-
Me Za Ka Yi don Allah Ya Amince da Bautarka?Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
2. Ta yaya za mu bauta wa Jehobah?
Jehobah ne Mahaliccinmu, saboda haka ya kamata mu bauta masa shi kaɗai. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Hakan yana nufin cewa wajibi ne mu ƙaunace shi kuma mu bauta masa shi kaɗai ba tare da yin amfani da gunki ko hoto ko kuma wani abu ba.—Karanta Ishaya 42:8.
Wajibi ne bautarmu ta zama “mai tsarki, da kuma abin karɓa” ga Jehobah. (Romawa 12:1) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu riƙa bin dokokinsa. Alal misali, waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna bin dokokinsa game da aure. Kuma suna guje wa halaye marasa kyau kamar, shan taba ko ƙwaya da kuma buguwa da giya.a
-
-
Ka Nuna Godiya don Ran da Allah Ya Ba KaKa Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
3. Ka kula da lafiyarka
Waɗanda suka yi alkawarin yin duk abin da Jehobah yake so, suna bauta masa da dukan ransu. Hakan ya yi kamar sun ba da ransu hadaya ga Allah. Ku karanta Romawa 12:1, 2, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne zai sa ka kula da lafiyarka?
A waɗanne hanyoyi ne za ka yi hakan?
-