Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
    • 3. Wane aiki ne Kiristoci na gaske suke yi?

      Yesu ya ba almajiransa aiki. “Ya . . . aike su su je su yi wa’azin mulkin Allah.” (Luka 9:2) Ba a wuraren ibada ne kawai Kiristoci na farko suka yi wa’azi ba, amma sun je wasu wurare har da gidajen mutane. (Karanta Ayyukan Manzanni 5:42; 17:17.) Kiristoci na gaske a yau ma suna wa’azi a duk inda suka sami mutane. Suna amfani da lokaci da kuzarinsu wajen koya wa mutane abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki don suna ƙaunar su. Hakan zai sa su sami bege kuma zai ƙarfafa su.—Markus 12:31.

  • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Dadi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
    • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Daɗi?

      Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don ya kawar da matsalolinmu. Wannan albishiri ne da ya kamata kowa ya ji. Yesu ya umurci mabiyansa su gaya wa kowa wannan albishirin! (Matiyu 28:​19, 20) Ta yaya Shaidun Jehobah suke bin umurnin Yesu?

      1. Ta yaya littafin Matiyu 24:14 take cika a yau?

      Yesu ya ce: “Za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma.” (Matiyu 24:14) Shaidun Jehobah suna farin cikin yin wannan aiki mai muhimmanci. Muna wa’azi a faɗin duniya a harsuna fiye da 1,000! Ana bukatar a tsara wannan gagarumin aiki da kyau. Jehobah ne yake taimaka mana mu yi hakan.

      2. Wane ƙoƙari ne muke yi don mu yi wa mutane wa’azi?

      Muna yin wa’azi a duk inda muka sami mutane. Kamar Kiristoci a ƙarni na farko, muna wa’azi “gida-gida.” (Ayyukan Manzanni 20:20) Hakan yana ba mu damar yi wa miliyoyin mutane wa’azi a kowace shekara. A wasu lokuta, mukan je wa’azi a wuraren da jama’a suke, da yake ba a koyaushe muke samun mutane a gida ba. A kowane lokaci, muna neman zarafin gaya wa mutane game da Jehobah da kuma nufinsa.

      3. Su waye ne ya kamata su riƙa yin wa’azi?

      Ya kamata dukan Kiristoci na gaske su yi wa’azi. Muna ɗaukan wannan hidimar da muhimmanci. Muna iya ƙoƙari mu yi wa mutane wa’azi domin mun san hakan zai iya sa su sami ceto. (Karanta 1 Timoti 4:16.) Ba a biyan mu kuɗi don wannan hidimar. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kun samu a kyauta, ku kuma bayar kyauta.” (Matiyu 10:​7, 8) Ba dukan mutane ne suke sauraron wa’azinmu ba. Duk da haka, za mu ci gaba da yin wa’azi domin ta yin hakan muna yi wa Jehobah biyayya kuma muna sa shi farin ciki.

      KA YI BINCIKE SOSAI

      Za mu koyi abubuwan da Shaidun Jehobah suke yi don su yi wa’azi a faɗin duniya da kuma yadda Jehobah yake taimaka mana.

      A. Shaidu biyu suna yi wa wani mutum wa’azi a wani tudu mai ciyayi a Costa Rica. B. Shaidu hudu suna yi wa masu kamun kifi wa’azi a gabar teku da ke Amirka. C. Shaidu biyu suna yi wa wani mutum wa’azi a kauye a Benin. D. Wata Mashaidiya tana yi wa wata mata mai sayar da kaya a kwalekwale wa’azi a Thailand. E. Shaidu biyu suna yi wa wata mata wa’azi a gaban wani babban dutse a Yap. F. Shaidu biyu suna yi wa wata mata wa’azi a wuri mai dusar kankara kusa da hanyar ruwa a Sweden.

      Wa’azi a faɗin duniya: (A) Costa Rica, (B) Amirka, (C) Benin, (D) Thailand, (E) Yap, (F) Sweden

      4. Muna ƙoƙari sosai don mu yi wa dukan mutane wa’azi

      Shaidun Jehobah suna iya ƙoƙarinsu don su yi wa mutane wa’azi a ko’ina. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

      BIDIYO: Sun Yaɗa Bishara a ‘Iyakar Duniya’ (7:33)

      • Me ya burge ka game da ƙoƙarin da Shaidun Jehobah suke yi don su yi wa’azi?

      Ku karanta Matiyu 22:39 da Romawa 10:13-15, sai ku tattauna tambayoyin nan:

      • Ta yaya wa’azin da muke yi ya nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu?

      • Yaya Jehobah yake ganin masu yin wa’azi?​—Ka duba aya ta 15.

      5. Mu abokan aikin Allah ne

      Labaran ’yan’uwanmu da yawa sun nuna cewa Jehobah ne yake yi wa aikinmu ja-goranci. Alal misali wata rana da safe, wata mata a ƙasar New Zealand ta yi amfani da sunan Allah wato Jehobah sa’ad da take addu’a, ta roƙe shi cewa tana so wani ya zo ya yi mata wa’azi. Da rana, wato awa uku bayan ta yi addu’a, sai ga wani ɗan’uwa mai suna Paul a ƙofar gidanta ya zo ya yi mata wa’azi.

      Ku karanta 1 Korintiyawa 3:​9, sai ku tattauna tambayar nan:

      • Ta yaya labarai kamar na wannan ɗan’uwan a New Zealand suka nuna cewa Jehobah ne yake mana ja-goranci a wa’azi?

      Ku karanta Ayyukan Manzanni 1:​8, sai ku tattauna tambayar nan:

      • Me ya sa muke bukatar taimakon Jehobah don mu yi nasara a hidimarmu?

      Ka sani?

      A kowane taron tsakiyar mako, ana koya mana yadda za mu yi wa’azi da kyau. Idan ka taɓa halartar taron nan, me ra’ayinka game da yadda ake koyar da mu?

      Shaidun Jehobah guda biyu suna nuna yadda za a yi wa’azi a wani taron ikilisiya.

      6. Muna bin umurnin Allah cewa mu yi wa’azi

      A ƙarni na farko, masu tsananta wa mabiyan Yesu sun yi ƙoƙari su hana su yin wa’azi. Kiristoci na farko sun yi ƙoƙari su kāre ’yancinsu na yin wa’azi “ta wurin kāre labarin nan mai daɗi.” (Filibiyawa 1:7) Shaidun Jehobah suna yin hakan a yau.a

      Ku kalli BIDIYON nan.

      BIDIYO: Kāre Labarin nan Mai Daɗi (2:28)

      Ku karanta Ayyukan Manzanni 5:27-42, sai ku tattauna tambayar nan:

      • Me ya sa ba za mu daina yin wa’azi ba?​—Ka duba ayoyi na 29 da 38 da kuma 39.

      WANI YANA IYA CEWA: “Me ya sa Shaidun Jehobah suke wa’azi gida-gida?”

      • Me za ka ce masa?

      TAƘAITAWA

      Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi wa’azi a dukan duniya. Jehobah yana taimaka wa mutanensa don su yi wannan aikin.

      Bita

      • Ta yaya ake wa’azi a dukan duniya?

      • Ta yaya hidimarmu ta nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu?

      • Yin wa’azi yana sa mu farin ciki ne? Me ya sa?

      Maƙasudi

      KA BINCIKA

      Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Shaidun Jehobah suke wa’azi a manyan birane.

      Yin Wa’azi da Amalanke a Paris (5:11)

      Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da Shaidun Jehobah suka yi don su taimaka wa ’yan gudun hijira.

      Biyan Bukatun Masu Gudun Hijira (5:59)

      Ku kalli bidiyon nan don ku ji yadda hidima ta cikakken lokaci ta taimaka wa wata mata ta riƙa farin ciki.

      Na Yi Murna da Na Zaɓi Wannan Hidimar (6:29)

      Ku karanta talifin nan don ku ga nasara da yawa muka yi a kotu da suka sa ya yi mana sauƙi mu riƙa wa’azi.

      “Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu” (Mulkin Allah Yana Sarauta!, babi na 13)

      a Allah ne ya ba mu ikon yin wa’azi. Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa bukatar izinin hukumomin ’yan Adam don su yi wa’azi.

Littattafan Hausa (1987-2025)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba