Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 7/1 p. 31
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ku Zauna Lafiya Da Dukan Mutane’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 7/1 p. 31

Tambayoyi Daga Masu Karatu

A Romawa 12:19, manzo Bulus yana nufin kada Kiristoci su yi fushi ne da ya ce: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi”?

A tsanance, a’a. A nan manzo Bulus yana nufin fushin Allah ne. Hakika, wannan ba ya nufin cewa Kiristoci ba za su lura da zancen fushi ba. Littafi Mai-Tsarki ya gargaɗe mu wajen yin fushi. Yi la’akari da wasu gargaɗi na Allah.

“Ka daina yin fushi, ka rabu da hasala: Kada ka dami ranka, wannan ba ya kawo kome ba sai mugunta.” (Zabura 37:8) “Kowanene ya yi fushi da ɗan’uwansa ya shiga hatsarin hukunci.” (Matta 5:22) “Ayyukan jiki fa a bayyane su ke, fasikanci ke nan, ƙazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kishe-kishe, hasala.” (Galatiyawa 5:19, 20) “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku.” (Afisawa 4:31) “Kowane mutum shi yi hanzarin ji, shi yi jinkirin yin magana, shi yi jinkirin yin fushi.” (Yaƙub 1:19) Bugu da ƙari, sau da yawa littafin Misalai ya faɗakar da mu game da yin fushi ko kuma hasala a kan wasu ƙananan laifi da kuskure da mutane ke yi mana.—Misalai 12:16; 14:17, 29; 15:1; 16:32; 17:14; 19:11, 19; 22:24; 25:28; 29:22.

Matani na Romawa 12:19 daidai yake da wannan gargaɗin. Bulus ya ce ya kamata ƙaunarmu ta kasance babu riya, mu albarkaci waɗanda suke tsananta mana, mu yi kirki ga wasu, kada mu rama mugunta da mugunta, kuma mu yi ƙoƙarin zaman lafiya da kowa. Sai kuma ya aririta da cewa: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.”—Romawa 12:9, 14, 16-19.

Hakika, ya kamata kada mu yarda fushi ya sa mu yi ramako. Yadda muke ganin abubuwa da kuma yin gaskiya ba cikakke ba ne. Idan muka yarda fushi ya sa mu yin ramako, zai sa muna aika abin da ba daidai ba. Wannan zai cika nufin Maƙiyin Allah ne, Iblis. A wani waje kuma Bulus ya rubuta: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.”—Afisawa 4:26, 27.

Abu mafi kyau, kuma mafi hikima shi ne a bar Allah ya san ko yaushe kuma a kan waye zai yi ramako. Zai iya yin haka don ya san kome kuma duk ramakon da ya yi zai yi daidai da kamiltaccen mizaninsa na yin gaskiya. Za mu iya gani cewa wannan shi ne abin da Bulus yake nufi a Romawa 12:19 idan mun lura da abin da ya ɗauko daga Kubawar Shari’a 32:35, 41, da ya haɗa da waɗannan kalmomi: “Ramawa gareni ta ke, da sakamako kuma.” (Gwada da Ibraniyawa 10:30.) Saboda haka, ko da furcin nan “na Allah” ba ya cikin ayoyin Helenanci, wasu masu fassara na zamani sun saka shi cikin Romawa 12:19. Wannan ya sa wasu karatun ya zama “bari Allah ya yi ramako” (The Contemporary English Version); “ku kauce ma fushin Allah” (American Standard Version); “bari Allah ya horar idan zai yi hakan” (The New Testament in Modern English); “ku bar sakamako na Allah ne.”—The New English Bible.

Ko idan an zage mu ko kuma magabtan gaskiya sun tsananta mana, za mu iya dogara ga kwatanci da aka yi na Jehovah Allah da Musa ya ji: “Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi: ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.”—Fitowa 34:6, 7, tafiyar tsutsa tamu ce.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba