Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 21 pp. 184-191
  • Nufin Jehovah Ya Yi Nasara Mai Girma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nufin Jehovah Ya Yi Nasara Mai Girma
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Isra’ila Sun Yi Hasarar Matsayi Mai Kyau
  • Tattara “Abubuwan da ke Cikin Sammai”
  • Tattara “Abubuwan da ke Bisa Duniya”
  • ’Yanci Mai Girma a Nan Gaba
  • Wakilci Na Cika Nufin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Abin Da Mulkin Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 21 pp. 184-191

Babi Na Ashirin Da Ɗaya

Nufin Jehovah Ya Yi Nasara Mai Girma

1, 2. (a) Menene ƙudurin Jehovah game da halittunsa masu basira? (b) Su wa ke haɗe cikin iyali masu haɗin kai na Allah?

DUKAN halittu masu hankali su haɗa kai cikin bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya, kuma dukansu suna more ’yanci mai girma na ’ya’yan Allah—wannan shi ne ƙudurin Jehovah na ƙauna. Abin da ma masu ƙaunar adalci suke ɗokin samu ke nan.

2 Jehovah ya soma cika wannan ƙuduri mai girma lokacin da ya soma aikinsa na halitta. Halittarsa ta farko Ɗa ne wanda tun tashinsa daga matattu “walƙiyar darajar [Allah], sura sosai kuma ta jauharinsa” ne. (Ibraniyawa 1:1-3) Wannan Ɗan farda ne, tun da Allah ne kansa ya halicce shi. Daga baya, ta wurin wannan Ɗan ne kowa ya kasance: da farko mala’iku a sama, sai kuma mutane a duniya. (Ayuba 38:7; Luka 3:38) Dukan waɗannan sun zama iyali ɗaya na dukan sararin samaniya. Ga dukansu, Jehovah Allah ne, kuma Mamallakin Dukan Halitta ne kuma Ubansu mai ƙauna.

3. (a) Menene dukanmu mun gāda daga iyayenmu na farko? (b) Wane tanadi na ƙauna Jehovah ya yi wa ’ya’yan Adamu?

3 Lokacin da aka yi wa iyayenmu na farko hukuncin kisa tun da masu zunubi da gangan ne, aka fitar da su daga Adnin kuma Allah ya yashe su. Daga nan ba su kasance cikin iyalinsa na dukan sararin samaniya ba kuma. (Farawa 3:22-24; Kubawar Shari’a 32:4, 5) Dukanmu ’ya’yansu ne, saboda haka an haife mu da nufin yin zunubi. Amma Jehovah ya sani cewa wasu daga cikin ’ya’yan Adamu da Hauwa’u za su so adalci. Saboda haka ya yi tanadi da waɗannan za su iya samun “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.”—Romawa 8:20, 21.

Isra’ila Sun Yi Hasarar Matsayi Mai Kyau

4. Wace gata Jehovah ya miƙa wa Isra’ila ta dā?

4 Shekaru 2,500 bayan da aka halicci Adamu, Jehovah ya ba wasu ’yan Adam gatar kasancewa da dangantaka ta musamman da Shi. Ya zaɓi Isra’ila ta dā ta zama mutanensa kuma ya ba su Dokarsa. (Farawa 12:1, 2) Ya sa sun zama al’umma, ya yi amfani da su a batun ƙudurinsa. (Kubawar Shari’a 14:1, 2; Ishaya 43:1) Amma, suna cikin bauta ga zunubi da mutuwa har ila, saboda haka ba su mori ’yanci mai girma da Adamu da Hauwa’u suke da shi a farko ba.

5. Yaya Isra’ilawa suka yi hasarar dangantakarsu ta musamman da Allah?

5 Duk da haka, Isra’ilawa suna da matsayi mai kyau a gaban Allah. Suna kuma da hakkin yin biyayya ga Jehovah Ubansu kuma su yi aiki da ya jitu da ƙudurinsa. Yesu ya nanata muhimmancin cika hakkinsu. (Matta 5:43-48) Amma al’ummar Isra’ila ta ƙi yin haka. Ko da yake waɗannan Yahudawa sun yi da’awar cewa, “muna da Uba ɗaya, Allah ne,” Yesu ya ce ayyukansu da halayensu sun ƙaryata wannan da’awar. (Yohanna 8:41, 44, 47) A shekara ta 33 A.Z., Allah ya kawar da Dokar, kuma dangantaka ta musamman ta Isra’ila ta ƙare. Amma wannan yana nufi ne cewa mutane ba za su ƙara morar dangantaka mai kyau da Allah ba kuma ke nan?

Tattara “Abubuwan da ke Cikin Sammai”

6. Menene manufar “wakilci” da Bulus ya ambata a Afisawa 1:9, 10?

6 Manzo Bulus ya nuna cewa wasu tsakanin ’yan Adam za su more dangantaka ta musamman da Allah. Alal misali, game da shirin da Jehovah ya yi domin waɗanda suka kasance da bangaskiya su zama cikin Iyalinsa, Bulus ya rubuta: “[Allah] da ya sanashe mu asirin nufinsa, bisa ga yardarsa da ya nufa a cikinsa zuwa wakilci na cikar wokatai, shi tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” (Afisawa 1:9, 10) Wannan “wakilci” a kan Yesu Kristi yake. Ta wurinsa, aka kawo mutane a matsayin amincewa a gaban Allah. Ƙaramin adadinsu suna da begen kasancewa a sama. Adadi mai yawa kuma za su zauna a duniya har abada.

7. Su waye ne “abubuwan da ke cikin sammai”?

7 Da farko, somi daga Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an mai da hankali ga “abubuwan da ke cikin sammai,” watau waɗanda za su zama magāda tare da Kristi cikin Mulki na samaniya. A kan tushin bangaskiyarsu na darajar hadayar Yesu, Allah ya ce da su masu adalci. (Romawa 5:1, 2) Daga baya, aka haɗa Yahudawa da kuma na Al’ummai ciki, da kuma “abubuwan da ke cikin sammai” suka zama 144,000. (Galatiyawa 3:26-29; Ru’ya ta Yohanna 14:1) Raguwarsu ne kawai ya rage a duniya.

Tattara “Abubuwan da ke Bisa Duniya”

8. Su waye ne “abubuwan da ke bisa duniya,” kuma wace dangantaka suke da ita da Jehovah?

8 Wannan wakilcin ne ke tattara “abubuwan da ke bisa duniya.” Yanzu ana tattara mutane miliyoyi zuwa samun begen zama har abada a duniya. A haɗa kai da raguwar magādan Mulki, suna girmama sunan Jehovah kuma suna ɗaukaka bautarsa. (Ishaya 2:2, 3; Zephaniah 3:9) Suna kuma kirar Jehovah “Uba” domin sun fahimci cewa shi ne tushen rai. Kuma suna da tsayawa mai kyau a gabansa domin bangaskiyarsu cikin jinin da Yesu ya zubar. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Amma domin har ila su ajizai ne, ɗaukansu ’ya’yan Allah na ainihi yana nan gaba tukuna.

9. Wane alkawari Romawa 8:21 ke ɗauke da shi ga mutane?

9 Waɗannan da suke da bege na duniya suna ɗokin lokacin da halittu mutane za su samu “tsira daga bautar ɓacewa.” (Romawa 8:21) Wannan ’yanci zai soma bayan Kristi da rundunarsa na samaniya sun kawo ƙunci mai girma ta wurin Armageddon. Wannan yana nufin halakar dukan zamanin Shaiɗan, sai albarkar Sarautar Kristi na Shekara Dubu ta biyo ta.—Ru’ya ta Yohanna 19:17-21; 20:6.

10. Wace waƙar yabo ce bayin Jehovah za su haɗa wajen rerawa?

10 Lallai zai zama abin farin ciki ƙwarai lokacin da bayin Jehovah a duniya za su haɗa murya da bayinsa cikin sama, su ce: “Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai. Wanene za ya rasa jin tsoro, ya rasa ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji? gama kai kaɗai mai-tsarki ne; gama dukan al’ummai za su zo su yi sujjada a gabanka; gama ayyukanka masu-adalci sun bayyanu.” (Ru’ya ta Yohanna 15:3, 4) Hakika, dukanmu bayin Jehovah za mu haɗu cikin bauta ta Allah makaɗaici na gaskiya. Za a ta da matattu ma su samu zarafin haɗa muryoyinsu a yin yabo ga Jehovah.—Ayukan Manzanni 24:15.

’Yanci Mai Girma a Nan Gaba

11. Wane ’yanci ne mai girma waɗanda suka tsira daga ƙunci mai girma za su more?

11 Bayan ƙunci mai girma da Armageddon zai kammala, ya tsabtace duniya daga mugunta, Shaiɗan Iblis ba zai sake zama “Allah na wannan zamani” ba. Masu bauta wa Jehovah ba za su bukaci su yi fama da mugun tasirin Shaiɗan ba. (2 Korinthiyawa 4:4; Ru’ya ta Yohanna 20:1, 2) Addinin ƙarya ba zai ƙara ɓata sunan Jehovah ba ko kuma ya jawo jayayya tsakanin jama’a ba. Bayin Allah na gaskiya ba za su ƙara shan zalunci daga hannun mutane masu mulki ba. Lallai ’yanci ne mai girma da za a more!

12. Yaya dukanmu za mu ’yantu daga zunubi da azabarsa?

12 Yadda shi “Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya,” Yesu, zai yi amfani da darajar hadayarsa don kawar da zunuban mutane. (Yohanna 1:29) Lokacin da Yesu yake duniya kuma ya gafarta zunubin wani mutum, ya nuna tabbacin haka ta warkar da mutumin. (Matta 9:1-7; 15:30, 31) Hakanan ma, Yesu Kristi, wanda Sarkin Mulkin Allah ne, cikin mu’ujiza zai warkar da makafi, masu nauyin harshe, kurame, naƙasassu, masu taɓin hankali, da waɗanda suke da wasu cututtuka. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Dukan waɗanda ke masu biyayya lokacin zai zama sun kawar da “shari’ar zunubi” domin tunani da ayyukansu za su zama masu faranta wa kansu da kuma wa Allah rai. (Romawa 7:21-23) A ƙarshen Alif ɗin, zai zama sun kai kamilta, cikin ‘siffa da kuma kamanin’ Allah makaɗaici na gaskiya.—Farawa 1:26.

13. A ƙarshen Sarauta ta Alif, menene Kristi zai yi, da wane sakamako kuma?

13 Bayan Kristi ya kawo mutane ga kamilta, sai ya ba wa Uba ikon da Ya ba shi na yin wannan aikin: “Ya bada mulki ga Allah, Uba; sa’anda ya rigaya ya kawarda dukan hukunci, da dukan sarauta, da dukan iko. Gama shi dole za ya yi mulki, har ya sa dukan maƙiyansa ƙarƙashin sawayensa.” (1 Korinthiyawa 15:24, 25) Sarauta ta Alif za ta cim ma manufarta ƙwarai; saboda haka babu bukatar wannan gwamnati ta kasance tsakanin Jehovah da mutane. Kuma tun da yake zai zama an kawar da zunubi da mutuwa gabaki ɗaya kuma an fanshi mutane, bukatar Yesu Mai Fansa za ta ƙare. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Sa’annan shi Ɗan da kansa kuma za ya sarayu ga wannan wanda ya sarayadda dukan kome a ƙarƙashin mulkinsa, domin Allah ya zama duka cikin duka.”—1 Korinthiyawa 15:28.

14. Menene dukan mutane kamiltattu za su fuskanta, kuma me ya sa haka?

14 Biye da wannan, mutane da sun kamilta za su sami zarafin nuna zaɓensu su bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya har abada. Saboda haka, kafin ya tallafa su ’ya’yansa, Jehovah zai ba da dukan ’yan Adam da suka kamilta ga gwaji. Za a kwance Shaiɗan da aljanunsa daga ramin. Wannan ba zai zama wani lahani na dindindin ba ga waɗanda suke ƙaunar Jehovah da gaske. Amma duk waɗanda suka yi rashin aminci suka ƙi yin biyayya ga Jehovah, za a halaka su har abada, tare da ɗan tawaye na asali da aljanunsa.—Ru’ya ta Yohanna 20:7-10.

15. Wane yanayi ne zai sake kasancewa tsakanin dukan halittu masu hankali na Jehovah?

15 Sai Jehovah ya ɗauki dukan mutane da suka ɗaukaka ikon mallaka na Allah su zama ’ya’yansa a lokacin gwaji na ƙarshe. Daga lokacin zuwa gaba, za su yi rabo sosai cikin ’yanci na ’ya’yan Allah da suke cikin iyalin Allah na dukan sararin samaniya. Sai kuma dukan halittu masu basira a sama da duniya za su sake zama cikin haɗin kai a bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya. A lokacin ƙudurin Jehovah zai zamana ya yi nasara mai girma! Kana son ka kasance cikin wannan iyali na dukan halitta, mai farin ciki na har abada? Idan haka ne, muna ƙarfafa ka ka tuna da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a 1 Yohanna 2:17: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Kafin tawaye a Adnin, wace dangantaka ce dukan masu bauta wa Jehovah suke da ita?

• Wane hakki ke kan waɗanda suke bauta wa Allah?

• Su wa har ila za su zama ’ya’yan Allah, kuma yaya wannan yake da nasaba da ƙudurin Jehovah na bauta ta haɗin kai?

[Hoto a shafi na 190]

’Yan Adam masu biyayya za su mori rayuwa cikin aljanna a duniya

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba