“Abin Da Ubangiji Ya Hurta” Ba Ya Kasawa
“Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta. Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne . . . Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai.”—ZABURA 2:7, 8.
1. Menene bambancin nufin Allah da na al’ummai?
JEHOVAH ALLAH yana da wata nufi game da ’yan Adam da kuma duniya. Al’ummai su ma suna da nufi. Amma, waɗannan nufe-nufe sun bambanta! Ya kamata mu yi tsammanin wannan, gama Allah ya ce: “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka al’amurana da tunanina suke nesa da naku.” Babu shakka, nufin Allah zai cika domin ya ci gaba da cewa: “Maganata kamar dusar ƙanƙara take, kamar kuma ruwan sama da ke saukowa domin ya jiƙe duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba, sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci. To, haka maganar da na faɗa take, ba ta kāsa cika abin da na shirya mata, za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.”—Ishaya 55:9-11.
2, 3. Menene aka bayyana sarai a zabura ta biyu, amma waɗanne tambayoyi aka yi?
2 An nuna sarai cewa wannan nufin Allah game da Sarkinsa Almasihu zai cika a zabura ta biyu. Allah ne ya hure Sarki Dauda na Isra’ila ta dā, wanda ya rera ta ya annabta cewa lokaci zai zo sa’ad da al’ummai za su yi tayarwa. Sarakunansu za su yi tayarwa gabā da Jehovah Allah da Zaɓaɓɓen Sarkinsa. Amma, mai Zabura ya kuma rera: “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta. Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne, . . . Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama taka.”—Zabura 2:7, 8.
3 Menene “abin da Ubangiji ya hurta” ke nufi ga al’ummai? Yaya wannan ya shafi galiban mutane? Menene waɗannan abubuwa suke nufi ga dukan masu tsoron Allah da suke karatun zabura ta biyu?
Al’ummai Suna Tayarwa
4. Ta yaya za ka taƙaita muhimman darussa na Zabura 2:1, 2?
4 Da yake nuni ga ayyukan al’ummai da sarakunansu, mai Zabura ya soma waƙarsa: “Don me al’ummai suke shirin tayarwa? Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun yi tayarwa, masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, gabā da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.”—Zabura 2:1, 2.a
5, 6. Al’ummai suna “ƙulla” waɗanne “shawarwarin banza”?
5 Wane “shawarwarin banza” al’ummai na zamani suke ‘ƙullawa’? Maimakon amince da Zaɓaɓɓen Sarkin Allah—Almasihu, ko Kristi—al’ummai suna “ƙulla,” ko yin bimbini yadda za su ci gaba a nasu ikon. Waɗannan kalmomi na zabura ta biyu sun cika a ƙarni na farko A.Z., lokacin da masu mulki na Yahuza da Roma suka haɗa kai su kashe Yesu Kristi, Sarki da Allah ya Zaɓa. Amma, cikawa na musamman ya soma a shekara ta 1914 sa’ad da aka naɗa Yesu Sarkin samaniya. Tun lokacin babu wani rukunin siyasa a duniya da ya amince da Sarkin da Allah ya naɗa.
6 Menene ake nufi sa’ad da mai zabura ya yi tambaya ‘don me al’ummai suke ƙulla shawarwarin banza’? Nufinsu ne abin banza, kuma ba zai yi nasara ba. Ba za su kawo salama da jituwa a duniya ba. Har suna wa sarautar Allah hamayya. Hakika, sun haɗa kai suna ƙiyayya da Maɗaukaki da Zaɓaɓɓen Sarkinsa. Wannan wauta ce!
Sarki Mai Nasara na Jehovah
7. Da suke addu’a, yaya mabiyan Yesu na farko suka yi amfani da Zabura 2:1, 2?
7 Mabiyan Yesu sun yi amfani da kalmomin Zabura 2:1, 2 game da shi. Da yake ana tsananta musu don bangaskiyarsu, sun yi addu’a: “Ya Mamallaki [Jehovah], Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu, wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce, ‘Don me al’ummai suka husata? Kabilai kuma suka yi makidar al’amuran wofi? Sarakunan duniya sun kafa dāga, Mahunkunta kuma sun haɗa kai, suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’ Gama hakika Hirudus [Antibas] da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al’ummai da jama’ar Isra’ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.” (Ayyukan Manzanni 4:24-27; Luka 23:1-12)b Hakika, an ƙulla wa Yesu bawan da Allah ya zaɓa a ƙarni na farko. Amma, wannan zabura za ta sake cika ƙarnuka nan gaba.
8. Ta yaya Zabura 2:3 ta shafi al’ummai na zamani?
8 Sa’ad da Isra’ila ta dā take da sarki na ’yan Adam kamar Dauda, al’umman arna da sarakuna sun haɗa kai gāba da Allah da zaɓaɓɓen sarkinsa da aka naɗa. Lokacinmu kuma fa? Al’ummai na zamani ba sa son su bi farillai na Jehovah da kuma Almasihun. Shi ya sa aka nuna suna cewa: “Bari mu ’yantar da kanmu daga mulkinsu, bari mu fice daga ƙarƙashinsu!” (Zabura 2:3) Sarakuna da al’ummai za su yi hamayya da kowane hani da Allah da Zaɓaɓɓen Sarkinsa suka yi. Hakika, duk ƙoƙarinsu su ’yantar da kansu kuma su fice daga ƙarƙashin Allah da sarkinsa zai zama banza.
Jehovah Ya Mai da Su Abin Dariya
9, 10. Me ya sa Jehovah ya mai da al’ummai abin dariya?
9 Ƙoƙarce-ƙoƙarcen sarakunan al’ummai su kafa nasu sarauta bai dami Jehovah ba. Zabura ta biyu ta ci gaba: “Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can sama, ya mai da su abin dariya.” (Zabura 2:4) Allah ya ci gaba da nufinsa kamar dai waɗannan sarakunan ba su da muhimmanci. Ya yi musu dariya don wautansu. Suna fahariyar abin da suke son su yi. A wajen Jehovah su abin dariya ne. Ya yi musu dariya don hamayyarsu na banza.
10 Wani wuri cikin zaburarsa, Dauda ya yi magana cewa mutane da al’ummai abokan gāba ne, ya rera: “Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni, ka tashi ka hukunta al’ummai, kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai! Da maraice suka komo, suna yaƙe haƙora kamar karnukan da ke yawo ko’ina a birni. Ji abin da suke faɗa! Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu, duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, ‘Wa zai ji mu?’ Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji, ka mai da al’ummai duka abin bandariya!” (Zabura 59:5-8) Jehovah ya yi wa al’ummai dariya don fahariyarsu da dimaucewa a ayyukansu na wauta, gāba da shi.
11. Me zai faru sa’ad da al’ummai suka yi ƙoƙari su kawar da nufin Allah?
11 Kalmomin Zabura ta 2 sun ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Allah zai iya magance kowace matsala. Za mu kasance da tabbaci cewa koyaushe yana cim ma nufinsa kuma ba ya yasar da bayinsa masu aminci. (Zabura 94:14) To, me zai faru sa’ad da al’ummai suka yi ƙoƙari su kawar da nufin Jehovah? Daidai da wannan zabura, Allah zai “yi musu magana da fushi” kamar tsawan aradu. Ƙari ga haka, “da hasalarsa” kamar haskakawar walƙiya zai “razanar da su.”—Zabura 2:5.
Allah Ya Naɗa Sarkinsa
12. Zabura 2:6 ta yi magana game da wane naɗawa ne?
12 Abin da Jehovah ya faɗi a gaba ta wurin mai Zabura babu shakka ya dami al’ummai. Allah ya ce: “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.” (Zabura 2:6) Dutsen Sihoyana tudu ne a Urushalima, inda aka naɗa Dauda sarki bisa Isra’ila. Amma Sarki Almasihu ba zai zauna a kan kursiyi a wannan birnin ko kuma wani waje a duniya ba. Hakika, Jehovah ya riga ya naɗa Yesu Kristi da ya zaɓa ya zama Sarkinsa Almasihu a Dutsen Sihiyona ta samaniya.—Wahayin Yahaya 14:1.
13. Wane alkawari ne Jehovah ya yi da Ɗansa?
13 Sarki Almasihu yanzu yana magana. Ya ce: “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta [wanda ya yi alkawarin Mulki da Ɗansa]. Ubangiji [Jehovah Allah] ya ce mini, ‘Kai ɗana ne, yau ne na zama mahaifinka.’ ” (Zabura 2:7) Kristi yana nuni ga alkawarin Mulki sa’ad da ya gaya wa manzanninsa: “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha. Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku iko.”—Luka 22:28, 29.
14. Me ya sa za a iya ce Yesu yana da ikon sarauta da babu wanda zai yi takara da shi?
14 Yadda aka annabta a Zabura 2:7, Jehovah ya nuna cewa Yesu, Ɗansa ne a lokacin da ya yi baftisma da kuma lokacin da ya tashe shi daga matattu zuwa rai na ruhu. (Markus 1:9-11; Romawa 1:4; Ibraniyawa 1:5; 5:5) Hakika, Sarkin Mulkin samaniya shi ne makaɗaicin Ɗan Allah. (Yahaya 3:16) Tun da yake ya fito daga zuriyar sarauta na Sarki Dauda, Yesu yana da matsayi da babu wanda zai yi takara da shi. (2 Sama’ila 7:4-17; Matiyu 1:6, 16) Bisa wannan zabura, Allah ya gaya wa Ɗansa: “Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama taka.”—Zabura 2:8.
15. Me ya sa Yesu ya ce a ba shi al’ummai su zama tasa?
15 Sarkin—Ɗan Allah—shi ne mai iko biye da Jehovah. Yesu tabbatacce ne na Jehovah kuma amini wanda ya isa a dogara gare shi. Ban da haka, Yesu ne magaji da yake shi ne Ɗan Fari na Allah. Hakika, Yesu Kristi “ne surar Allah marar ganuwa, magaji ne tun ba a halicci kome ba.” (Kolosiyawa 1:15) Abin da yake bukata ya yi shi ne ya faɗi kuma Allah ya ‘ba shi dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama tasa.’ Yesu ya yi wannan roƙo da yake shi ‘yana murna da ’yan Adam’ kuma domin yana son ya yi nufin Ubansa na samaniya game da duniya da ’yan Adam sosai.—Karin Magana 8:30, 31.
Abin da Jehovah Ya Hurta Game da Al’ummai
16, 17. Bisa Zabura 2:9, menene zai faru wa al’ummai?
16 Tun da yake zabura ta biyu tana cika yanzu, a lokacin bayyanuwar Yesu Kristi marar ganuwa, menene zai faru wa al’ummai? Sarkin ba da daɗewa ba zai cim ma shelar Allah: “Za ka mallake su [al’ummai] da sandan ƙarfe, za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.”—Zabura 2:9.
17 Sandan sarakuna na lokacin dā alamun ikon sarauta ne. Ana yin wasu sanduna da ƙarfe, kamar wanda wannan zaburar take maganarta. Yaren alama da aka yi amfani da shi a nan yana nuna cewa zai yi wa Sarki Kristi sauƙi ya halaka al’ummai. Idan aka buga yumɓu da ƙarfi da sandan ƙarfe, zai farfashe yadda ba za a iya gyaransa ba.
18, 19. Don Allah ya amince da su, menene sarakunan duniya suke bukatar su yi?
18 Sarakunan duniya za su shaida wannan halaka? A’a, domin mai Zabura ya roƙe su da waɗannan kalmomi: “Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna, ku mai da hankali ku mahukunta!” (Zabura 2:10) An gaya wa sarakuna su kasa kunne kuma su mai da hankali. Ya kamata su yi la’akari da ƙullinsu na banza, da ya yi dabam da abin da Mulkin Allah zai yi don amfanin ’yan Adam.
19 Don su sami amincewar Allah, sarakunan duniya suna bukatar su canja tafarkinsu. An gargaɗe su su ‘bauta wa Ubangiji da tsoro, su yi rawar jiki, su rusuna masa.’ (Zabura 2:11) Menene zai faru idan suka yi hakan? Maimakon su yi tayarwa, za su iya murna da bege da Sarki Almasihu zai sa a gabansu. Zai zama wajibi sarakunan duniya su bar fahariya da girman kai da suke yi a sarautarsu. Ƙari ga haka, ya kamata su canja babu ɓata lokaci kuma su mai da hankali game da mafificin ikon mallakar Jehovah da babu na biyunsa da kuma ikon da ba za a iya ƙi ba na Allah da Sarkinsa Almasihu.
“Ku Yi Ma Ɗa Sumba”
20, 21. Menene yake nufi a yi wa ‘ɗan sumba’?
20 Zabura ta 2 ta yi wa sarakunan al’ummai gayya mai kyau. Maimakon su haɗa kai suna hamayya, an yi musu gargaɗi: “Ku yi ma ɗa sumba, domin kada ya yi fushi, har kuwa ku lalace a hanya, gama ba wuya fushinsa za ya tashi.” (Zabura 2:12a; Litafi Mai-Tsarki) Ya kamata a yi biyayya da abin da Ubangiji Jehovah Mai Ikon Mallaka ya hurta. Ya kamata sarakunan duniya su daina “ƙulla shawarwarin banza” sa’ad da Allah ya ɗora Ɗansa a kan kursiyin. Ya kamata su amince da Sarkin nan da nan kuma su yi masa biyayya sosai.
21 Me ya sa za su “yi ma ɗa sumba”? Sa’ad da aka rubuta wannan zaburar, ana sumba don a nuna abokantaka kuma ana yinsa don a yi wa baƙi maraba cikin gidan mutum, inda za a yi musu liyafa. Sumba tana kuma nuna alamar aminci. (1 Sama’ila 10:1) A wannan aya ta zabura ta biyu, Allah yana ba al’ummai umurni su yi wa Ɗansa Sarki da aka zaɓa sumba, ko kuma maraba.
22. Ya kamata sarakunan al’ummai su yi biyayya da wane gargaɗi?
22 Waɗanda suka ƙi su amince da ikon Sarki da Allah ya zaɓa suna zargin Jehovah. Ba su yarda ba cewa Jehovah Allah ne mamallakin dukan sararin samaniya, ba su kuma yarda ba cewa yana da iko da iyawar ya zaɓi Sarki da ya fi ma ’yan Adam kyau. Sarakunan al’ummai za su gane cewa hasalar Allah zai sha kansu farat ɗaya, sa’ad da suke ƙoƙari su yi abin da suka ƙulla. “Ba wuya fushinsa za ya tashi,” ko kuma ya yi hasala da sauri kuma ba zai yiwu a ƙi ba. Ya kamata sarakunan al’ummai su yi godiya su yarda da wannan gargaɗin kuma su aikata cikin jituwa da shi. Yin hakan zai sa su sami rai.
23. Akwai lokaci har ila da mutane za su yi menene?
23 Wannan zabura ta alama ta kammala: “Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi [Jehovah] neman mafaka!” (Zabura 2:12b) Har ila mutane suna da lokaci da za su tsira. Hakan ma zai faru wa sarakuna ɗaɗɗaya da suke goyon bayan ƙullin al’ummai. Suna iya ruga zuwa wurin Jehovah, wanda yake tanadin mafaka ta sarautar Mulki. Amma dole su aikata kafin Mulkin Almasihu ya halaka al’ummai masu hamayya.
24. Ta yaya za mu fi yin rayuwa mai ma’ana har ma a wannan duniya da ta wahala?
24 Idan muna nazarin Nassosi da kyau kuma muna amfani da gargaɗinsu a rayuwa, za mu yi rayuwa mai gamsarwa yanzu ma a wannan duniya da ta wahala. Yin amfani da gargaɗi na Nassi na sa iyalai su yi dangantaka ta farin ciki kuma ba za su damu da wahaloli da tsoro da wannan duniya ke fuskanta ba. Bin farillan Littafi Mai Tsarki na sa mu kasance da tabbaci cewa muna faranta wa Mahalicci rai. Idan ba Mamallakin Dukan Halitta ba, babu wani da zai iya ba da tabbacin “rai na yanzu da na nan gaba” bayan ya kawar da waɗanda suke tsayayya da abin da ke daidai ta wurin ƙin sarautar Mulkin.—1 Timoti 4:8.
25. Tun da yake “abin da Ubangiji ya hurta” ba ya kasawa, menene za mu yi tsammanin zai faru a lokacinmu?
25 “Abin da Ubangiji ya hurta” ba ya kasawa. Da yake shi ne Mahaliccinmu, Allah ya san abin da ya fi dacewa da ’yan Adam kuma zai cika nufinsa na yi wa mutane masu biyayya albarka ta wurin kawo musu salama, wadar zuci, da kwanciyar rai na dindindin a Mulkin Ɗansa ƙaunatacce. Game da lokacinmu, annabi Daniyel ya rubuta: “A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, . . . zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.” (Daniyel 2:44) Saboda haka, lokaci ne yanzu na “yi ma ɗa sumba” kuma a bauta wa Ubangiji Jehovah Mai Ikon Sarauta!
[Hasiya]
a Da farko, Sarki Dauda ne “zaɓaɓɓen sarkinsa” kuma sarakunan Filistiyawa da suka shirya maƙarƙashiya tare gabā da shi su ne “sarakunan duniya.”
b Wasu ayoyi na Nassosin Kirista na Helenanci sun kuma nuna cewa Yesu ne Zaɓaɓɓen Sarki na Allah da aka yi maganarsa a zabura ta biyu. Za a ga wannan idan an kwatanta Zabura 2:7 da Ayyukan Manzanni 13:32, 33 da kuma Ibraniyawa 1:5; 5:5. Ka kuma duba Zabura 2:9 da Wahayin Yahaya 2:27.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane “shawarwarin banza” ne sarakunan al’ummai suke ‘ƙullawa’?
• Me ya sa Jehovah ya mai da al’ummai abin dariya?
• Menene Allah ya hurta game da al’ummai?
• Menene yake nufi a “yi ma ɗa sumba”?
[Hoto a shafi na 12]
Dauda ya rera game da Sarki Almasihu mai nasara
[Hoto a shafi na 13]
Sarakuna da mutanen Isra’ila suka ƙulla wa Yesu Kristi
[Hoto a shafi na 14]
An naɗa Kristi Sarki a Dutsen Sihiyona na samaniya