Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 5/1 pp. 22-26
  • Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙwararrun Makiyaya Ne Suka Koyar da Su
  • Kalmar Allah Ce ta Koyar da Su
  • “Bawan Nan Mai-Aminci, Mai-Hikima” ya Koyar da Su
  • Makiyaya Waɗanda “Gurbi Ne Ga Garken”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 5/1 pp. 22-26

Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa

“Ubangiji yana bada hikima: daga cikin bakinsa ilimi da fahimi su ke fitowa.”—MISALAI 2:6.

1, 2. Me ya sa maza da suka yi baftisma suke biɗan ƙarin hakki a cikin ikilisiya?

“NA YI farin ciki sosai sa’ad da aka naɗa ni dattijo,” in ji Nick wanda yake hidima na dattijo shekara bakwai yanzu. “Na ɗauki wannan gatar zarafi ne na faɗaɗa hidimata ga Jehobah. Ina jin kamar yana bi na bashin godiya don dukan abin da ya yi mini. Ina son in taimaki waɗanda suke cikin ikilisiya iyaka yadda ya yiwu, na taimake su yadda wasu dattawa suka taimake ni.” Amma, ko da yana farin ciki yana da wasu damuwa. Nick ya ci gaba, “tun da yake na kusan shekaru 30 lokacin da aka naɗa ni, na damu cewa ba ni da iyawa da ake bukata, wato fahimi da hikima na kiwon ikilisiya da kyau.”

2 Waɗanda Jehobah ya naɗa su kula da garkensa suna da dalilai da yawa na yin farin ciki. Manzo Bulus ya tuna wa dattawa na Afisa dalili ɗaya na farin ciki sa’ad da ya yi ƙaulin maganar Yesu, ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Hidima na bawa mai hidima ko kuma dattijo na ba wa maza da suka yi baftisma ƙarin hanyoyi na yi wa Jehobah da ikilisiyar kyauta. Alal misali, bayi masu hidima, suna aiki tare da dattawa. Waɗannan bayin suna kula da ayyuka da yawa masu cin lokaci amma kuma suna da muhimmanci. Ƙauna ga Allah da maƙwabci ne yake motsa irin waɗannan ’yan’uwan su yi hidima mai daraja.—Markus 12:30, 31.

3. Me ya sa wasu suke jinkirin biɗan gata a cikin ikilisiya?

3 Namiji da yake jinkirin biɗan gatan zama bawa da kuma dattijo domin yana jin bai cancanta ba fa? Kamar Nick, zai damu cewa ba shi da iyawa da ake bukata don makiyayi da ya ƙware. Kana cikin ’yan’uwa maza da suka yi baftisma da suke jin hakan? Irin wannan damuwa daidai ne. Jehobah zai riƙe makiyaya da alhaki don yadda suka bi da garken. Yesu ya ce: “Dukan wanda an ba shi dayawa, za a nemi dayawa a gareshi: wanda kuwa an sanya masa dayawa a hannu, a wurinsa za a fi biɗa.”—Luka 12:48.

4. Ta yaya Jehobah yake taimakon waɗanda ya naɗa su kula da tumakinsa?

4 Jehobah yana bukatar waɗanda ya naɗa bayi ko dattawa su cika hakkinsu ban da taimako ne? Maimakon haka, yana ba da taimako da ke sa su jimre kuma su yi nasara. Kamar yadda aka tattauna a darasi da ya shige, Jehobah yana ba su ruhunsa mai tsarki, ’yar ruhun na taimakonsu su kula da tumakin da kyau. (Ayukan Manzanni 20:28; Galatiyawa 5:22, 23) Ƙari ga haka, Jehobah na ba su hikima, sani, da kuma fahimi. (Misalai 2:6) Yaya yake yin hakan? Bari mu tattauna hanyoyi uku da Jehobah yake koyar da mutane da ya naɗa su kula da tumakinsa.

Ƙwararrun Makiyaya Ne Suka Koyar da Su

5. Me ya sa Bitrus da Yohanna suka zama makiyaya da suka ƙware?

5 Sa’ad da manzanni Bitrus da Yohanna suka tsaya a gaban Majalisa, alƙalan kotun masu hikima na duniya suna ɗaukan mutanen cewa su “marasa-karatu ne, talakawa.” Suna iya karatu da rubutu, amma ba su sami koyarwa na zama malaman Nassosi ba. Duk da haka, Bitrus da Yohanna da wasu almajirai sun zama malamai da suka ƙware, sun motsa mutane da yawa da suka saurare su su zama masu bi. Ta yaya waɗannan talakawa suka zama sanannun malamai? Bayan sun saurari Bitrus da Yohanna, kotun “suka ɗauki zobe a kansu dā suna tare da Yesu.” (Ayukan Manzanni 4:1-4, 13) Hakika, ruhu mai tsarki na tare da su. (Ayukan Manzanni 1:8) Amma a bayane yake har ga waɗannan alƙalai marasa fahimi na ruhaniya cewa Yesu ne ya koyar da waɗannan mutane. Sa’ad da yake tare da su a duniya, Yesu ya koya wa manzannin yadda za su tara mutane masu kama da tumaki da kuma yadda za su yi kiwonsu muddin sun shigo cikin garken.—Matta 11:29; 20:24-28; 1 Bitrus 5:4.

6. Wane misali ne Yesu da Bulus suka kafa wajen koyar da wasu?

6 Bayan tashin Yesu daga matattu, ya ci gaba da koyar da waɗanda ya naɗa makiyaya. (Ru’ya ta Yohanna 1:1; 2:1–3:22) Alal misali, shi da kansa ne ya zaɓi Bulus kuma ya lura da yadda ake koyar da shi. (Ayukan Manzanni 22:6-10) Bulus ya ɗauki wannan koyarwa da tamani kuma ya koya wa sauran dattawan abin da ya koya. (Ayukan Manzanni 20:17-35) Alal misali, ya ba da lokaci da kuzari sosai wajen koyar da Timothawus ya zama “ma’aikaci” wanda “babu dalilin kunya gareshi,” a hidimar Allah. (2 Timothawus 2:15) Waɗannan mutanen biyu sun ƙulla abuta na kud da kud. Bulus ya rubuta game da Timothawus: “Kamar da ɗa ya ke bauta ma uba, haka ya yi bauta tare da ni zuwa yaɗuwar bishara.” (Filibbiyawa 2:22) Bulus bai nemi ya sa Timothawus ko wani ya zama nasa almajirin ba. Maimakon haka, ya ƙarfafa ’yan’uwa masu bi su zama ‘masu-koyi da shi, kamar yadda shi kuma na Kristi ne.’—1 Korinthiyawa 11:1.

7, 8. (a) Wane labari ne ya nuna amfanin da ake samu sa’ad da dattawa suka yi koyi da Yesu da Bulus? (b) Yaushe ne ya kamata dattawa su soma koya wa waɗanda za su zama bayi masu hidima da dattawa?

7 Ta yin koyi da Yesu da Bulus, makiyaya da suka manyanta suna koyar da ’yan’uwa maza da suka yi baftisma kuma suna samun sakamako mai kyau. Ga labarin Chad. An yi renonsa cikin iyali mai bin addini dabam dabam amma kwanan baya an naɗa shi dattijo. Ya ce: “Shekaru da yawa, dattawa da yawa da sun ƙware sun taimake ni na sami cin gaba a ruhaniya. Domin babana ba mai bi ba ne, waɗannan dattawa sun kula da ni musamman, suka zama kamar baba na ruhaniya a wajena. Sun ba da lokaci su koyar da ni a hidima, kuma bayan haka, wani dattijo musamman ya koya mini yadda ake kula da ayyuka ta ikilisiya.”

8 Yadda labarin Chad ya nuna, makiyaya masu fahimi suna soma koya wa waɗanda za su zama bayi masu hidima da dattawa nan gaba da daɗewa kafin su cancanci samun irin wannan gatan. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ba da umurni cewa bayi masu hidima da dattawa su kasance da mizanan ɗabi’a da na ruhaniya mai girma kafin a naɗa su. Dole ne a “fara gwada su.”—1 Timothawus 3:1-10.

9. Wane hakki ne makiyaya da suka manyanta suke da shi, kuma me ya sa?

9 Idan za a gwada ’yan’uwa maza, yana da kyau a fara koyar da su. Alal misali: Idan aka gaya wa ɗalibi ya yi jarabawa mai wuya da malaman ba su koya masa ba, ɗalibin zai ci jarabawar ne? Hakika, ba zai ci ba. Saboda haka, ana bukatar koyarwa. Amma malamai masu koyarwa da kyau suna taimakon ɗaliban su ci jarabawa kuma su yi amfani da ilimin da suka samu. Hakanan ma, dattawa masu ƙwazo suna taimakon ’yan’uwa maza da suka yi baftisma su koyi halaye da ake bukata daga namiji da aka naɗa ta wajen yi musu ainihin koyarwa da ya dace. Suna yin haka ba don kawai suna son a naɗa waɗannan ’yan’uwan ba amma don su taimake su su iya kula da garken da kyau. (2 Timothawus 2:2) Hakika, ’yan’uwa maza da suka yi baftisma za su yi iya ƙoƙarinsu kuma su yi aiki tuƙuru su cika abubuwa da ake bukata daga bawa ko dattijo. (Titus 1:5-9) Duk da haka, ta wajen koyar da waɗanda suke biɗan aikin ikilisiya da yardan rai, dattawa da suka kware za su taimake su su sami ci gaba da sauri.

