Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 7/1 pp. 22-26
  • “Kada Ku Sāka Ma Kowane Mutum Mugunta Da Mugunta”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kada Ku Sāka Ma Kowane Mutum Mugunta Da Mugunta”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Don Haka Ina Roƙonku”
  • “Bari Ƙauna ta Zama ba Tare da Riya Ba”
  • “Ku Albarkaci Waɗanda Ke Tsananta Ku”
  • ‘Ku Zauna Lafiya da Dukan Mutane’
  • “Kada Ku Ɗauka Ma Kanku Fansa”
  • Abin da Ya Sa Ba Ma Ramawa
  • ‘Ku Zauna Lafiya Da Dukan Mutane’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Nagarta Za Ta Yi Nasara Bisa Mugunta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Darussa Daga Wasiƙa ga Romawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Ɗaukaka Allah Da‘baki Ɗaya’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 7/1 pp. 22-26

“Kada Ku Sāka Ma Kowane Mutum Mugunta Da Mugunta”

“Kada ku sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta. Ku yi tattalin al’amura na girma a gaban dukan mutane.”—ROMAWA 12:17.

1. Wane irin hali ne ya zama gama gari?

IDAN yaro ya ture ɗan’uwansa, wanda aka ture zai fara tunanin ramawa. Hakika, ba yara kaɗai ba ne suke da irin wannan hali na ramako ba. Har manya ma suna yin haka. Idan wani ya ɓata musu rai, za su so su rama. Hakika, yawancin manya ba za su tura juna a zahiri ba, amma suna yin hakan ne cikin dabara. Wataƙila za su yaɗa mugun ƙarya game da wanda ya ɓata masu rai ko kuma su nemi hanyar hana shi samun ci gaba. Kowace hanya aka bi, manufar ɗaya ce, wato, ramuwa.

2. (a) Me ya sa Kiristoci suke guje wa yin ramuwa? (b) Waɗanne tambayoyi da kuma sura na Littafi Mai Tsarki ne za mu tattauna?

2 Ko da yake mutane sun saba rama mugunta da mugunta, Kiristoci na gaskiya suna guje wa irin wannan halin. Maimakon haka, suna ƙoƙarin su bi shawarar manzo Bulus: “Kada ku sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.” (Romawa 12:17) Menene zai motsa mu mu bi wannan mizani mai muhimmanci? Ga wanene ainihi bai kamata mu yi ramuwa ba? Wace albarka ce za mu samu idan muka guji rama mugunta da mugunta? Don mu amsa waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna kalaman Bulus kuma mu ga yadda Romawa sura 12 ta nuna cewa guje wa rama mugunta shi ne tafarkin da ya fi dacewa, na ƙauna, da filako da ya kamata mu bi. Za mu tattauna duka waɗannan hanyoyi uku ɗaya bayan ɗaya.

“Don Haka Ina Roƙonku”

3, 4. (a) Menene Bulus ya tattauna a Romawa sura 12, kuma menene ma’anar wannan furcin “don haka” da ya yi amfani da shi? (b) Ta yaya ne ya kamata alherin Allah ya shafi Kiristoci na Roma?

3 A farkon sura ta 12, Bulus ya tattauna abubuwa guda huɗu da suka shafi rayuwar Kirista. Ya kwatanta dangantakarmu da Jehobah, da ’yan’uwanmu masu bi, da marasa bi, da kuma gwamnati. Bulus ya nuna cewa akwai dalilin da ya sa ya kamata a guje wa mugun tunani, har da yin ramuwa, sa’ad da ya ce: ‘Don haka ina roƙonku ’yan’uwa, saboda yawan jinƙai na Allah.’ (Romawa 12:1;LMT) Ka lura da furcin nan “don haka,” wanda yake nufin “saboda haka.” Wato Bulus yana cewa, ‘saboda abin da na bayyana maku, ina roƙonku ku yi abin da zan gaya maku yanzu.’ Menene Bulus ya bayyana wa waɗannan Kiristoci na Roma?

4 A sura ta 1 zuwa 11 ta wasiƙarsa, Bulus ya tattauna zarafi mai kyau da aka ba Yahudawa da ’Yan Al’ummai su zama masu sarauta da Kristi a Mulkin Allah, begen da Isra’ilawa na jiki suka ƙi karɓa. (Romawa 11:13-36) Wannan gata mai tamani ya tabbata ne “saboda yawan jinkai na Allah.” Ta yaya ne ya kamata Kiristoci su ɗauki wannan alheri na Allah? Ya kamata su nuna godiyarsu ta wurin yin abin da Bulus ya sake cewa: “Ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.” (Romawa 12:1; LMT) Ta yaya ne waɗannan Kiristocin za su iya miƙa jikinsu “hadaya” ga Allah?

