Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 pp. 3-6
  • “Idanun” Jehobah Suna Duban Dukan ’Yan Adam

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Idanun” Jehobah Suna Duban Dukan ’Yan Adam
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Ganin Zuciya
  • Yin Bincike Cikin Ƙauna
  • Jehobah Yana Ganin Kome kuma Yana Aikatawa Yadda Ya Kamata
  • Babu Zunubi da Za a Iya Ɓoyewa
  • Ka Kasance da Aminci a Kowane Lokaci
  • Ka Kasance da Sahihiyar Zuciya
  • Fushi Ya Jawo Kisan Kai
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ɗan Kirki, Da Kuma Mugun Ɗa
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Ya Sa Bai Kamata Mu Yi Karya Ba
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • A Ina ne Kayinu Ya Sami Matarsa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 pp. 3-6

“Idanun” Jehobah Suna Duban Dukan ’Yan Adam

“Idanun [Jehobah] suna duban yan adam.”—ZAB. 11:4.

1. Waɗanne irin mutane ne muke so mu yi kusa da su?

YAYA kake ji game da mutanen da suka nuna suna son ka? Suna faɗin gaskiya idan ka yi musu tambaya. Suna shirye su taimake ka sa’ad da kake bukatar taimako. Suna ba ka shawara a cikin ƙauna sa’ad da kake bukatar haka. (Zab. 141:5; Gal. 6:1) Abin farin ciki ne ka kusaci irin waɗannan mutanen. Hakika, Jehobah da Ɗansa suna ƙaunarka. Ƙaunar da suke yi maka ta fi ta mutane, kuma muraɗin su ba na son kai ba ne; suna son su taimake ka ka sami “hakikanin rai.”—1 Tim. 6:19; R. Yoh. 3:19.

2. Wace irin ƙauna ce Jehobah yake nuna wa bayinsa?

2 Mai zabura Dauda ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu sosai, sa’ad da ya ce: “Idanun [Jehobah] suna duban ’yan adam, maƙyaptansa suna gwada su.” (Zab. 11:4) Hakika, Allah ba ya kallonmu kawai, amma yana gwada mu. Dauda ya rubuta: “Kā rigaya ka innace zuciyata; kā ziyarce ni da dare; . . . Na ƙudurta bakina ba za shi saɓa ba.” (Zab. 17:3) Hakika, Dauda ya san cewa Jehobah yana ƙaunarsa sosai. Ya san cewa zai iya ɓata wa Jehobah rai kuma ya sa Jehobah ya ƙi shi idan bai kawar da mugun tunani a zuciyarsa ba. Kamar Dauda, ka gaskata cewa Jehobah yana wanzuwa?

Jehobah Yana Ganin Zuciya

3. Ta yaya ne Jehobah ya nuna cewa ya fahimci kasawarmu?

3 Ainihin abin da Jehobah yake sha’awar sani shi ne yanayin zuciyarmu. (Zab. 19:14; 26:2) Ba ya mai da hankali a kan kowane irin kasawa. Alal misali, sa’ad da Saratu matar Ibrahim ta yi wa mala’ika ƙarya, mala’aikan ya ga cewa tana jin tsoro ne ko kuma tana jin kunya ne, shi ya sa ya ɗan gargaɗe ta. (Far. 18:12-15) Duk da cewa Ayuba uban iyali ya ga kamar ya fi “Allah gaskiya,” Jehobah ya albarkace shi, don ya san cewa Ayuba ya wahala sosai a hannun Shaiɗan. (Ayu. 32:2; 42:12) Hakazalika, Jehobah bai yi fushi saboda abin da gwauruwa ’yar Zarephath ta ce wa annabi Iliya ba. Allah ya fahimci cewa tana baƙin cikin mutuwar ɗanta ne.—1 Sar. 17:8-24.

4, 5. Ta yaya ne Jehobah ya nuna wa Abimelech alheri?

4 Saboda Jehobah yana bincika zuciyarmu, hakan ya sa yana nuna jin ƙai har ga marasa bi. Yi la’akari da labarin Abimelech, sarkin birnin Falasɗinu da ke Gerar. Abimelech bai san cewa Saratu matar Ibrahim ce ba, sai ya ɗauki Saratu ta zama matarsa. Amma kafin Abimelech ya yi jima’i da ita, a cikin mafarki Jehobah ya ce masa: “I, na sani cikin sahihancin zuciyarka ka yi wannan, ni kuwa na hana ka da ba za ka yi mani zunubi ba: domin wannan ban bar ka ka shafe ta ba. Yanzu fa sai ka mayasda matar mutumin; gama annabi ne shi, za ya kuwa yi maka addu’a, za ka rayu kuma.”—Far. 20:1-7.

5 Hakika, da Jehobah ya hukunta Abimelech mai bauta wa allolin ƙarya. Amma Allah ya ga cewa mutumin ya yi abin da ya kamata a wannan lokaci. Da ya ga haka, sai Jehobah ya gaya wa sarkin yadda zai sami gafara kuma ya “rayu.” Ba irin wannan Allah ba ne kake so ka bauta wa?

6. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya yi koyi da Ubansa?

6 Yesu ya yi koyi da Ubansa sosai, ya mai da hankali ga halaye masu kyau na almajiransa kuma ya gafarta musu kurakuransu. (Mar. 10:35-45; 14:66-72; Luk 22:31, 32; Yoh. 15:15) Halayen Yesu sun jitu da kalmominsa da ke Yohanna 3:17: “Allah ya aiko Ɗan cikin duniya ba domin shi yi ma duniya shari’a ba; amma domin duniya ta tsira ta wurinsa.” Hakika, Jehobah da Yesu suna ƙaunarmu sosai a koyaushe. Suna so su ga mun sami rai. (Ayu. 14:15) Irin wannan ƙaunar ta nuna abin da ya sa Jehobah yake bincika mu, yadda yake ɗaukanmu da kuma yadda yake aikata bisa abin da yake gani.—Ka karanta 1 Yohanna 4:8, 19.

Yin Bincike Cikin Ƙauna

7. Da wane irin ra’ayi ne Jehobah yake bincika mu?

7 Ba zai dace ba mu ɗauki Jehobah a matsayin wanda yake kallon mu don ya kama mu muna zunubi ba. Shaiɗan ne yake zarginmu kuma ya ce muna son kai. (R. Yoh. 12:10) Yana ma zargin mutane a kan abin da ba su yi ba. (Ayu. 1:9-11; 2:4, 5) Mai zabura ya rubuta game da Allah: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zab. 130:3) Amsar ita ce, babu wanda zai iya tsayawa. (M. Wa. 7:20) Maimakon haka, Jehobah yana nuna mana jin ƙai da alheri kamar uba da yake kiyaye yaransa daga mugunta. Sau da yawa yana tuna mana ajizancinmu da kuma kasawarmu don mu guji la’anta kanmu.—Zab. 103:10-14; Mat. 26:41.

8. Ta yaya Jehobah yake koyar da bayinsa kuma yake yi musu horo?

8 Allah yana nuna ƙaunarsa ta wurin horo da umurnin da ke cikin Nassosi da kuma abinci na ruhaniya da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake tanadinsa. (Mat. 24:45; Ibran. 12:5, 6) Jehobah kuma yana taimako ta wurin ba da umurni ta hanyar ikilisiyar Kirista da kuma “kyautai ga mutane.” (Afis. 4:8) Bugu da ƙari, Jehobah yana kallo ya ga yadda za mu yi biyayya ga umurninsa, don ya ci gaba da taimakonmu. Zabura 32:8 ta ce: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” Yana da muhimmanci mu saurari Jehobah a koyaushe. Ya kamata mu kasance da tawali’u a gabansa a koyaushe, da sanin cewa shi ne Ubanmu da Malaminmu mai ƙauna.—Ka karanta Matta 18:4.

9. Waɗanne halaye ne ya kamata mu guje wa, kuma me ya sa?

9 Bugu da ƙari, kada mu bari fahariya, rashin bangaskiya, ko kuma “rikicin zunubi” su sa mu zama masu taurin kai. (Ibran. 3:13; Yaƙ. 4:6) Sau da yawa irin waɗannan halayen suna somawa ne idan mutum ya yi tunanin abubuwa marasa kyau. Hakan zai sa ya soma ƙin umurni daga cikin Nassi. Mafi muni ma, zai nace ga mugun halayensa da za su sa ya zama maƙiyin Allah, hakika wannan yanayi ne mai ban tsoro. (Mis. 1:22-31) Yi la’akari da misalin Kayinu, ɗan fari na Adamu da Hauwa’u.

Jehobah Yana Ganin Kome kuma Yana Aikatawa Yadda Ya Kamata

10. Me ya sa Jehobah ya ƙi hadayar Kayinu, kuma menene Kayinu ya yi?

10 Sa’ad da Kayinu da Habila suka kawo hadayarsu ga Jehobah, ba kyauta kaɗai yake so ba, amma dalilin da ya sa suka ba da kyautar. A sakamakon haka, Allah ya nuna ya amince da hadayar da Habila ya bayar cikin bangaskiya, amma bai amince da ta Kayinu ba don ya nuna rashin bangaskiya. (Far. 4:4, 5; Ibran. 11:4) Maimakon ya koyi darasi daga abin da ya faru kuma ya canja halinsa, Kayinu ya ji haushin ɗan’uwansa sosai.—Far. 4:6.

11. Ta yaya ne Kayinu ya nuna zuciya mai rikici, kuma menene muka koya?

11 Jehobah ya lura cewa Kayinu ba shi da hali mai kyau, kuma ya gaya masa cewa idan ya canja halinsa, zai yi farin ciki. Abin baƙin ciki, Kayinu ya ƙi bin umurnin Mahaliccinsa kuma ya kashe ɗan’uwansa. Kayinu ya nuna mugun zuciyarsa sa’ad da ya amsa tambayar da Allah ya yi masa: “Ina Habila ƙanenka? Ya ce, ban sani ba: ni mai-tsaron ƙanina ne?” (Far. 4:7-9) Zuciya tana iya rinjayarmu, har ta sa mu ƙi umurnin Allah. (Irm. 17:9) Bari mu yi koyi daga irin waɗannan labaran kuma mu ƙi tunani da sha’awa marasa kyau. (Ka karanta Yaƙub 1:14, 15.) Idan aka ba mu shawara daga cikin Nassi, ya kamata mu ɗauke ta a matsayin ƙauna daga wurin Jehobah.

Babu Zunubi da Za a Iya Ɓoyewa

12. Wane mataki ne Jehobah yake ɗauka game da masu yin abubuwa marasa kyau?

12 Wasu suna ganin cewa idan babu wanda ya gan su, ba za a yi musu horo ba. (Zab. 19:12) Da gaske, babu zunubi da za a iya ɓoyewa. “Abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibran. 4:13) Jehobah alƙali ne da yake bincika ra’ayinmu, kuma yadda yake hukunta masu yin abubuwa marasa kyau ya nuna cewa shi mai adalci ne. Shi “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” Duk da haka, “ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan” sa’ad da ya yi ‘zunubi da nufin zuciyarsa’ ko kuma ya yi cuku-cuku. (Fit. 34:6, 7; Ibran. 10:26) Jehobah ya nuna hakan a matakin da ya ɗauka a kan Achan, Hananiya da Safiratu.

13. Ta yaya ne tunani marar kyau ya sa Achan ya yi sata?

13 Ta wajen ketare dokar Allah da gangan, Achan ya ɗauki kaya daga birnin Jericho kuma ya ɓoye su a cikin tantinsa da haɗin kan iyalinsa. Sa’ad da aka fallasa zunubinsa, Achan ya nuna cewa abin da ya yi ba shi da kyau, sa’ad da ya ce: “Na yi ma Ubangiji, Allah . . . zunubi.” (Josh. 7:20) Kamar Kayinu, Achan ya kasance da zuciya marar kyau. Haɗama ce ta sa Achan ya yi sata, kuma hakan ya sa shi ya kasance marar gaskiya. Tun da kayayyakin da ke Jericho na Jehobah ne, Achan ya yi wa Allah sata, hakan ya sa shi da iyalinsa suka rasa ransu.—Josh. 7:25.

14, 15. Me ya sa ya dace da Allah ya ƙi Hananiya da Safiratu, kuma wane darassi ne muka koya daga wannan?

14 Hananiya da matarsa Safiratu suna cikin ikilisiyar Kirista a Urushalima. Bayan Fentakos na shekara ta 33 K.Z., an ce a tara kuɗi don a kula da sababbi da suka zama masu bi daga ƙasa mai nisa da suka rage a Urushalima. An sami kuɗin ta wurin gudummawa. Hananiya ya sayar da fili ya ba da rabin kuɗin. Amma da sanin matarsa sai ya nuna kamar ya ba da duka kuɗin. Babu shakka, waɗannan ma’aurata suna son ikilisiyar ta yaba musu sosai. Amma ƙarya suka yi. Ta hanyar mu’ujiza, Jehobah ya gaya wa manzo Bitrus cewa ƙarya ce suka yi, Bitrus kuwa ya tambayi Hananiya dalilin da ya sa ya yi ƙarya. Bayan haka, Hananiya ya faɗi a ƙasa ya mutu. Daga baya sai Safiratu ta mutu.—A. M. 5:1-11.

15 Kumamancin Hananiya da Safiratu ba na ɗan lokaci ba ne. Sun shirya ne su yi ƙarya don su ruɗi manzannin. Mafi muni, sun ‘yi ma Ruhu Mai tsarki da Allah ƙarya.’ Jehobah ya nuna sarai cewa yana shirye ya kāre ikilisiyar daga munafukai. Hakika, “abin ban tsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai-rai.”—Ibran. 10:31.

Ka Kasance da Aminci a Kowane Lokaci

16. (a) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin ya ɓata mutanen Allah? (b) Waɗanne hanyoyi ne Iblis yake amfani da su don ya ɓata mutane da ke yankinku?

16 Shaiɗan yana iya ƙoƙarinsa don ya ɓata mu kuma ya sa mu yi rashin tagomashin Jehobah. (R. Yoh. 12:12, 17) Ana ganin mugun nufin Iblis a cikin duniya da ta cika da lalata da kuma mugunta. Ana iya ganin batsa da sauƙi yanzu ta wurin kwamfuta da kuma wasu na’urori. Kada mu faɗa wa farmakin Shaiɗan. Maimakon haka, bari furcinmu ya zama kamar na mai zabura Dauda, da ya rubuta: “Da azanci zan lura da al’amurana cikin tafarki kamili . . . Cikin kamalar zuciya zan yi tafiya a cikin gidana.”—Zab. 101:2.

17. (a) Me ya sa Jehobah yake fallasa zunubai da ke ɓoye? (b) Menene ya kamata ya zama ƙudurinmu?

17 A yau, Jehobah ba ya fallasa zunubi mai tsanani da kuma mugun hali ta hanyar mu’ujiza kamar yadda ya yi a dā. Duk da haka, yana ganin kome kuma a nasa lokaci da kuma hanyarsa zai fallasa abubuwa da ke ɓoye. Bulus ya ce: “Zunuban waɗansu mutane a sarari su ke, suna yin gaba zuwa hukunci; waɗansu kuwa suna bin baya.” (1 Tim. 5:24) Ƙauna ce ainihin dalilin da ya sa Jehobah yake fallasa ayyuka marasa kyau. Yana ƙaunar ikilisiya kuma yana son ya tsare tsarkinta. Bugu da ƙari, yana nuna jin ƙai ga waɗanda suka yi zunubi amma suka tuba da gaske. (Mis. 28:13) Saboda haka, bari mu yi ƙoƙari mu kasance da zuciya ɗaya da Allah kuma mu ƙi dukan lalatattun tasiri.

Ka Kasance da Sahihiyar Zuciya

18. Yaya Sarki Dauda yake son ɗansa ya ji game da Allah?

18 Sarki Dauda ya gaya wa ɗansa Sulemanu: “Ka san Allah na ubanka, ka bauta masa da sahihiyar zuciya da yardan rai kuma: gama Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan siffofin tunani.” (1 Laba. 28:9) Dauda yana son ɗansa ya gaskata cewa akwai Allah kuma ya ƙaunace shi. Yana son Sulemanu ya fahimci yawan yadda Jehobah yake ƙaunar bayinsa. Kana godiya da yadda Jehobah yake ƙaunar bayinsa ne?

19, 20. Bisa ga Zabura 19:7-11, menene ya taimaki Dauda ya kusaci Allah, kuma yaya za mu yi koyi da Dauda?

19 Jehobah ya san cewa mutane masu zuciyar kirki za su kusace shi kuma sanin halayensa masu kyau zai sa su yi kusa da shi. Shi ya sa Jehobah yake son mu san shi kuma mu san halayensa masu kyau. Ta yaya za mu yi hakan? Ta wurin nazarin Kalmarsa da kuma ganin albarkarsa a rayuwarmu.—Mis. 10:22; Yoh. 14:9.

20 Kana karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma ka fahimci cewa daga wajen Allah ne, kuma ka yi addu’a ya taimake ka ka bi umurninsa? Ka ga amfanin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? (Ka Karanta Zabura 19:7-11.) Idan haka ne, bangaskiyarka ga Jehobah da kuma ƙaunarka za su ƙaru. Shi kuma zai kusace ka, kamar yana tafiya tare da kai. (Isha. 42:6; Yaƙ. 4:8) Hakika, Jehobah zai nuna yana ƙaunarka ta wurin yi maka albarka da kuma kāre ka a ruhaniya sa’ad da kake tafiya a matsatsiyar hanya ta rayuwa.—Zab. 91:1, 2; Mat. 7:13, 14.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa Jehobah yake gwada mu?

• Menene ya sa wasu mutane suka zama abokan gaban Allah?

• Ta yaya za mu nuna mun yarda cewa Jehobah ya wanzu?

• Ta yaya za mu kasance da sahihiyar zuciya ga Allah?

[Hoto a shafi na 5]

Wane darassi muka koya daga misalin Hananiya?

[Hoto a shafi na 6]

Menene zai taimake mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba