Kana A Kan Gaba Wajen Girmama ’Yan’uwa Masu Bi Kuwa?
“Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.”—ROM. 12:10.
1, 2. (a) Wane gargaɗi ne Bulus ya ba da a cikin wasiƙarsa zuwa ga Romawa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?
A CIKIN wasiƙarsa zuwa ga Romawa, manzo Bulus ya nanata muhimmancin nuna ƙauna cikin ikilisiya a matsayin Kiristoci. Ya tuna mana cewa kada ƙaunarmu ta zama na “ganin ido.” Ya kuma ambata “ƙaunar ’yan’uwa” kuma ya faɗa cewa ya kamata a nuna irin wannan ƙaunar da “daɗin soyayya.”—Rom. 12:9, 10a.
2 Hakika, ƙaunar ’yan’uwa ba son mutane ba ne kawai. Ya kamata a nuna irin wannan ƙauna ta wurin ayyuka. Ballantana ma, babu wanda zai san cewa muna da ƙauna da soyayya sai dai ko mun aikata. Shi ya sa Bulus ya daɗa wannan gargaɗin: “Kuna gabatar da juna cikin bangirma.” (Rom. 12:10b) Mene ne girmama mutane ya ƙunsa? Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a kan gaba wajen girmama ’yan’uwa masu bi? Ta yaya za mu iya yin hakan?
Daraja da Bangirma
3. Wace ma’ana ce kalmar nan “bangirma” take da shi a harsuna na asali na Littafi Mai Tsarki?
3 Ainihin kalmar Ibrananci na “bangirma” a zahiri tana nufin “nauyi.” Ana ɗaukan wanda ake girmama a matsayin mai nauyi ko kuma mai muhimmanci. Sau da yawa an fassara wannan kalmar Ibrananci a cikin Nassosi zuwa ‘ɗaukaka,’ wanda yake nuna daraja da ake nuna wa wanda ake girmama. (Far. 45:13) Kalmar Helenanci da aka fassara “bangirma” a cikin Littafi Mai Tsarki tana ɗauke da azancin daraja, muhimmanci, da tamani. (Luk 14:10) Hakika, waɗanda muke girmama suna da tamani, da kuma muhimmanci a gare mu.
4, 5. Yaya nuna girma da daraja suke da nasaba? Ka ba da misali.
4 Mene ne girmama mutane ya ƙunsa? Yana somawa da daraja su. Hakika, sau da yawa ana amfani da kalaman nan “bangirma” da “daraja” tare domin suna da nasaba. Girmama mutane yana nufin nuna musu daraja. A wata sassa, daraja tana nuna yadda muke ɗaukan ɗan’uwanmu, yayin nan kuma bangirma yana nuna yadda muke bi da ɗan’uwanmu.
5 Ta yaya Kirista zai nuna cewa yana girmama ’yan’uwa masu bi idan ba ya daraja su da dukan zuciyarsa? (3 Yoh. 9, 10) Kamar yadda shuka za ta iya girma sosai idan an sa ta a ƙasa mai kyau, hakan ma girmama mutane zai zama tabbatacce da kuma na dindindin idan ya dangana ne ga daraja ta gaske. Tun da yake bangirma na munafunci ba ta nuna daraja na gaske, za ta shuɗe da shigewar lokaci. Babu shakka, hakan ne ya sa Bulus ya soma gargaɗinsa na nuna bangirma da wannan kalmar ta kai tsaye: “Bari ƙaunan da ba na ganin ido ba ya zauna tare da ku.”—Rom 12:9; karanta 1 Bitrus 1:22.
Ka Girmama Waɗanda Aka Halicci “Bisa ga Kamanin Allah”
6, 7. Me ya sa muke bukatan mu daraja mutane?
6 Tun da yake muna bukatan daraja mutane domin mu iya girmama su, bai kamata mu manta da dalilai na Nassi da muke da su ba don daraja dukan ’yan’uwanmu. Saboda haka, bari mu bincika biyu cikin waɗannan dalilan.
7 Ba kamar sauran halittu a duniya ba, an halicci ’yan Adam “bisa ga kamanin Allah.” (Yaƙ. 3:9) Saboda haka, muna da halaye na Allah kamar su ƙauna, hikima, da yin gaskiya. Ka lura da wani abu kuma da muka samu daga Mahaliccinmu. Marubucin wannan zabura ya faɗa: “Ya Ubangiji, . . . Kai da ka sa girmanka bisa sammai. . . . Gama da kaɗan ka sa [mutum] ya gaza mala’iku, da daraja da girma kuma ka naɗa shi.” (Zab. 8:1, 4, 5; 104:1)a Allah ya naɗa ko ƙawata ’yan Adam gabaki ɗaya da daraja, girma da ɗaukaka. Saboda haka, sa’ad da muka daraja wani, wato, muna amincewa cewa Jehobah ne Tushen ɗaukaka na ’yan Adam. Idan muna da ƙwaƙƙwaran dalilai na daraja mutane gabaki ɗaya, ya kamata mu daraja ’yan’uwanmu masu bi!—Yoh. 3:16; Gal. 6:10.
Muna Cikin Iyali Ɗaya
8, 9. Bulus ya ambata wane dalili na daraja ’yan’uwa masu bi?
8 Bulus ya ambata wani dalili da ya sa muke daraja juna. Kafin ya ba da umurni mu girmama juna, ya ce: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa.” Furcin Helenanci da aka fassara “daɗin soyayya” yana nuni ga gami mai ƙarfi da ke sa iyali mai ƙauna ta kasance da haɗin kai kuma ta tallafa wa juna. Da haka, ta wajen yin amfani da wannan furcin, Bulus yana nanata cewa ya kamata dangantaka a cikin ikilisiya ya kasance da ƙarfi da kuma ƙauna yadda yake a cikin iyali mai haɗin kai. (Rom. 12:5) Bugu da ƙari, ka san cewa Bulus ya rubuta waɗannan kalmomi ga Kiristoci shafaffu, dukan waɗanda aka amince da su a matsayin ’ya’yan Uba, Jehobah. A cikin azanci mai muhimmanci, suna cikin iyali mai haɗin kai. Saboda haka, shafaffu Kiristoci a zamanin Bulus suna da dalili mai ƙarfi na daraja juna. Hakan ma yake da shafaffu a yau.
9 Waɗanda suke cikin “waɗansu tumaki” kuma fa? (Yoh. 10:16) Ko da yake ba a amince da su a matsayin ’ya’yan Allah ba, ya dace su kira juna ɗan’uwa da ’yar’uwa domin suna cikin iyalin Kirista na dukan duniya da ke da haɗin kai. (1 Bit. 2:17; 5:9) Idan waɗanda suke cikin waɗansu tumaki sun fahimci abin da ya sa suke kiran juna “ɗan’uwa” ko “’yar’uwa,” su ma suna da ƙwaƙƙwarar dalili na daraja ’yan’uwansu masu bi.—Karanta 1 Bitrus 3:8.
Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Sosai?
10, 11. Me ya sa daraja da kuma nuna bangirma suke da muhimmanci?
10 Me ya sa bangirma da kuma daraja ’yan’uwa suke da muhimmanci sosai? Domin ta wurin girmama ’yan’uwanmu maza da mata, muna sa dukan ikilisiya ta kasance da zaman lafiya da haɗin kai.
11 Hakika, mun fahimci cewa kasancewa da dangantaka na kud da kud da Jehobah da kuma samun tallafawar ruhunsa su ne tushe mai ƙarfi da muke da shi a matsayin Kiristoci na gaskiya. (Zab. 36:7; Yoh. 14:26) Hakazalika, sa’ad da ’yan’uwa masu bi suka nuna suna son mu, hakan yana ƙarfafa mu. (Mis. 25:11) Muna samun ƙarfafa sa’ad da wani ya faɗa ko kuma yi wani abu da ya nuna yana daraja mu. Yana daɗa ba mu ƙarfi mu ci gaba da yin tafiya da farin ciki kuma mu ƙuduri aniya mu kasance a kan hanyar rai. Wataƙila ka shaida hakan da kanka.
12. Ta yaya kowanenmu zai sa a kasance da yanayi na ƙauna a cikin ikilisiya?
12 Tun da yake Jehobah ya san muna bukatan a daraja mu, ta wurin Kalmarsa ya aririce mu mu “yi ɗokin daraja juna.” (Rom. 12:10, Today’s English Version; karanta Matta 7:12.) Dukan Kiristoci da suke yin amfani da wannan shawara da ba ta shuɗewa suna sa ’yan’uwanci na Kirista ya kasance da yanayi na ƙauna. Saboda haka, yana da kyau mu dakata mu tambayi kanmu, ‘Yaushe ne lokaci na ƙarshe da na nuna ta kalamai da ayyuka cewa ina daraja ɗan’uwa ko ’yar’uwa a cikin ikilisiya da dukan zuciyata?’—Rom. 13:8.
Dukanmu Mu Kasance a Kan Gaba Wajen Girmama Mutane
13. (a) Wane ne ya kamata ya kasance a kan gaba wajen girmama mutane? (b) Mene ne kalaman Bulus da ke Romawa 1:7 suka nuna?
13 Wane ne ya kamata ya kasance a kan gaba wajen girmama mutane? A cikin wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, Bulus ya kwatanta dattawan Kirista a matsayin “waɗanda ke shugabanninku.” (Ibran. 13:17) Hakika, dattawa suna shugabanci a ayyuka masu yawa. Har ila, a matsayin makiyayan tumaki, suna bukatan su kasance a kan gaba wajen girmama ’yan’uwa masu bi, har da ’yan’uwansu dattawa. Alal misali, sa’ad da dattawa suka taru don su yi la’akari da bukatu na ruhaniya na ikilisiyar, suna girmama juna ta wajen saurarawa da kyau ga furcin da wani dattijo cikinsu yake yi. Bugu da ƙari suna girmama juna ta wajen yin la’akari da ra’ayi da furcin dukan dattawa sa’ad da suke tsai da shawara. (A. M. 15:6-15) Amma ya kamata mu tuna cewa wasiƙar Bulus zuwa ga Romawa ga dukan ikilisiya ne ba ga dattawa kaɗai ba. (Rom. 1:7) Da haka, umurni a kasance a kan gaba wajen girmama mutane ya shafi dukanmu a yau.
14. (a) Ka kwatanta bambanci da ke tsakanin nuna bangirma da kuma gabatar da juna cikin bangirma. (b) Wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?
14 Ka lura kuma da wannan fanni na shawarar Bulus. Ya aririce ’yan’uwa masu bi a Roma kada kawai su nuna bangirma amma su gabatar da juna cikin bangirma. Me ya sa wannan ya kasance dabam? Ka yi tunanin wannan misalin. Malami zai aririce rukunin ɗalibai masu ilimi su koya yadda ake karatu? A’a. Sun riga sun san yadda ake karatu. Maimakon hakan, malamin zai so ya taimaka wa ɗaliban su yi karatu da kyau. Hakan nan ma, an riga an san cewa Kiristoci na gaskiya suna ƙaunar juna, wadda take motsa mu mu girmama juna. (Yoh. 13:35) Amma, kamar yadda ɗalibai masu ilimi za su samu ci gaba ta wajen kyautata iyawarsu na yin karatu, mu ma za mu ƙara ci gaba wajen gabatar da juna cikin bangirma. (1 Tas. 4:9, 10) An ba kowannenmu wannan aiki na musamman na girmama mutane. Muna iya tambayar kanmu, ‘Ina yin hakan, wato kasancewa a kan gaba wajen girmama mutane a cikin ikilisiya?’
Ka Girmama “Fakirai”
15, 16. (a) Sa’ad da muke girmama mutane, su waye bai kamata mu manta da su ba, kuma me ya sa? (b) Mene ne zai iya nuna cewa muna daraja dukan ’yan’uwanmu maza da mata da dukan zuciyarmu?
15 Sa’ad da muke girmama mutane, su waye ne a cikin ikilisiya bai kamata mu manta da su ba? Kalmar Allah ta ce: “Mai-jin tausayin fakirai yana ba da rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” (Mis. 19:17) Yaya ya kamata ƙa’idar da ke cikin waɗannan kalaman ta shafe mu yayin da muke ƙoƙari mu kasance a kan gaba wajen girmama mutane?
16 Za ka yarda cewa yawancin mutane suna ƙoƙari su girmama shugabanninsu, amma ba sa daraja waɗanda suke ƙasa da su. Amma, Jehobah ba ya haka. Ya ce: “Waɗanda su ke girmamana, ni kuma zan girmama su.” (1 Sam. 2:30; Zab. 113:5-7) Jehobah yana girmama dukan waɗanda suke bauta masa da kuma girmama shi. Ba ya mantawa da “masu-tawali’u.” (Karanta Ishaya 57:15; 2 Laba. 16:9) Muna son mu yi koyi da Jehobah. Saboda haka, idan muna son mu san yadda muke girmama mutane da gaske, yana da kyau mu tambayi kanmu, ‘Yaya nake bi da waɗanda ba sanannu ba ne, ko kuma ba su da hakki, ko matsayi a cikin ikilisiya?’ (Yoh. 13:14, 15) Amsar wannan tambayar tana nuna yawan yadda muke daraja wasu da dukan zuciyarmu.—Karanta Filibiyawa 2:3, 4.
Muna Girmama Mutane ta Wajen Ba da Lokacinmu
17. A wace hanya ce ta musamman za mu iya kasance a kan gaba wajen girmama mutane, kuma me ya sa hakan?
17 A wace hanya ce ta musamman za mu kasance a kan gaba wajen girmama dukan mutane da ke cikin ikilisiya? Ta wajen ba da lokacinmu. Me ya sa? A matsayin Kiristoci, muna da ayyuka da yawa, kuma yin ayyukan ikilisiya masu muhimmanci da muke da su suna cin lokacinmu. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da muke ɗaukan lokaci da tamani. Mu ma mun fahimci cewa bai kamata mu bukaci ’yan’uwanmu su ba mu lokacinsu mai yawa ba. Hakazalika, muna godiya sa’ad da wasu a cikin ikilisiya suka fahimci cewa bai kamata su riƙa yawan bukatar lokacinmu ba.
18. Kamar yadda aka nuna a hoton da ke shafi na 18, yaya za mu nuna muna a shirye mu ba da wasu cikin lokacinmu ga ’yan’uwa masu bi?
18 Duk da haka, mun kuma fahimci (musamman waɗanda suke hidimar makiyaya a cikin ikilisiya) cewa kasancewa a shirye mu daina ayyukanmu domin mu ba da wasu cikin lokacinmu ga ’yan’uwa masu bi yana nuna cewa muna daraja su. A wace hanya? Ta wajen barin ayyukanmu don mu ba da wasu cikin lokacinmu ga ’yan’uwanmu, muna gaya musu, ‘Kuna da amfani a wajena har ya fi muhimmanci a gare ni in ba da wasu cikin lokacina don na kasance tare da ku maimakon na ci gaba da abin da nake yi.’ (Mar. 6:30-34) Wannan ma gaskiya ne. Idan muna jinkirin barin ayyukanmu don mu ba da wasu cikin lokacinmu ga ɗan’uwanmu, muna iya sa ya ji cewa ba shi da muhimmanci a gare mu. Hakika, da akwai lokacin da ba za a iya barin batu na gaggawa ba. Har ila kasancewa a shirye, ko kuma yin jinkirin ba da wasu cikin lokacinmu ga wasu yana nuna yawan yadda muke daraja ’yan’uwanmu da dukan zuciyarmu.—1 Kor. 10:24.
Ka Ƙuduri Aniyar Kasancewa a Kan Gaba
19. Ban da ba da lokacinmu, a wace hanya ce za mu nuna muna girmama ’yan’uwa masu bi?
19 Da akwai wasu hanyoyi masu muhimmanci da za mu iya nuna muna girmama ’yan’uwa masu bi. Alal misali, sa’ad da muke ba su lokacinmu, ya kamata mu saurare su. A nan kuma Jehobah ya kafa mana misali. Dauda marubucin wannan zabura ya ce: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.” (Zab. 34:15) Muna ƙoƙari mu yi koyi da Jehobah ta wajen kafa idanunmu da kunnuwanmu, wato, dukan hankalinmu ga ’yan’uwanmu, musamman waɗanda suka nemi taimakonmu. Ta yin hakan, muna girmama su.
20. Wane tunasarwa game da girmama mutane ne ya kamata mu riƙa tunawa?
20 Kamar yadda muka bincika, muna son mu riƙa tuna dalilin da ya sa ya kamata mu daraja ’yan’uwa masu bi da dukan zuciyarmu. Ƙari ga haka, muna neman zarafi mu kasance a kan gaba wajen girmama dukan mutane, har da fakirai. Ta wajen ɗaukan waɗannan matakai, za mu ƙarfafa gami na ƙaunar ’yan’uwa da kuma haɗin kai a cikin ikilisiya. Saboda haka, bari dukanmu mu ci gaba ba kawai wajen girmama mutane ba amma musamman gabatar da juna cikin bangirma. Ka ƙuduri aniya za ka yi hakan?
[Hasiya]
a Furcin da Dauda ya yi a Zabura ta 8 na annabci ne, kuma yana nuni ga kamiltaccen mutum, Yesu Kristi.—Ibran. 2:6-9.
Ka Tuna?
• Yaya bangirma da daraja suke da nasaba?
• Waɗanne dalilai muke da su na girmama ’yan’uwa masu bi?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu girmama juna?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya girmama ’yan’uwa masu bi?
[Hoton da ke shafi na 18]
Ta yaya za mu iya girmama ’yan’uwa masu bi?