Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 6/1 pp. 17-22
  • Halitta Na Shelar Ɗaukakar Allah!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Halitta Na Shelar Ɗaukakar Allah!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dalilin da Ya Sa Ba Su da “Hujja”
  • Sarari na Shelar Ɗaukakar Allah
  • Taurari da Damin Taurari Masu Ban Tsoro
  • Duniya da Halittunta Suna Ɗaukaka Jehovah
  • Ikon Halitta—‘Mahaliccin Sama da Kasa’
    Ka Kusaci Jehobah
  • Su Waye Suke Ɗaukaka Allah A Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ruhu Mai Tsarki Ya Yi Aiki Wajen Halitta!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 6/1 pp. 17-22

Halitta Na Shelar Ɗaukakar Allah!

“Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.”—ZABURA 19:1.

1, 2. (a) Me ya sa ’yan Adam ba za su iya ganin ɗaukakar Allah fuska da fuska ba? (b) Ta yaya dattiɓai 24 suke ɗaukaka Allah?

“BA KA da iko ka ga fuskata: gama mutum ba shi ganina shi rayu.” (Fitowa 33:20) Haka Jehovah ya gargaɗi Musa. Saboda jikin ’yan Adam raunana ne, ba za su iya jure wa ganin ɗaukakar Allah fuska da fuska ba. Amma a cikin wahayi, manzo Yohanna ya ga Jehovah a kan kursiyinsa mai daraja.—Ru’ya ta Yohanna 4:1-3.

2 Halittu na ruhu masu aminci suna iya ganin fuskar Jehovah, ba kamar ’yan Adam ba. “Dattiɓai ashirin da huɗu” ne a wahayin samaniya da Yohanna ya gani, suna wakiltan 144,000. (Ru’ya ta Yohanna 4:4; 14:1-3) Menene suka yi sa’ad da suka ga ɗaukakar Allah? Bisa ga Ru’ya ta Yohanna 4:11, sun ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.”

Dalilin da Ya Sa Ba Su da “Hujja”

3, 4. (a) Me ya sa gaskata da Allah ba ƙin kimiyya ba ne? (b) A wasu lokatai, menene dalilin ƙin gaskata da Allah?

3 Ka motsa ka ɗaukaka Allah? Yawancin mutane ba su motsa ba, wasu ma suna musun wanzuwar Allah. Alal misali, wani mai ilimin taurari ya rubuta: “Ashe Allah ne da ikonsa ya halicce sarari domin amfaninmu? . . . Batu ne mai ban sha’awa. Amma na yarda cewa wannan yaudara ce kawai. . . . Bai isa ba kawai a ce Allah ne ya zana sararin halitta.”

4 Binciken kimiyya tana da iyaka—suna yinsa ne bisa abin da mutane suke iya gani ko kuwa koya. Idan ba haka ba, kome nazari ne kawai ko kuma ka-cici-ka-cici. Da yake “Allah ruhu ne,” ba yadda za a yi wani irin binciken kimiyya a kansa. (Yohanna 4:24) Saboda haka, girman kai ne mutum ya ƙi gaskata da Allah cewa bai jitu da ilimin kimiyya ba. Ɗan kimiyya Vincent Wigglesworth na Jami’ar Cambridge ya lura cewa kimiyya ma “tafarkin addini ne.” Ta yaya? “Kimiyya tana bisa wannan tabbatacciyar gaskiya cewa aukuwa na halitta ta dangana ne ga ‘ƙa’idodin halitta.’ ” Saboda haka, sa’ad da wani ya ƙi da wanzuwar Allah, yana musanyar imaninsa ne kawai da wani? A wasu lokatai, rashin gaskatawa kamar ƙin gaskiya ne da ganga. Mai Zabura ya rubuta: ‘Mugu, bisa tattada hancinsa, yana cewa, Ba za shi biɗa ba. Dukan tunaninsa a nan ya ke, cewa, Babu Allah.’—Zabura 10:4.