5. (a) Ta yaya ne mutum zai miƙa kansa “hadaya” ga Allah? (b) Wane mizani ne ya kamata ya shafi halin Kirista?

5 Bulus ya ci gaba da bayani: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (Romawa 12:2) Maimakon su ƙyale ruhun duniya ya daidaita tunaninsu, ya kamata su canja halinsu ta wurin barin tunaninsu ya zama daidai da na Kristi. (1 Korinthiyawa 2:16; Filibbiyawa 2:5) Ya kamata wannan mizanin ya shafi halin dukan Kiristoci na yau da kullum, duk da mu a yau.

6. Bisa ga dalilin da aka bayar a Romawa 12:1, 2, menene ke motsa mu mu guji ramawa?

6 Ta yaya ne abin da Bulus ya ce a Romawa 12:1, 2 yake taimaka mana? Kamar shafaffun Kiristoci na ruhu da ke Roma, muna godiya sosai saboda yadda Allah ya ci gaba da yi mana alheri kowace rana a rayuwarmu. Saboda haka, zama masu godiya yana motsa mu mu bauta wa Allah da dukan ƙarfinmu, arzikinmu, da kuma iyawarmu. Wannan sha’awa ta zuci tana motsa mu mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi tunani ba kamar duniya ba amma kamar Kristi. Kasancewa da ra’ayin Kristi yakan shafi yadda muke bi da ’yan’uwanmu masu bi da marasa bi. (Galatiyawa 5:25) Alal misali: Idan muka yi tunani kamar Kristi, za mu guji abin da zai sa mu yi ramuwa.—1 Bitrus 2:21-23.

“Bari Ƙauna ta Zama ba Tare da Riya Ba”

7. Wace irin ƙauna ce aka tattauna a Romawa sura 12?

7 Muna guje wa rama mugunta da mugunta saboda tafarki ne mai kyau, kuma na ƙauna. Ka lura da yadda manzo Bulus ya tattauna amfanin ƙauna. A cikin littafin Romawa, Bulus ya yi amfani da kalmar nan “ƙauna,” wato, (a·gaʹpe a Helenanci) sau da yawa sa’ad da yake magana a kan ƙaunar Allah da ta Kristi. (Romawa 5:5, 8; 8:35, 39) Amma, a sura ta 12, Bulus ya yi amfani da a·gaʹpe a wata hanyar dabam sa’ad da yake magana a kan ƙaunar da ake nuna wa mutane. Bayan ya ambata cewa mutane suna da kyauta dabam dabam ta ruhaniya kuma wasu masu bi suna da wannan kyautar, Bulus ya ambata wani irin halin da ya kamata duka Kiristoci su kasance da shi. Ya ce: “Bari ƙauna ta zama ba tare da riya ba.” (Romawa 12:4-9) Nuna ƙauna ga waɗansu ita ce alamar da ke nuna Kiristoci na gaskiya. (Markus 12:28-31) Bulus ya aririce mu Kiristoci mu tabbata cewa ƙaunar da muke nunawa ta gaskiya ce.

8. Ta yaya za mu iya nuna ƙauna marar riya?

8 Bayan haka, Bulus ya faɗi yadda za a nuna ƙauna marar riya, sa’ad da ya ce: “Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku lizimci abin da ke nagari.” (Romawa 12:9) ‘Ƙyama’ da kuma “lizimci” kalamai ne masu muhimmanci. Ana iya fassara ‘ƙyama’ ta zama “mugun ƙiyayya.” Dole ne mu ƙi jinin mugunta da kuma sakamakonsa. (Zabura 97:10) Kalmar nan “lizimci” fassara ce ta aikatau na Helenanci da take nufin “mannewa.” Kirista da yake nuna ƙauna ta gaskiya yana manne wa halin yin nagarta har ya zama jininsa.

9. Wane umurni ne Bulus ya maimaita a kai a kai?

9 Bulus ya maimaita wata hanya guda da za a nuna ƙauna. Ya ce: “Ku albarkaci waɗanda ke tsananta ku; ku albarkace su, kada ku la’anta.” “Kada ku sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.” “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu.” “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Romawa 12:14, 17-19, 21) Kalaman Bulus sun nuna mana yadda za mu bi da marasa bi, har da waɗanda suke hamayya da mu.

“Ku Albarkaci Waɗanda Ke Tsananta Ku”

10. Ta yaya ne za mu iya yi wa waɗanda suke tsananta mana albarka?

10 Ta yaya za mu yi amfani da umurnin da Bulus ya bayar: “Ku albarkaci waɗanda ke tsananta ku”? (Romawa 12:14) Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.” (Matta 5:44; Luka 6:27, 28) Saboda haka, wata hanya guda da muke yi wa waɗanda suke tsananta mana albarka ita ce, ta wajen yi musu addu’a, mu roƙi Allah cewa idan suna tsananta mana ne saboda rashin sani, Jehobah ya buɗe idanunsu su san gaskiya. (2 Korinthiyawa 4:4) Hakika, zai iya zama abin mamaki a ce mu roƙi Allah ya albarkaci masu tsananta mana. Duk da haka, idan muka yi tunani kamar Kristi, hakan zai sa mu nuna ƙauna ga maƙiyanmu. (Luka 23:34) Menene zai iya zama sakamakon irin wannan ƙaunar?

11. (a) Menene za mu iya koya daga misalin Istifanus? (b) Kamar yadda aka kwatanta da rayuwar Bulus, wane irin canji ne matsananta za su iya yi?

11 Istifanus ya yi wa waɗanda suka tsananta masa addu’a, kuma bai yi addu’ar a banza ba. Ba da daɗewa ba bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., masu tsananta wa ikilisiyar Kirista sun kama Istifanus, suka kai shi bayan Urushalima, suka jejjefe shi. Kafin ya mutu, ya ta da murya da ƙarfi ya ce: “Ubangiji, kada ka lissafta wannan zunubi a garesu.” (Ayukan Manzanni 7:58–8:1) Ɗaya daga cikin mutanen da Istifanus ya yi wa addu’a shi ne Shawulu, wanda ya shaida kuma ya amince a kashe Istifanus. Bayan haka, Yesu da aka ta da daga matattu ya bayyana ga Shawulu. Wannan mai tsanantawa a dā ya zama mabiyin Kristi har ya zama manzo Bulus, wanda ya rubuta wasiƙa ga Romawa. (Ayukan Manzanni 26:12-18) Daidai da addu’ar da Istifanus ya yi, Jehobah ya gafartawa Bulus zunubin zama mai tsanantawa. (1 Timothawus 1:12-16) Babu shakka, shi ya sa Bulus ya umurce Kiristoci: “Ku albarkaci waɗanda ke tsananta ku!” Bisa ga abin da ya faru da shi, ya san cewa waɗansu da suke tsananta wa mutane suna iya zama bayin Allah a nan gaba. A zamaninmu, wasu da suke tsananta wa mutane a dā sun zama masu bi saboda halin zaman lafiya na bayin Jehobah.

‘Ku Zauna Lafiya da Dukan Mutane’

12. Ta yaya umurnin da ke Romawa 12:9, 17 suka jitu da juna?

12 Wani umurnin da Bulus ya ba da game da yadda za a bi da masu bi da marasa bi shi ne: “Kada ku sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.” Wannan furcin sakamakon abin da ya ce ne a dā, wato: “Ƙyamar abin da ke mugu.” Hakika, ya mutum zai iya cewa yana ƙyamar mugunta da gaske, idan ya rama mugunta da mugunta? Yin hakan bai jitu da nuna ƙauna “ba tare da riya ba.” Sai Bulus ya ce: “Ku yi tattalin al’amura na girma a gaban dukan mutane.” (Romawa 12:9, 17) Ta yaya za mu yi amfani da waɗannan kalaman?

13. Ta yaya ne za mu iya tafiyar da al’amuranmu “a gaban dukan mutane”?

13 A wasiƙarsa ga Korinthiyawa, Bulus ya rubuta game da tsanantawar da manzannin suka fuskanta. Ya ce: “An maishe mu abin kallo ga duniya, da mala’iku, da mutane kuma. . . . Ana zaginmu, muna sa albarka; ana tsanantanmu, muna haƙuri; ana yi mana ƙire, muna bada haƙuri.” (1 Korinthiyawa 4:9-13) Hakazalika, a yau mutanen duniya suna sa wa Kiristoci na gaskiya ido. Sa’ad da waɗanda suke tare da mu suka lura da abubuwa masu kyau da muke yi a lokacin da ake tsananta mana, hakan zai sa su saurari saƙonmu na Kirista.—1 Bitrus 2:12.

14. Menene ya kamata mu yi don mu zauna lafiya da mutane?

14 Menene za mu iya yi don mu zauna lafiya da mutane? Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu. Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” (Romawa 12:18) “Idan ya yiwu” da “gwargwadon iyawarku” furci ne da ke nuna cewa zaman lafiya da waɗansu ba zai yiwu ba a kullum. Alal misali, ba za mu taka dokar Allah don muna son mu zauna lafiya da mutane ba. (Matta 10:34-36; Ibraniyawa 12:14) Duk da haka, muna yin iya ƙoƙarinmu ba tare da ƙetare mizanai masu aminci ba, don muna son mu zauna lafiya “da dukan mutane.”

“Kada Ku Ɗauka Ma Kanku Fansa”

15. Menene dalilin da ya sa Romawa 12:19 ta ce kada a yi ramuwa?

15 Bulus ya sake ba da wani dalilin da ya sa bai dace mu yi ramuwa ba; domin hakan ne tafarki mafi kyau da ya kamata mu bi. Ya ce: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” (Romawa 12:19) Kirista da ya yi ƙoƙarin yin ramuwa yana da girman kai. Ya ba kansa matsayin da ke na Allah. (Matta 7:1) Ƙari ga haka, ta wajen yin ramuwa da kansa, ya nuna rashin bangaskiya ga tabbacin da Jehobah ya bayar: “Ni zan yi sakamako.” Akasin haka, Kiristoci na gaskiya sun yarda cewa Jehobah zai “rama ma zaɓaɓunsa.” (Luka 18:7, 8; 2 Tassalunikawa 1:6-8) Shi ya sa suka bar ramuwa a hannun Allah.—Irmiya 30:23, 24; Romawa 1:18.

16, 17. (a) Menene ma’anar “tara garwashin wuta” a kan wani? (b) Ka taɓa ganin yadda alheri ya taɓa zuciyar wani marar bi? Idan haka ne, ka ba da misali.

16 Yin ramuwa a kan maƙiyi na iya sa ya daɗa muguntarsa, amma idan ka yi masa alheri zai iya kwantar masa da zuciya. Me ya sa? Ka lura da kalaman Bulus ga Kiristoci a Roma. Ya ce: “Idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka cishe shi; idan yana ƙishi, ka ba shi sha; gama garin yin haka, za ka tara masa garwashin wuta a kansa.” (Romawa 12:20; Misalai 25:21, 22) Menene wannan yake nufi?

17 “Tara masa garwashin wuta a kansa” karin magana ce da aka samo daga yadda ake narkar da ƙarfe a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ana saka sinadarin da ke zama ƙarfe a cikin wuta, kuma a ɗora garwashin wuta a bisa sinadarin da kuma ƙarƙashinsa. Garwashin wuta da aka tara a sama yana ƙara zafin wutan wanda yake sa ƙarfen ya narke har ya ware kansa daga dattin da ke cikin sinadarin. Hakazalika, ta wurin yi wa ɗan hamayya alheri, za mu iya “narkar” da muguntarsa kuma mu fito da halayensa masu kyau. (2 Sarakuna 6:14-23) Hakika, yawancin waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista sun sami gaskiya ne saboda alherin da bayin Jehobah suka yi masu.

Abin da Ya Sa Ba Ma Ramawa

18. Me ya sa ya dace kuma nuna kauna ce da yin filako idan muka guji ramawa?

18 A wannan tattaunawar na Romawa sura 12, mun ga dalilai masu muhimmanci da suka sa ba ma “sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.” Na farko, guje wa ramuwa shi ne tafarkin da ya dace da za mu bi. Saboda juyayin da Allah ya nuna mana, ya dace mu miƙa kanmu ga Jehobah kuma mu bi dokokinsa da son rai, har da dokarsa da ta ce mu ƙaunaci maƙiyanmu. Na biyu, ƙin rama mugunta da mugunta tafarki ne na ƙauna da ya kamata mu bi. Ta wajen son zaman lafiya da kuma ƙin ramuwa, za mu so mu taimaki masu yin hamayya sosai su zama masu bauta wa Jehobah. Na uku, guje wa rama mugunta da mugunta zai nuna cewa muna da filako. Ramawa da kanmu zai nuna cewa muna da girman kai, saboda Jehobah ya ce: “Ni zan yi sakamako.” Kalmar Allah kuma ta yi gargaɗi: “Lokacin da girman kai ya zo, kunya tana nan tafe: Amma wurin masu-tawali’u akwai hikima.” (Misalai 11:2) Barin ramuwa a hannun Allah zai nuna cewa muna da filako.

19. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Bulus ya kammala bayaninsa game da yadda ya kamata mu bi da mutane. Ya umurci Kiristoci: “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Romawa 12:21) Waɗanne mugayen ruhu ne muke fuskanta yau? Ta yaya za mu ci nasara a kansu? Za a tattauna amsar waɗannan tambayoyi da waɗansu a talifi na gaba.

Za Ka Iya Ba da Bayani?

• Wane umurni ne aka maimaita a kai a kai a Romawa sura 12?

• Menene zai hana mu yin ramuwa?

• Wace albarka ce mu da waɗansu za mu samu idan muka guje wa “sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta”?

[Akwati a shafi na 22]

Romawa sura 12 ta kwatanta dangantakar Kirista da

• Jehobah

• ’yan’uwa masu bi

• marasa bi

[Hoto a shafi na 23]

Wasiƙar Bulus ga Romawa ta ba Kiristoci shawara mai kyau

[Hoto a shafi na 25]

Menene za mu iya koya daga misalin almajiri Istifanus?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba