‘Ku Huru A Cikin Ruhu’
“Cikin ƙwazo kada ku yi ragonci; kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta wa Ubangiji.”—ROM. 12:11.
1. Me ya sa Isra’ilawa suka yi hadayun dabbobi da sauransu?
JEHOBAH yana farin ciki domin sadaukarwar da bayinsa suka yi da son rai don su nuna ƙaunarsu a gare shi kuma su miƙa kansu su yi nufinsa. A zamanin dā, ya karɓi hadayun dabbobi dabam-dabam da wasu abubuwa da suka bayar. Isra’ilawa da suke neman a gafarta musu zunubansu kuma su nuna godiyarsu sun miƙa waɗannan hadayun bisa Dokar Musa. A cikin ikilisiyar Kirista, Jehobah ba ya bukatan mu miƙa irin waɗannan hadayu na zahiri. Amma, a sura ta 12 na wasiƙarsa ga Kiristocin da ke Roma, Manzo Bulus ya nuna cewa har ila muna bukatan mu miƙa hadayu. Bari mu ga yadda za mu yi hakan.
Hadaya Mai Rai
2. A matsayin Kiristoci, wace irin rayuwa ce ya kamata mu yi, kuma menene hakan ya ƙunsa?
2 Karanta Romawa 12:1, 2. A farkon wasiƙarsa, Bulus ya nuna sarai cewa Kiristoci shafaffu, Yahudawa ko kuma ’Yan Al’ummai, za su zama masu adalci ne a gaban Allah domin bangaskiyarsu, ba ayyuka ba. (Rom. 1:16; 3:20-24) A sura ta 12, Bulus ya bayyana cewa ya kamata Kiristoci su nuna godiyarsu ta wajen yin rayuwar sadaukar da kai. Don mu cim ma hakan, dole ne mu sabonta azancinmu. Domin ajizancin da muka gada, muna ƙarƙashin “shari’ar zunubi da ta mutuwa.” (Rom. 8:2) Saboda haka, muna bukatan mu canja, wato, mu “sabonta kuma cikin ruhun azancin[mu]” ta wurin canja tunaninmu gaba ɗaya. (Afis. 4:23) Za mu iya yin irin wannan canjin ne kawai ta wurin taimakon Allah da ruhunsa. Muna bukatan mu ƙoƙarta sosai, ta wajen yin amfani da hankalinmu. Hakan yana nufin cewa za mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu guji “kamantu bisa ga kamar wannan zamani,” tare da lalatattun ɗabi’unsa, ƙazamin nishaɗi da kuma tunani marar kyau.—Afis. 2:1-3.
3. Me ya sa muke ayyuka na Kirista?
3 Bulus ya gaya mana mu yi amfani da hankalinmu don mu tabbatar wa kanmu “nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” Me ya sa muke karanta Littafi Mai Tsarki a kullum, mu yi bimbini a kan abin da muka karanta, mu yi addu’a, mu halarci taron Kirista, kuma mu yi wa’azin bishara na Mulki? Muna haka ne domin dattawan ikilisiya sun aririce mu yi hakan? Hakika, muna godiya domin tunasarwa masu kyau da dattawa ke yi mana. Amma, muna yin ayyuka na Kirista ne domin ruhun Allah ya motsa mu mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah da dukan zuciyarmu. Ƙari ga haka, muna da tabbaci cewa nufin Allah ne mu yi irin waɗannan ayyukan. (Zech. 4:6; Afis. 5:10) Muna samun gamsuwa da kuma farin ciki sosai sa’ad da muka fahimci cewa ta wajen yin rayuwar Kirista na gaskiya, za mu zama karɓaɓɓu ga Allah.
Baiwa Iri-Iri
4, 5. Yaya ya kamata dattawa Kiristoci su yi amfani da baiwarsu?
4 Karanta Romawa 12:6-8, 11. Bulus ya bayyana cewa muna da baiwa iri-iri “gwargwadon alherin da aka ba mu.” Wasu cikin baiwar da Bulus ya ambata kamar yin gargaɗi da shugabanci, musamman ya shafi dattawa Kiristoci ne, waɗanda aka aririce su su yi shugabanci “da ƙwazo.”
5 Bulus ya faɗi cewa ya kamata a ga irin wannan ƙwazon a yadda dattawa suke koyarwa a matsayin malamai da kuma yadda suke cika ‘hidimarsu.’ A nan kamar Bulus yana maganar “hidima” da ake yi a cikin ikilisiya ne, ko kuma a cikin “jiki ɗaya.” (Rom. 12:4, 5) Wannan hidimar ta yi kama da wadda aka ambata a Ayyukan Manzanni 6:4, inda manzanni suka ce: “Mu dai zamu lizima kullayaumi ga addu’a da hidimar kalman.” Menene irin wannan hidimar ta ƙunsa? Dattawa Kiristoci suna yin amfani da baiwarsu su ƙarfafa waɗanda suke cikin ikilisiya. Za su nuna cewa suna yin ‘wannan hidimar’ sa’ad da suka kasance da ƙwazo wajen ba da ja-gora da kuma umurni ga ikilisiya daga Kalmar Allah ta wajen yin nazari, bincike, koyarwa da kuma ziyarar ƙarfafawa tare da addu’a. Ya kamata masu kula su yi amfani da baiwarsu da kyau kuma su kula da tumakin “da fara’a.”—Rom. 12:7, 8; 1 Bit. 5:1-3.
6. Ta yaya za mu bi shawarar da ke Romawa 12:11, ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin?
6 Bulus ya daɗa cewa: “Cikin ƙwazo kada ku yi ragonci; kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta wa Ubangiji.” Idan muka lura cewa ba mu da ƙwazo a hidimarmu, muna bukatan mu canja yadda muke nazari kuma mu daɗa yin addu’a a kai a kai don Jehobah ya ba mu ruhunsa, wanda zai taimaka mana mu yaƙi kowane rashin ƙwazo kuma mu sabonta ƙwazonmu. (Luk 11:9, 13; R. Yoh. 2:4; 3:14, 15, 19) Ruhu mai tsarki ya ƙarfafa Kiristoci na farko su yi magana game da “ayyuka masu-girma na Allah.” (A. M. 2:4, 11) Hakazalika, zai iya motsa mu mu kasance da ƙwazo a hidima, mu ‘huru a cikin ruhu.’
Tawali’u da Filako
7. Me ya sa ya kamata mu yi hidima da tawali’u da filako?
7 Karanta Romawa 12:3, 16. Baiwar da muke da ita don “alherin” Jehobah ne. Bulus ya faɗa a wani wuri: “Iyawarmu daga Allah take.” (2 Kor. 3:5, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, bai kamata mu ɗaukaka kanmu ba. Ya kamata mu fahimci cewa duk wata nasarar da muka samu a hidimarmu domin albarkar Allah ce, ba iyawarmu ba. (1 Kor. 3:6, 7) Cikin jituwa da wannan, Bulus ya ce: “Na ke fāɗa wa kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata.” Yana da muhimmanci mu daraja kanmu kuma mu samu farin ciki da gamsuwa a hidimarmu ta Mulki. Amma, zama masu filako ko kuma sanin kasawarmu, zai hana mu mu manne wa ra’ayinmu. Maimakon haka, muna bukatan mu “tuna yadda za [mu] aza da hankali.”
8. Yaya za mu guji kasancewa ‘masu hikima’ a idanunmu?
8 Wawanci ne mu yi fahariya don abubuwan da muka cim ma. “Allah [ne] wanda ke bada anfani.” (1 Kor. 3:7) Bulus ya ce Allah ya ɗiba “rabon bangaskiya” ga kowane mutum da ke cikin ikilisiya. Maimakon mu ji cewa mun fi wasu, ya kamata mu fahimci abin da wasu suke cim ma daidai da rabon bangaskiyar da suke da ita. Bulus ya daɗa cewa: “Ku yi zaman jituwa da junanku.” A cikin wata wasiƙarsa, manzon ya gaya mana “kada a yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya maida wani ya fi kansa.” (Filib. 2:3) Idan muna da tawali’u kuma muna ƙoƙartawa sosai, za mu fahimci cewa kowanne a cikin ’yan’uwanmu maza da mata ya fi mu a wata hanya. Tawali’u zai hana ‘mu zama masu hikima’ a idanunmu. Ko da yake gatan hidima na musamman zai iya sa a san wasu sosai, dukanmu za mu yi farin ciki sosai wajen cim ma ‘ƙanƙananan’ abubuwa da sau da yawa mutane ba za su gani ba.—1 Bit. 5:5.
Haɗin Kanmu Na Kirista
9. Me ya sa Bulus ya kwatanta Kiristoci da aka shafa da ruhu da gaɓoɓi jiki?
9 Karanta Romawa 12:4, 5, 9, 10. Bulus ya kwatanta shafaffu Kiristoci da gaɓoɓin jiki da suke hidima tare a ƙarƙashin Shugabansu, Kristi. (Kol. 1:18) Ya tuna wa shafaffu Kiristoci cewa jiki yana da gaɓoɓi da yawa da suke ayyuka dabam-dabam kuma ko da yake suna da yawa, “jiki ɗaya ne cikin Kristi.” Hakazalika, Bulus ya shawarci Kiristoci shafaffu da ke Afisa: “Cikin ƙauna, mu yi girma cikin abu duka zuwa cikinsa, wanda shi ne kai, wato Kristi; daga wurinsa kuwa dukan jiki, haɗaɗe kuwa ta wurin taimakon kowace gaɓa, bisa ga aikin kowane yanki gwargwadon ma’auni nasa, yana sa ƙaruwar jiki zuwa ginin kansa cikin ƙauna.”—Afis. 4:15, 16.
10. Wane iko ne ya kamata “waɗansu tumaki” su amince da shi?
10 Ko da yake “waɗansu tumaki” ba sa cikin sashen haɗaɗɗen jiki na Kristi, za su iya koyan abubuwa da yawa daga wannan kwatancin. (Yoh. 10:16) Bulus ya ce Jehobah “ya sarayar da dukan abu kuma ƙarƙashin sawayen [Kristi], ya sanya shi kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya.” (Afis. 1:22) A yau, waɗansu tumaki suna cikin “dukan abu” da Jehobah ya saka ƙarƙashin shugabancin Ɗansa. Suna cikin “dukan abin” da Kristi yake da shi da ya ɗanka wa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45-47) Saboda haka, ya kamata waɗanda suke da begen zama a duniya su amince cewa Kristi ne Shugabansu kuma su miƙa kai ga bawan nan mai aminci mai hikima da kuma Hukumarsa na Mulki da kuma dattawa da aka naɗa a matsayin masu kula a cikin ikilisiya. (Ibran. 13:7, 17) Hakan na daɗa ga haɗin kan Kiristoci.
11. Haɗin kanmu ya dangana ne a kan menene, wane gargaɗi Bulus ya ba da kuma?
11 Irin wannan haɗin kan ana yin sa ne bisa ƙauna, wato, “magamin kamalta.” (Kol. 3:14) A Romawa sura 12, Bulus ya nanata wannan, yana cewa bai kamata ƙaunarmu ta zama “na ganin ido ba” kuma “cikin ƙaunar ’yan’uwa” ya kamata mu yi “zaman daɗin soyayya da juna.” Hakan zai sa mu daraja juna. Manzon ya ce: “Kuna gabatar da juna cikin bangirma.” Hakika, dole ne mu san bambancin ƙauna da motsin rai. Ya kamata mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu sa ikilisiya ta kasance da tsabta. Sa’ad da yake ba da gargaɗi game da ƙauna, Bulus ya daɗa: “Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku rungumi abin da ke nagari.”
Nuna Karimci
12. Game da nuna karimci, menene za mu iya koya daga Kiristocin da ke Makidoniya ta dā?
12 Karanta Romawa 12:13. Ƙaunar da muke yi wa ’yan’uwanmu za ta motsa mu mu ‘rarraba dukiyarmu zuwa biyan bukatan tsarkaka’ kuma bisa iyawarmu. Ko matalauta ne mu, za mu iya raba abin da muke da shi da wasu. Sa’ad da yake rubutu game da Kiristocin da ke Makidoniya, Bulus ya ce: “Cikin gwada shan ƙunci mai-yawa, yalwar murnarsu duk da talaucinsu ainu suka yawaita zuwa wadatar sakin hannuwansu. Gama ina shaida, gwargwadon ikonsu, har gaba da ikonsu, da yardan ransu suka bayar, da naciya mai-yawa suna roƙonmu a yarda masu wannan alheri su yi tarayya cikin hidima ga tsarkaka [da ke Yahudiya].” (2 Kor. 8:2-4) Ko da yake su matalauta ne, Kiristocin da ke Makidoniya masu karimci ne sosai. Suna ganin gata ne su raba abin da suke da shi da ’yan’uwansu da ke Yahudiya.
13. Menene “gyaran baƙi” yake nufi?
13 Furcin nan “gyaran baƙi” kalma ce ta Helenanci da ke nufin ɗaukan mataki. The New Jerusalem Bible ya fassara furcin nan zuwa “neman zarafin yin karimci.” Ana nuna karimci a wasu lokatai ta wajen gayyatar wani ya ci abinci a gidanmu, kuma hakan abin yabawa ne idan ƙauna ce ta motsa mu yin hakan. Amma idan muka soma yin hakan, za mu gano wasu hanyoyi da yawa na yin karimci. Idan rashin kuɗi ko kuma rashin lafiya ya hana mu gayyatar wasu su zo gidanmu su ci abinci, muna iya ba su kunu, ko kuma wasu abubuwan da ake sha, hakan ma nuna karimci ne.
14. (a) Kalmomin Helenanci da aka fassara “gyaran baƙi” sun ƙunshi waɗanne kalmomi? (b) Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da baƙi a hidimarmu?
14 Yin karimci ya ƙunshi halinmu. Kalmar Helenanci da aka fassara “gyaran baƙi” ya ƙunshi kalmomi biyu da ke nufin “ƙauna” da “baƙo.” Yaya muke ji game da baƙi ko ’yan ƙasashen waje? Kiristocin da suka ƙoƙarta sosai don su koyi wani yare domin su yi wa baƙin da suka shigo cikin yankin ikilisiyarsu wa’azin bishara, za a iya cewa suna bin tafarkin karimci da gaske. Hakika, yawancinmu ba za mu iya koyan wani yare ba don yanayinmu. Duk da haka, mu duka za mu iya taimaka wa baƙi ta wajen yin amfani sosai da ƙasidar nan Good News for People of All Nations, wadda ke ɗauke da saƙon Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa. Ka samu sakamako mai kyau ta wajen yin amfani da wannan ƙasidar a hidima kuwa?
Nuna Juyayi
15. Ta yaya Yesu ya bi shawarar da ke Romawa 12:15?
15 Karanta Romawa 12:15. Za a iya taƙaita shawarar da Bulus ya ba da a wannan ayar da kalmomi biyu: Nuna juyayi. Muna bukatan mu fahimci yadda wani yake ji, ko yana farin ciki ne ko kuma baƙin ciki. Idan muna cike da ruhu, nuna farin cikinmu ko kuma juyayi ga wasu zai bayyana. Sa’ad da almajirai saba’in na Kristi suka dawo cike da farin ciki daga wa’azi kuma suka ba da labarin sakamako mai kyau na aikinsu, Yesu da kansa “ya yi murna a cikin ruhu mai-tsarki.” (Luk 10:17-21) Ya taya su farin ciki. A wata sassa kuma, Yesu ‘ya yi kuka da mutane da suke kuka’ sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu.—Yoh. 11:32-35.
16. Ta yaya za mu nuna juyayi, kuma su waye musamman suke bukatar su yi hakan?
16 Muna son mu bi misalin Yesu na nuna juyayi. Sa’ad da Kirista yake farin ciki, ya kamata mu taya shi ko ita farin ciki. Hakazalika, ya kamata mu nuna juyayi ga wahala da baƙin cikin da ’yan’uwanmu maza da mata suke fuskanta. Sau da yawa, za mu iya sa ’yan’uwanmu masu bi da suke wahalar sosuwar zuciya su sami sauƙi idan muka saurare su sosai cikin juyayi. A wani lokaci, za mu ga cewa hakan ya shafe mu sosai har mu kai ga nuna juyayin mu da hawaye. (1 Bit. 1:22) Ya kamata dattawa musamman, su bi shawarar da Bulus ya ba da game da nuna juyayi.
17. Menene muka koya daga Romawa sura 12 a yanzu haka, kuma menene za mu bincika a talifi na gaba?
17 Ayoyin da muka bincika a Romawa sura 12 sun ba mu shawara da za mu yi amfani da su a rayuwarmu a matsayin Kiristoci da kuma dangantakarmu da ’yan’uwanmu. A talifi na gaba, za mu bincika sauran ayoyin wannan surar, waɗanda za su tattauna yadda ya kamata mu ɗauki da kuma bi da mutane da ba sa cikin ikilisiyar Kirista, har da masu hamayya da matsananta.
Ta Hanyar Bita
• Yaya muke nuna cewa muna “huruwa a cikin ruhu”?
• Me ya sa za mu bauta wa Allah da tawali’u da filako?
• A waɗanne hanyoyi za mu nuna juyayi da tausayi ga ’yan’uwa masu bi?
[Hotunan da ke shafi na 4]
Me ya sa muke yin waɗannan ayyuka na Kirista?
[Hotunan da ke shafi na 6]
Yaya kowannenmu zai sa hannu wajen taimaka wa baƙi su koya game da Mulkin?