kira shi Harmasa kuma suka kira Barnaba Zafsa.

16:6, 7—Me ya sa ruhu mai tsarki ya hana Bulus da abokansa su yi wa’azi a yankin Asiya da Bithiniya? Domin masu aikin kaɗan ne. Shi ya sa ruhu mai tsarki ya yi musu ja-gora su je inda zai fi ba da amfani.

18:12-17—Me ya sa Galiyo mai mulki bai sa baki ba sa’ad da mutane suka soma dukan Sustanisu? Wataƙila Galiyo ya yi tunani cewa abin da ake yi wa mutumin ya dace da yake shi ne shugaban ’yan iska da suke son su yi wa Bulus dūka. Amma, abin da ya faru ya samu sakamako mai kyau da yake hakan ya sa Sustanisu ya tuba ya zama Kirista. Daga baya, Bulus ya kira Sustanisu “ɗan’uwanmu.”—1 Kor. 1:1.

18:18—Wane alkawari ne Bulus ya yi? Wasu masana sun ce Bulus ya yi alkawari ne na Banazare. (Lit. Lis. 6:1-21) Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗi irin alkawarin da Bulus ya yi ba. Bugu da ƙari, Nassosi bai ambata ba ko Bulus ya yi alkawarin ne kafin ya zama Kirista ko kuwa bayan hakan, ko kuma ya soma alkawarin ne ko kuma ya cika shi. Ko yaya dai, yin irin wannan alkawarin ba zunubi ba ne.

Darussa Dominmu:

12:5-11. Ya kamata mu yi wa ’yan’uwanmu addu’a.

12:21-23; 14:14-18. Hirudus ya karɓi daraja da ya kamata a ba wa Allah kaɗai. Hakan ya bambanta da yadda Bulus da Barnaba nan da nan suka ƙi yabo da daraja da ba su cancance su ba! Bai kamata mu nemi yabo don duk wani abin da muka cim ma a hidimar Jehobah ba.

14:5-7. Mai da hankali zai taimake mu mu kasance da ƙwazo a hidimarmu.—Mat. 10:23.

14:22. Kiristoci sun san za a tsananta musu. Ba sa ƙoƙari su gudu ta wajen ƙin bangaskiyarsu.—2 Tim. 3:12.

16:1, 2. Ya kamata matasa Kiristoci su zama masu ruhaniya kuma su nemi taimakon Jehobah don su samu sunan kirki.

16:3. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Nassi don mu sa mutane su karɓi bishara.— 1 Kor. 9:19-23.

20:20, 21. Wa’azi gida gida fanni ne mai muhimmanci a hidimarmu.

20:24; 21:13. Kasancewa da aminci ga Allah ya fi muhimmanci da mu ceci ranmu.

21:21-26. Ya kamata mu kasance a shirye mu karɓi shawara mai kyau.

25:8-12. Kiristoci a yau za su iya kuma ya kamata su yi amfani da tanadin doka don “kāriyar bishara da ƙarfafawarta.”—Filib. 1:7.

26:24, 25. Ya kamata mu yi shelar “furtadda zantattuka na gaskiya da na natsuwa” ko da yake wawanci ne ga “mutum mai-tabi’ar jiki.”—1 Kor. 2:14.

[Hoto a shafi na 30]

Yaushe ne Bitrus ya yi amfani da “maƙublai na mulkin”?

[Hoto a shafi na 31]

Aikin wa’azi na dukan duniya ba zai yiwu ba sai da taimakon ruhu mai tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba