-
2 | Kar Ka Rama da MuguntaHasumiyar Tsaro (Na Wa’azi)—2022 | No. 1
-
-
Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
“Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta . . . Ku yi iyakar ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. Kada ku zama masu ramuwa . . . Don kuwa a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, ‘Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji Ubangiji.’”—ROMAWA 12:17-19.
Abin da Ayar Take Nufi:
Ba laifi ba ne mu yi fushi idan wani ya mana laifi, amma Allah ba ya so mu rama. Ya ce mu yi haƙuri domin nan ba da daɗewa ba, zai gyara kome.—Zabura 37:7, 10.
-