5. Me ya sa babu hujjar ƙin gaskata da Allah?

5 Duk da haka, gaskata da Allah ba imani da ba shi da tushe ba ne, domin akwai tabbaci mai ɗimbin yawa cewa Allah ya wanzu. (Ibraniyawa 11:1) Masanin taurari Allan Sandage ya ce: “Na iske shi da wuyan gaskatawa cewa irin tsari da ke cikin [sararin halitta] sun auku ne ta wurin tsautsayi. Da akwai wani tushen ƙa’idar tsari. A gare ni kam, Allah gaibi ne, domin dalilin da ya sa aka halicci wani abu mu’ujizar rayuwa ce.” Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci a Roma cewa ‘al’amuran Allah da ba su ganuwa, watau ikonsa madawwami da allahntakarsa, a sarari a ke ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su; har kuwa [marasa bi] su rasa hujja.’ (Romawa 1:20) Tun “halittar duniya”—musamman lokacin da aka halicci mutane masu basira, waɗanda sun fahimci wanzuwar Allah—an sami tabbaci cewa akwai Mahalicci mai yawan iko, Allah wanda ya isa a bauta masa. Saboda haka, waɗanda sun ƙi su yarda da ɗaukakar Allah ba su da hujja. Amma, wane tabbaci ke cikin halitta?

Sarari na Shelar Ɗaukakar Allah

6, 7. Ta yaya sammai suke shelar ɗaukaka Allah?

6 Zabura 19:1 ta amsa cewa: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.” Dauda ya gane cewa taurari suke haskaka “sararin sama,” ko kuma sarari, sun ba da tabbacin wanzuwar Allah maɗaukaki da ba za a yi musunsa ba. Ya ci gaba: “Yini yana magana da yini, kuma dare yana gwada ma dare sani.” (Zabura 19:2) Kowane dare da rana, sammai suna nuna hikimar Allah da ikonsa na halitta. Kamar sammai suna “maganar” yabo ga Allah ne.

7 Amma, ana bukatar fahimi domin a ji wannan yabon. “Babu magana garesu ko harshe: muryarsu ba ta jiyuwa.” Duk da haka, shaidar sammai da ba a ji tana da ƙarfi sosai. “Ɗamararsu ta fita har iyakar ƙasa, zantattukansu kuma har iyakacin duniya.”—Zabura 19:3, 4.

8, 9. Waɗanne gaskiya ta musamman ake da shi game da rana?

8 Sai kuma Dauda ya kwatanta wata halittar Jehovah mai ban mamaki: “A cikinsu [sararin sama] ya sanya ma rana tanti, ita fa tana kama da ango mai-fitowa daga cikin ɗakinsa, yana murna kamar ƙaƙarfan mutum garin yin tsere. Fitowarta daga iyakar nisan sama ce, zagowarta kuma zuwa iyakar nisanta: babu abin da ke ɓoye ga zafinta.”—Zabura 19:4-6.

9 Rana ƙarama ce idan aka gwada ta da wasu taurari. Duk da haka babbar tauraruwa ce, tana ƙasƙantar da wasu taurari da suke zagaya ta. Wani tushe ya ce rana ta fi duniyarmu girma sau 330,000. Wato, rana tana da girma da ta kai kusan dukan tsarin rana! Ƙarfin maganaɗiso na rana yana sa duniya tana zagayawa na nisan mil miliyan 93 ba tare da bijirewa ko kuwa ta matsa kusa ba. Zafin rana mitsitsi ne kawai yake isa duniyarmu, hakan kuwa ya isa ya rayar rayuka.

10. (a) Yaya rana take faɗuwa kuma take fitowa daga “tanti”? (b) Ƙaƙa take gudu kamar “ƙaƙarfan mutum”?

10 Mai Zabura ya yi maganar rana da furci na alama, cewa “ƙaƙarfan mutum” ne wanda yake gudu daga wani ɓangaren duniya zuwa wani da zai huta daddare a cikin “tanti.” Sa’ad da wannan babbar tauraruwa ta faɗi, kamar ta shiga cikin “tanti” ne domin ta huta a faɗuwar rana. Da safe kuma kamar ta ɓullo farat ɗaya ne, tana walƙiya “kama da ango mai-fitowa daga cikin ɗakinsa.” Da yake makiyayi ne, Dauda ya san tsananin sanyi da ake yi daddare. (Farawa 31:40) Ya tuna yadda tsirkiyar rana take ɗuma shi da kuma daji da ke kewaye shi. Hakika, ranar kamar “ƙaƙarfan mutum” ba ta gajiya da “tafiyarta” daga gabas zuwa yamma ba, tana shirye ta sake tafiyar.

Taurari da Damin Taurari Masu Ban Tsoro

11, 12. (a) Me ya sa yadda Littafi Mai Tsarki ya gwada taurari da yashi yake da ban sha’awa? (b) Yaya girman sararin halitta yake?

11 Dauda ya iya ganin taurari dubbai kalilan ne kawai domin ba shi da madubi mai kawo nesa kusa. Bisa ga wani binciken kwanan bayan nan, yawan taurari da madubi mai kawo nesa kusa yake iya gani cikin sarari sun kai miliyan miliyan sau shida—wato, bakwai mai sifiri 22! Jehovah ya nuna cewa taurari suna da ɗimbin yawa da ya gwada su da ‘yashi wanda ke a bakin teku.’—Farawa 22:17.

12 Da daɗewa, masana taurari sun lura da abin da aka kwatanta shi da “ƙananan yankuna da suke da haske da hazo hazo, da ba a bayyane ba.” Masana kimiyya a dā sun ɗauka cewa waɗannan “tarin taurari masu kama da hazo mai juyawa” suna cikin damin taurari na Kwalkwaɗa tamu. A shekara ta 1924, an gano cewa wani tarin taurari mai kama da hazo, Andromeda, da suka fi kusa, damin taurari ne—mai nisan tafiyar haske na shekara miliyan biyu!a Masana kimiyya yanzu sun kimanta cewa da akwai biliyoyin damin taurari, kowanne yana ɗauke da dubbai—wasu taurari ma—biliyoyi. Duk da haka, Jehovah “yana ƙididigan yawan taurari; dukansu yana ba su sunayensu.”—Zabura 147:4.

13. (a) Wane abu na musamman ne ke cikin tarin taurari? (b) Ta yaya aka sani cewa masana kimiyya ba su san “ƙa’idodin sammai” ba?

13 Jehovah ya tambayi Ayuba: “Ka iya ka ɗaure tattaruwan Pleiades ko ka kwance maɗauran Orion?” (Ayuba 38:31) Pleiades tarin taurari ne da suke fitowa kuma tafarkinsu dabam dabam. Ko da yake nisan taurarin suna da yawa ainu da juna, ba sa kauce wa matsayinsu a duniya. Domin an riga an shirya matsayinsu, taurari suna “taimaka a tuƙin jirgin ruwa, da ’yan sama-jannati a koyon tuƙin jirgin sama da suke yi, kuma don su san tauraruwa.” (The Encyclopedia Americana) Duk da haka, babu wanda ya iya gane tarin “tattaruwan Pleiades.” Hakika, masana kimiyya har ila ba su iya amsa tambayar da ke Ayuba 38:33 ba: “Ka san ƙa’idodin sammai?”

14. A wace hanya ce raba haske gaibi ne?

14 Masana kimiyya ba za su iya amsa wata tambaya da aka yi wa Ayuba ba: “Ta wace hanya a ke raba haske?” (Ayuba 38:24) Wani marubuci ya kira wannan bincike game da haske “tambayar da ta yi wa kimiyyar zamani wuya.” Akasarin haka, wasu ’yan falsafar Helenanci sun yarda cewa haske daga idon mutum yake. A wannan zamanin kuma, masana kimiyya suna jin cewa haske yana da burbuɗi. Wasu suna tsammanin yana tafiya cikin taguwa. A yau, ’yan kimiyya sun gaskata cewa haske yana da kamanin taguwa da kuma burbuɗi. Duk da haka, ba a iya fahimta sarai yadda “a ke raba haske” ba.

15. Kamar Dauda, yaya ya kamata mu ji sa’ad da mun lura da sammai?

15 Idan ka yi tunanin wannan sai ka ji yadda mai Zabura Dauda ya ji, wanda ya ce: “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; Wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi? Ɗan adam kuma da ka ke ziyartarsa?”—Zabura 8:3, 4.

Duniya da Halittunta Suna Ɗaukaka Jehovah

16, 17. Ƙaƙa halittu da ke cikin ‘zurfafan teku’ ke yabon Jehovah?

16 Zabura ta 148 ya lissafta wasu hanyoyi da halitta ke ɗaukaka Allah. Aya 7 ta ce: “Ku yabi Ubangiji daga duniya, ya ku dodoni na ruwa, da kuma dukan zurfafan teku.” I, “dukan zurfafa” na cike da al’ajabai da suke nuna hikima da ikon Allah. Wani babban kifi mai matsakaicin nauyin tan 120 ne—wato nauyin giwaye 30! Nauyin zuciyarsa kaɗai ya fi kilogiram 1,000 kuma yana hura jini kilogiram 6,400 cikin jikinsa! Ashe waɗannan manyan dodanin teku suna da nauyin jiki ne cikin ruwa? A’a. Wani rahoton European Cetecean Bycatch Campaign ya ce: Suna “iyo cikin teku” da gudu mai ban mamaki. Tafarkin kumbo ta nuna cewa “wani kifi ya ƙaura zuwa fiye da mil 10,000 a cikin watanni 10.”

17 Babban kifin nan dolpin yana iya tsalle daga sama zuwa daben ruwa da zurfinsa ya kai ƙafa 150, amma tsalle mafi zurfi da ya taba yi da aka rubuta shi ne na ƙafa 1,795! Ta yaya wannan sha-nono ke tsira ma irin wannan nitso? Bugun zuciyarsa yana raguwa lokacin nitsawar, kuma jininsa yana zagayawa zuwa zuciya, huhu, da ƙwaƙwalwa. Kuma tsokarsa tana ɗauke da wani magani da ke ajiyar iskar sheƙa. Babban kifin nan Elephant seals da sperm whales sukan iya nitse da zurfi sosai. Jaridar Discover ta ce, “maimakon yin tsayayya da nauyin jikinsu, suna barinsa ya danna huhunsu gaba ɗaya.” Suna ajiyar yawancin iskar sheƙa da suke amfani da shi a cikin tsokarsu. Lallai waɗannan halittun, rayayyen tabbaci ne na hikimar Allah mafi iko!

18. Ta yaya ruwan teku ke nuna hikimar Jehovah?

18 Ruwan teku ma yana nuna hikimar Jehovah. Jaridar Scientific American ta ce: “Kowane ɗigon ruwa na nisan mita 100 a babban teku yana ɗauke da dubban tsiro marar ganuwa da suke kwantawa a kan ruwa sai da madubi mai ƙara girman abu ake iya ganinsu.” Waɗannan “tsiro marar ganuwa kamar kurmi suke” da yake tsabtace iska ta wurin cire biliyoyin tan na iskar ƙuna. Ƙananan tsiro marar ganuwar nan suna ba da fiye da rabin iskar da muke sheƙawa.

19. Ta yaya wuta da dusar ƙanƙara suke cika nufin Jehovah?

19 Zabura 148:8 ta ce: “Wuta da ƙanƙara, [dusar ƙanƙara] da tururi; hadari mai-iska, suna iyarda maganatasa.” Hakika, Jehovah yana amfani ma da abubuwa marasa rai na halitta domin ya cika nufinsa. Ka yi la’akari da wuta. A shekarun da suka shige, ana ɗaukan cewa saka wuta a daji ɓarna kawai take yi. Yanzu masu bincike sun gaskata cewa wuta tana da muhimmin amfani a mahalli, tana kawar da tsofaffin itatuwa, tana taimaka wa tsiro su tsiro, tana sabonta tsarin abubuwan gina tsiro, kuma tana rage gobarar daji. Ana bukatar dusar ƙanƙara ma, tana ban ruwa, tana sa ƙasa ni’ima, tana cika koguna, tana kāre shuke-shuke da dabobbi daga yanayi mai sa daskarewa.

20. Ta yaya duwatsu da itatuwa suke amfane ’yan Adam?

20 Zabura 148:9 ta ce: “Duwatsu da dukan tuddai; itatuwa masu-’ya’ya da dukan [kurama].” Manyan duwatsu suna ba da tabbacin iko mai girma na Jehovah. (Zabura 65:6) Amma suna cika wata nufi mai kyau kuma. Wani rahoto daga Ƙungiyar Labarin Ƙasa a Bern, Switzerland, ya ce: “Dukan manyan koguna na duniya suna da maɓulɓulansu daga duwatsu ne. Kusan rabin ’yan Adam suna dogara ga ruwa da ke cikin duwatsu . . . Waɗannan ‘tankin ruwaye’ yana da muhimmanci ga rayuwar ’yan Adam.” Itatuwa da ke ko’ina ma suna ɗaukaka Mahaliccinsu. Wani rahoto daga Tsarin Mahalli na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce itatuwa “suna da amfani ƙwarai domin zaman lafiyar mutane a dukan ƙasashe . . . Wasu irin itatuwa suna da amfanin tattalin arziki kamar katako, ’ya’yan itace, ƙaro, da danƙo. A dukan duniya, mutane biliyan 2 suna amfani ne da itace don dahuwa da mai.”

21. Ka bayyana yadda ganye ya nuna tabbacin tsari.

21 Ana ganin tabbacin Mahalicci mai hikima a yadda ya shirya itatuwa. Ka yi la’akari da ganye. Bayan kamar kaki ne da ke hana ganyen bushewa. A jikin kakin, a samansa da akwai jerin ƙwayoyin rai da ba a iya gani. Waɗannan suna ɗauke da kore, wanda yake shan hasken rana. Wata hanya da haske da ƙarfi suke aiki suna kamar “masana’antar abinci.” Saiwar itacen tana ɗaukan ruwa ta kai wa ganyayen ta hanya mai wuyan ganewa kamar “tsarin aikin famfo.” Dubban ƙananan ramuka da ke jikin ganye a gefe biyun yakan rufe domin ya sha iskar ƙuna. Haske yana ba da kuzari ga ruwa da iskar ƙuna su ba da kabohaidaret. Sa’an nan itacen zai ci abincin da shi ya shirya. Ba a jin muryar wannan “masana’antar” amma mai kyau ce. Maimakon ƙazantar da wuri, yana ba da iskar sheƙa!

22, 23. (a) Waɗanne muhimman iyawa ne wasu tsuntsaye da dabbobin ƙasa suke da shi? (b) Waɗanne tambayoyi muke bukatar mu bincika?

22 Zabura 148:10 ta ce: “Dabbobi da dukan bisashe; masu-rarrafe da dukan tsuntsaye masu-fukafukai.” Yawancin dabbobin ƙasa da halittu masu firiya suna da iyawa ta ban mamaki. Tsuntsu Laysan albatross yana firiya mai nisa (a wani lokaci mil 25,000 a cikin kwanaki 90). Tsuntsu tsigi yana tafiya daga Arewacin Amirka zuwa Kudancinta, tana firiya fiye da awoyi 80 babu tsayawa. Raƙumi ba ya ajiyar ruwa a tozonsa yadda da ake tsammani, yana ajiyarsa a tsarin narke abincinsa, da yake sa ya daɗe bai ji kishi ba. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne cewa, injiniyoyi suna lura da dabbobi sosai sa’anda suke ƙera injuna da sababbin ababa. “Idan za ka gina wani abin da zai yi aiki da kyau . . . kuma ya jitu da mahallinsu,” in ji marubuciya Gail Cleere, “za ka iya samun misali mai kyau cikin halitta.”

23 Hakika, halitta na shelar ɗaukakar Allah! Daga sararin halitta zuwa tsiro, da dabbobi, kowanne a yadda suke suna yabon Mahaliccinsu. Amma mu ’yan Adam kuma fa? Ta yaya za mu haɗa da halitta a rera yabo ga Allah?

[Hasiya]

a Tafiyar haske mil 186,000 ne cikin daƙiƙa guda.

Ka Tuna?

• Me ya sa waɗanda suke musun wanzuwar Allah ba su da hujja?

• Ta yaya taurari da duniyoyi suke ɗaukaka Allah?

• Ƙaƙa dabbobin teku da na ƙasa suke ba da tabbaci cewa Mahalicci mai ƙauna ne?

• Ta yaya halitta marasa rai suke cika nufin Jehovah?

[Hoto a shafi na 18]

’Yan kimiyya sun kimanta cewa yawan taurari da ake iya gani ya kai miliyan miliyan sau shida!

[Inda aka Dauko]

Frank Zullo

[Hoto a shafi na 20]

Kifi dolpin

[Hoto a shafi na 21]

Ƙwayar dusar ƙanƙara

[Inda aka Dauko]

snowcrystals.net

[Hoto a shafi na 21]

Ɗan tsuntsu Laysan albatross

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba