‘Zurfin Hikimar Allah!’
“Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bincika su duka!”—ROM. 11:33.
1. Kiristoci da suka yi baftisma suna da wane gata mafi girma?
WANE gata mafi girma ne aka taɓa ba ka? Da farko za ka yi tunanin wasu ayyuka da aka ba ka ko kuma girma da aka ɗanka maka. Amma, gata mafi girma da aka ba Kiristoci da suka yi baftisma shi ne kasancewa da dangantaka na kud da kud da Jehobah, Allah makaɗaici na gaskiya. Hakan ya sa muka zama ‘sanannu gare shi.’—1 Kor. 8:3; Gal. 4:9.
2. Me ya sa sanin Jehobah da kuma zama sanannu gare shi gata ne mai girma?
2 Me ya sa sanin Jehobah da kuma zama sanannu gare shi gata ne mai girma? Domin shi ne Mafi girma a dukan sararin samaniya kuma yana kāre waɗanda yake ƙauna. An hure annabi Nahum ya rubuta: “Ubangiji nagari ne, kagara ne cikin ranar wahala; ya kuwa san waɗanda ke sa danganarsu gareshi.” (Nah. 1:7; Zab. 1:6) Begen samun rai madawwami ya dangana ga sanin Allah na gaskiya da kuma Ɗansa, Yesu Kristi.—Yoh. 17:3.
3. Mene ne sanin Allah ya ƙunsa?
3 Sanin Allah ba ya nufin sanin sunansa kawai. Dole ne mu san shi a matsayin Aboki kuma mu san abin da yake so da abin da ba ya so. Yin rayuwa da ta jitu da wannan sani yana da muhimmanci wajen nuna cewa mun zo ga sanin Allah sosai. (1 Yoh. 2:4) Amma idan muna son mu san Jehobah da gaske, muna bukatar yin wani abu. Muna bukatar mu san abin da ya yi da dalilin da ya sa ya yi hakan. Idan muka ƙara fahimtar waɗannan nufe-nufen Jehobah, za mu ƙara yin mamaki game da ‘zurfin hikimar Allah.’—Rom. 11:33.
Jehobah Allah ne Mai Manufa
4, 5. (a) Kamar yadda aka yi amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki, mene ne ma’anar kalmar nan “nufi?” (b) Ka ba da misalin yadda za a cim ma wani nufi ta hanyoyi da yawa.
4 Jehobah Allah ne mai manufa, kuma Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “madawwamin nufi.” (Afis. 3:10, 11) Mene ne wannan furucin yake nufi? Kamar yadda aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “nufi” tana nuni ne ga wani maƙasudi ko kuma buri da za a cim ma ta wurin hanyoyi da yawa.
5 Alal misali: Mutum zai iya so ya yi tafiya zuwa wani wuri. Maƙasudinsa ko nufinsa shi ne ya kai wurin. Yana iya yin zaɓi dabam dabam game da irin sufurin da zai hau da kuma hanyar da zai bi. Yayin da yake tafiya a hanyar da ya zaɓa, ana iya soma yin ruwa ko hazo, go-sulo, ko kuma a rufe hanya da zai bukaci ya bi wata hanya. Zai cim ma maƙasudinsa sa’ad da ya isa wurin da yake son ya je, duk da gyare-gyare da yake bukatar ya yi.
6. Ta yaya Jehobah ya yi gyare-gyare don ya cika nufinsa?
6 Jehobah ya yi gyare-gyare da yawa domin ya cika madawwamin nufinsa. Da yake yana la’akari da ’yancin zaɓe na halittunsa masu basira, da yardan rai ya yi gyara a yadda yake cim ma nufinsa. Alal misali, bari mu yi la’akari da yadda Jehobah yake cim ma nufinsa game da Zuriya da aka yi alkawarinsa. Da farko, Jehobah ya gaya wa mutane biyu na farko: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Far. 1:28) Shin tawaye da aka yi a lambun Adnin ya sa ba a cika wannan nufin ba? A’a! Jehobah nan da nan ya yi wani abu game da wannan sabon yanayi ta wajen yin amfani da wata “hanya” don ya cim ma nufinsa. Ya annabta cewa wani “zuriya” zai zo da zai kawar da ɓarna da masu tawayen suka yi.—Far. 3:15; Ibran. 2:14-17; 1 Yoh. 3:8.
7. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya kwatanta kansa kamar yadda yake rubuce a Fitowa 3:14?
7 Yadda Jehobah yake daidaitawa zuwa sabon yanayi don ya cim ma nufinsa ya jitu da kwatancin kansa da ya yi. Sa’ad da Musa ya gaya wa Jehobah abubuwa da za su hana shi yin aiki da aka ba shi, Jehobah ya tabbatar masa cewa: “Ni ina yadda Ni ke; ya ce kuma, Haka za ka ce ma ’ya’yan Isra’ila, NI NE ya aike ni a gare ku.” (Fit. 3:14) A yare na asali, furucin da aka fassara “Ni ina yadda Ni ke” yana nufin cewa Jehobah yana iya zama kome da yake bukatar ya zama domin ya cim ma nufinsa sosai! Manzo Bulus ya kwatanta wannan da kyau a sura ta 11 ta littafin Romawa. Ya yi magana game da itacen zaitu na alama a wajen. Bincika wannan kwatancin zai sa mu nuna godiya sosai don zurfin hikimar Jehobah, ko idan begenmu na zuwan sama ne ko kuma samun rai madawwami a nan duniya.
Nufin Jehobah Game da Zuriyar da Aka Yi Annabcinsa
8, 9. (a) Waɗanne abubuwa huɗu masu muhimmanci ne za su taimaka mana mu fahimci kwatanci na itacen zaitun? (b) Amsar wace tambaya ce ta bayyana yadda Jehobah yake yin gyara don ya cika nufinsa?
8 Kafin mu fahimci kwatanci na itacen zaitun, muna bukatar mu san abubuwa huɗu game da cikar nufin Jehobah a kan zuriyar da aka yi annabcinsa. Da farko, Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa “dukan al’umman duniya za su sami albarka” ta zuriyarsa, ko kuma ’ya’yansa. (Far. 22:17, 18) Na biyu, an miƙa wa al’ummar Isra’ila da ta fito daga Ibrahim begen zama “mulki na firistoci.” (Fit. 19:5, 6) Na uku, Jehobah ya ɗauki wasu matakai don a samu “mulki na firistoci” sa’ad da yawancin Isra’ilawa ba su amince da Almasihu ba. (Mat. 21:43; Rom. 9:27-29) A ƙarshe an ba wasu gatan zama sashe na wannan zuriya ko da yake Yesu ne sashe na farko na zuriyar Ibrahim.—Gal. 3:16, 29.
9 Daga waɗannan abubuwa huɗu masu muhimmanci, mun koya a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna cewa adadin mutane 144,000 za su yi sarauta da Yesu a matsayin sarakuna da firistoci a sama. (R. Yoh. 14:1-4) An kira waɗannan “’ya’yan Isra’ila.” (R. Yoh. 7:4-8) Amma shin dukan wannan adadin 144,000 Isra’ilawa ko Yahudawa na zahiri ne? Amsar wannan tambayar ta nuna yadda Jehobah yake yin gyara don ya cika nufinsa. Bari mu gani yadda wasiƙar manzo Bulus zuwa Romawa za ta taimaka mana mu samu amsar.
“Mulki na Firistoci”
10. Wane gata na musamman ne al’ummar Isra’ila take da shi?
10 Kamar yadda aka ambata ɗazun, al’ummar Isra’ila tana da gatar tanadar da waɗanda za su zama ‘mulki na firistoci da al’umma mai tsarki.’ (Karanta Romawa 9:4, 5.) Amma mene ne zai faru sa’ad da Zuriyar da aka yi alkawarinsa ya zo? Shin al’ummar Isra’ila ta zahiri za ta tanadar da cikakken adadin Isra’ilawa na ruhaniya guda 144,000, waɗanda za su zama sashe na biyu na zuriyar Ibrahim?
11, 12. (a) A wane lokaci ne aka soma zaɓan waɗanda za su kasance cikin Mulki na samaniya, kuma yaya yawancin Yahudawa da suke zama a lokacin suka aikata? (b) Ta yaya Jehobah ya ‘cika’ adadin waɗanda za su zama zuriyar Ibrahim?
11 Karanta Romawa 11:7-10. A matsayin al’umma, Yahudawa na ƙarni na farko sun ƙi Yesu. Saboda haka, ba su samu zarafin haifan zuriyar Ibrahim ba. Amma, da akwai wasu Yahudawa masu zukatan kirki da suka yi na’am da gayyatar sa’ad da aka soma zaɓan waɗanda za su kasance cikin “mulki na firistoci” na samaniya a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Da yake su kalilan dubbai ne, waɗannan suna kama da ‘ragowa’ idan aka gwada su da dukan al’ummar Yahuda.—Rom. 11:5.
12 Amma, ta yaya Jehobah zai ‘cika’ adadin waɗanda za su zama zuriyar Ibrahim? (Rom. 11:12, 25) Ka lura da amsar da manzo Bulus ya ba da: “Ba dai cewa maganar Allah ta zama wofi ba. Gama ba dukan waɗanda ke na cikin Isra’ila [na zahiri], Isra’ilawa ne ba: ba kuwa domin zuriyan Ibrahim [’ya’ya] ne dukansu suka zama ’ya’ya [na sashe na zuriyar Ibrahim] ba . . . Wato, ’ya’yan jiki ba su ne ’ya’yan Allah ba; amma ’ya’yan alkawari ne ana lissafinsu zuriya.” (Rom. 9:6-8) Saboda haka, Jehobah ba ya bukatar cewa dole ne waɗanda za su zama sashe na zuriyar su kasance ’ya’ya na zahiri na Ibrahim.
Itacen Zaitun na Alama
13. Mene ne (a) itacen zaitun, (b) saiwarsa, (c) gangar jikinsa da kuma (d) rassan sa, suke wakilta?
13 Manzo Bulus ya ci gaba da kwatanta waɗanda suka zama sashe na zuriyar Ibrahim da rassan itacen zaitun na alama.a (Rom. 11:21) Wannan itacen zaitun da ake nomewa yana wakiltar cikar nufin Allah game da alkawarin da aka yi da Ibrahim. Saiwar itacen tana da tsarki kuma tana wakiltar Jehobah a matsayin wanda yake ba da rai ga Isra’ila ta ruhaniya. (Isha. 10:20; Rom. 11:16) Gangar jikin itacen tana wakiltar Yesu a matsayin sashe na farko na zuriyar Ibrahim. Dukan rassan suna wakiltar ‘cikakken’ adadin waɗanda suke sashe na biyu na zuriyar Ibrahim.
14, 15. Sa waye ne aka “karye” daga itacen zaitu na gida, kuma su waye aka ɗaure a kan itacen?
14 A cikin kwatancin itacen zaitun, an kamanta Yahudawa da suka ƙi Yesu da rassa na itacen zaitun da suka “karye.” (Rom. 11:17) Da haka kuma suka yi hasarar zarafin kasancewa cikin sashe na zuriyar Ibrahim. Amma su wane ne za su ɗauki matsayinsu? Yahudawa da suka yi fahariyar cewa su ’ya’yan Ibrahim ne ba za su samu wannan zarafin ba. Amma Yohanna mai baftisma ya riga ya yi musu gargaɗi cewa idan Jehobah yana son ya yi hakan, zai iya ta da ’ya’ya ga Ibrahim daga cikin duwatsu.—Luk 3:8.
15 To, mene ne Jehobah ya yi don ya cika nufinsa? Bulus ya bayyana cewa an ɗauko rassa na itacen zaitun na jeji aka ɗaura su a kan na gida don su ɗauki matsayin waɗanda suka karye. (Karanta Romawa 11:17, 18.) Da haka, a hanya ta alama an ɗauko shafaffun Kiristoci na al’ummai, kamar waɗansu da suke cikin ikilisiya ta Roma, zuwa cikin wannan itacen zaitun na alama. Ta wannan hanyar suka kasance sashe na zuriyar Ibrahim. Da farko, tun da yake ba su da zarafin kasancewa a wannan alkawari na musamman, suna kama da rassan zaitun na jeji. Amma Jehobah ya buɗe musu hanya su zama Yahudawa na ruhaniya.—Rom. 2:28, 29.
16. Ta yaya manzo Bitrus ya bayyana yadda aka kafa sabuwar al’umma ta ruhaniya?
16 Manzo Bitrus ya bayyana yanayin hakan: ‘Ku fa [Isra’ilawa na ruhaniya, haɗe da ’yan Al’umman Kiristoci] masu-ba da gaskiya, a gare ka [Yesu Kristi] daraja ke nan: Amma ga waɗanda suka ƙi ba da gaskiya, dutsen da magina suka ƙi, shi ne aka maishe shi kan ƙusurwa; kuma, Dutsen tuntuɓe, da pa na zargi; . . . Amma ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi: ku da ba jama’a ba ne a dā, amma yanzu jama’ar Allah ne, dā ba ku sami jinƙai ba, amma yanzu kun sami jinƙai.’—1 Bit. 2:7-10.
17. Ta yaya abin da Jehobah ya yi ya kasance ‘saɓanin da abin da aka saba’?
17 Jehobah ya yi wani abu da mutane da yawa ba su yi tsammaninsa ba. Bulus ya kwatanta abin da ya faru cewa ya yi “saɓanin yadda aka saba.” (Rom. 11:24) Ta yaya ya kasance hakan? Domin zai kasance abin da bai dace ba a kawo reshen itacen zaitun na jeji a ɗaura a kan na gida, amma, wasu manoma sun yi hakan a ƙarni na farko.b Haka nan ma, Jehobah ya yi wani abu mai ban mamaki. A ra’ayin Yahudawa, ’yan Al’ummai ba za su iya haifan ’ya’ya masu kyau ba. Amma, Jehobah ya mai da waɗannan zuwa sashen “al’umma” mai ba da ’ya’ya na Mulki. (Mat. 21:43) Somawa da naɗa Karniliyus, ɗan Al’umma na farko da ya zama Kirista a shekara ta 36 A.Z., an ba waɗanda ba Yahudawa ba ne zarafin shigowa cikin wannan itacen zaitun na alama.—A. M. 10:44-48.c
18. Wane zarafi ne Yahudawa na zahiri suka samu bayan shekara ta 36 A.Z.?
18 Shin hakan yana nufi cewa bayan shekara ta 36 A.Z., Yahudawa ba su da zarafin zama sashe na zuriyar Ibrahim kuma? A’a. Bulus ya bayyana: “Su kuma [Yahudawa na zahiri], idan ba su lizima cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a tswafa su ciki: gama Allah yana da iko ya sake tswafa su a ciki. Gama idan aka cire ka daga cikin abin da ke itacen zaitun na jeji bisa ga tabi’a, saɓanin tabi’a kuma aka tswafa ka cikin itacen zaitun na kirki: balle fa waɗannan, da su ke ressa na tabi’a, za a tswafa su cikin nasu itacen zaitun!”—Rom. 11:23, 24.
“Dukan Isra’ila Za Su Tsira”
19, 20. Mene ne Jehobah ya cim ma kamar yadda aka kwatanta da itacen zaitun na alama?
19 Hakika, nufin Jehobah game da “Isra’ila na Allah” yana cika a hanya mai ban al’ajabi. (Gal. 6:16) Kamar yadda Bulus ya faɗa “dukan Isra’ila za su tsira.” (Rom. 11:26) A lokacin da Jehobah ya ga ya dace “dukan Isra’ila” wato, cikakken adadi na Isra’ilawa na ruhaniya za su yi hidima a matsayin sarakuna da firistoci a sama. Babu abin da zai iya hana nufin Jehobah ya cika!
20 Kamar yadda aka annabta, Yesu Kristi zuriyar Ibrahim tare da mutane 144,000 za su kawo albarka ga “dukan al’umman duniya.” (Far. 22:18) Ta hakan, dukan mutanen Allah za su amfana daga wannan tsarin. Hakika, yayin da muke nazari a kan yadda Jehobah ya cika madawwamin nufinsa, za mu yi mamaki sosai don “zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!”—Rom. 11:33.
[Hasiya]
a Hakika, itacen zaitun ba ya wakiltar Isra’ila na zahiri. Ko da yake Isra’ila na zahiri sun haifar da sarakuna da firistoci, amma al’ummar ba ta zama mulki na firistoci ba. Doka ta hana sarakuna a Isra’ila su zama firistoci. Saboda haka, Isra’ila na zahiri ba ta kasance itacen zaitun na zahiri ba. Bulus yana kwatanta yadda nufin Allah na haifar da “mulki na firistoci” ta samu cikawa a kan Isra’ila na ruhaniya. Wannan ya ba da sabon fahimi a kan abin da aka wallafa a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 1983, shafuffuka na 14-19 na Turanci.
b Ka duba akwatin nan “Me Ya Sa Aka Ɗaura Rassan Itacen Zaitun na Jeji a Kan na Gida?”
c Hakan ya faru a ƙarshen shekara uku da rabi da aka ba Yahudawa na zahiri zarafin zama sashe na sabuwar al’umma na ruhaniya. Annabci na makonni 70 na shekaru ya annabta cewa hakan zai faru.—Dan. 9:27.
Ka Tuna?
• Mene ne muka koya game da Jehobah daga hanyar da ya cika nufinsa?
• A littafin Romawa sura ta 11, mene ne waɗannan suke wakilta . . .
itacen zaitun?
saiwarsa?
gangar jikinsa?
rassansa?
• Me ya sa hanyar ɗaura itacen ya kasance “saɓanin yadda aka saba”?
[Akwati/Hoton da ke shafi na 24]
Me Ya Sa Aka Ɗaura Rassan Itacen Zaitun na Jeji a Kan na Gida?
▪ Lucius Junius Moderatus Columella wani sojan ƙasar Roma ne da kuma manomi da ya yi rayuwa a ƙarni na farko A.Z. An fi saninsa da littattafai 12 da ya rubuta game da rayuwar karkara da kuma noma.
A cikin littafinsa na biyar, ya yi ƙaulin wannan karin magana: “Wanda ya nome itatuwan zaitun, ’ya’yan itacen yake nema, wanda ya zuba masa taki roƙan ’ya’yan yake yi; wanda ya ƙundume shi, ya sa shi ya ba da ’ya’ya dole.”
Bayan da ya kwatanta itatuwan da suke yin fure kuma ba sa ba da ’ya’ya, ya ce a yi amfani da wannan hanyar: “Tsari ne mai kyau a huɗa itatuwan da kayan aiki kuma a yi masa ɗamara da reshen da aka yanka daga itacen zaitun na jeji; sakamakon shi ne itacen zai soma ba da ’ya’ya sosai.”
[Hoton da ke shafi na 23]
Ka fahimci kwatancin itacen zaitun na alama?