10, 11. Ta yaya makiyaya za su koya wa wasu don samun ƙarin gata?

10 Musamman, ta yaya makiyaya da suka ƙware za su koya wa wasu su kula da ayyukan ikilisiya? Na farko, ya kamata makiyaya su san ’yan’uwa da suke cikin ikilisiya, suna zuwan hidimar fage a kai a kai tare da su kuma su taimake su su kyautata iyawarsu wajen “rarrabe kalmar gaskiya sosai.” (2 Timothawus 2:15) Makiyaya da suka manyanta za su tattauna farin cikin da ake samu daga yi wa wasu hidima da waɗannan ’yan’uwan da kuma gamsuwa da su kansu za su samu wajen kafa da kuma cim ma burinsu na ruhaniya. Za su kuma ba da ainihin shawarwari a kan yadda ɗan’uwa zai kyautata zama ‘gurbi ga garken.’—1 Bitrus 5:3, 5.

11 Muddin aka naɗa ɗan’uwa bawa mai hidima, makiyaya masu hikima za su ci gaba da koyar da shi. Ɗan’uwa Bruce, da ya yi hidima na dattijo shekaru da yawa ya ce: “Ina zama da wanda aka naɗa bawa mai hidima kuma na maimaita umurni na amintaccen bawan nan mai hikima da shi. Muna kuma karanta kowace farilla game da aikinsa, kuma ina aiki tare da shi har sai ya saba da ayyukansa.” Yayin da bawa ya ƙware, za a iya koya masa aikin ziyarar kiwo. Bruce ya ci gaba: “Sa’ad da na fita ziyara da bawa mai hidima, ina taimakonsa ya zaɓi ainihin nassosi da zai ƙarfafa kuma ya motsa mutumin ko iyalin da za mu kai wa ziyara. Koyan yadda ake amfani da Nassosi da zai motsa zuciya yana da muhimmanci idan bawa zai zama makiyayi da ya ƙware.”—Ibraniyawa 4:12; 5:14.

12. Ta yaya makiyaya da suka ƙware suke koyar da sababbin dattawa?

12 Sababbin makiyaya suna amfana sosai daga ƙarin koyarwa. Nick, da aka ambata da farko ya ce: “Koyarwa da na samu daga dattawa biyu musamman yana da ban taimako. Waɗannan ’yan’uwan sun san yadda ya kamata a bi da wasu matsaloli. Koyaushe suna sauraro na cikin haƙuri kuma su yi la’akari da ra’ayina sosai, ko idan ba su yarda da shi ba. Na koyi abubuwa da yawa ta wajen lura da yadda suke bi da ’yan’uwa a cikin ikilisiya da tawali’u kuma cikin ladabi. Waɗannan dattawan sun nanata mini bukatar yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kyau sa’ad da nake magance matsaloli ko kuma sa’ad da nake ƙarfafa mutum.”

Kalmar Allah Ce ta Koyar da Su

13. (a) Menene ɗan’uwa yake bukata domin ya zama makiyayi da ya ƙware? (b) Me ya sa Yesu ya ce: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne”?

13 Hakika, Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki na ɗauke da dokoki, ƙa’idodi, da misalai da makiyayi yake bukata domin ya “zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Mai yiwuwa ɗan’uwa ya je makaranta sosai, amma iliminsa na Nassosi da kuma yadda yake amfani da shi ne yake sa ya zama makiyayi da ya ƙware. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ya fi kowa ilimi, da fahimi, shi ne kuma makiyayi na ruhaniya da ya fi hikima da ya taɓa rayuwa a duniya; duk da haka bai dogara ga nasa fahimi ba sa’ad da yake koya wa tumakin Jehobah. Ya ce: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.” Me ya sa Yesu ya yabi Ubansa na samaniya? Ya yi bayani: “Wanda ya ke yin magana domin kansa, darajar kansa ya ke nema.”—Yohanna 7:16, 18.

14. Ta yaya makiyaya suke guje wa neman nasu daraja?

14 Makiyaya masu aminci suna kauce wa neman nasu daraja. Suna ba da gargaɗi da ƙarfafa bisa Kalmar Allah ba nasu hikima ba. Sun fahimci cewa aikin makiyayi shi ne ya taimaka wa tumaki su san “nufin Kristi,” ba nufin dattawa ba. (1 Korinthiyawa 2:14-16) Alal misali, idan dattijo da yake taimakon ma’aurata su magance matsaloli na aure ya ba da shawararsa bisa abin da ya sani maimakon bisa ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki da kuma bayani da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya wallafa kuma fa? (Matta 24:45) Mai yiwuwa ya ba da shawararsa bisa al’adu domin ba shi da cikakken sani game da batun. Hakika, wasu al’adu suna da kyau, kuma wataƙila dattijon ya fahimci rayuwa. Amma tumakin za su fi amfana sa’ad da makiyaya suka ƙarfafa su su saurari muryar Yesu da kuma maganar Jehobah maimakon ra’ayin mutane ko kuma ƙa’idodin al’adu.—Zabura 12:6; Misalai 3:5, 6.

“Bawan Nan Mai-Aminci, Mai-Hikima” ya Koyar da Su

15. Wane aiki ne Yesu ya ba “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” kuma wane dalili ne ya sa rukunin suke yin nasara?

15 Makiyaya kamar manzanni Bitrus, Yohanna, da Bulus suna cikin rukunin da Yesu ya kwatanta da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Wannan ajin bawa ya ƙunshi ’yan’uwan Yesu a duniya da aka shafa da ruhu, waɗanda suke da begen sarauta da Kristi a sama. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) A wannan kwanaki na ƙarshe, adadin ’yan’uwan Kristi da suke a duniya sun ragu sosai. Amma yanzu, an fi faɗaɗa aikin wa’azin bishara na Mulki da Yesu ya ce su yi kafin ƙarshen ya zo. Duk da haka, ajin bawan nan sun yi nasara sosai! Me ya sa? Domin sun koyar da “waɗansu tumaki” su taimake su a aikin wa’azi da kuma koyarwa. (Yohanna 10:16; Matta 24:14; 25:40) A yau, wannan rukunin na masu aminci ne suke yawancin aikin.

16. Ta yaya ajin bawa ke koyar da maza da aka naɗa?

16 Ta yaya ajin bawa suke wannan koyarwa? A ƙarni na farko, an ba wakilan ajin bawan izini su koyar su kuma naɗa masu kula a cikin ikilisiyoyi, su kuma za su koyar da tumakin. (1 Korinthiyawa 4:17) Hakan yake a yau. Hukumar Mulki, wato, ƙaramin rukunin dattawa shafaffu da suke wakiltan ajin bawa sun ba wakilansu iko su koyar kuma su naɗa bayi da dattawa a dubban ikilisiyoyin da ke duniya. Ƙari ga haka, Hukumar Mulki tana shirya makarantu don a koyar da Kwamitin Reshe, masu kula masu ziyara, dattawa, da kuma bayi masu hidima a yadda za su fi kula da tumakin. Ana ba da ƙarin ja-gora ta wurin wasiƙu, ta talifai da ake bugawa a cikin Hasumiyar Tsaro, da kuma wasu littattafai, kamar littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will.a

17. (a) Ta yaya Yesu ya nuna ya amince da ajin bawa? (b) Ta yaya makiyaya na ruhaniya suka nuna cewa sun amince da ajin bawa?

17 Yesu ya amince da ajin bawan sosai da ya sanya su su kula da “dukan abin da ya ke da shi” wato, dukan abubuwansa na ruhaniya a duniya. (Matta 24:47) Makiyaya da aka naɗa suna nuna cewa su ma sun amince da ajin bawan ta yin amfani da ja-gora da suka samu daga Hukumar Mulki. Hakika, sa’ad da makiyaya suka koyar da wasu, suka ƙyale Kalmar Allah ta koyar da su, kuma suka yi amfani da koyarwa da ajin bawa ya yi tanadinsa, suna ɗaukaka haɗin kai tsakanin garken. Muna godiya cewa Jehobah ya koyar da maza da suke kula da waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista sosai!

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya makiyaya na ruhaniya da suka manyanta suke koyar da wasu?

• Me ya sa makiyaya ba sa koyarwa bisa nasu ra’ayin?

• Ta yaya makiyaya suke nuna sun amince da ajin bawa, kuma me ya sa?

[Hoto a shafi na 25]

Dattawa suna koyar da matasa maza cikin ikilisiya

[Hoto a shafi na 26]

“Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” na tanadin koyarwa da yawa don dattawa

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba