Ka ‘Fassara Kalmar Allah Daidai’
“Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.”—2 TIMOTHAWUS 2:15.
1, 2. (a) Me ya sa ma’aikata suke bukatar kayan aiki? (b) Wane aiki Kiristoci suke yi, kuma yaya suke nuna suna fara biɗan Mulkin?
MA’AIKATA suna bukatar kayan aiki don su yi aikinsu. Kasance da kowane irin kayan aiki kawai bai isa ba. Ma’aikaci yana bukatar kayan aiki da ya dace, kuma dole ya yi amfani da su a hanyar da ta dace. Alal misali, idan kana gina rumfa, kuma kana so ka haɗa katakai biyu, za ka bukaci ba kawai hamma da ƙusoshi ba. Za ka san yadda ake kafa ƙusa cikin katako ba tare da lanƙwashe ƙusan ba. Ƙoƙarin kafa ƙusa cikin katako ba tare da sanin yadda ake amfani da hamma ba zai yi wuya, zai ma sa ka yi sanyin gwiwa. Amma yin amfani da kayan aiki da kyau zai sa aikinmu ya zama mai kyau.
2 Mu Kiristoci, muna da aikin da za mu yi. Aiki ne da ya fi muhimmanci. Yesu Kristi ya aririce mabiyansa su ‘fara biɗan mulkin.’ (Matta 6:33) Yaya za mu yi hakan nan? Hanya ɗaya ita ce kasance da himma wajen aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. Sa hidimarmu ta kahu cikin Kalmar Allah wata hanya ce. Hanya ta uku kuma hali mai kyau ne. (Matta 24:14; 28:19, 20; Ayukan Manzanni 8:25; 1 Bitrus 2:12) Domin mu yi wannan aiki na Kirista da kyau da kuma farin ciki, muna bukatar kayan aiki da suka dace da kuma sanin yadda za mu yi amfani da su da kyau. Game da wannan, manzo Bulus ya kafa misali na musamman na ma’aikaci Kirista, kuma ya ƙarfafa ’yan’uwa masu bi su yi koyi da shi. (1 Korinthiyawa 11:1; 15:10) To, me za mu iya mu koya daga Bulus, abokin aikinmu?
Bulus—Mai Shelar Mulki da Himma
3. Me ya sa za a ce manzo Bulus ma’aikaci ne na Mulki mai himma?
3 Wane irin ma’aikaci ne Bulus? Babu shakka mai himma ne. Bulus ya yi himma sosai wajen yaɗa bishara a wurare masu faɗi kewaye da Bahar Maliya. Da yake ba da dalilin shelar Mulki da ƙwazo, wannan manzo mai himma sosai ya ce: “Idan ina wa’azin bishara, ba ni da abin fahariya; gama ya zama mini dole; kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.” (1 Korinthiyawa 9:16) Bulus yana son ya ceci ransa ne kawai? A’a. Shi ba mai son kai ba ne. Maimako, yana son wasu ma su amfana daga bisharar. Ya rubuta: “Ina kuwa yin abu duka sabili da bishara, domin in yi tarayya cikin samunta.”—1 Korinthiyawa 9:23.
4. Wane kayan aiki Kiristoci ma’aikata suka fi amfani da shi?
4 Manzo Bulus ma’aikaci ne mai tawali’u da ya fahimci cewa ba zai dangana gabaki ɗaya ga iyawarsa ba. Yadda kafinta yake bukatar hamma, Bulus ya bukaci kayan aiki da suka dace don ya sahinta gaskiyar Allah cikin zukatan masu sauraronsa. Wane kayan aiki musamman ya yi amfani da shi? Kalmar Allah ce, Nassosi Masu Tsarki. Haka nan ma, Littafi Mai Tsarki ne ainihin kayan aiki da muke amfani da shi wajen almajirantarwa.
5. Don mu zama masu hidima da kyau, me muke bukata mu yi ban da yin ƙaulin nassosi kawai ba?
5 Bulus ya sani cewa fassara Kalmar Allah daidai ba kawai a yi ƙaulinta ne ba. Ya yi amfani da ‘rinjaya.’ (Ayukan Manzanni 28:23) Ta yaya? Bulus ya yi nasara ta amfani da rubutacciyar Kalmar Allah ya rinjaye mutane da yawa su karɓi gaskiyar Mulki. Ya yi mahawara da su. Bulus “yana kawo dalilai, yana rinjaya[r] mutane a kan al’amura na wajen mulkin Allah,” watanni uku cikin majalisa a Afisus. Ko da “waɗansu suka taurare, suka ƙi biyayya,” wasu sun saurara. Domin hidimar Bulus a Afisus, “maganar Ubangiji ta yawaita da iko ƙwarai, ta yi nasara.”—Ayukan Manzanni 19:8, 9, 20.
6, 7. Ta yaya Bulus ya daraja hidimarsa, kuma yaya za mu yi hakan?
6 Da yake shi mai shelar Mulki ne da himma, Bulus ya ‘daraja hidimarsa.’ (Romawa 11:13) Ta yaya? Ba ya son ya ɗaukaka kansa; ba ya kuwa jin kunya a san da shi a fili cewa shi abokin aikin Allah ne. Maimakon haka, yana ɗaukan hidimarsa daraja ce mafi girma. Bulus ya fassara Kalmar Allah daidai kuma da kyau. Hidimarsa ta ba da amfani ta wajen motsa wasu, ta taimake su su yi hidimarsu da kyau. A ta haka ma, an daraja hidimarsa.
7 Kamar Bulus, za mu iya daraja aikinmu na masu hidima ta yin amfani da Kalmar Allah sosai a kai a kai. A dukan fannonin hidimarmu ta fage, muradinmu ya kamata ya zama gaya wa mutane da yawa wani abu daga Nassosi. Ta yaya za mu yi haka da rinjaya? Ka yi la’akari da hanyoyi uku masu muhimmanci: (1) Jawo hankali ga Kalmar Allah a hanya da za ta kawo daraja. (2) Ba da bayani cikin basira kuma yin amfani da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. (3) Ba da bayani daga Nassosi a hanya da take tabbatarwa.
8. Waɗanne kayan aiki na wa’azin Mulki muke da su a yau, yaya kake yin amfani da su?
8 Masu shelar Mulki na zamani suna da kayan aiki da Bulus ba shi da shi a lokacin hidimarsa. Waɗannan sun ƙunshi littattafai, jaridu, mujallu, warƙoƙi, kaset da kuma bidiyo. A ƙarnin da ya shige, an yi amfani da katuna, garmaho, motoci masu ɗauke da lasafika, da kuma wa’azi ta rediyo. Hakika, Littafi Mai Tsarki ne kayan aikinmu mafi kyau, kuma muna bukatar mu yi amfani da wannan kayan aiki na musamman da kyau.
Hidimarmu Dole ne ta Kahu Cikin Kalmar Allah
9, 10. Game da yin amfani da Kalmar Allah, me za mu iya koya daga gargaɗin da Bulus ya yi wa Timothawus?
9 Ta yaya za mu iya amfani da Kalmar Allah cewa kayan aiki ne mai kyau? Ta bin waɗannan kalmomi da Bulus ya gaya wa abokin aikinsa Timothawus: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.” (2 Timothawus 2:15) Menene ‘fassara kalmar gaskiya daidai’ ta ƙunsa?
10 Kalmar Helenanci da aka juya ‘fassara daidai’ a zahiri tana nufin “yanka a miƙe” ko kuma “a yanka babu karkata.” Sai a gargaɗin da Bulus ya yi wa Timothawus aka yi amfani da wannan furci a Nassosin Helenanci na Kiristoci. Ana iya amfani da wannan kalmar a kwatanta yin kunya da ke a miƙe a gona. Zai zama abin kunya ga manomi idan ya yi kunyoyi da suke a karkace. Don ya zama “ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi,” an tuna wa Timothawus cewa ba za a yi na’am da bijirewa daga koyarwa ta gaskiya na Kalmar Allah ba. Timothawus ba zai yarda ra’ayinsa ya rinjayi koyarwarsa ba. Dole wa’azinsa da koyarwarsa su kasance bisa Nassosi. (2 Timothawus 4:2-4) A wannan hanya, za a ja-goranci masu zukatan kirki, su kasance da ra’ayin Jehovah a kan al’amura, ba za su yi koyi da falsafa ta duniya ba. (Kolossiyawa 2:4, 8) Wannan haka yake a yau.
Dole Halinmu Ya Zama na Yabawa
11, 12. Yaya halinmu zai shafi yadda muke fassara Kalmar Allah daidai?
11 Ba kawai za mu fassara Kalmar Allah daidai ta yin shelar gaskiyarta ba. Dole halinmu ya yi daidai da ita. Da yake “mu abokan aiki na Allah ne,” ba za mu zama ma’aikata masu riya ba. (1 Korinthiyawa 3:9) Kalmar Allah ta ce: “Kai fa mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba? kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata? kai da ka ke faɗi kada a yi zina, kana yin zina? kai da ka ke ƙyamar gumaka, mai saɓon haikali ne kai?” (Romawa 2:21, 22) Saboda haka, da yake mu ma’aikata na zamani na Allah ne, hanya ɗaya na fassara Kalmar Allah daidai ita ce ta yin biyayya da wannan gargaɗin: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.
12 Waɗanne fa’idodi za mu samu daga fassara Kalmar Allah daidai? Ka yi la’akari da ikon da rubutacciyar Kalmar Allah take da shi a rayuwar mutane masu zukatan kirki.
Kalmar Allah Tana da Ikon Canja Mutum
13. Menene yin amfani da Kalmar Allah zai sa mutum ya yi?
13 Sa’ad da muka goyi bayansa, saƙon Kalmar Allah yana rinjaya da ke taimakon mutane su yi canji na musamman a rayuwarsu. Bulus ya ga kalmar Allah tana aiki kuma ya ga yadda ta shafi waɗanda suka zama Kiristoci a Tassaluniki na dā da kyau. Saboda haka, ya gaya musu: “Muna yabon Allah kuma ba fasawa, domin, sa’anda kuka karɓi maganar jawabi daga garemu, watau maganar Allah ke nan, kuka karɓe ta, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah, magana da ke aiki daga cikinku kuma, ku da ke masu-bada gaskiya.” (1 Tassalunikawa 2:13) Ga waɗancan Kiristoci—hakika, ga dukan mabiyan Kristi na gaskiya—ba za a gwada tunanin ɗan Adam da mafificiyar hikimar Allah ba. (Ishaya 55:9) Tassalunikawa sun “karɓi magana cikin ƙunci mai-yawa, tare da farinzuciya na Ruhu Mai-tsarki” kuma sun zama misalai ga wasu masu bi.—1 Tassalunikawa 1:5-7.
14, 15. Yaya ikon saƙon Kalmar Allah yake, kuma me ya sa?
14 Kalmar Allah tana da iko sosai, yadda Tushenta, Jehovah yake da shi. Ta fito daga “Allah mai-rai,” wanda ta wurin maganarsa “aka yi sammai,” kuma wannan maganar koyaushe ‘tana cika abin da aka nufa ta yi.’ (Ibraniyawa 3:12; Zabura 33:6; Ishaya 55:11) Wani manazarcin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba ya ware kansa daga Kalmarsa. Ba ya ƙinta sai ka ce sabon abu ne da bai sani ba. . . . Abin da ya faru bayan an faɗe ta yana shafansa; magami ne da Allah mai rai.”
15 Yaya ikon saƙon da ke zuwa daga Kalmar Allah yake? Yana da iko sosai. Ya dace da Bulus ya rubuta: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.”—Ibraniyawa 4:12.
16. Yaya Kalmar Allah za ta iya canja mutum gabaki ɗaya?
16 Saƙon rubutacciyar Kalmar Allah ya “fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci.” Ta haka, yana da ikon ratsa ciki mutum yadda ya wuce kowane kayan aiki na ’yan Adam. Kalmar Allah tana huda gaɓoɓin mutum kuma ta canja shi, tana shafan yadda yake tunani da kuma abin da yake so, ta sa ya zama ma’aikaci na ibada da aka amince da shi. Lallai kayan aiki ne mai iko!
17. Ka bayyana yadda Kalmar Allah take da ikon canja mutum.
17 Kalmar Allah tana nuna irin mutumin da kake a ciki idan aka gwada da yadda kake tunanin kake a zahiri ko kuma yadda mutane suke ganinka a waje. (1 Samu’ila 16:7) Har ma mugu, wani lokaci zai iya ɓoye ainihin halinsa ta wajen da’awar nuna alheri ko kuma ibada. Miyagu suna ɓoye kamaninsu. Masu fahariya suna da’awar sauƙin kai na riya domin kawai mutane su yaba musu. Ta nuna abin da yake zuciyarsa, Kalmar Allah za ta iya motsa mutum mai tawali’u ya tuɓe tsohon hali kuma ya “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afisawa 4:22-24) Koyarwar Kalmar Allah za ta iya canja mutane da suke jin kunya su zama Shaidun Jehovah masu gaba gaɗi kuma masu shelar Mulki da himma.—Irmiya 1:6-9.
18, 19. Bisa abin da aka faɗa a waɗannan sakin layi ko kuma abin da ya faru a hidimar fage, ka nuna yadda gaskiyar Nassi za ta iya canja halin mutum.
18 Ikon canja mutum da Kalmar Allah take da shi na shafan mutane a ko’ina da kyau. Alal misali, masu shelar Mulki daga Phnom Penh, Cambodia, suna wa’azi a jihar Kompong Cham sau biyu a wata. Bayan ta ji wasu limamai suna kushe wa Shaidun Jehovah, wata fasto ta shirya ta saurari Shaidun wani lokaci da suka ziyarci jihar. Ta yi musu tambayoyi game da bikin kwanakin hutu kuma ta saurara sosai sa’ad da suke mata bayani daga Nassosi. Sai ta ce: “Yanzu na sani cewa abin da ’yan’uwana fastoci suke faɗa game da ku ba gaskiya ba ce! Suna da’awa cewa ba ku amfani da Littafi Mai Tsarki, amma shi kaɗai kuka yi amfani da shi da safen nan!”
19 Wannan matar ta ci gaba da tattauna Littafi Mai Tsarki da Shaidun, barazanar cewa za a cire ta daga aikin fasto bai hana ta saurara ba. Ta gaya wa abuyarta abin da take koya daga Nassi, sai ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun. Abokiyarta ta kasance da ƙwazo game da abin da take koyo har da a lokacin wata hidima a cocinta, ta motsa ta ce, “Ku zo ku yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah!” Jim kaɗan bayan haka, fasto ɗin ta dā, da wasu kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah.
20. Ta yaya abin da ya faru wa wata mata a Ghana ya nuna ikon Kalmar Allah?
20 An nuna ikon Kalmar Allah a batun Paulina, wata mata a Ghana. Wata mai shelar Mulki na cikakken lokaci tana nazarin Littafi Mai Tsarki da ita a littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada.a Mijin Paulina yana da mata da yawa kuma ta ga bukatar ta yi canji, amma mijinta da dukan danginta suka yi hamayya da ita ƙwarai. Kakanta, wanda alƙali ne a babban kotu kuma shugaba a coci, ya yi ƙoƙari ya hana ta, ta wajen yin amfani da Matta 19:4-6 a karkace. Alƙalin kamar yana da gaskiya, amma da sauri Paulina ta fahimci cewa wannan ya yi daidai da yadda Shaiɗan ya murguɗe Nassosi sa’ad da yake gwada Yesu Kristi. (Matta 4:5-7) Ta tuna da furcin Yesu da ke a bayyane game da aure, da ya faɗi cewa Allah ya halicce ’yan Adam namiji da tamace, ba namiji da mata da yawa ba, kuma cewa biyun, ba ukun ba za su zama jiki ɗaya. Ta ɗage a shawararta kuma daga baya aka yarda mata ta kashe aure. Ba da daɗewa ba ta zama mai shelar Mulki mai farin ciki da ta yi baftisma.
Ka Ci Gaba da Fassara Kalmar Allah Daidai
21, 22. (a) Da yake mu masu shelar Mulki ne me za mu kasance da ƙudurin yi? (b) Menene za mu bincika a talifi na gaba?
21 Hakika rubutacciyar Kalmar Allah kayan aiki ne mai iko da za mu yi amfani da shi a taimakon wasu su yi canji a rayuwarsu domin su kusaci Jehovah. (Yaƙub 4:8) Yadda gwanaye suke amfani da kayan aiki su cim ma abu mai kyau, bari ya zama ƙudurinmu mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu yi amfani da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, da kyau wajen aikin da Allah ya ba mu na masu shelar Mulki.
22 Ta yaya za mu fassara Nassosi da kyau wajen aikinmu na almajirantarwa? Hanya ɗaya, ta koyar da iyawarmu ne mu zama masu koyarwa da ke rinjaya. Don Allah ku mai da hankali zuwa talifi na gaba, domin ya nuna hanyoyi da za a koyar kuma taimake wasu su karɓi saƙon Mulki.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga
Ka Tuna?
• Waɗanne kayan aiki masu shelar Mulki suke da su?
• A waɗanne hanyoyi Bulus ya kasance misali na ma’aikacin Mulki?
• Mecece fassara Kalmar Allah daidai ta ƙunsa?
• Ta yaya rubutacciyar Kalmar Jehovah take da iko?
[Hotuna a shafi na 6]
Wasu kayan aiki da Kiristoci suke amfani da su a aikin shelar Mulki