Su Waye Suke Ɗaukaka Allah A Yau?
“Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, kā sami ɗaukaka, da girma, da iko.”—WAHAYIN YAHAYA 4:11.
1, 2. (a) Waɗanne misalai suka kwatanta kimiyya da ke kwaikwayon halitta? (b) Wace tambaya ta taso, kuma mecece amsar?
WATA rana a shekarun 1940, wani injiniya ɗan Switzerland, George de Mestral ya fita shan iska da karensa. Da suka dawo gida, ya lura cewa tufafinsa da kuma gashin karen ya cika da ƙarangiya. Domin yana son ya san game da ƙarangiyar, ya bincika ta da madubi mai ƙara girman abubuwa sai ya yi mamakin ƙananan abubuwa da ke manne wa tufafi mai huji da ya gani. Daga baya ya ƙera wani abu daidai da haka. Ba de Mestral ne kaɗai yake kwaikwayon halitta ba. A Amirka, Wilbur da Orville Wright sun gina jirgin sama bayan sun yi nazarin manyan tsuntsaye da suke tashiwa. Injiniya ɗan Faransa, Alexandre-Gustave Eiffel ya gina hasumiya a Paris mai ɗauke da sunansa, ya yi amfani da ƙa’idodi da ke sa ƙashin cinya na mutum ya tallafa wa nauyin jiki.
2 Waɗannan misalai sun kwatanta fannin kimiyya da ke kwaikwayon zane na halitta. Amma ya dace a yi tambaya: Sau nawa ne masu ƙirƙirowa suke yabon Wanda ya shirya ƙananan ƙarangiya, manyan tsuntsaye, da ƙashin cinya na mutum, da dukan abubuwa na asali masu kyau da masu ƙirƙirowa suke gani kafin su yi nasu? Abin baƙin ciki ne cewa a duniyar yau, da kyar a yabi Allah ko a yi masa ɗaukaka da ta cancanta.
3, 4. Mecece ma’anar kalmar Ibrananci da aka fassara “ɗaukaka,” menene yake nufi sa’ad da aka yi amfani da shi ga Jehovah?
3 Wasu za su yi tunanin ‘yana da muhimmanci kuwa a ɗaukaka Allah? Allah ba maɗaukaki ba ne?’ Hakika, Jehovah ne ya fi ɗaukaka a sararin halitta, amma wannan ba ya nufin cewa dukan mutane suna ganinsa maɗaukaki ne. A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar Ibrananci da aka fassara “ɗaukaka” tana da ma’anar “girma.” Tana nuni ga kome da ke sa mutum ya fi wasu girma ko muhimmanci. Idan aka yi amfani da shi ga Allah, yana nuni ga abin da ya sa Allah ya fi ’yan Adam.
4 Ba dukan mutane ba ne suka lura da abin da ya sa Allah ya fi ɗaukaka. (Zabura 10:4; 14:1) Hakika mutane masu daraja, idan ma sun gaskata da Allah sau da yawa sun rinjayi mutane su ƙi daraja Mahalicci maɗaukaki. A waɗanne hanyoyi ne suka yi hakan?
“Sun Rasa Hanzari”
5. Yaya masana kimiyya da yawa suke neman hujja don al’ajabi na halitta?
5 Masana kimiyya da yawa sun nace cewa babu Allah. To, ta yaya suke bayyana al’ajabi na halitta, har da mutane? Sun bai wa abubuwan al’ajabi na halitta wa ra’in bayyanau, iko marar tafarki. Alal misali, ɗan ra’in bayyanau Stephen Jay Gould ya rubuta: “Mun kasance domin wani irin kifi mai filafili da zai iya canzawa ya zama ƙafafuwa na ’yan Adam ne . . . Muna bukatar amsa ‘mafi kyau’—amma babu.” Haka nan ma, ’yan ra’in bayyanau Richard E. Leakey da Roger Lewin sun rubuta: “Wataƙila mutane sun kasance ne domin kuskure na yanayi.” Har wasu masana kimiyya da suke yaba wa kyau da zane na halitta sun kasa yabon Allah.
6. Menene ke hana mutane da yawa yi wa Allah yabo da ya cancanta da yake shi Mahalicci ne?
6 Sa’ad da mutane masu ilimi suka ce ra’in bayyanau gaskiya ne, suna nuna cewa jahilai ne kawai suka ƙi gaskatawa. Yaya mutane da yawa suke ji game da wannan ra’ayin? Wasu shekaru da suka shige, wani mutum da ya san game da ra’in bayyanau sosai ya gana da mutane da suka amince da ra’in bayyanau. Ya ce: “Na fahimci cewa yawancin mutane da suka gaskata da ra’in bayyanau sun yi hakan ne domin an gaya musu cewa dukan mutane masu basira sun gaskata.” Hakika, sa’ad da mutane masu rinjaya suka furta ra’ayin musun wanzuwar Allah, ana rinjayar mutane ne kada su yi wa Allah yabo da ya cancanta da yake shi Mahalicci ne.—Karin Magana 14:15, 18.
7. Bisa Romawa 1:20, menene za a ga sarai ta halitta na zahiri, kuma me ya sa?
7 Masana kimiyya sun kammala ne domin tabbaci ya nuna hakan? Da kyar! Tabbacin da ya nuna cewa akwai Mahalicci ya kewaye mu. Manzo Bulus ya rubuta game da shi: “Tun daga halittar duniya [’yan Adam] al’amuran Allah marasa gānuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane [marasa bi] sun rasa hanzari.” (Romawa 1:20) Muna ganin tabbacin akwai Mahalicci ta abin da ya halitta. Da haka Bulus yana cewa tun daga farkon wanzuwar mutane, ya yiwu ’yan Adam su ‘fahimci’ tabbacin wanzuwar Allah ta halitta da ake gani. Daga ina ne ake samun wannan tabbacin?
8. (a) Yaya samaniya na zahiri ya ba da tabbacin ikon Allah da hikimarsa? (b) Menene ya nuna cewa sararin samaniya yana da Aukuwa ta Farko?
8 Muna ganin tabbacin cewa akwai Allah ta abubuwa da suke sammai. “Dubi yadda sararin sama ke bayyana ɗaukakar Allah,” in ji Zabura 19:1. “Sararin sama”—rana, wata, da taurari—suna ba da tabbacin ikon Allah da hikimarsa. Yawan taurari marar iyaka yana sa mu mamaki. Dukan waɗannan halittu na sama suna da tafarki da suke bi bisa dokoki na zahiri.a (Ishaya 40:26) Daidai ne a ce irin wannan tsari ya kasance haka kawai? Masana kimiyya da yawa sun ce sararin samaniya ya soma farat ɗaya. Da yake ba da bayanin abin da yake nufi da cewa sararin samaniya ya soma farat ɗaya, wani farfesa ya rubuta: “Sararin samaniya da ya kasance da daɗewa ya yi daidai da [ra’ayin] musun wanzuwar Allah ko kuma rashin yarda wai za a iya sanin Allah. Haka nan ma, sararin samaniya da yake da masomi yana da tushen abubuwa da suke cikinsa; wanene zai yi tunanin irin wannan aukuwar idan babu abin da ya sa ya faru?”
9. Yaya hikimar Jehovah take a bayyane a halittun dabbobi?
9 Mun kuma ga tabbacin cewa akwai Allah a duniya. Mai Zabura ya furta: “Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa! Da hikima ƙwarai ka halicce su! Duniya cike take da talikanka.” (Zabura 104:24) “Talikan” Jehovah sun ƙunshi halittun dabbobi da suke nuna tabbacin hikimarsa. Yadda muka lura a farko, domin kyan tsarin halitta, masana kimiyya suna kwaikwayonsa. Ka yi la’akari da wasu misalai. Masu bincike suna nazarin ƙahon wata dabba da nufin su yi kwalkwali mai ƙwari; suna binciken ƙudaje iri-iri da suke da fasalin jin abubuwa sosai don su kyautata abin jin magana; kuma suna binciken fukafukan mujiya domin su kyautata jirgin sama da rada ba ta gani. Amma ko yaya suka ƙoƙarta ’yan Adam ba za su iya kwaikwayon abubuwa na halitta daidai yadda suke da kyau ba. Littafin nan Biomimicry—Innovation Inspired by Nature ya ce: “Abubuwa masu rai sun yi kome da muke son mu yi, ba tare da shan mai da ake samu daga ƙasa ba, halaka duniya, ko kuma ɓata rayuwarsu ta nan gaba.” Lallai wannan abin hikima ce!
10. Me ya sa wauta ce a ƙi cewa akwai Mahalicci Mai Girma? Ka kwatanta.
10 Ko ka kalli sama ko kuma halitta a nan duniya, da tabbacin cewa akwai Mahalicci. (Irmiya 10:12) Ya kamata mu yarda da halittu na sama da dukan zuciyarmu, da suka ce: “Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, kā sami ɗaukaka, da girma, da iko, domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa, da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.” (Wahayin Yahaya 4:11) Duk da haka, masana kimiyya da yawa sun kasa ganin tabbacin akwai mahalicci da “idon zuci,” ko da suna mamakin zane a cikin abubuwan da suka gani da idanunsu na zahiri. (Afisawa 1:18) Za mu iya kwatanta yanayin haka: Idan mutum yana sha’awar halitta da kyan su amma yana musun akwai Mahaliccinsu Mai Girma daidai yake da yin sha’awar wani hoto da aka zana da kyau kuma aka yi musun cewa babu wanda ya zana shi. Ba abin mamaki ba ne da aka ce da waɗanda suka ƙi gaskata da Allah “sun rasa hanzari”!
“Makafin Ja-gora” Suna Ruɗin Mutane da Yawa
11, 12. Koyarwar ƙaddara na bisa wane tsammani ne, kuma menene ya nuna cewa wannan koyarwa ba ta ɗaukaka Allah?
11 Mutane da yawa masu bin addini sun gaskata sosai cewa hanyar bautarsu tana ɗaukaka Allah. (Romawa 10:2, 3) Duk da haka, addini wani sashe ne na jam’iyyar ’yan Adam da ya hana miliyoyin mutane su ɗaukaka Allah. Ta yaya? Bari mu bincika hanyoyi biyu.
12 Na farko, addinai suna sa kada a ɗaukaka Allah ta wajen koyarwar ƙarya. Alal misali, koyarwar ƙaddara. Wannan koyarwar na nuna cewa tun da yake Allah yana da ikon sanin gaba, ya riga ya san dukan abin da zai faru. Da haka, koyarwar ƙaddara na nuna cewa Allah da daɗewa ya ƙaddara rayuwa ta nan gaba na kowane mutum—ko za ta yi kyau ko muni. Bisa wannan ra’ayin, ana jibga wa Allah alhakin wahala da muguntar duniyar yau. Ba a ɗaukaka Allah yayin da an ɗora masa alhakin da na Shaiɗan ne, babban Magabci, wanda Littafi Mai Tsarki ya kira “mai mulkin duniyan nan”!—Yahaya 14:30; 1 Yahaya 5:19.
13. Me ya sa wauta ce a yi tunanin cewa Allah ba zai iya sarrafa iyawarsa na sanin gaba ba? Ka ba da misali.
13 Koyarwar ƙaddara ba ta da tushe daga Nassi, kuma tana tsegunta Allah. Tana rikita abin da zai iya yi da abin da ainihi yake yi. An ambata cikin Littafi Mai Tsarki sarai cewa Allah yana iya sanin gaba. (Ishaya 46:9, 10) Amma, ba daidai ba ne a yi tunanin cewa ba ya iya ƙin sanin gaba ko yana sa hannu a kowane abu da ya faru. Ga misali: A ce kana da ƙarfi sosai. Da za ka so ka ɗaga kowane abu mai nauyi da ka gani? A’a! Haka nan ma, iya sanin gaba ba ya sa Allah ya san ko kuma ya ƙaddara kome. Yana amfani da sanin gaba wasu lokatai.b A bayyane yake cewa koyarwar ƙarya har da na ƙaddara ba ta ɗaukaka Allah.
14. A wace hanya ce addinai suke rena Allah?
14 Hanya ta biyu da addinai suke rena Allah ita ce ta halin mabiyansu. Ana bukatar Kiristoci su bi koyarwar Yesu. Yesu ya koya wa mabiyansa su “ƙaunaci juna” kuma kada su zama “na duniya.” (Yahaya 15:12; 17:14-16) Limaman Kiristendam fa? Sun bi waɗannan koyarwar kuwa?
15. (a) Yaya limamai suka sa hannu a yaƙe-yaƙen al’ummai? (b) Yaya halin limamai ya shafi mutane miliyoyi?
15 Yi la’akari da tarihin limamai game da yaƙi. Sun tallafa, sun yi na’am, har sun yi ja-gora a yaƙe-yaƙen al’ummai masu yawa. Sun albarkaci sojoji, sun kuma ce kashe mutane daidai ne. Abin mamaki shi ne, ‘Ba sa tunani cewa abokan gābansu su ma suna hakan?’ (Dubi akwati “Gefen Su Waye Allah Yake?”) Limamai ba sa ɗaukaka Allah sa’ad da suke da’awa cewa yana goyon bayansu a yaƙe-yaƙe da suke zubar da jini; ba sa kuwa ɗaukaka shi sa’ad da suke faɗin cewa mizanan Littafi Mai Tsarki yayin dā ne kuma suna na’am da kowace irin lalata. Suna tuna mana shugabannan addinai da Yesu ya kira “masu yin mugun aiki” da “makafin ja-gora.” (Matiyu 7:15-23; 15:14) Halin limamai ya sa ƙaunar mutane miliyoyi ga Allah ta yi sanyi.—Matiyu 24:12.
Su Waye ne da Gaske Suke Ɗaukaka Allah?
16. Don amsa tambayar waɗanda suke ɗaukaka Allah, me ya sa za mu bincika Littafi Mai Tsarki?
16 Idan shahararru da masu daraja na duniya sun kasa ɗaukaka Allah, su waye suke hakan da gaske? Littafi Mai Tsarki ne zai amsa wannan tambayar. Ballantana ma, Allah yana da ikon ya faɗi yadda za a ɗaukaka shi, kuma ya kafa mizanan cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 42:8) Bari mu yi la’akari da hanyoyi uku da za a ɗaukaka Allah, a kowane za a ambata su waye ne suke hakan a yau.
17. Ta yaya Jehovah da kansa ya nuna cewa ɗaukaka sunansa muhimmin sashe ne na nufinsa, kuma su waye a yau suke yabon sunan Allah a dukan duniya?
17 Na farko, za mu iya ɗaukaka Allah ta yabon sunansa. Ta abin da Jehovah ya gaya wa Yesu mun san cewa yin hakan muhimmin sashe ne na nufin Allah. Kwanaki kaɗan kafin ya mutu, Yesu ya yi addu’a: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai wata murya ta amsa: “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” (Yahaya 12:28) Mai maganar babu shakka Jehovah ne. Ta abin da ya faɗa, a bayyane yake cewa ɗaukaka sunansa yana da muhimmanci gare shi. To, su waye ne suke ɗaukaka Jehovah ta sanar da sunansa da kuma yabonsa a dukan duniya? Shaidun Jehovah ne, kuma suna hakan a ƙasashe 235!—Zabura 86:11, 12.
18. Ta yaya za mu san waɗanda suke bauta wa Allah da “gaskiya,” kuma wane rukuni ne suke koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki na fiye da ƙarni guda?
18 Na biyu, za mu iya ɗaukaka Allah ta koyar da gaskiya game da shi. Yesu ya ce masu bauta ta gaskiya za su “yi [wa Allah] sujada . . . da gaskiya.” (Yahaya 4:24) Ta yaya za mu san waɗanda suke bauta wa Allah da “gaskiya”? Dole su ƙi da koyarwar da ba bisa Littafi Mai Tsarki da ke murguɗa Allah da nufinsa. Maimakon haka, dole su koyar da gaskiyar Kalmar Allah, har da waɗannan: Jehovah ne Allah Maɗaukaki Duka, ya cancanci a ɗaukaka shi kaɗai a wannan matsayin (Zabura 83:18); Yesu Ɗan Allah ne da Sarki da aka naɗa na Mulkin Almasihu na Allah (1 Korantiyawa 15:27, 28); Mulkin Allah zai tsarkake sunan Jehovah kuma ya cika ƙudurinsa game da wannan duniya da mutane da ke cikinta (Matiyu 6:9, 10); dole a yi wa’azin wannan Mulkin a dukan duniya. (Matiyu 24:14) Fiye da ƙarni guda, rukuni ɗaya ne kaɗai cikin aminci suke koyar da irin wannan gaskiya mai tamani—Shaidun Jehovah ne!
19, 20. (a) Me ya sa hali mai kyau na Kirista yake ɗaukaka Allah? (b) Waɗanne tambayoyi za su taimake mu mu san waɗanda a yau suke ɗaukaka Allah ta halinsu mai kyau?
19 Na uku, za mu iya ɗaukaka Allah ta yin rayuwa daidai da mizanansa. Manzo Bitrus ya rubuta: “Ku yi halin yabo a cikin al’ummai, don duk sa’ad da suke kushenku, wai ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah ran da alheri ya sauko musu.” (1 Bitrus 2:12) Halin Kirista yana nuna yawan bangaskiyarsa. Sa’ad da mutane suka lura—wato, sa’ad da suka ga cewa hali mai kyau na Kirista domin bangaskiyarsa ne—yana ɗaukaka Allah.
20 Su waye a yau suke ɗaukaka Allah ta kasance da hali mai kyau? Wane rukunin addini ne gwamnati take yabonsa don kasance da salama, masu bin doka da suke biyan harajinsu? (Romawa 13:1, 3, 6, 7) Waɗanne mutane aka sani a dukan duniya don haɗin kansu da ’yan’uwa masu bi—haɗin kai da ya sha kan bambanci na launin fātā, na ƙasa, da na ƙabila? (Zabura 133:1; Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Wane rukuni aka sani a dukan duniya don aikin ilimantarwansu na Littafi Mai Tsarki da ke sa a daraja doka, a san amfanin iyali, da tarbiyyar Littafi Mai Tsarki? Rukuni ɗaya ne kaɗai suke da hali mai kyau a waɗannan da wasu wurare da ke ba da tabbacin waɗannan abubuwa—Shaidun Jehovah ne!
Kana Ɗaukaka Allah Kuwa?
21. Me ya sa ya kamata mu bincika ko muna ɗaukaka Jehovah?
21 Yana da kyau kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Ina ɗaukaka Jehovah kuwa? Bisa Zabura ta 148, yawancin halittu suna ɗaukaka Allah. Mala’iku, sararin samaniya, duniya da halittunta na dabbobi—duka suna yabon Jehovah. (Ayoyi 1-10) Abin baƙin ciki ne cewa yawancin mutane a yau ba sa hakan! Ta yin rayuwa da ke ɗaukaka Allah, kana aikata daidai da sauran halitta da ke yabon Jehovah. (Ayoyi 11-13) Hanya ce da ta fi kyau na yin amfani da rayuwarka.
22. Domin ɗaukaka Jehovah, a waɗanne hanyoyi ka sami albarka, me ya kamata ka ƙudura niyyar yi?
22 Ta ɗaukaka Jehovah, an albarkace ka a hanyoyi da yawa. Yayin da kake ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Kristi, ka sulhunta da Allah kuma za ka more dangantaka ta salama da albarka da Ubanka na samaniya. (Romawa 5:10) Yayin da kake neman dalilai na ɗaukaka Allah, za ka daɗa kasance da hali mai kyau, kana godiya. (Irmiya 31:12) Sa’annan, za ka iya taimakon wasu su yi rayuwa ta farin ciki, mai gamsarwa, da haka kai ma za ka yi farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Bari ka kasance cikin waɗanda suka tsai da cewa za su riƙa ɗaukaka Allah—yanzu da kuma har abada!
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da yadda samaniya na zahiri yake nuna hikimar Allah da ikonsa, dubi babi 5 da 17 na littafin nan Ka Kusaci Jehovah, da Shaidun Jehovah suka buga.
b Ka duba Littafi Na 1, shafi na 853 na littafin nan Insight on the Scriptures da Shaidun Jehovah suka buga.
Ka Tuna?
• Me ya sa za mu ce masana kimiyya ba su taimaki mutane su ɗaukaka Allah ba?
• A waɗanne hanyoyi biyu addini ya hana mutane ɗaukaka Allah?
• A waɗanne hanyoyi za mu iya ɗaukaka Allah?
• Me ya sa za ka bincika ko kana ɗaukaka Jehovah?
[Akwati a shafi na 24]
“Gefen Su Waye Allah Yake?”
Wani mutum da yake cikin sojojin Mayaƙan Sama na Jamus lokacin Yaƙin Duniya na II amma daga baya ya zama Mashaidin Jehovah ya tuna haka:
“Abin da ya dame ni a shekarun waɗannan yaƙe-yaƙen . . . shi ne ganin limamai na dukan coci—Katolika, cocin Lutheran, da ’yan Bishop, da sauransu—suna wa jirgin yaƙi da mayaƙansu albarka kafin su tashi zuwa kayayyakin kisa. Sau da yawa ina tunani, ‘Gefen su waye Allah yake?’
“Sojojin Jamus suna saka bel wanda aka rubuta Gott mit uns (Allah yana tare da mu) a kansa. Amma ina mamaki, ‘Me ya sa Allah ba zai kasance da sojoji da ke wancan gefe da suke bin addini ɗaya da suke masa addu’a hakan ba?’ ”
[Hoto a shafi na 22]
A dukan duniya, Shaidun Jehovah suna ɗaukaka Allah da gaske