Ku Zama Masu Hidima Da Ke Cin Gaba Kuma Masu Daidaituwa
“Na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.”—1 KORANTIYAWA 9:22.
1, 2. (a) A waɗanne hanyoyi ne manzo Bulus ya kasance ƙwararren mai hidima? (b) Yaya Bulus ya kwatanta halinsa game da aikinsa?
YANA tattaunawa da mutane masu ilimi da kuma maɗinkan tanti masu tawali’u cikin sauƙin kai. Ya rinjayi Romawa masu ɗaukaka da kuma talakawan Firijiya. Rubutunsa ya motsa Heleniyawa masu sassaucin ra’ayi da kuma Yahudawa masu bin al’ada. Ba a iya jayayya da hujjojinsa kamar yadda suke motsa zuciyar sosai. Ya nemi hanya mai sauƙi domin ya jawo mutane ga Kristi.—Ayyukan Manzanni 20:21.
2 Manzo Bulus ne mutumin, babu shakka, ƙwararre ne a hidima kuma mai cin gaba. (1 Timoti 1:12) Ya sami umurni daga Yesu ya ‘sanar da sunan [Kristi] ga al’ummai, da sarakuna, da kuma Isra’ilawa.’ (Ayyukan Manzanni 9:15) Menene ra’ayinsa game da wannan aikin? Ya ce: “Na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu. Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarka tata.” (1 Korantiyawa 9:19-23) Menene za mu iya koya daga misalin Bulus da zai taimaka mana mu zama ƙwararru a wa’azinmu da koyarwa?
Mutumin da ya Tuba ya yi Nasara a Hidimarsa Mai Wuya
3. Yaya Bulus ya ji game da Kiristoci kafin ya tuba?
3 Bulus yana da jimiri da kuma karimci a dā kuwa, har da ya cancanci aikin da aka ba shi? Ko kaɗan! Zafin hali na addini ya sa Shawulu (sunan Bulus a dā) ya zama mai tsananta wa mabiyan Kristi. Da yake matashi, ya amince a kashe Istafanus. Bayan haka, Bulus ya yi ta farautar Kiristoci ba ji ba gani. (Ayyukan Manzanni 7:58; 8:1, 3; 1 Timoti 1:13) Ya kuwa ci gaba da “tsananta kashedi gāba da masu bi Ubangiji, cewa zai kashe su.” Da yake farautar masu bi da suke Urushalima bai ishe shi ba, ya ci gaba da yaɗa ƙiyayyarsa har Dimashƙu.—Ayyukan Manzanni 9:1, 2.
4. Wane canji ne Bulus yake bukatar ya yi domin ya cika aikinsa?
4 Wataƙila dalilin da ya sa Bulus ya tsani Kiristanci shi ne, yana ganin cewa Kiristanci zai gurɓata Yahudanci ta wajen haɗa shi da wani baƙuwar al’ada, da ba a so. Ban da haka, Bulus “Bafarisiye ne,” sunan da ke nufin “keɓaɓɓe.” (Ayyukan Manzanni 23:6) Ka yi tunanin mamakin da Bulus ya yi sa’ad da ya ji cewa Allah ya zaɓe shi ya yi wa’azin Kristi ga dukan mutane, musamman ma, ga mutanen Al’ummai! (Ayyukan Manzanni 22:14, 15; 26:16-18) Farisiyawa ba sa cin abinci da waɗanda suke ganin masu zunubi ne! (Luka 7:36-39) Babu shakka, yana bukatar ya canja ra’ayinsa ya daidaita shi ya jitu da nufin Allah domin dukan ire-iren mutane su sami ceto.—Galatiyawa 1:13-17.
5. Ta yaya za mu yi koyi da Bulus a hidimarmu?
5 Wataƙila muma muna bukatar mu yi haka. Yayin da muke saduwa da mutane dabam dabam a yankunanmu inda ake yare dabam dabam, muna bukatar mu bincika halayenmu kuma mu yi watsi da ƙabilanci. (Afisawa 4:22-24) Ko mun san haka ko ba mu sani ba, mahallinmu da kuma iliminmu na shafanmu. Hakan na iya sa mu kasance da ra’ayoyi da kuma halaye na nuna bambanci, ƙabilanci, da tsattsauran ra’ayi. Dole ne mu yi watsi da irin waɗannan halayen idan muna so mu yi nasara wajen nema da kuma taimaka wa masu kama da tumaki. (Romawa 15:7) Abin da Bulus ya yi ke nan. Ya karɓi ƙalubalen faɗaɗa hidimarsa. Da yake ƙauna ce ta motsa shi, ya gina iya koyarwarsa wanda ya kamata mu yi koyi da shi. Hakika, bincike na hidimar ‘manzo ga al’ummai’ ya nuna cewa yana sauraro, ba shi da tsattsauran ra’ayi, kuma yana da basira wajen wa’azi da koyarwa.a—Romawa 11:13.
Mai Hidima da ke Cin Gaba A kan Aikinsa
6. Ta yaya ne Bulus ya mai da hankali ga inda masu sauraronsa suka fito, kuma menene sakamakon haka?
6 Bulus ya mai da hankali ga imani da kuma inda masu sauraronsa suka fito. Sa’ad da yake magana da Sarki Agaribas na biyu, Bulus ya faɗi cewa sarkin “gwani ne [wajen] sanin al’adun Yahudawa da maganganunsu.” Bulus ya yi amfani da sanin imanin Agaribas, kuma ya tattauna abubuwan da sarkin zai iya fahimta sosai. Muhawwarar Bulus ta fita sarai kuma tana da rinjaya wanda hakan ya sa Agaribas ya ce: “Wato a ɗan wannan taƙaitaccen lokaci kake nufin mai da ni Kirista?”—Ayyukan Manzanni 26:2, 3, 27, 28.
7. Ta yaya ne Bulus ya nuna sauƙin kai sa’ad da yake wa’azi ga wasu mutane a Listira?
7 Bulus mutum ne mai sauƙin kai. Yi la’akari da halin da ya nuna sa’ad da yake ƙoƙarin hana mutane a birnin Listira su bauta masa da Barnaba. An ce waɗannan mutanen da suke yaren Likoniya suna cikin mutane marasa ilimi kuma yawancinsu ’yan camfi ne. In ji Ayyukan Manzanni 14:14-18, Bulus ya yi nuni ga halittu da kuma abubuwa masu kyau da suka nuna cewa Allah na gaskiya ya fi duka. Wannan abu ne mai sauƙin fahimta, kuma hakan ya “hana jama’an nan yin hadaya” ga Bulus da Barnaba.
8. A waɗanne hanyoyi ne Bulus ya nuna cewa shi ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne duk da cewa ya nuna ɓacin rai a wasu lokatai?
8 Hakika, Bulus ba kamiltaccen mutum ba ne, kuma a wasu lokatai yana nuna ɓacin rai game da wasu abubuwa. Alal misali, a wani lokaci sa’ad da aka tozarta shi, Bulus ya gaya wa wani Bayahude mai suna Hananiya magana. Amma sa’ad da aka gaya wa Bulus cewa ya zagi babban firist ba da sanin shi ba, nan take ya nemi gafara. (Ayyukan Manzanni 23:1-5) A Atina, da farko “ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko’ina gumaka ne a birnin.” Duk da haka, a jawabinsa na Tudun Arasa, Bulus bai nuna wannan fushi ba. Maimakon haka, ya yi wa Atinawa jawabi a wajen taronsu, ya yi mahawara da su a kan abin da suka yarda da shi ta wajen yin nuni ga bagadensu wanda aka rubuta “Saboda Allahn da ba a sani ba,” kuma ya yi ƙaulin mawaƙansu.—Ayyukan Manzanni 17:16-28.
9. Ta yaya ne Bulus ya nuna basira sa’ad da yake sha’ani da mutane?
9 Sa’ad da yake sha’ani da mutane dabam dabam, Bulus ya nuna basira ƙwarai. Ya yi la’akari da al’ada da kuma mahalli da suka shafi tunanin masu sauraronsa. Sa’ad da ya rubuta wa Kiristoci da ke Roma, ya sani sarai cewa suna zaune ne a ƙasa mai iko da duniya. Muhimmin bayanin da ke cikin wasiƙar Bulus ga Kiristocin da ke Roma shi ne, ikon ceto na Kristi ya sami nasara bisa ikon zunubin Adamu na lalaci. Ya yi amfani da yaren da zai daɗaɗa wa Kiristocin da ke Roma zuciya da kuma waɗanda suke yi yau da kullum.—Romawa 1:4; 5:14, 15.
10, 11. Ta yaya ne Bulus ya daidaita misalansa da masu sauraronsa? (Dubi hasiya kuma.)
10 Menene Bulus ya yi sa’ad da yake son ya yi bayani akan zurfafan gaskiya na Littafi Mai Tsarki ga masu sauraronsa? Manzon ya ƙware wajen yin amfani da sanannun misalai masu sauƙin fahimta, don ya bayyana abubuwa na ruhaniya masu wuyan fahimta. Alal misali, Bulus ya sani cewa mutanen Roma sun san tsarin bauta da ke Daular Roma. Babu shakka, wataƙila yawancin mutanen da ya rubuta wa wasiƙar bayi ne. Saboda haka, Bulus ya yi amfani da misalin bayi don ya ƙarfafa bayaninsa game da zaɓin mutum na yin biyayya ga zunubi ko aminci.—Romawa 6:16-20.
11 Wani bincike ya ce, “a cikin Romawa, ubangida na iya ƙyale bawansa, ko kuwa bawan ya ƙwaci ’yancinsa ta wajen biyan ubangidansa. Bawan na iya samun ’yanci idan aka bayar da shi kyauta ga wani allah.” Bawan da aka ’yanta na iya ci gaba da yi wa ubangidansa aiki a biya shi. Shi ya sa Bulus ya yi amfani da wannan tsarin sa’ad da ya rubuta game da zaɓan ubangidan da ya kamata a yi wa biyayya, wato, zunubi ko aminci. An ’yanta Kiristocin Roma daga zunubi kuma sun zama dukiyar Allah. Ko da yake suna da ’yancin bauta wa Allah, duk da haka, suna iya yanke shawarar bauta wa zunubi, wato, ubangidansu na dā, idan suka ga dama. Wannan sanannen misali kuma mai sauƙi, zai motsa Kiristocin da ke zaune a Roma su tambayi kansu, ‘Wane ubangida ne nike bauta wa?’b
Koyo Daga Misalin Bulus
12, 13. (a) Menene ake bukatar yi a yau domin a motsa zukatan mutane dabam dabam? (b) Menene ka ga cewa yana da amfani sa’ad da kake yin wa’azi ga mutanen da suka fito daga wurare dabam dabam?
12 Kamar Bulus, dole ne mu kasa kunne, mu zama masu sauƙin kai, kuma masu basira domin mu motsa zuciyar mutane dabam dabam. Domin mu taimaka wa masu sauraronmu su fahimci bishara, muna bukatar fiye da ziyara kawai, ba da saƙo, ko kuwa ba da wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu yi ƙoƙari mu fahimci bukatunsu, damuwarsu, abubuwan da suke so da waɗanda ba sa so, fargabansu da kuma yadda suke nuna wariyar ƙabila. Ko da yake wannan na bukatar tunani da ƙoƙari mai yawa, masu shelar Mulki a dukan duniya suna ɗokin yin haka. Alal misali, ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke Hungary ya ba da rahoto: “ ’Yan’uwan suna daraja al’adu da kuma salon rayuwar ’yan wasu ƙasashe kuma ba sa tilasta musu su canja al’adunsu.” Shaidu a sauran wurare suna ƙoƙarin yin haka.
13 A wata ƙasa a Can Gabas, yawancin mutanen da ke wurin sun damu ne da lafiya, renon yara, da kuma ilimi. Masu shelar Mulki da ke ƙasar suna yin amfani da waɗannan batutuwa maimakon tattauna batutuwa kamar su, taɓarɓarewar yanayin duniya ko kuwa matsaloli. Hakazalika, masu shela a wani babban birni a Amirka sun lura cewa mutane a wata unguwa da ke yankinsu sun damu da abubuwa kamar su cin hanci, yawan cinkoson motoci, da kuma aikata laifi. Shaidun sun yi nasara wajen yin amfani da waɗannan batutuwan don soma tattauna Littafi Mai Tsarki da su. Ƙwararrun malamai na Littafi Mai Tsarki suna ƙoƙarin su ga cewa duk batun da suka zaɓa zai kasance mai kyau kuma mai ƙarfafawa, zai nanata muhimmancin yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a yanzu, da kuma bege mai kyau da Allah ya ba da don nan gaba.—Ishaya 48:17, 18; 52:7.
14. Ka kwatanta hanyoyin da za mu iya daidaita kanmu da bukatu da kuma yanayi dabam dabam na mutane.
14 Tun da yake mutane suna da al’adu, ilimi, da addinai da suka bambanta, yana da kyau idan muna canja yadda muke tattaunawa a hidimarmu. Yadda za mu tattauna da mutanen da suka gaskata da Mahalicci amma ba su yarda da Littafi Mai Tsarki ba, zai bambanta da waɗanda ba su yarda da wanzuwar Allah ba. Yadda za mu tattauna da wanda yake ganin cewa dukan littattafai na addini hanyar yaɗa labaran ƙarya ne, zai bambanta da mutumin da ya yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ke koyarwa. Muna bukatar mu kasance masu daidaitawa sa’ad da muke tattaunawa da mutanen da iliminsu ya bambanta. Ƙwararrun malamai suna yin amfani da dalilai da kuma misalai da suka dace da abin da suke tattaunawa.—1 Yahaya 5:20.
Taimako ga Sababbin Masu Hidima
15, 16. Me ya sa ake bukatar koyar da sababbin masu hidima?
15 Bulus bai damu kawai da yadda zai kyautata hanyoyin koyarwarsa kaɗai ba. Amma ya lura cewa yana bukatar ya koyar ya kuma shirya matasa kamar su Timoti da Titus su zama ƙwararrun masu hidima. (2 Timoti 2:2; 3:10, 14; Titus 1:4) Hakazalika, akwai bukatu na gaggawa na koyarwa a yau.
16 A shekara ta 1914, kusan masu shelar Mulki 5,000 ne kaɗai ne ke akwai a dukan duniya; amma a yau kusan mutane 5,000 ne ake wa baftisma a kowane mako! (Ishaya 54:2, 3; Ayyukan Manzanni 11:21) Sa’ad da sababbi suka soma zuwa ikilisiyar Kirista kuma suna son zuwa hidima, suna bukatar koyarwa da ja-gora. (Galatiyawa 6:6) Yana da muhimmanci mu bi misalin Ubangijinmu Yesu sa’ad da muke koyar da almajirai.c
17, 18. Ta yaya za mu iya taimaka wa sababbi su sami gaba gaɗi a hidima?
17 Yesu bai nemi jama’a ba kawai kuma ya gaya wa manzanninsa su soma yi musu wa’azi. Ya soma ne da nanata musu muhimmancin aikin wa’azi kuma ya ƙarfafa su su dinga yin addu’a. Bayan haka, ya yi musu tanadin abubuwa uku da zai taimaka musu: abokin aiki, yankin da za su yi aiki, da kuma saƙo. (Matiyu 9:35-38; 10:5-7; Markus 6:7; Luka 9:2, 6) Muma za mu iya yin haka. Ko ɗanmu ne muke taimaka wa, ko sabon ɗalibi, ko kuwa wanda ya daɗe bai yi wa’azi ba, zai dace idan muka koyar da su a wannan hanyar.
18 Sababbi suna bukatar taimako sosai domin su sami gaba gaɗin gabatar da saƙon Mulki. Kana iya taimakonsu su shirya gabatarwa mai sauƙi kuma mai daɗi? Bari su koya daga misalinka yayin da kake wa’azi a hidima. Kana iya bin gurbin Gidiyon, wanda ya gaya wa mayaƙansa: “Sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi.” (Littafin Mahukunta 7:17) Bayan haka, sai ka ba sabon mutumin zarafi shi ma ya yi wa’azi. Ka yaba wa ƙoƙarin da sababbi suka yi, kuma sa’ad da ya dace, ka ba su ɗan shawara na yadda za su ci gaba da gyara.
19. Menene ƙudurinka yayin da kake ƙoƙarin cika hidimarka sosai?
19 Domin mu ‘cika hidimarmu,’ mun ƙudurta cewa za mu kasance da sauƙi a maganarmu, kuma muna so mu koya wa sababbin masu hidima su yi hakan. Sa’ad da muka yi la’akari da muhimmancin makasudinmu, wato, koyar da sanin Allah da ke kai ga samun ceto, muna da tabbacin cewa kwalliya za ta biya kuɗin sabulu domin mun zama “kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa [mu] ceci waɗansu.”—2 Timoti 4:5; 1 Korantiyawa 9:22.
[Hasiya]
a Domin ganin irin waɗannan halayen a hidimar Bulus, ka duba Ayyukan Manzanni 13:9, 16-42; 17:2-4; 18:1-4; 19:11-20; 20:34; Romawa 10:11-15; 2 Korantiyawa 6:11-13.
b Hakazalika, sa’ad da yake bayani game da sabuwar dangantakar da ke tsakanin Allah da ‘ ’ya’yansa’ na ruhu, Bulus ya yi amfani da batu na shari’a wanda sananne ne ga masu karatunsa da ke Daular Roma. (Romawa 8:14-17) “Al’adar Romawa ne su ɗauki reno, kuma hakan na da nasaba ta kusa da ra’ayin Romawa game da iyali,” in ji littafin nan, St. Paul at Rome.
c Ana tafiyar da tsarin nan Majagaba Ku Taimaki Wasu a dukan ikilisiyoyin Shaidun Jehobah. Wannan tsarin na ba masu hidima na cikakken lokaci damar koyar da masu shela waɗanda ba su ƙware ba.
Ka Tuna?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu yi koyi da Bulus a hidimarmu?
• Waɗanne canje-canje ne muke bukatar mu yi a tunaninmu?
• Ta yaya za mu iya kasancewa da sauƙi a saƙonmu?
• Menene sababbin masu hidima suke bukatar su yi domin su kasance da gaba gaɗi?
[Bayanin da ke shafi na 25]
Manzo Bulus ya kasa kunne, yana da sauƙin kai, kuma ya bi da yanayi dabam dabam a hanyar da ta dace a wa’azi da koyarwa
[Bayanin da ke shafi na 27]
Yesu ya yi wa almajiransa muhimman tanadi uku: abokin aiki, yankin da za su yi aiki, da kuma saƙo
[Hotuna a shafi na 24]
Bulus ya yi nasarar kai ga mutane dabam dabam domin ya daidaita
[Hoto a shafi na 26]
Ƙwararrun masu hidima suna yin la’akari da al’adun masu sauraronsu
[Hoto a shafi na 27]
Masu hidima da suke cin gaba suna taimaka wa sababbi su yi shirin hidima