Babi Na Biyar
’Yanci da Masu Bauta wa Jehovah Suke Morewa
1, 2. (a) Wane irin ’yanci Allah ya ba wa mutane biyu na farko? (b) Ka ambata wasu cikin dokoki da suka ja-goranci ayyukan Adamu da Hauwa’u.
SA’AD da Jehovah ya halicci mace da namiji na farko, sun more ’yancin da ya fi wani ’yanci da wani bil Adam yake da shi a yau. Gidansu Aljanna ce, kyakkyawar Lambun Adnin. Babu ciwo da ke damun rayuwarsu, domin suna da kamiltattun azantai da jikuna. Mutuwa ba ta jiransu kamar yadda take jiran kowa tun daga lokacin. Kuma, su ba ’yar tsana ba ne, amma suna da babbar kyauta ta ’yanci, iya tsai da tasu shawara. Amma, domin su ci gaba da morar ’yanci mai kyau haka, suna bukatar yin biyayya ga dokokin Allah.
2 Alal misali, ka lura da dokoki na zahiri da Allah ya kafa. Hakika, ba zai zama an rubuta waɗannan dokoki ba, amma an halicci Adamu da Hauwa’u a hanyar da za su yi musu biyayya. Yunwa tana nuna ya kamata su ci abinci; ƙishi, suna bukatar ruwa; faɗuwar rana, suna bukatar barci. Jehovah kuma ya ba su aikin yi. Aikin hakika doka ne, domin zai ja-goranci ayyukansu. Za su haifi ’ya’ya, su mallaki iri-irin rayuka a duniya su faɗaɗa iyakar Aljanna har sai ta kai dukan duniya. (Farawa 1:28; 2:15) Lallai, dokar tana da amfani! Ya ba su aiki mai gamsarwa ƙwarai, ya sa su yi amfani da hankalinsu ƙwarai a hanya mai kyau. Har ila, suna da ’yanci su tsai da shawarwari yadda za su cika aikinsu. Me suke bukata kuma?
3. Ta yaya Adamu da Hauwa’u suka koyi su yi amfani da kyau da ’yancinsu na tsai da shawarwari?
3 Hakika, da aka ba Adamu da Hauwa’u gatar tsai da shawara, wannan ba ya nufi cewa kowacce shawara da suka tsai da za ta zama mai kyau. ’Yancinsu na tsai da shawarwari za su yi amfani da shi ne daidai cikin jituwa da dokoki da kuma ƙa’idodin Allah. Ta yaya za su koyi waɗannan? Ta wurin sauraron Mahaliccinsu da yin nazarin ayyukansa. Allah ya ba Adamu da Hauwa’u haziƙanci da suke bukata don yin amfani da abin da suka koya. Da yake an halicce su kamiltattu, halinsu zai kasance irin na Allah sa’ad da suke tsai da shawarwari. Babu shakka, za su mai da hankali don su yi hakan idan suna da godiya ga abin da Allah ya yi musu da son su faranta masa rai.—Farawa 1:26, 27; Yohanna 8:29.
4. (a) Umurni da aka ba wa Adamu da Hauwa’u kada su ci ɗaya cikin itatuwa bai hana su sukuni ba ne? (b) Me ya sa wannan farilla ce da ta dace?
4 Daidai kuwa, sai Allah ya zaɓi ya gwada ibadarsu gare shi Mai Ba Su Rai da kuma aniyarsu su kasance cikin iyaka da ya kafa musu. Jehovah ya yi wa Adamu wannan umurnin: “An yarda maka ka ci daga kowanne itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:16, 17) Bayan da aka halicci Hauwa’u ita ma, an sanar mata wannan dokar. (Farawa 3:2, 3) Wannan hanin ya hana su sukuni ne? A’a. Suna da abinci masu kyau iri-iri a yalwace da za su ci ba tare da sun ci wancan itacen ba. (Farawa 2:8, 9) Ya kamata fa su fahimci cewa duniyar ta Allah ce, tun da yake shi ya halicce ta. Saboda haka, yana da iko ya kafa dokoki da sun yi daidai da nufinsa kuma da za su amfani mutane.—Zabura 24:1, 10.
5. (a) Ta yaya Adamu da Hauwa’u suka yi hasarar ’yanci mai kyau da suke da shi? (b) Menene ya ɗauki matsayin ’yanci da Adamu da Hauwa’u suka more, kuma ta yaya wannan ya shafe mu?
5 Amma me ya faru? Saboda dogon buri na son kai, wani mala’ika ya lalata ’yancinsa kuma ya zama Shaiɗan, wanda yake nufin “Mai-Hamayya.” Ya ruɗi Hauwa’u ta wajen tabbatar mata da abin da ya saɓa da nufin Allah. (Farawa 3:4, 5) Adamu ya haɗa hannu da Hauwa’u suka taka dokar Allah. Ta wajen ɗaukan abin da ba nasu ba, suka yi hasarar ’yancinsu mai girma. Zunubi ya zama shugabansu, kuma kamar yadda Allah ya yi gargaɗi, a ƙarshe mutuwa ta biyo baya. Gadōn da suka bar wa ’ya’yansu ke nan zunubi—yana bayyane cikin nufi da ke cikinsu na mugunta. Zunubi kuma ya zo da wasu kumamanci da ke kawo cuta, tsufa, da kuma mutuwa. Nufi na aikata mugunta, ƙari ga tasirin Shaiɗan, ya sa an sami jam’iyyar mutane da suke da tarihi da ke cike da aikata laifi, zalunci, da kuma yaƙe-yaƙe da sun ci miliyoyin rayuka. Lallai ya saɓa wa ’yanci da Allah ya ba mutane da farko!—Kubawar Shari’a 32:4, 5; Ayuba 14:1, 2; Romawa 5:12; Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Inda Za a Iya Samun ’Yanci
6. (a) A ina za a iya samun ’yanci na gaske? (b) Wane irin ’yanci ne Yesu ya yi maganarsa?
6 Saboda munanan yanayi da ya cika ko’ina a yau, ba abin mamaki ba ne da mutane suna da muradin ’yanci mai ƙarfi. Amma a ina za a iya samun ’yanci na gaske? Yesu ya ce: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.” (Yohanna 8:31, 32) Wannan ’yanci ba irin da mutane suke son su samu ba ne sa’ad da an ƙi wani sarki ko gwamnati domin wani. Maimako, wannan ’yanci yana kaiwa har cibiyar matsalolin ’yan Adam. Abin da Yesu yake faɗa shi ne ’yanci daga bauta wa zunubi. (Yohanna 8:24, 34-36) Saboda haka, idan mutum ya zama almajirin gaske na Yesu Kristi, zai ga canji na ƙwarai a rayuwarsa, ’yanci!
7. (a) Ta wace hanya ce za mu iya ’yantuwa daga zunubi a yanzu? (b) Domin mu sami wannan ’yancin, menene dole za mu yi?
7 Wannan ba ya nufin cewa a yanzu Kiristoci na gaskiya ba su da zuciya mai son zunubi ba. Tun da yake sun gāji zunubi, suna da kokawa domin shi. (Romawa 7:21-25) Amma idan mutum yana rayuwa daidai da koyarwar Yesu, ba zai zama bawan zunubi ba kuma. Zunubi ba zai mallake shi dole ba. Ba zai kamu ba cikin rayuwa da ba ta da ma’ana da za ta bar shi da mummunar lamiri. Zai more lamiri mai tsabta a gaban Allah domin an gafarta masa zunubansa bisa ga bangaskiyarsa cikin hadayar Kristi. Nufe-nufe na zunubi suna iya neman danne shi, amma idan ya ƙi ya yi su domin ya tuna da koyarwar Kristi mai tsabta, ya nuna cewa zunubi ba ya sarauta a kansa kuma ba.—Romawa 6:12-17.
8. (a) Wane ’yanci ne Kiristanci na gaskiya ke ba mu? (b) Wane irin hali za mu kasance da shi game da sarakuna na duniya?
8 Ka yi la’akari da ’yanci da mu Kiristoci muke mora. An ’yantar da mu daga tasirin koyarwar ƙarya, daga tsoro na camfi, da kuma daga ɗauri na zunubi. Gaskiya mai girma game da yanayin matattu da tashin matattu sun ’yantar da mu daga tsoro na mutuwa. Sanin cewa gwamnati ta mutane ajizai ba da daɗewa ba za a sake ta da Mulkin Allah mai adalci yana ba mu bege. (Daniel 2:44; Matta 6:10) Amma, irin ’yancin nan bai ba mu dalilin raina gwamnatoci da dokokinsu ba.—Titus 3:1, 2; 1 Bitrus 2:16, 17.
9. (a) Yaya Jehovah ya taimake mu da kyau mu more ɗan ’yanci da ke yiwuwa a yau? (b) Ta yaya za mu tsai da shawara mai kyau?
9 Jehovah bai ƙyale mu ba mu nemi hanya mafi kyau da za mu rayu ta faɗi-ka-tashi. Ya san halittarmu, abin da yake gamsar da mu sosai, da kuma fa’idar da za mu samu ta dindindin. Ya san tunani da kuma halayen da za su iya lalata dangantakar mutum da Shi da kuma ’yan’uwansa bil Adam, ƙila ma ya hana mutum shiga sabuwar duniya. Cikin ƙauna, Jehovah ya gaya mana dukan waɗannan abubuwa ta wurin Littafi Mai Tsarki da ƙungiyarsa da ake gani. (Markus 13:10; Galatiyawa 5:19-23; 1 Timothawus 1:12, 13) Wannan ya rage mana mu yi amfani da ’yanci na son rai da Allah ya bayar, mu tsai da shawarar yadda za mu yi amfani da shi. Ba kamar Adamu ba, idan mun bi abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya mana, to, za mu tsai da shawara mai kyau. Za mu nuna cewa dangantaka mai kyau da Jehovah ne muhimmin abu a rayuwarmu.
Bukatar Wani Irin ’Yanci
10. Wane irin ’yanci ne wasu da suke Shaidun Jehovah suka nema?
10 A wasu lokatai Shaidun Jehovah waɗanda matasa ne—har ma da wasu manya—suna iya jin cewa suna bukatar wani irin ’yanci dabam. Za su ga duniya tana da ban sha’awa, da zarar suna tunaninta, haka muradinsu su yi abubuwan da ba na Kirista ba da suka cika duniya zai daɗa ƙarfi. Irin waɗannan ba su yi shirin shan miyagun ƙwayoyi ba, shan giya da yawa, ko kuma su yi fasikanci. Amma za su soma yin tarayya da waɗanda ba Kiristoci na gaskiya ba, suna neman waɗannan su karɓe su. Za su fara yin koyi da furcinsu da kuma halayensu.—3 Yohanna 11.
11. A wasu lokatai, daga ina ne jarrabar yin mummunar aba ke fitowa?
11 A wasu lokatai jarrabar yin abin da ba halin Kirista ba takan fito daga wurin wani ne da yake da’awar yana bauta wa Jehovah. Haka gaskiya ne game da wasu Kiristoci na farko, kuma hakan zai iya faruwa a zamaninmu. Irin mutanen nan sau da yawa suna son yin abubuwan da suke jin zai kawo musu farin ciki, amma waɗannan abubuwa sun saɓa da dokokin Allah. Suna ariritar wasu cewa su ma su “more.” Suna ‘yi musu alkawarin ’yanci, yayin da su bayi ne ga ruɓa.’—2 Bitrus 2:19.
12. Menene mugun sakamakon halaye da suka saɓa da dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa?
12 Sakamakon irin ’yancin nan kullum mummuna ne, da yake yana nufin yin rashin biyayya ga dokokin Allah. Alal misali, lalata tana jawo baƙin ciki, cuta, mutuwa, cikin shege, da kuma kisan aure. (1 Korinthiyawa 6:18; 1 Tassalunikawa 4:3-8) Shan miyagun ƙwayoyi yana sa yin batsa, gani hazo hazo, jiri, raunana numfashi, mugun mafarki, da kuma mutuwa. Zai iya kai wa ga jaraba, wadda za ta iya sa mutum yin laifi don ya ci gaba da wannan halin. Irin sakamakon da ake samu ke nan daga yawan shaye-shaye. (Misalai 23:29-35) Waɗanda suka shagala cikin irin wannan halayen suna tunanin cewa suna da ’yanci, amma bayan sun makara sai su fahimci cewa sun zama bayin zunubi. Kuma zunubi mugun sarki ne! Yin tunani a kan batun yanzu zai taimaka wajen kāre mu daga irin aukuwan nan.—Galatiyawa 6:7, 8.
Inda Matsaloli ke Farawa
13. (a) Ta yaya sha’awa da take jawo matsaloli take farawa? (b) Don mu fahimci abin da “zama da miyagu” yake nufi, ra’ayin wa muke bukata? (c) Yayin da kake amsa tambayoyi da aka jera a izifi na 13, ka nanata ra’ayin Jehovah.
13 Ka yi tunanin inda matsaloli sau da yawa ke farawa. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacinda sha’awa ta habala, ta kan haifi zunubi: zunubi kuwa, sa’anda ya ƙasaita, ya kan fidda mutuwa.” (Yaƙub 1:14, 15) Ta yaya sha’awa take tasowa? Ta abin da ke shiga zuciya. Sau da yawa wannan daga tarayya da waɗanda ba sa amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne. Hakika, mun san ya kamata mu guji “zama da miyagu.” (1 Korinthiyawa 15:33) Amma wace irin tarayya ce mummuna? Yaya Jehovah yake ji game da batun? Yin tunani a kan tambayoyi na gaba da kuma bincika nassosi da aka nuna ya kamata ya taimake mu mu zo ga kammala mai kyau.
Domin wasu mutane kamar suna da ɗaukaka yana nufin cewa su abokanan kirki ne? (Farawa 34:1, 2, 18, 19)
Taɗinsu, ƙila ma wasa da suke yi, ya nuna cewa za mu iya zama abokanansu ne? (Afisawa 5:3, 4)
Yaya Jehovah yake ji idan muka zaɓi mu yi abota ta kusa kusa da mutane da ba sa ƙaunarsa? (2 Labarbaru 19:1, 2)
Ko da yake muna iya yin aiki tare ko makaranta tare da mutanen da ba sa cikin imaninmu, me ya sa muke bukatar mu mai da hankali? (1 Bitrus 4:3, 4)
Kallon telibijin da siliman, yin amfani da Intane, karanta littattafai, jaridu, hanyoyi ne na abokantaka da wasu. Game da wane irin abu ne cikin waɗannan za mu mai da hankali? (Misalai 3:31; Ishaya 8:19; Afisawa 4:17-19)
Menene zaɓenmu na abokane ke gaya wa Jehovah game da irin mutanen da muke? (Zabura 26:1, 4, 5; 97:10)
14. Wane ’yanci mai girma ne ke nan gaba domin waɗanda suke amfani da gargaɗin Kalmar Allah cikin aminci?
14 A nan gaba kaɗan ga sabuwar duniyar Allah. Ta wurin Mulkin Allah na samaniya, za a ’yantar da dukan mutane daga rinjayar Shaiɗan da dukan mugun tsarinsa. A hankali, za a kawar da dukan sakamakon zunubi daga mutane masu biyayya, yana kawo kamilta ta azanci da jiki, domin mu more rai na har abada a Aljanna. A ƙarshe dukan halitta za su more ’yanci da ya jitu da “Ruhun Ubangiji.” (2 Korinthiyawa 3:17) Hikima ce a yi hasarar dukan wannan domin yin banza da gargaɗin Kalmar Allah yanzu? Ta yin amfani da ’yancinmu na Kirista da hikima a yau, bari dukanmu mu nuna sarai cewa “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah” muke so da gaske.—Romawa 8:21.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Wane irin ’yanci ne mutane na farko suka more? Yaya wannan yake idan an gwada da yanayin da mutane ke ciki a yanzu?
• Wane irin ’yanci ne Kiristoci na gaskiya suke da shi? Ta yaya wannan ya saɓa wa abin da duniya take kira ’yanci?
• Me ya sa yake da muhimmanci ƙwarai mu guje wa mugun abota? Ba kamar Adamu ba, shawarwarin wanene muka amince da shi a batun munanan abubuwa?
[Hotuna a shafi na 46]
Kalmar Allah ta yi gargaɗi: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki”