Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu, Kuma Za Ka Samu Rai Da Salama
‘Ku yi tafiya ba bisa ga tabi’ar jiki ba, amma bisa ga ruhu.’—ROM. 8:4.
1, 2. (a) Mene ne sakamakon yin wasu abubuwa sa’ad da mutum yake tuƙi? (b) Wane haɗari ne zai iya kasance sa’ad da ba mu mai da hankali ba a ruhaniya?
SAKATAREN sufuri a Amirka ya ce: “Rashin mai da hankali sa’ad da ake tuƙi yana daɗa muni kowace shekara.” Wayar selula tana ɗaya daga cikin abin da ke raba hankalin matuƙi, sa’ad da yake kan hanya. Fiye da mutane kashi ɗaya cikin uku da aka gana da su sun ce matuƙin da ke amfani da waya sa’ad da yake tuƙi ya taɓa kaɗe su ko ya kusan buge su. Za a iya gani kamar yin abubuwa da yawa sa’ad da ake tuƙi ba laifi ba ne, amma hakan zai iya kasance da haɗari.
2 Ruhaniyarmu ma za ta iya kasance hakan. Kamar yadda matuƙin da bai mai da hankali ba ba ya ganin alamun haɗari, hakan nan ma mutumin da bai mai da hankali ba zai iya faɗi cikin haɗari na ruhaniya. Idan muka bijire daga ayyuka na tsarin Allah, sakamakon zai iya zama haɗari ga bangaskiyarmu. (1 Tim. 1:18, 19) Manzo Bulus ya ba Kiristocin da ke Roma gargaɗi a kan wannan haɗarin: “Himmantuwar jiki mutuwa ce: amma himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.” (Rom. 8:6) Mene ne Bulus yake nufi? Ta yaya za mu iya guje wa “himmantuwar jiki” kuma mu mai da hankali ga “himmantuwar ruhu”?
Ba Su da “Kayarwa”
3, 4. (a) Bulus ya rubuta game da wanne fama da ya yi? (b) Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga yanayin Bulus?
3 A wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya rubuta game da famar da ya yi, wato, fama tsakanin jikinsa da tunaninsa. (Karanta Romawa 7:21-23.) Bulus bai ce hakan ba don neman hujja ko kuma ya ji tausayin kansa. Kuma ba ya nufin cewa ba zai yiwu ya yi abu mai kyau ba. Ballantana ma, shi Kirista shafaffe ne da ya manyanta, kuma aka zaɓe shi ya zama “manzon Al’ummai.” (Rom. 1:1; 11:13) Amma me ya sa Bulus ya rubuta game da famar da ya yi?
4 Bulus yana bayyana ne dalla-dalla cewa ba zai iya yin nufin Allah daidai yadda yake so da kansa ba. Domin “dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Rom. 3:23) Da yake shi ɗan Adam ne, Bulus ajizi ne kuma yana da sha’awa marar kyau. Yanayinmu kamar nasa ne domin dukanmu ajizai ne kuma muna fama kamar shi kullum. Bugu da ƙari, akwai abubuwa da yawa da za su iya raba hankalinmu kuma su sa mu bijire daga ‘hanya matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai.’ (Mat. 7:14) Amma dai, Bulus bai kasance marar bege ba, mu ma hakan.
5. Daga ina ne Bulus ya samu taimako da kuma hutu?
5 Bulus ya rubuta: “Wanene zai tsamo ni . . . ? Na gode ma Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Rom. 7:24, 25) Sai ya yi wa Kiristoci shafaffu magana, wato, “waɗanda ke cikin Kristi Yesu.” (Karanta Romawa 8:1, 2.) Jehobah ya ɗauke su a matsayin ’ya’ya, ta wajen kiransu su zama “masu-tarayyan gādo da Kristi.” (Rom. 8:14-17) Ruhun Allah tare da imaninsu ga hadayar fansa ta Kristi, sun sa su yi nasara a famar da Bulus ya bayyana kuma ba su da “kayarwa.” An ’yantar da su “daga dokar zunubi da ta mutuwa,” NW.
6. Me ya sa yake da muhimmanci dukan bayin Jehobah su mai da hankali ga kalamin Bulus?
6 Ko da yake kalamin Bulus ga Kiristoci shafaffu ne, amma abin da ya faɗa game da ruhun Allah da kuma hadayar fansa ta Kristi za ta iya amfane dukan bayin Jehobah ko da suna da begen kasancewa a sama ko kuma a duniya. Yana da muhimmanci dukan bayin Allah su fahimci abin da Bulus ya rubuta kuma su yi ƙoƙarin amfana daga shi, domin an hure Bulus ya rubuta wannan kalami ga Kiristoci shafaffu.
Yadda Allah Ya “Kada Zunubi Cikin Jiki”
7, 8. (a) A wane azanci ne Doka “rarrauna ce ta wurin jiki”? (b) Mene ne Allah ya cim ma ta ruhunsa da kuma fansar?
7 A cikin sura ta 7 ta littafin Romawa, Bulus ya bayyana ikon zunubi a jikinmu ajizi. A sura ta 8, ya yi magana game da ikon ruhu mai tsarki. Manzon ya bayyana yadda ruhun Allah zai iya taimaka wa Kiristoci a famar da suke yi da zunubi domin su yi rayuwar da ta jitu da nufin Jehobah kuma su samu amincewarsa. Bulus ya nuna cewa ta ruhun Allah da kuma hadayar fansa ta Ɗansa, Allah zai iya cim ma abin da Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ba ta iya cim ma ba.
8 Dokar ta hukunta masu zunubi domin ba su iya bin dukan Dokokin ba. Bugu da ƙari, babban firist na Isra’ila da ke hidima bisa Doka ajizi ne kuma bai iya ba da daidaitaciyar hadaya don zunubi ba. Shi ya sa Dokar “rarrauna ce ta wurin jiki.” Amma ta aiko da “Ɗa nasa cikin kamanin jiki mai-zunubi” da kuma ba da shi a matsayin hadaya, Allah ya “kada zunubi cikin jiki,” da hakan ya shawo kan “abin da shari’a ba ta da iko ta aika.” Da hakan an sanar da Kiristoci shafaffu masu aminci bisa ga imaninsu ga hadayar fansa ta Kristi. An ƙarfafa su su yi “tafiya ba bisa ga tabi’ar jiki ba, amma bisa ga ruhu.” (Karanta Romawa 8:3, 4.) Hakika, wajibi ne su yi hakan cikin aminci har ƙarshen rayuwarsu a duniya domin su samu “rawanin rai.”—R. Yoh. 2:10.
9. Mene ne ma’anar kalmar nan “doka” da aka ambata a littafin Romawa 8:2?
9 Ƙari ga “Dokar,” Bulus ya ambata, “dokar ruhu” da “dokar zunubi da ta mutuwa.” (Rom. 8:2) Mene ne waɗannan dokokin? Kalmar nan “doka” da aka ambata a nan ba ta nufin wasu ƙa’idodi, kamar waɗanda suke cikin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. Wani aikin bincike ya ce: “A Hellenanci, kalmar nan doka tana nufin nagarta da muguntan da mutane suke yi da ke ja-gorarsu kamar doka. Yana kuma iya nufin ƙa’idodin da suka zaɓa su bi.”
10. Ta yaya muke ƙarƙashin ikon dokar zunubi da ta mutuwa?
10 Manzo Bulus ya rubuta: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Rom. 5:12) A matsayinmu na ’ya’yan Adamu, dukanmu muna ƙarƙashin dokar zunubi da kuma mutuwa. Kullum, jikinmu ajizi yana motsa mu mu yi abubuwan da ba sa faranta wa Allah rai, da suke jawo mutuwa. Bulus ya kira waɗannan “ayyukan jiki” a cikin wasiƙarsa ga Galatiyawa. Kuma ya daɗa cewa: “Su waɗanda ke aika waɗannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.” (Gal. 5:19-21) Irin waɗannan mutanen ba su da bambanci da waɗanda suke tafiya bisa ga jiki. (Rom. 8:4) Suna yin abin da jikinsu ajizi ya ce su yi. Amma shin waɗanda suke fasikanci da bautar gumaka da sihiri ko kuma suka yi wasu zunubai masu tsanani ne kaɗai suke yin ayyukan jiki? A’a, gama ayyukan jiki sun haɗa da abubuwan da wasu suke ɗauka kasawa ne kawai kamar su, kishi da fushi da tsatsaguwa da kuma hassada. Wane ne zai iya ce ya riga ya ’yantu daga ayyukan jiki?
11, 12. Wane tanadi ne Jehobah ya yi don ya ’yantar da mu daga dokar zunubi da ta mutuwa, kuma mene ne ya wajaba mu yi don mu more tagomashin Allah?
11 Abin farin ciki ne sosai sanin cewa Jehobah ya taimaka mana mu shawo kan dokar zunubi da ta mutuwa! Yesu ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Idan mun amince da ƙaunar Allah kuma mun ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu Kristi, za a ’yantar da mu daga zunubin da muka gada. (Yoh. 3:16-18) Saboda haka, za mu iya furta kalami kamar Bulus, wanda ya ce: “Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.”
12 Yanayinmu yana kama da warkar da mutum mai mugun ciwo. Idan muna son mu warke sosai, wajibi ne mu yi abin da likitan ya ce mu yi. Ko da yake ba da gaskiya ga fansar za ta iya ’yantar da mu daga dokar zunubi da ta mutuwa, duk da haka mu ajizai ne kuma muna yin zunubi. Akwai ƙarin abubuwa da yawa da ya kamata mu yi don mu ƙulla dangantaka mai kyau da Allah kuma mu samu tagomashinsa da albarkarsa. Idan muna son mu samu sauƙi daga ajizanci, Bulus ya gaya mana wajibi ne mu yi tafiya bisa ga ruhu.
Ta Yaya Za Mu Yi Tafiya Bisa ga Ruhu?
13. Mene ne yin tafiya bisa ga ruhu yake nufi?
13 Sa’ad da muke tafiya, muna yin hakan ne domin muna son mu isa wani wuri. Saboda haka, yin tafiya bisa ga ruhu yana nufin mu ci gaba da kyautata ruhaniyarmu, ba ya nufin cewa ba za mu taɓa yin kuskure ba. (1 Tim. 4:15) Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu kowacce rana don mu yi tafiya, ko kuma yi rayuwa da ta jitu da ja-gorancin ruhun. Yin “tafiya bisa ga Ruhu” yana kai ga samun amincewar Allah.—Gal. 5:16.
14. Yaya waɗanda suka mai da hankali ga “al’amuran jiki” suke aikatawa?
14 A wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya kuma yi magana game da mutane iri biyu da suke da ra’ayoyi dabam-dabam. (Karanta Romawa 8:5.) A wannan ayar, kalmar nan jiki ba ta nufin jikinmu na zahiri. A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “jiki” a wani lokaci tana nufin jikinmu ajizi da kuma mai zunubi. Wannan ne ya jawo saɓani tsakanin jiki da tunani da Bulus ya ambata ɗazun. Akasin Bulus da ya yi fama da jikinsa ajizi, mutane da yawa a yau ba sa fama. Maimakon su yi la’akari da abin da Allah yake bukata kuma su amince da taimakon da ya tanadar, suna mai da hankali ga “al’amuran jiki.” Suna yawan mai da hankali ga gamsar da sha’awarsu. Akasin haka, tunanin waɗanda suke “bisa tabi’ar ruhu” yana a kan “al’amuran ruhu,” wato, tanadi da ayyuka na ruhaniya.
15, 16. (a) Ta yaya mai da hankali ga wani abu zai iya shafan ra’ayinmu? (b) Mene ne za mu iya cewa game da abin da yawancin mutane suka mai da wa hankali?
15 Karanta Romawa 8:6. Wajibi ne mutum ya fara mai da hankali ga wani abu kafin ya yi shi. Ba ya wa mutanen da suke yawan yin tunani game da abubuwa na jiki wuya su shaƙu sosai ga abubuwan jiki. Ra’ayinsu da muradinsu da kuma sha’awarsu sukan shaƙu da waɗannan abubuwan.
16 Mene ne mutane a yau suka fi mai da wa hankali? Manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.” (1 Yoh. 2:16) Waɗannan sha’awace-sha’awace sun haɗa da abubuwa kamar su lalata da samun suna da kuma abubuwan mallaka. Waɗannan abubuwan suna cikin littattafai da jaridu da fina-finai da wasannin talabijin da Intane, musamman domin abin da mutane suka fi mai da wa hankali ne ke nan. Yin hakan za ta iya sa mu rasa dangantakarmu da Jehobah yanzu, kuma a nan gaba mu rasa ranmu. Me ya sa? “Domin himmantuwar jiki gāba ce da Allah; gama ba ta cikin biyayya ga shari’ar Allah ba, ba ta iya kuwa: waɗanda ke cikin jiki kuwa ba su da iko su gami Allah ba.”—Rom. 8:7, 8.
17, 18. Ta yaya za mu iya ƙyale ruhun Allah ya ja-gorance mu, kuma da wane sakamako?
17 A wani ɓangaren kuma, “himmantuwar ruhu rai ne da lafiya,” wato, rai na har abada a nan gaba da kasancewa da wadar zuci da kuma salama da Allah yanzu. Ta yaya za mu iya biɗan “himmantuwar ruhu”? Idan muna bin ja-gorar Allah da kuma ruhunsa mai tsarki, za mu samu ra’ayin da ya jitu da na Allah. Yayin da muke yin hakan, tunaninmu zai yi “biyayya ga shari’ar Allah” kuma zai jitu da nufinsa. Idan muna fuskantar gwaje-gwaje, za mu san daidai abin da ya kamata mu yi. Hakan zai motsa mu mu yi zaɓin da ya dace, wanda ya jitu da ruhun.
18 Saboda haka, yana da muhimmanci mu mai da hankali ga abubuwa na ruhu. Muna son mu sa ayyukanmu na Kirista su zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Waɗannan ayyukan sun ƙunshi yin addu’a a kai a kai da karatun Littafi Mai Tsarki da halartar tarurruka da kuma fita hidimar fage. (1 Bit. 1:13) Maimakon mu ƙyale abubuwa na jiki su janye hankalinmu, ya kamata mu mai da hankali ga abubuwa na ruhu. Idan mun yi hakan za mu ci gaba da yin tafiya bisa ga ruhu. Yin hakan zai kawo mana albarka, domin himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.—Gal. 6:7, 8.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Mene ne “abin da shari’a ba ta da iko ta aika,” kuma yaya Allah ya shawo kanta?
• Mene ne “dokar zunubi da ta mutuwa,” kuma yaya za mu iya samun ’yanci daga gare ta?
• Mene ne ya wajaba mu yi don mu ‘himmatu a ruhu’?
[Hotona a shafi na 12, 13]
Shin kana tafiya bisa ga jiki ne ko bisa ga ruhu?