Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 10/1 pp. 26-31
  • “Ku Ƙaunaci Juna Gaya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Ƙaunaci Juna Gaya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Soyayya da Ƙauna
  • “Allah Ya Koya Muku Ku Ƙaunaci Juna”
  • Kana Bukatar Ka “Saki Zuciya” Ne?
  • Ka Faɗi Zuciyarka!
  • “Ina Farin Ciki da Kai Ƙwarai”
  • “Ubangiji Yake Mai Yawan Tausayi”
  • Ka Ci Gaba da Nuna Kauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Ma’aurata Za Su Rika Nuna Kauna Ga Juna
    Taimako don Iyali
  • Kana bin “Hanya Mafificiya” Ta Ƙauna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ku Zama da Ƙauna Mai-Huruwa Zuwa ga Junanku”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 10/1 pp. 26-31

“Ku Ƙaunaci Juna Gaya”

“Game da ƙaunar ’yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya.”—ROMAWA 12:10.

1, 2. Wace dangantaka ce wani mai wa’azi a ƙasan waje na zamani da kuma Bulus suka mora da ’yan’uwansu?

DUK shekaru 43 na hidimarsa a ƙasan waje Can Gabas, an san Don da yadda yake ƙaunar waɗanda yake wa hidima. Yayin da yake jimre wa ciwon da daga baya ya kashe shi, wasu da ya yi nazari da su dā suka yi tafiya miloli da yawa don su ziyarce shi, suka ce: “Kamsahamnida, kamsahamnida!”—wato, “Mun gode, mun gode” a yaren Koriya. Ƙaunar Don ta motsa zuciyarsu.

2 Ba misalin Don kaɗai muke da shi ba. A ƙarni na farko, manzo Bulus ya nuna ƙaunarsa sosai ga waɗanda ya yi musu hidima. Bulus ya sadaukar da kansa. Ko da mutum ne mai tabbaci, yana da taushin hali kuma yana kula, “kamar yadda mai goyo ke kula da goyonta.” Ya rubuta wa ikilisiya da ke Tasalonika: “Muna ƙaunarku ƙwarai da gaske ne ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.” (1 Tasalonikawa 2:7, 8) Daga baya, sa’ad da Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Afisawa cewa ba za su gan shi kuma ba, “duk suka fashe da kuka, suka rungume Bulus, suna ta sumbantarsa.” (Ayyukan Manzanni 20:25, 37) A bayyane yake cewa dangantaka da ke tsakanin Bulus da ’yan’uwansa ba kawai don suna bin imani ɗaya ba ne. Amma don suna ƙaunar juna ne.

Soyayya da Ƙauna

3. Ta yaya kalmomin Littafi Mai Tsarki na soyayya da ƙauna suke da nasaba?

3 A cikin Nassosi, soyayya, juyayi, da tausayi suna da nasaba ta kusa da halin Kirista da ya fi kyau—ƙauna. (1 Tasalonikawa 2:8; 2 Bitrus 1:7) Kamar fasalin kyakkyawar lu’u-lu’u, dukan waɗannan halaye na Allah suna aiki tare su ba da sakamako mai kyau. Suna jawo Kiristoci kurkusa ba kawai ga juna ba amma kuma ga Ubansu na samaniya. Shi ya sa, manzo Bulus ya aririce ’yan’uwansa masu bi: “Ƙauna ta kasance sahihiya. . . . Game da ƙaunar ’yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya.”—Romawa 12:9, 10.

4. Menene ake nufi da kalmar nan “ƙauna”?

4 Kalmar Helenanci da Bulus ya yi amfani da ita don “ƙauna” ta ƙunshi sashe biyu, ɗaya na nufin abuta ɗayan kuma, a so mutum. Yadda wani manazarcin Littafi Mai Tsarki ya yi bayani, wannan na nufin cewa za a san Kiristoci da “ibada da take nuna iyali mai ƙauna, haɗin kai, da ke tallafa wa juna.” Haka kake ji game da ’yan’uwanka Kiristoci? Yanayi mai daɗaɗawa—na abuta—ya kamata ya kasance cikin ikilisiyar Kirista. (Galatiyawa 6:10) Da haka, juyin New Testament in Modern English na J. B. Phillips ya fassara Romawa 12:10 haka: “Bari mu ƙaunaci juna kamar ’yan’uwa.” Litafi Mai-Tsarki ya ce: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa.” Kiristoci suna ƙaunar juna ba don ya kamata su yi hakan ba kawai ba don wajibi ne su yi hakan ba. Da “sahihiyar ƙauna ga ’yan’uwa” ya kamata mu “himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.”—1 Bitrus 1:22.

“Allah Ya Koya Muku Ku Ƙaunaci Juna”

5, 6. (a) Yaya Jehovah ya yi amfani da taron ƙasashe ya koya wa mutanensa game da ƙauna ta Kirista? (b) Yaya gami da ke tsakanin ’yan’uwa yake ƙarfi da shigewar lokaci?

5 Ko da a wannan duniya “ƙaunar yawancin mutane” tana sanyi, Jehovah yana koya wa mutanensa na zamani su “ƙaunaci juna.” (Matiyu 24:12; 1 Tasalonikawa 4:9) Taro na dukan ƙasashe na Shaidun Jehovah lokatai ne na musamman na wannan koyarwar. A waɗannan taron, Shaidu suna saduwa da ’yan’uwa da suke ƙasashe masu nisa, kuma da yawa sun ba masu halartar taro daga wasu ƙasashe masauki a gidajensu. A wani taro kwanan nan, wasu sun zo daga ƙasashe inda mutane ba sa nuna sosuwar zuciyarsu a fili. “Sa’ad da masu halartar suka isa da farko, ba su saki jiki ba kuma suna kunya,” in ji wani Kirista da ya taimaka da aikin wurin kwanciya. “Amma bayan kwanaki shida sa’ad da suke wa juna ban kwana, su da masu masaukinsu suna rungumar juna suna kuka. Sun ji daɗin ƙauna ta Kirista da ba za su taɓa mantawa ba.” Nuna wa ’yan’uwanmu halin karɓan baƙi, ko daga ina suka fito, zai kawo amfani mafi kyau ga baƙon da kuma mai karɓan baƙin.—Romawa 12:13.

6 Waɗannan labarai na taro suna da daɗi, amma Kiristoci suna daɗa kasance da dangantaka ta kud da kud sa’ad da suka bauta wa Jehovah tare na dogon lokaci. Sa’ad da muka san ’yan’uwanmu da kyau, za mu yi sha’awar halayensu mafi ban sha’awa—na gaskiya, na tabbaci, na aminci, na kirki, alheri, na la’akari, juyayi, da rashin son kai. (Zabura 15:3-5; Karin Magana 19:22) Mark da ya yi hidima na ƙasan waje a Afirka ta Gabas ya ce, “Yin aiki da zuciya ɗaya tare da ’yan’uwanmu na sa a ƙulla gami da ba a karyawa.”

7. Menene ake bukata a gare mu don mu more ƙauna ta Kirista cikin ikilisiya?

7 Don a cim ma kuma ci gaba da irin wannan gami cikin ikilisiya, waɗanda suke ciki dole su jawo kusa ga juna. Ta wajen halartan taron Kirista a kai a kai, muna ƙarfafa gami da ’yan’uwanmu. Ta kasancewa a wajen taro kafin lokaci da kuma bayan taron, muna ƙarfafa da kuma ta da juna a tsimi don mu “yi ƙauna da aiki nagari.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Wani dattijo a Amirka ya ce: “Na tuna sosai cewa sa’ad da nake yaro, iyalina ne na ƙarshe da suke barin Majami’ar Mulki, muna more abokantaka da taɗi mai kyau yadda ya yiwu.”

Kana Bukatar Ka “Saki Zuciya” Ne?

8. (a) Menene Bulus yake nufi sa’ad da ya aririce Korantiyawa su “saki zuciya”? (b) Menene za mu yi don mu ƙara ƙauna cikin ikilisiya?

8 Don mu nuna irin wannan ƙauna, muna bukatar mu “saki” zuciyarmu. Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiya da ke Koranti: “Mun saki zuciya da ku ƙwarai. Ai, ba wata rashin yarda a zuciyarmu.” Bulus ya aririce su su “saki zuciya” su ma. (2 Korantiyawa 6:11-13) Kai ma za ka iya ‘sakin zuciya’ a yadda kake nuna ƙaunarka? Ba ka bukatar ka jira sai wasu sun soma ƙaunarka. A wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus ya haɗa bukatar nuna ƙauna da wannan shawara: “Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa.” (Romawa 12:10) Don ka ba wa mutane girma, za ka soma gai da su a taro. Kana iya gayyatarsu su bi ka a hidimar fage ko kuma sa’ad da kake shirya taro. Yin hakan na sa ƙauna ta ƙaru.

9. Menene wasu suka yi don su zama aminai da Kiristoci masu bi? (Ka haɗa da misalai daga yankin.)

9 Iyalai da mutane ɗaiɗai cikin ikilisiya za su iya su “saki zuciya” ta ziyarar juna, wataƙila cin abinci tare, da yin ayyuka masu kyau tare. (Luka 10:42; 14:12-14) Hakop yana shirya yawon shan iska da ƙananan rukuni lokaci lokaci. Ya ce: “Yara da manya suna wajen, da kuma iyaye gwauraye, kowa yana koma gida da farin ciki, kuma wannan ya sa suna kurkusa da juna.” Da yake mu Kiristoci ne, ya kamata mu yi ƙoƙari mu zama ba kawai ’yan’uwa masu bi ba amma aminai.—3 Yahaya 14.

10. Menene za mu iya yi sa’ad da muke da damuwa da ’yan’uwanmu?

10 Amma wani lokaci, ajizanci zai iya kawo kaluɓale ga ƙulla abokantaka da ƙauna. Menene za mu yi? Na farko, za mu yi addu’a don dangantaka mai kyau da ’yan’uwanmu. Nufin Allah ne bayinsa su yi abokantaka da juna, kuma zai amsa irin wannan sahihiyar addu’a. (1 Yahaya 4:20, 21; 5:14, 15) Ya kamata mu aikata daidai da addu’o’inmu. Ric, wani mai kula mai ziyara a Afirka ta Gabas, ya tuna da ɗan’uwa da halinsa na saurin fushi ya sa yake da wuya mutane su yi sha’ani da shi. Ric ya ba da bayani: “Maimako na guji ɗan’uwan, na ƙudura niyya na san shi sosai, na fahimci cewa baban ɗan’uwan mai tsanantawa ne. Bayan da na fahimci yadda ɗan’uwan ya yi fama ya sha kan halinsa da cin gaba da ya yi, na yi sha’awarsa. Muka zama abokai sosai.”—1 Bitrus 4:8.

Ka Faɗi Zuciyarka!

11. (a) Menene ake bukata don ƙauna ta ƙaru a cikin ikilisiya? (b) Me ya sa kaɗaici yake da lahani a ruhaniya?

11 A yau, mutane da yawa suna rayuwa ba tare da ƙulla abuta ta kud da kud da kowa ba. Abin baƙin ciki ne! Wannan ba zai zama haka ba—kuma bai kamata ya zama haka a cikin ikilisiyar Kirista ba. Ƙaunar ’yan’uwa ba kawai yin taɗi da kuma nuna hali mai kyau ba ne; ba kuwa yawan nuna sosuwar zuciya ba ne. Maimakon haka, ya kamata mu kasance a shirye mu faɗi zuciyarmu, yadda Bulus ya yi ga Korantiyawa, kuma mu nuna wa ’yan’uwanmu masu bi cewa mun damu da gaske game da zaman lafiyarsu. Ko da ba kowa ba ne yake son sha’ani da wasu ko yawan magana, yawan kaɗaitawa yana da lahani. Littafi Mai Tsarki ya yi kashedi: “Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da ke daidai ba zai yarda ba.”—Karin Magana 18:1.

12. Me ya sa sadarwa da kyau yake da muhimmanci ga dangantaka ta kud da kud a ikilisiya?

12 Sadarwa tana da muhimmanci ga abuta ta gaskiya. (Yahaya 15:15) Dukanmu muna bukatar abokai da za mu iya gaya musu zuciyarmu da yadda muke ji. Ban da haka, idan mun san juna sosai zai yi sauƙi mu biya bukatar juna. Idan mun damu da harkokin juna a wannan hanya, muna nuna ƙauna, kuma za mu shaida gaskiyar kalmomin Yesu: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35; Filibiyawa 2:1-4.

13. Menene za mu iya yi don mu nuna muna ƙaunar ’yan’uwanmu da gaske?

13 Don ƙaunarmu ta kasance da amfani sosai muna bukatar mu nuna ta. (Karin Magana 27:5) Idan ƙaunarmu ta gaske ce, za a gani a fuskarmu kuma za ta iya motsa zuciyar mutane su ƙaunace mu. Mutum mai hikima ya rubuta: “Fuska mai fara’a takan sa ka yi murna.” (Karin Magana 15:30) Ayyuka masu kyau na ƙara sa a nuna ƙauna. Ko da babu wanda zai iya sayan ƙauna ta gaske, kyauta da aka ba da da zuciya ɗaya tana da muhimmanci. Kati, wasiƙa da “manufar da aka bayyana sosai”—dukan waɗannan za su nuna ƙauna. (Karin Magana 25:11; 27:9) Muddin muka soma abota da mutane, dole mu ci gaba ta nuna ƙauna marar sonkai. Musamman a lokacin bukata, za mu so mu tallafa wa abokanmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “A koyaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, ’yan’uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.”—Karin Magana 17:17.

14. Menene za mu yi idan mutum kamar ba ya son mu yi abokantaka da shi?

14 Hakika, ba za mu iya kusa da kowa da ke cikin ikilisiya ba. Akwai wasu da za mu fi kusa da su. Saboda haka, idan wani bai yi kusa da kai ba yadda kake so, kada ka yi saurin kammala cewa akwai matsala tsakanin ka da mutumin. Kuma kada ka yi ƙoƙari ka tilasta wa mutumin ya soma dangantaka ta kud da kud da kai. Idan ka yi ƙoƙari ka yi abuta da mutum iyakar yadda yake so, za ku iya abokantaka ta kud da kud nan gaba.

“Ina Farin Ciki da Kai Ƙwarai”

15. Yaya yabawa ko kuma rashinta ke shafan mutane?

15 Babu shakka, a lokacin baftismarsa Yesu ya yi farin ciki sa’ad da ya ji murya daga sama: “Ina farin ciki da kai ƙwarai”! (Markus 1:11) Wannan furci na amincewa ya tabbatar wa Yesu cewa Ubansa yana ƙaunarsa. (Yahaya 5:20) Abin baƙin ciki, wasu ba sa samun irin wannan yabawa daga waɗanda suke ƙauna da kuma daraja. “Matasa da yawa kamar ni ba su da waɗanda suke cikin iyali da ke bin imaninsu na Kirista,” in ji Ann. “A gida sai sūkanmu ake yi. Wannan na sa mu baƙin ciki.” Amma sa’ad da suka shigo cikin ikilisiya, suna ganin ƙaunar iyali na ruhaniya da ke kula da kuma tallafawa—baba, mama, da ’yan’uwa da suke cikin iyalin imani.—Markus 10:29, 30; Galatiyawa 6:10.

16. Me ya sa halin kushe wasu ba ya taimako?

16 A wasu al’adu, da kyar iyaye, tsofaffi, da malamai su yabi matasa da dukan zuciyarsu, suna tunani cewa irin wannan yabo zai iya sa su zama ragwaye ko masu girman kai. Irin wannan tunani zai iya shafan iyalan Kirista da kuma ikilisiya. Idan suna magana game da jawabi ko wani abu da matashi ya yi, tsofaffi suna iya cewa: “Yana da kyau, amma za ka daɗa ƙoƙari!” Ko kuma a wata hanya, sukan nuna ba sa son wani matashi. Ta yin hakan, mutane da yawa sun gaskata cewa suna motsa matasa su daɗa ƙoƙari sosai ne. Amma irin wannan mataki sau da yawa bai da amfani, da yake matasa suna iya daina ko su ji ba za su iya cika irin wannan farilla ba.

17. Me ya sa za mu nemi zarafi mu yabi mutane?

17 Amma bai kamata a yabi mutum kawai don ana son a yi masa gargaɗi ba. Yabo na gaske na sa ƙauna ta ƙaru cikin iyali da kuma ikilisiya, wannan na ƙarfafa matasa su nemi ’yan’uwa da suka ƙware don shawara. Maimakon mu ƙyale al’ada ta zama ja-gorarmu a yadda muke bi da mutane, bari mu “ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.” Ka yi yabo yadda Jehovah yake yi.—Afisawa 4:24.

18. (a) Matasa, yaya ya kamata ku ɗauki gargaɗi daga tsofaffi? (b) Me ya sa tsofaffi suke mai da hankali a yadda suke ba da gargaɗi?

18 A wata sassa, matasa kada ku kammala cewa idan tsofaffi suka yi muku gargaɗi ko kuma ba ku shawara, yana nufin ba sa son ku ne. (Mai Hadishi 7:9) Akasarin haka! Mai yiwuwa don sun damu da kai ne kuma suna ƙaunarka. Idan ba haka ba, me ya sa za su dami kansu da yi maka magana game da batun? Domin sun san yadda magana take shafan mutane, tsofaffi, musamman dattawa na ikilisiya sau da yawa suna tunani sosai da kuma addu’a kafin su ba da gargaɗi, tun da yake suna son su yi abu mai kyau.—1 Bitrus 5:5.

“Ubangiji Yake Mai Yawan Tausayi”

19. Me ya sa waɗanda aka ɓata musu rai za su nemi taimakon Jehovah?

19 Munanan abubuwa da suka shaida na iya sa wasu su ji cewa nuna ƙauna zai kai ga ɓacin rai kawai. Suna bukatar gaba gaɗi da bangaskiya mai ƙarfi su gaya wa wasu zuciyarsu kuma. Amma kada su manta cewa Jehovah “ba ya nesa da kowane ɗayanmu.” Yana gayyatarmu mu kusace shi. (Ayyukan Manzanni 17:27; Yakubu 4:8) Ya fahimci cewa muna tsoro kada a ɓata mana rai, kuma ya yi alkawari zai tallafa mana kuma ya taimake mu. Mai Zabura Dauda ya tabbatar mana: “Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.”—Zabura 34:18.

20, 21. (a) Ta yaya muka sani cewa za mu iya kasancewa da dangantaka na kusa da Jehovah? (b) Menene ake bukata don a more dangantaka na kud da kud da Jehovah?

20 Abota ta kud da kud da Jehovah ne dangantaka da ta fi muhimmanci da za mu yi. Amma irin wannan gami zai yiwu kuwa? Hakika. Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda maza da mata masu aminci suka yi kusa da Ubanmu na samaniya. An adana furcinsu mai daɗaɗa rai don ya ba mu tabbaci cewa mu ma za mu iya matsa kusa da Jehovah.—Zabura 23, 34, 139; Yahaya 16:27; Romawa 15:4.

21 Kowannenmu zai iya yin abin da Jehovah yake bukata don a yi abota da shi. Dauda ya yi tambaya: “Wanene zai iya zama cikin Haikalinka? . . . Sai dai mutumin da ke biyayya ga Allah da kowane abu, yana kuwa aikata abin da ke daidai, wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya.” (Zabura 15:1, 2; 25:14) Yayin da muka ga cewa bauta wa Allah yana kawo amfani mai kyau kuma sa mu samu ja-gorarsa da kāriya, za mu san yadda “Ubangiji yake mai yawan tausayi.”—Yakubu 5:11.

22. Wane irin dangantaka ne Jehovah yake son mutanensa su mora?

22 Albarka ce gare mu da Jehovah yake son ya kasance da irin wannan dangantaka da mutane ajizai! Saboda haka bai kamata mu nuna ƙauna ga juna ba? Da taimakon Jehovah, kowannenmu zai nuna kuma a nuna masa ƙauna da ke na ’yan’uwancinmu na Kirista. A cikin Mulkin Allah, za a nuna wa kowa a duniya irin wannan ƙaunar har abada.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Wane irin yanayi ya kamata ya kasance cikin ikilisiyar Kirista?

• Yaya kowannenmu zai sa a daɗa nuna ƙauna a cikin ikilisiya?

• Ta yaya yabo da dukan zuciya ke sa ƙauna ta Kirista ta ƙaru?

• Ta yaya ƙaunar Jehovah ke tallafa kuma kiyaye mu?

[Hoto a shafi na 27]

Ƙauna tsakanin Kiristoci ba kawai abin da ya kamata su yi ba ne

[Hotuna a shafuffuka na 28, 29]

Za ku iya ‘sakin zuciya’ a nuna ƙauna?

[Hoto a shafi na 30]

Kuna sūka ko kuma ƙarfafawa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba