Yanzu Ne Lokaci Na Alheri”
“Ga shi yanzu ne lokaci na alheri; ga shi, yanzu ne ranar ceto.”—2 KOR. 6:2.
1. Me ya sa muke bukata mu san abin da ya fi muhimmanci da dole ne mu yi a wani lokaci?
“GA KOWANE niya akwai nasa kwanaki, akwai lokaci kuma domin kowane abu a ƙarƙashin sama.” (M. Wa. 3:1) Sulemanu yana rubutu ne game da muhimmancin sanin lokacin da ya fi kyau don yin wani abu mai amfani, ko yin noma ne, yin tafiya, kasuwanci, ko kuma tattaunawa da wasu. Har ila, muna bukata kuma mu san aikin da ya fi muhimmanci da dole ne mu yi a wani lokaci. A wata sassa, dole ne mu san abubuwa da suka fi muhimmanci a gare mu.
2. Sa’ad da Yesu yake wa’azi, yaya muka sani cewa yana sane da lokacin da yake ciki?
2 Sa’ad da yake duniya, Yesu ya san lokacin da yake ciki da abin da yake bukatar ya yi. Da yake ya san abubuwa da suka fi muhimmanci a gare shi, ya san cewa lokaci ya kai da annabcen-annabcen Almasihu da yawa da ake jira da daɗewa za su cika. (1 Bit. 1:11; R. Yoh. 19:10) Yana da aikin da zai yi don ya sanar cewa shi ne Almasihu da aka yi alkawarinsa. Zai ba da shaida sosai game da koyarwar Mulki kuma ya tattara waɗanda za su yi tarayyar gādo a nan gaba da shi a cikin Mulkin. Kuma dole ne ya kafa tushe don ikilisiyar Kirista da za ta yi aikin wa’azi da almajirantarwa har iyakar duniya.—Mar. 1:15.
3. Ta yaya sanin lokaci ya shafi ayyukan Yesu?
3 Sanin wannan yanayin gaggawa ya motsa Yesu sosai ya kasance da himma wajen yin nufin Ubansa. Ya gaya wa almajiransa: “Girbi dayawa ya ke, amma ma’aikata kadan suke: ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi shi aiki ma’aikata cikin girbinsa.” (Luk 10:2; Mal. 4:5, 6) Yesu ya zaɓi 12 da farko kafin ya zaɓi 70 daga cikin almajiransa, kuma ya ba su takamammun umurni, kuma ya aika su su yi wa’azin saƙon mai motsa mutane su aikata: “Mulkin sama ya kusa.” Game da Yesu da kansa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda Yesu ya gama ba almajiransa goma sha biyu umurni, ya tashi daga wurin, domin ya yi koyaswa da wa’azi a cikin biranensu.”—Mat. 10:5-7; 11:1; Luk 10:1.
4. A wacce hanya ce Bulus ya yi koyi da Yesu Kristi?
4 Yesu kamiltaccen misali ne na himma da kuma na ba da kai ga dukan mabiyansa. Wannan ne manzo Bulus yake magana a kai sa’ad da ya umurci ’yan’uwansa masu bi: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Kor. 11:1) A wacce hanya ce Bulus ya yi koyi da Kristi? Musamman ta wurin yin iyakacin ƙoƙarinsa a wa’azin bishara. A cikin wasiƙu da Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiyoyi, mun sami kalamai irin su “cikin ƙwazo kada ku yi ragonci,” “kuna bauta wa Ubangiji,” “kullum kuna yawaita cikin aikin Ubangiji,” da kuma “iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji.” (Rom. 12:11; 1 Kor. 15:58; Kol. 3:23) Bulus bai taɓa manta da abin da ya faru a hanyar Dimashka ba da kuma kalaman Yesu da almajiri Hananiya ya gaya masa daga baya ba: “Wannan santali zaɓaɓe ne a gare ni, zai ɗauki sunana gaban al’ummai da sarakuna, da ’ya’yan Isra’ila.”—A. M. 9:15; Rom. 1:1, 5; Gal. 1:16.
“Lokaci na Alheri”
5. Mene ne ya motsa Bulus ya yi hidimarsa da himma?
5 Idan muka karanta littafin Ayyukan Manzanni, za mu ga dalla-dalla gaba gaɗi da kuma himma da Bulus ya nuna a wajen yin hidima. (A. M. 13:9, 10; 17:16, 17; 18:5) Bulus ya fahimci muhimmancin lokacin da ya yi rayuwa. Ya ce: “Ga shi, yanzu ne lokaci na alheri; ga shi, yanzu ne ranar ceto.” (2 Kor. 6:2) Shekara ta 537 K.Z., lokaci ne na alheri ga waɗanda suke zaman bauta a Babila su koma ƙasarsu. (Isha. 49:8, 9) Amma mene ne Bulus yake nufi a nan? Mahallin ya taimaka mana mu ga abin da yake nufi.
6, 7. Wace ɗaukaka mai girma ce aka ba Kiristoci shafaffu a yau, da kuma waɗanda suke aiki tare da su?
6 A farkon wasiƙarsa, Bulus ya yi magana game da ɗaukaka mai girma da aka ba shi da kuma ’yan’uwansa Kiristoci shafaffu. (Karanta 2 Korintiyawa 5:18-20.) Ya bayyana cewa Allah ya kira su don wani abu na musamman, don su yi “hidima ta sulhu,” su roƙi mutane su “sulhuntu ga Allah.”
7 Tun lokacin da aka yi tawaye a Adnin, dukan ’yan Adam suna bāre ko a ware daga Jehobah. (Rom. 3:10, 23) Kasancewa a ware daga Allah ya sa ’yan Adam gabaki ɗaya su kasance cikin duhu na ruhaniya, hakan ya kawo wahala da mutuwa. Bulus ya rubuta: “Mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” (Rom. 8:22) Amma Allah ya ɗauki matakai don ya aririce ko ya “roƙi” mutane su dawo, ko kuma su sulhunta da shi. Wannan hidima ne aka ɗanka wa Bulus da kuma ’yan’uwansa shafaffu Kiristoci a lokacin. Wannan “lokaci na alheri” zai iya zama “ranar ceto” ga waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu. Dukan shafaffu Kiristoci da abokansu, “waɗansu tumaki,” da suke aiki tare da su sun ci gaba da gayyatar mutane su amfana daga “lokaci na alheri.”—Yoh. 10:16.
8. Mene ne ya sa kiran a sulhunta da Allah yake da ban mamaki?
8 Roƙo a sulhunta da Allah yana da ban mamaki domin ko da ’yan Adam ne suke da alhakin ɓata dangantakarsu da Allah don tawayen da aka yi a Adnin, Allah da kansa ne ya fara ɗaukan mataki don ya magance matsalar. (1 Yoh. 4:10, 19) Mene ne ya yi? Bulus ya amsa: “Allah yana cikin Kristi yana sulhunta duniya zuwa kansa, ba ya lissafta laifofinsu a gare su ke nan, ya kuma damƙa mana maganar sulhu.”—2 Kor. 5:19; Isha. 55:6.
9. Mene ne Bulus ya yi don ya nuna godiyarsa don jin ƙan Allah?
9 Ta wajen yin tanadin hadayar fansa, Jehobah ya sa ya yiwu a gafarta laifofin waɗanda suka ba da gaskiya kuma a mai da su ga dangantaka da shi ko kuma su jitu da shi. Ƙari ga haka, ya aika da wakilansa su aririci mutane a ko’ina su sulhunta da shi yayin da za su iya. (Karanta 1 Timotawus 2:3-6.) Da yake ya fahimci nufin Allah da kuma lokaci da yake zama ciki, Bulus ya ba da kansa sosai a “hidima ta sulhu.” Nufin Jehobah bai canja ba. Hakan nufinsa ne har ila a zamaninmu. Har ila, kalaman Bulus cewa “yanzu ne lokaci na alheri” kuma “yanzu ne ranar ceto” suna da muhimmanci. Jehobah, Allah ne mai jin ƙai da tausayi!—Fit. 34:6, 7.
Kada Ka Karɓe Shi a “Banza”
10. Mene ne “ranar ceto” take nufi ga shafaffu Kiristoci a dā da kuma zamanin yau?
10 Waɗanda suka fara amfanawa daga wannan nuni na alheri sune waɗanda suke “cikin Kristi.” (2 Kor. 5:17, 18) A gare su, “ranar ceto” ta soma a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Tun daga lokacin, an ɗanka wa waɗannan aikin shelar “maganar sulhu.” A yau, shafaffu Kiristoci da suka rage suna yin “hidima ta sulhu.” Sun fahimci cewa mala’iku huɗu waɗanda manzo Yohanna ya gani a wahayi na annabci suna “riƙe da iskoki huɗu na duniya, domin kada kowane iska ya hura bisa ƙasa.” Saboda haka, har ila “ranar ceto” ce da kuma “lokaci na alheri.” (R. Yoh. 7:1-3) Saboda haka, tun farkon ƙarni na ashirin, shafaffu da suka rage suna yin wannan aikin “hidima ta sulhu” da himma zuwa wurare masu nisa na duniya.
11, 12. A farkon ƙarni na ashirin, ta yaya shafaffu Kiristoci suka nuna cewa suna sane da lokaci da suke ciki? (Ka duba hoton da ke shafi na 15.)
11 Alal misali, kamar yadda aka faɗa a littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, sa’ad da ƙarni na ashirin ya kusa, “C. T. Russell da abokansa sun gaskata sosai cewa suna lokacin kaka kuma mutane suna bukatar su ji gaskiya da za ta ’yantar da su.” Mene ne suka yi game da wannan? Da yake sun fahimci cewa suna lokacin kaka, wato, “lokaci na alheri,” waɗannan ’yan’uwan ba sa ganin ya isa kawai su gayyaci mutane su zo su saurari jawabi na addini. Limaman Kiristendam suna hakan da daɗewa. Maimakon haka, waɗannan shafaffu Kiristoci sun soma bincika wasu hanyoyi masu kyau na yaɗa bishara. Alal misali, sun yi amfani mai kyau da fasaha na zamani don su faɗaɗa aikinsu.
12 Don su yaɗa bishara ta Mulki, wannan ƙaramin rukuni na masu hidima da himma sun yi amfani da warƙoƙi, mujallu, da littattafai. Sun kuma rubuta jawabai da talifofi kuma suka rarraba su don a wallafa a cikin dubban jaridu. Sun watsa jawabai na ruhaniya ta gidan rediyo na cikin ƙasar da kuma na dukan ƙasashe. Sun wallafa da kuma yi amfani da majigi da aka saka wa sauti, kafin ma masu yin fim suka fito da silima da aka saka wa sauti don mutane su kalla. Mene ne sakamakon irin wannan himma? A yau, akwai mutane miliyan bakwai da suka yi na’am da kuma sa hannu a shelar saƙon: “Sulhuntu ga Allah.” Hakika, waɗannan bayin Jehobah na farko misalai ne masu kyau na masu himma duk da cewa ba su da yawa kuma ba su ƙware ba.
13. Wane nufin Allah ne ya kamata mu riƙa tunawa?
13 Furcin Bulus cewa “yanzu ne lokaci na alheri” har ila gaskiya ne. Mu da muka shaida alherin Jehobah muna godiya cewa an ba mu zarafi mu ji da kuma karɓi saƙon sulhu. Maimakon mu gamsu da kanmu, muna ɗaukan kalaman Bulus na gaba da muhimmanci: “Muna roƙonku kuwa kada ku karɓi alherin Allah banza.” (2 Kor. 6:1) Nufin alherin Allah shi ne ya “sulhunta duniya zuwa kansa” ta wurin Kristi.—2 Kor. 5:19.
14. Waɗanne abubuwa ne suke faruwa a ƙasashe da yawa?
14 Yawancin mutane da Shaiɗan ya makantar da su har ila suna ware daga Allah kuma ba su san nufin alherin Allah ba. (2 Kor. 4:3, 4; 1 Yoh. 5:19) Amma, yanayin duniya da take daɗa muni yana sa mutane da yawa su saurari saƙon sa’ad da aka nuna musu cewa kasancewa a bāre daga Allah ne dalilin da ya sa ’yan Adam suke fuskantar mugunta da wahala. Har yawancin mutane a ƙasashen da ba sa son su ji game da aikinmu na wa’azi, a yanzu suna saurarar bisharar kuma suna ɗaukan mataki don su sulhunta ga Allah. Shin mun fahimci cewa yanzu ne ya kamata mu kasance da himma wajen shelar wannan roƙo: Ku “sulhuntu ga Allah”?
15. Maimakon mu riƙa wa’azin saƙo kawai don mu sa mutane su yi farin ciki, mene ne muke son mutane a ko’ina su sani?
15 Aikinmu ba kawai mu gaya wa mutane cewa idan sun soma bauta wa Allah zai taimaka musu da dukan matsalolinsu kuma za su samu sauƙi ba. Abin da mutane da yawa suke nema ne sa’ad da suka je coci, kuma coci da yawa suna ɗokin biyan wannan muradin. (2 Tim. 4:3, 4) Ba wannan ba ne manufar hidimarmu. Bisharar da muke wa’azinta ita ce cewa, Jehobah a cikin ƙaunarsa yana shirye ya gafarta laifofi ta wurin Kristi. Saboda haka, mutane za su daina kasancewa a bāre kuma su sulhunta ga Allah. (Rom. 5:10; 8:32) Amma, “lokaci na alheri” ya kusan ƙarewa.
“Kuna Huruwa a Cikin Ruhu”
16. Mene ne ya taimaki Bulus ya kasance da gaba gaɗi da kuma himma?
16 To, ta yaya za mu gina da kuma ci gaba da kasancewa da himma don bauta ta gaskiya? Wasu suna iya zama masu jin kunya ko kuma ba sa yawan magana kuma hakan zai sa ya yi musu wuya su kasance da fara’a. Amma, yana da kyau a tuna cewa kasancewa da himma ba kawai abin da ake nunawa a fili ba ne kuma bai dangana ga mutuntakar mutum ba. Bulus ya nuna yadda za a ci gaba da kasancewa da irin wannan himma sa’ad da ya aririce Kiristoci masu bi: “Kuna huruwa a cikin ruhu.” (Rom. 12:11) Ruhun Jehobah ya taimaki manzon ya kasance da gaba gaɗi da kuma jimiri a aikin wa’azi. Tun daga lokacin da Yesu ya kira shi har zuwa sa’ad da aka ɗaura shi a kurkuku na ƙarshe kuma aka kashe shi a Roma, fiye da shekara talatin, Bulus ya ci gaba da kasancewa da himma. Ya ci gaba da dogara ga Allah, wanda ta ruhunsa ya ba Bulus ƙarfin da yake bukata. Ya ce: “Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.” (Filib. 4:13) Za mu iya amfana sosai ta wurin koya daga misalinsa!
17. Ta yaya za mu riƙa “huruwa a cikin ruhu”?
17 A Romawa 12:11, manzo Bulus ya yi amfani da kalmar Helenanci da a zahiri tana nufin “tafasawa.” Don ruwa ya ci gaba da tafasawa, muna bukata mu ci gaba da hura masa wuta. Haka nan ma, don mu ci gaba da “huruwa a cikin ruhu,” muna bukata a ci gaba da zubo mana ruhun Allah. Za a yi mana hakan idan muka yi amfani da dukan tanadodi da Jehobah yake yi don ya ƙarfafa mu a ruhaniya. Hakan yana nufin mu ɗauki bautarmu ta iyali da ikilisiya da muhimmanci, muna nazari na kanmu da na iyali a kai a kai, mu riƙa yin addu’a a ko da yaushe, kuma muna halartan taro da ’yan’uwanmu Kiristoci. Waɗannan tanadodi za su taimaka mana muna “huruwa a cikin ruhu,” kamar wuta da ke sa ruwa ya ci gaba da tafasawa.—Karanta Ayyukan Manzanni 4:20; 18:25.
18. A matsayin Kiristoci da suka yi baftisma, ya kamata mu mai da hankali ga wane muradi?
18 Mutum da ya keɓe kansa yana mai da hankali gabaki ɗaya a kan muradi ɗaya kuma ba a janye hankalinsa da sauƙi ko kuma ya yi sanyin gwiwa don biɗan wannan muradin. A matsayin Kiristoci da suka yi baftisma, muradinmu shi ne mu yi duk abin da Jehobah yake son mu yi, kamar yadda Yesu ya yi. (Ibran. 10:7) A yau, nufin Jehobah shi ne mutane da yawa su sulhunta da shi. Saboda haka, bari mu kasance da himma sosai wajen yin koyi da Yesu da Bulus a wannan aikin da ya fi muhimmanci da kuma gaggawa da za a cim ma a yau.
Ka Tuna?
• Mene ne “hidima ta sulhu” da aka ɗanka wa Bulus da sauran shafaffu Kiristoci?
• Ta yaya shafaffu da suka rage suke yin amfani da “lokaci na alheri” da kyau?
• Ta yaya Kiristoci masu hidima za su riƙa “huruwa a cikin ruhu”?
[Hoton da ke shafi na 12]
Bulus bai taɓa manta da abin da ya faru a hanyar Dimashka ba