Hadayu Da Suke Faranta Wa Allah Rai
“Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu.”—IBRANIYAWA 8:3.
1. Me ya sa mutane suke jin ya kamata su juya ga Allah?
“HADAYA a gare mutum tana daidai da yadda addu’a take; hadaya tana nuna yadda yake ji game da kansa, addu’a kuma tana nuna yadda yake ji game da Allah,” haka Alfred Edersheim ɗan tarihi na Littafi Mai Tsarki ya rubuta. Tun daga lokacin da zunubi ya shigo duniya, ya kawo baƙin ciki, raɓewa daga Allah, da zama abin tausayi. Ana bukatar sauƙi daga waɗannan abubuwan. Yana da sauƙi a fahimci dalili da ya sa lokacin da mutane suka iske kansu cikin irin wannan matsalar, sai su ji ya kamata su juya ga Allah don taimako.—Romawa 5:12.
2. Waɗanne labarai ne game da sadaka ga Allah, na dā muka samu a Littafi Mai Tsarki?
2 Rubutu na farko da aka yi game da sadaka cikin Littafi Mai Tsarki ga Allah shi ne na Kayinu da Habila. Mun karanta: “Sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin ’ya’yan fari na garkensa.” (Farawa 4:3, 4) Sai kuma Nuhu, wanda Allah ya tsare shi lokacin babbar Ambaliya da ta halaka miyagun tsara na lokacinsa, ya motsa shi “ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden” ga Jehovah. (Farawa 8:20) Sau da yawa, alkawura da albarkar Allah sun motsa Ibrahim mai aminci bawan Allah, kuma abokinsa ya ‘gina bagade, ya kira sunan Jehovah.’ (Farawa 12:8; 13:3, 4, 18) Daga baya, Ibrahim ya fuskanci gwajin bangaskiya mafi tsanani lokacin da Jehovah ya gaya masa ya miƙa ɗansa Ishaƙu hadaya ta ƙonawa. (Farawa 22:1-14) Ko da yake waɗannan gajerun labarai ne, sun ba da fahimi sosai game da batun hadaya, yadda za mu gani a gaba.
3. Wane matsayi ne hadayu suke da shi wajen bauta?
3 Daga waɗannan da wasu labarai na Littafi Mai Tsarki, a bayyane yake sarai cewa miƙa wasu hadayu tushe ne na bauta da daɗewa kafin Jehovah ya ba da dokoki game da hadayu. Saboda da haka, wani littafin bincike ya ba da ma’anar “hadaya” cewa “al’adar addini ce wadda ake ba da wani abu ga Allah don a kafa, adana, ko kuma mai da dangantaka mai kyau tsakanin mutane da abin da suke ɗauka tsarkake.” Amma wannan ya kawo wasu muhimman tambayoyi da ya cancanta mu bincika sosai, kamar su: Me ya sa ake bukatar hadaya wajen bauta? Waɗanne irin hadayu ne Allah ya amince da su? Kuma wace ma’ana ce hadayu na dā suke da shi a garemu a yau?
Me Ya Sa Ake Bukatar Hadaya?
4. Menene sakamakon zunubi da Adamu da Hauwa’u suka yi?
4 Yayin da Adamu ya yi zunubi, ya yi hakan ne da gangan. Cin ’ya’yan itace na sanin nagarta da mugunta da ya yi, rashin biyayya ne da ya yi da gangan. Sakamakon rashin biyayya da ya yi, mutuwa ce, kamar yadda Allah ya bayyana dalla-dalla: “A ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.” (Farawa 2:17) A ƙarshe Adamu da Hauwa’u sun girbe sakamakon zunubi—sun mutu.—Farawa 3:19; 5:3-5.
5. Me ya sa Jehovah ya zaɓa ya warware matsalar saboda ’ya’yan Adamu, kuma menene Ya yi musu?
5 ’Ya’yan Adamu kuma fa? Da yake sun gaji zunubi da ajizanci daga Adamu, aka ƙasƙantar da su zuwa irin wannan raɓewar daga Allah, suka zama abin tausayi suna mutuwa kuma kamar yadda Adamu da Hauwa’u suka mutu. (Romawa 5:14) Amma, Jehovah ba Allah ba ne na gaskiya kawai mai iko—amma mafi muhimmanci—yana da ƙauna. (1 Yahaya 4:8, 16) Saboda haka shi ya zaɓa ya warware tashin hankalin nan. Bayan da ya faɗi cewa “sakamakon zunubi mutuwa ne,” Littafi Mai Tsarki ya ci gaba, “amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.”—Romawa 6:23.
6. Menene nufin Jehovah game da ɓarnar da zunubin Adamu ya yi?
6 Abin da Jehovah Allah ya yi don ya ba da kyauta mai kyau shi ne, yin tanadin abin da zai rufe hasara da laifin Adamu ya jawo. A Ibrananci, kalmar nan ka·phar’ wataƙila da farko tana nufin “rufewa” ko kuma “kawarwa,” kuma an fassara ta “kafara.”a A wasu kalmomi, Jehovah ya yi tanadi da ya dace don ya rufe zunubi da aka gada daga Adamu kuma ya kawar da sakamakon da ya biyo baya don a ’yantar da waɗanda suka cancanci wannan kyautar daga zunubi da mutuwa.—Romawa 8:21.
7. (a) Wane bege aka yi tanadinsa ta hukunci da Allah ya yi wa Shaiɗan? (b) Menene dole za a biya don a yantar da mutane daga zunubi da mutuwa?
7 Begen za a ’yantar da mutane daga zunubi da mutuwa an yi maganarsa bayan mutane biyu na farko sun yi zunubi. Da yake yanke hukuncinsa bisa Shaiɗan wanda maciji ya wakilce shi, Jehovah ya ce: “Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ƙuje diddigensa.” (Farawa 3:15) Ta wannan furci na annabci, duk waɗanda suka ba da gaskiya cikin wannan alkawari sun sami bege. Amma akwai abin da za a biya don wannan ’yancin. Ɗan da aka yi alkawarinsa ba zai zo haka kawai ya halaka Shaiɗan ba; dole a ƙuje diddigensa, wato, dole ya mutu, ko da ba zai kasance dindindin ba.
8. (a) Ta yaya Kayinu ya zama abin kunya? (b) Me ya sa Allah ya amince da hadayar Habila?
8 Babu shakka Adamu da Hauwa’u sun yi tunani sosai game da wannan Zuriya na alkawari. Lokacin da Hauwa’u ta haifi ɗanta na fari Kayinu, ta ce: “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” (Farawa 4:1) Tana tunani ne cewa wataƙila shi ne zai zama Zuriyar? Ko ta yi ko babu, Kayinu da kuma sadakarsa sun zama abin kunya. A wata sassa kuma, ɗan’uwansa Habila ya ba da gaskiya ga alkawari da Allah ya yi kuma wannan ya motsa shi ya miƙa ’yan fari na garkensa hadaya ga Jehovah. Mun karanta: “Ta bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan ta Kayinu, ta wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne.”—Ibraniyawa 11:4.
9. (a) A menene Habila ya ba da gaskiya, kuma yaya ya nuna ta? (b) Menene hadayar Habila ta cim ma?
9 Bangaskiyar Habila ba imani ba ne kawai cewa da akwai Allah, wadda tilas Kayinu ma ya gaskata da wannan. Habila yana da bangaskiya cewa alkawarin Allah na Ɗa zai kawo ceto ga mutane masu aminci. Ba a bayyana masa yadda za a cim ma wannan ba, amma alkawarin Allah ya sa Habila ya sani cewa za a ƙuje wani a diddige. Hakika, ya kammala da cewa dole a zubar da jini—ainihin ra’ayin yin hadaya ke nan. Habila ya miƙa sadaka da ta ƙunshi rai da jini ga Tushen rai, mai yiwuwa a nuna marmarinsa mai yawa da kuma zatonsa na cikar alkawarin Jehovah. Wannan nuna bangaskiyar ne ya sa hadayar Habila ta faranta wa Jehovah rai, kuma a ƙaramin hanya ya nuna ainihin dalilin hadaya—hanyar da mutane masu zunubi za su matso kusa da Allah kuma su sami alherinsa.—Farawa 4:4; Ibraniyawa 11:1, 6.
10. Ta yaya aka fayyace ma’anar hadaya da Jehovah ya gaya wa Ibrahim ya ba da Ishaku?
10 Muhimmancin hadaya an fayyace ta cikin alama lokacin da Jehovah ya umarci Ibrahim ya ba da ɗansa hadaya ta ƙonawa. Ko da ba a yi hadayar a zahiri ba, ta nuna hoton abin da Jehovah kansa zai yi a ƙarshe—zai ba da Ɗansa makaɗaici wajen hadaya mafi girma da aka taɓa yi don a cim ma nufinsa domin mutane. (Yohanna 3:16) Da hadayu da sadakoki na Dokar Musa, Jehovah ya kafa tafarki ne na annabci ya koya wa mutanensa da ya zaɓa abin da dole su yi don a gafarta musu zunubansu kuma don begensu na ceto ya yi ƙarfi. Menene za mu koya daga waɗannan?
Hadayu da Jehovah Ya Amince da Su
11. Wane irin sadakoki biyu na musamman babban firist na Isra’ila yake miƙawa, da wane dalili?
11 “Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu,” in ji manzo Bulus. (Ibraniyawa 8:3) Ka lura cewa Bulus ya raba sadakoki da babban firist na Isra’ila ta dā yake yi, zuwa gida biyu, wato, “sadakoki” da “hadayu,” ko kuma “hadayu domin kawar da zunubai.” (Ibraniyawa 5:1) Mutane suna ba da kyauta don su nuna ƙauna da godiya, da kuma gina abokantaka, don su sami alheri, ko kuma amincewa. (Farawa 32:20; Karin Magana18:16) Hakanan ma, yawancin sadakoki da Doka ta ce a yi “kyauta” ce ga Allah don a biɗi amincewarsa da alherinsa.b Ƙarya Doka tana bukatar gyara, kuma don a yi gyarar ana miƙa “hadayu domin kawar da zunubai.” Littattafai biyar na farko musamman Fitowa, Littafin Firistoci, da Littafin Ƙidaya, sun yi magana game da hadayu da sadakoki iri dabam dabam. Ko da yake zai yi mana wuya sosai mu fahimci kuma tuna dukansu dalla-dalla, ya kamata mu mai da hankali ga wasu muhimman darussa game da hadayu iri dabam dabam.
12. A ina ne cikin Littafi Mai Tsarki za mu samu inda aka taƙaita batun hadayu, ko sadakoki na Doka?
12 Za mu lura cewa a Littafin Firistoci sura 1 zuwa 7, an kwatanta sadakoki na musamman guda biyar—hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya ta salama, hadaya ta zunubi, da hadaya domin laifi—an kwatanta su dabam dabam, ko da ana miƙa wasu tare. Mu lura kuma cewa an kwatanta waɗannan sadakoki sau biyu cikin waɗannan surori, da manufa dabam dabam: sau ɗaya, a Littafin Firistoci 1:2 zuwa 6:7 an nuna abin da za a miƙa dalla-dalla a kan bagade, kuma na biyu, a Littafin Firistoci 6:8 zuwa 7:36, an nuna sashen da aka kafa dabam dabam domin firistoci da waɗanda aka ajiye don mai miƙawa. Sai kuma a Littafin Ƙidaya sura ta 28 da ta 29, mun ga abin da za a iya ɗaukarsa ma’ajin lokaci, ya ba da tsarin irin abin da za a miƙa kowace rana, na kowane mako, da kowane wata, da kuma a idodi na shekara shekara.
13. Ka kwatanta sadakoki na kyauta da ake miƙawa da son rai ga Allah.
13 Tsakanin sadakoki da ake miƙawa da son rai ko kuma don a matsa kusa da Allah don a samu alherinsa shi ne hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da hadaya ta salama. Wasu manazarta sun gaskata cewa kalmar Ibrananci na “hadaya ta ƙonawa” na nufin “hadaya mai hawa” ko kuma “hadaya da ke haurawa.” Wannan daidai ne saboda a hadaya ta ƙonawa, ana ƙona dabba da aka yanka a kan bagade sai ƙanshi mai daɗi, zai haura zuwa sama ga Allah. Abin da ya sa hadaya ta ƙonawa ta bambanta ita ce, bayan an kewaye bagadin da jininta da aka yafa, sai a miƙa dabbar ga baki ɗayanta ga Allah. Firistocin za su “ƙone duka a kan bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.”—Littafin Firistoci 1:3, 4, 9; Farawa 8:21.
14. Ta yaya ake miƙa hadayar gari?
14 An kwatanta hadaya ta gari a Littafin Firistoci sura 2. Hadaya ce ta son rai da ta ƙunshi fulawa mai kyau, da aka dama da mai, haɗe da turare. “[Firist] zai ɗibi tafi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.” (Littafin Firistoci 2:2) Lubba ɗaya ce cikin kayan turaren wuta mai tsarki da ake ƙonawa a kan bagaden turare a cikin mazauni da kuma haikali. (Fitowa 30:34-36) Wataƙila wannan ne ya faɗo wa Sarki Dauda a zuciya yayin da ya ce: “Ka karɓi addu’ata kamar turaren ƙonawa, ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.”—Zabura 141:2.
15. Menene manufar hadaya ta salama?
15 Wata hadaya kuma ita ce ta salama hadaya ce ta son rai, da aka kwatanta a Littafin Firistoci sura 3. A Ibrananci kalmar “salama” na da nufi fiye da a kasance babu damuwa ko kuma yaƙi. “A cikin Littafi Mai Tsarki, salama tana nufin zama babu yaƙi ko damuwa, tana kuma nufin yanayin kasancewa da salama tare da Allah, ni’ima, yin murna, da farin ciki,” in ji littafin Studies in the Mosaic Institutions. Da haka ana miƙa hadayu na salama, ba don a kasance da salama da Allah, kamar ana lallashinsa, amma don a nuna godiya ko kuma yi bikin yanayin albarka ta salama tare da Allah da waɗanda ya amince da su suke morewa. Firistocin da mai miƙawa suna cin hadayar bayan an miƙa wa Jehovah jinin da kitsen. (Littafin Firistoci 3:17; 7:16-21; 19:5-8) A hanya mai kyau kuma ta alama, mai miƙawa, firistocin, da Jehovah Allah suna cin abinci tare, yana nuna dangantaka ta salama da ke tsakaninsu.
16. (a) Menene manufar hadaya ta zunubi da hadaya ta laifi? (b) Yaya waɗannan suka bambanta daga hadaya ta ƙonawa?
16 Hadayu da ake miƙawa don a nemi gafarar zunubi ko kuma a yi gafarar laifuffuka da aka yi wajen taka Doka ya haɗa da hadaya ta zunubi da hadaya ta laifi. Ko da ana ƙone waɗannan hadayu a kan bagade, sun bambanta daga hadaya ta ƙonawa domin ba a miƙa dabbar ga baki ɗayanta ga Allah, kitsen da wasu wurare ne kawai ake miƙawa. Ana zubar da sauran naman a waje da zangon ko kuma a wasu lokatai firistocin su ci. Wannan bambanci yana da ma’ana. Ana miƙa kyautar hadaya ta ƙonawa ga Allah don a iya zuwa wurinsa, saboda haka ana miƙa ta ga Allah ga baki ɗayanta. Abin marmari shi ne, ana miƙa hadaya ta zunubi ko kuma hadaya ta laifi kafin hadaya ta ƙonawa, wannan yana nuna cewa don Allah ya karɓi kyautar mai zunubi ana bukata a gafarta masa zunubi da ya yi.—Littafin Firistoci 8:14, 18; 9:2, 3; 16:3, 5.
17, 18. Don menene aka yi tanadin hadaya ta zunubi, menene kuma manufar hadaya ta laifi?
17 Ana karɓan hadaya ta zunubi kaɗai don zunubi da aka yi game da Doka ba da gangan ba, zunubi ne da aka yi domin kumamancin jiki. “In wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,” mai zunubin zai miƙa hadaya ta zunubi daidai da yanayi ko kuma matsayinsa a yankin. (Littafin Firistoci 4:2, 3, 22, 27) A wata sassa kuma, za a datse masu zunubi da suka ƙi su tuba; babu hadayu game da su.—Fitowa 21:12-15; Littafin Firistoci 17:10; 20:2, 6, 10; Littafin Ƙidaya 15:30; Ibraniyawa 2:2.
18 An bayana ma’ana da manufar hadaya ta laifi sarai a Littafin Firistoci sura 5 da 6. Wani zai iya zunubi ba da gangan ba. Duk da haka, laifinsa zai iya taka damar ko ’yan’uwansa ko kuma Jehovah Allah, kuma ya kamata a gyara ko kuma warware laifin. An ambata zunubi da yawa. Wasu zunubi ne na kai (5:2-6), wasu zunubi ne ga “tsarkakkun abubuwa na Ubangiji” (5:14-16), wasu kuma ko da ba da saninsu, su ne zunubi da ake yi don mummunar sha’awa ko kuma kumamanci na jiki (6:1-3). Ƙari ga yin ikirari na waɗannan zunubai, ana bukatar mai laifi ya biya inda ya dace sai kuma ya miƙa hadaya ta laifi ga Jehovah.—Littafin Firistoci 6:4-7.
Abu Mafi Kyau Zai Zo
19. Ko da suna da Dokar da hadayunta, me ya sa Isra’ila ba ta samu alherin Allah ba?
19 Dokar Musa, da hadayunta mai yawa da sadakoki, an ba Isra’ilawa don su iya kusatowa ga Allah, su sami kuma su adana alherinsa da albarka har zuwan Zuriya na alkawari. Manzo Bulus, Bayahude a jiki ya ce: “Shari’a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta bangaskiya.” (Galatiyawa 3:24) Abin baƙin ciki, al’ummar Isra’ila ba ta bi tsarewan nan ba amma sun yi banza da wannan gatar. Saboda haka, yawan hadayunsu ya zama abin ƙyama ga Jehovah wanda ya ce: “Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki.”—Ishaya 1:11.
20. Menene ya faru a shekara ta 70 A.Z. game da Dokar da hadayunta?
20 A shekara ta 70 A.Z., tsarin abubuwa na Yahudawa, da haikalinta da tsarin firistoci suka zo ƙarshensu. Bayan haka, yin hadayu yadda Doka ta faɗa ba zai yiwu kuma ba. Wannan yana nufin cewa hadayu, sashe ne na musamman na Dokar, sun yi hasarar duk ma’anarsu ga masu bauta wa Allah a yau? Za mu bincika wannan a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Insight on the Scriptures, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga ya yi bayani: “Kamar yadda take cikin Littafi Mai Tsarki, ‘yin kafara’ na nufin ‘rufe’ ko kuma ‘musanya,’ ko kuma abin da aka yi musanya da shi, ko kuma a ‘rufe,’ wani abu, dole ne ya zama wanda zai iya sake shi. . . . Don ya ba da kafara daidai ga abin da Adamu ya yi hasarar, ya kamata a yi tanadin hadaya ta zunubi da darajarta take daidai da na kamiltaccen rai na mutum.”
b Kalmar Ibrananci da sau da yawa ake fassarawa “sadakoki” ita ce qor·banʹ. Lokacin da yake rubuta hukuncin Yesu game da mummunar ayyuka na Marubuta da Farisawa, Markus ya bayyana cewa “Korban” na nufin ‘abin da aka bai wa Allah.’—Markus 7:11.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene ya motsa mutane masu aminci na dā su miƙa hadayu ga Jehovah?
• Me ya sa ake bukatar hadayu?
• Wane irin hadayu musamman ake miƙawa a ƙarƙashin Doka, kuma menene manufarsu?
• Bisa ga abin da Bulus ya faɗa, menene musamman manufar Dokar da hadayunta?
[Hoto a shafi na 6]
Hadayar Habila ta faranta wa Jehovah rai domin ta nuna bangaskiyarsa ga alkawarinsa
[Hoto a shafi na 7]
Ka gane ma’anar wannan wurin?