-
Ka San Gaskiya Game da Allah Kuwa?Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
4. Jehobah yana so ka san sunansa kuma ka yi amfani da sunan
Ta yaya ka san cewa Jehobah yana so ka san sunansa? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
Kana ganin Jehobah yana so mutane su san sunansa? Me ya sa ka ce haka?
Jehobah yana so mutane su riƙa amfani da sunansa. Ku karanta Yowel 2:32, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne muhimmancin yin amfani da sunan Allah, Jehobah?
Yaya kake ji sa’ad da wani ya tuna da sunanka kuma ya kira ka da sunan?
Yaya kake ganin Jehobah yake ji sa’ad da ka yi amfani da sunansa?
-
-
Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan AllahKa Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
1. Ta yaya addinan ƙarya suke ɓata sunan Allah ta koyarwarsu?
Addinan ƙarya “sun mai da gaskiyar Allah ta zama ƙarya.” (Romawa 1:25) Alal misali, yawancin addinai ba sa koya wa mabiyansu sunan Allah. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne a yi amfani da sunan Allah. (Romawa 10:13, 14) Idan wani mugun abu ya faru, wasu malaman addinai sukan ce nufin Allah ne, amma hakan ba gaskiya ba ne. Allah ba ya jarrabtar kowa da mugunta. (Karanta Yakub 1:13.) Abin taƙaici, ƙaryace-ƙaryace da shugabannin addinai suke yi game da Allah, ya sa mutane ba sa ƙaunar Allah.
-