Sarautar Shaiɗan Ba Za Ta Yi Nasara ba
“Babu lafiya ga miyagu.”—M. WA. 8:13.
1. Me ya sa hukuncin da za a yi wa miyagu a nan gaba labari ne mai ƙarfafawa?
BA DA daɗewa ba za a yi wa miyagu shari’a. Za su amsa abubuwan da suka yi. (Mis. 5:22; M. Wa. 8:12, 13) Wannan labari ne mai ban ƙarfafa, musamman ga waɗanda suke son adalci da waɗanda suka sha wahalar rashin gaskiya da wulakanci a hannun miyagu. Wanda ke kan gaba a cikin miyagu da za a yi wa shari’a shi ne uban mugunta, Shaiɗan Iblis.—Yoh. 8:44.
2. Me ya sa ake bukatan lokaci don a sasanta batun da aka ta da a Adnin?
2 A Adnin, Shaiɗan, wanda cike yake da girman kai, ya sa ’yan Adam su ƙi sarautar Jehobah. Saboda haka, iyayenmu na farko sun bi Shaiɗan wajen ƙalubalantar ikon Jehobah kuma suka zama masu zunubi a gabansa. (Rom. 5:12-14) Hakika, Jehobah ya san abin da zai zama sakamakon tafarkinsu na rashin ladabi da tawaye. Amma, dole ne a sa dukan halittu masu basira su san sakamakon. Saboda haka, ana bukatan lokaci don a sasanta batun kuma a nuna sarai cewa ’yan tawayen maƙaryata ne.
3. Menene matsayinmu game da gwamnatocin ’yan Adam?
3 Tun da yake ’yan Adam sun ƙi sarautar Jehobah, hakan ya sa suka kafa tasu gwamnatin. Sa’ad da yake rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan’uwa masu bi a Roma, manzo Bulus ya kira irin waɗannan gwamnatoci na ’yan Adam a matsayin “masu-mulki.” A zamanin Bulus, masu mulki su ne gwamnatin Roma da ke ƙarƙashin Sarki Nero, wanda ya yi sarauta daga 54-68 A.Z. Bulus ya ce irin waɗannan masu mulki “sanyayyu ne na Allah.” (Karanta Romawa 13:1, 2.) Hakan yana nufi ne cewa Bulus yana ɗaukaka sarautar ’yan Adam fiye da sarautar Allah? A’a. Maimakon haka, yana cewa muddin Jehobah ya ƙyale sarautar ’yan Adam ta wanzu, ya kamata Kiristoci su daraja “umurnin Allah” kuma su amince da irin waɗannan sarakuna.
Tafarkin da ke Kai ga Bala’i
4. Ka bayyana abin da ya sa sarautar ’yan Adam ba za ta yi nasara ba.
4 Har ila, sarautar ’yan Adam wadda ke ƙarƙashin tasirin Shaiɗan ba za ta yi nasara ba. Me ya sa? Abu ɗaya, domin ba ta bisa hikimar Allah. Jehobah ne kaɗai yake da cikakkiyar hikima. Saboda haka, shi kaɗai ne tabbataccen mai ja-gora da zai yi sarautar da za ta yi nasara. (Irm. 8:9; Rom. 16:27) Ba kamar ’yan Adam ba da sau da yawa suna koyo ta hanyar kame-kame ne, a koyaushe Jehobah ya san hanya mafi kyau da zai aikata. Duk wani tsarin gwamnati da bai bi ja-gorarsa ba, ba zai yi nasara ba. Don wannan dalili kaɗai, ban da ma mugun muradin da hakan ya ƙunsa, yadda Shaiɗan yake sarauta ta hanyar gwamnatin ’yan Adam ba zai yi nasara ba tun daga farko.
5, 6. Me ya kai Shaiɗan ga tafarkinsa na yin hamayya da Jehobah?
5 Mutum mai hankali ba zai soma yin abin da ba zai yi nasara ba. Idan ya nace yin hakan, zai gane kuskurensa. Sau da yawa, tarihi ya nuna cewa yin hamayya da Mahalicci maɗaukaki duka bai da amfani. (Karanta Misalai 21:30.) Amma, da yake girman kai da fahariya sun makantar da Shaiɗan, ya juya wa Jehobah baya. Saboda haka, Shaiɗan da gangan ya zaɓi hanyar da za ta kai shi ga halaka.
6 Wannan hali na girman kai na Shaiɗan ya bayyana a wani sarki na Babila wanda aka rubuta yana cewa: “Har sama zan hau, zan ɗaukaka kursiyina bisa taurarin Allah: zan zauna bisa dutse na taron jama’a, can ƙurewar arewa: in hau can bisa maɗaukakan hadura; in maida kaina kamar Mai-iko duka.” (Isha. 14:13-15) Wannan abu na rashin hankali da wannan sarki ya soma bai yi nasara ba, kuma daular Babila ta yi mummunar faɗuwa. Hakazalika, ba da daɗewa ba za a halaka Shaiɗan da duniyarsa gabaki daya.
Me Ya sa Allah Ya Ƙyale ’Yancin Kai Daga Sarautarsa?
7, 8. Waɗanne amfani muka samu daga yadda Jehobah ya ƙyale mugunta ta kasance na ɗan lokaci?
7 Wasu suna iya yin mamakin abin da ya sa Jehobah bai hana ’yan Adam goyon bayan Shaiɗan ba da kuma bin wani shiri na sarauta da ba zai yi nasara ba. Zai iya yin hakan a matsayin Allah Maɗaukaki Duka. (Fit. 6:3) Duk da haka, ya ja da baya. Hikimarsa ta nuna cewa ƙin sa hannu na ɗan lokaci a cikin tawayen ’yan Adam zai kawo sakamako mafi kyau a ƙarshe. Daga baya, za a ɗaukaka Jehobah a matsayin Masarauci mai adalci da ƙauna, kuma ’yan Adam masu aminci za su amfana daga shawarar Allah.
8 Da iyalin ’yan Adam ba su fuskanci wahala ba da a ce sun ƙi dabarun Shaiɗan kuma sun ƙi neman ’yancin kai daga sarautar Allah! Duk da haka, shawarar da Jehobah ya tsai da na ƙyale ’yan Adam su yi sarautar kansu na ɗan lokaci yana da amfani. Ya koya wa mutane masu zuciyar kirki amfanin saurarar Allah da kuma dogara gare shi. Ƙarnuka da yawa yanzu, ’yan Adam sun gwada gwamnatoci dabam-dabam, amma babu wadda ta dace. Wannan gaskiyar ta ƙarfafa masu bauta wa Allah su kasance da tabbaci cewa hanyar sarautar Jehobah ita ce kawai mafi kyau. Hakika, yadda Jehobah ya ƙyale sarautar Shaiɗan, ya jawo wahala ga ’yan Adam, har da waɗanda suke bauta wa Allah da aminci. Amma dai, ƙyale mugunta da Allah ya yi na ɗan lokaci ya kawo amfani ga waɗannan masu bauta da aminci. A waɗanne hanyoyi?
Tawayen da Ya Sa Aka Ɗaukaka Jehobah
9, 10. Ka bayyana yadda sarautar Shaiɗan ta sa aka girmama Jehobah.
9 Ƙyale Shaiɗan ya rinjayi ’yan Adam su yi sarautar kansu bai hana ɗaukaka sarautar Jehobah ba. Akasin haka, tarihi ya nuna cewa maganar Irmiya da aka hure cewa ’yan Adam ba za su iya sarautar kansu ba gaskiya ne. (Karanta Irmiya 10:23.) Ƙari ga haka, tawayen Shaiɗan ya ba Jehobah zarafin nuna halayensa masu kyau a ƙarin hanyoyi da ke a bayyane. Ta yaya?
10 Tun da yake mun ga mummunar sakamakon sarautar Shaiɗan, halayen Jehobah masu kyau sun kasance a bayyane fiye da yadda suke. A wannan hanyar, ya samu ƙarin ɗaukaka a gaban waɗanda suke ƙaunarsa. Hakika, ko da yake za a ga kamar hakan ya saɓa da juna, sarautar Shaiɗan ta ɗaukaka Allah da gaske. Ta nanata hanya mafi kyau da Jehobah ya bi da wannan ƙalubalantar da aka yi wa ikon mallakarsa. Don kwatanta wannan gaskiyar, bari mu ɗan bincika wasu cikin halayen Jehobah kuma mu ga yadda muguwar sarautar Shaiɗan ta motsa Jehobah ya nuna waɗannan halaye a ƙarin hanyoyi.
11. Yaya Jehobah ya nuna ƙauna?
11 Ƙauna. Nassosi sun gaya mana cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Da farko, halittar ’yan Adam alama ce da ke nuna ƙaunar Allah. Bugu da ƙari, hanya mai ban mamaki da ban al’ajabi da aka halicce mu ta bayyana ƙaunar Allah. Jehobah kuma cikin ƙauna ya yi wa ’yan Adam tanadin gida mai kyau da ke ɗauke da duk wani abin da suke bukata don su yi farin ciki. (Far. 1:29-31; 2:8, 9; Zab. 139:14-16) Amma sa’ad da iyalin ’yan Adam ta yi zunubi, Jehobah ya nuna ƙaunarsa a sababbin hanyoyi. Ta yaya? Manzo Yohanna ya yi ƙaulin Yesu yana cewa: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Da akwai wata hanya mafi kyau da Allah zai nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam wadda ta fi ta aiko da Ɗansa makaɗaici zuwa duniya domin ya fanshi masu zunubi? (Yoh. 15:13) Wannan ƙauna mai girma da ya nuna ta zama gurbi ga ’yan Adam, hakan ya ba su zarafin nuna ƙaunar Allah ta sadaukar da kai a rayuwarsu ta yau da kullum, yadda Yesu ya yi.—Yoh. 17:25, 26.
12. A wace hanya ce Jehobah ya nuna ikonsa?
12 Iko. “Allah, Mai-iko duka” ne kaɗai yake da ikon halittar rai. (R. Yoh. 11:17; Zab. 36:9) Sa’ad da aka haifi mutum, yana soma rayuwa ce kamar fallen takarda da ba a rubuta kome a kai ba. Sa’ad da ya mutu, ya cika wannan fallen takarda da shawarwari, ayyuka, da abubuwa da ya fuskanta a rayuwa da suka shafe shi da kuma halayensa. Ana iya ajiye waɗannan abubuwa a cikin tunanin Jehobah. A lokacin da ya dace, Jehobah zai dawo da mutumin zuwa rai kuma, da cikakken salon rayuwarsa. (Yoh. 5:28, 29) Ko da yake ba ainihin nufin Allah ba ne ga ’yan Adam, mutuwa ta ba Jehobah zarafin nuna cewa yana da ikon ta da matattu. Hakika, Jehobah “Allah, Mai-iko duka” ne.
13. Ta yaya hadayar Yesu ta nuna cikakken adalci na Jehobah?
13 Adalci. Jehobah ba ya yin ƙarya; kuma ba ya rashin adalci. (K. Sha 32:4; Tit. 1:2) A koyaushe yana manne wa mizanai masu girma na gaskiya da adalci, har sa’ad da yin hakan ba zai amfane shi ba. (Rom. 8:32) Jehobah ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya ga Ɗansa ƙaunatacce ya mutu a kan gungumen azaba sai ka ce Yesu mai saɓo ne marar aminci! Duk da haka, don yana ƙaunar ’yan Adam ajizai, Jehobah ya ƙyale wannan abin baƙin ciki ya faru domin ya ɗaukaka cikakken mizaninsa na adalci. (Karanta Romawa 5:18-21.) Duniya da take cike da rashin adalci ta ba Jehobah zarafin nuna cewa shi ne mafi adalci.
14, 15. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna hikimarsa da haƙuri da babu kamarsu?
14 Hikima. Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, nan da nan Jehobah ya bayyana yadda zai kawar da dukan mugun sakamako da tawayensu ya jawo. (Far. 3:15) Irin wannan matakin da ya ɗauka nan da nan, da kuma yadda ya bayyana wannan nufin ga bayinsa a hankali, ya nuna cewa Jehobah mai hikima ne sosai. (Rom. 11:33) Babu abin da zai iya hana Allah yin nasara wajen bi da al’amura. A duniyar da take cike da lalata, yaƙe-yaƙe, rashin sanin ya kamata, rashin biyayya, rashin tausayi, son kai, da munafunci, Jehobah ya samu zarafi mai yawa na nuna wa halittunsa abin da hikima ta gaske take nufi. Almajiri Yaƙub ya ce: “Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, marar-kokanto, marar-riya ce.”—Yaƙ. 3:17.
15 Haƙuri da Tsawon Jimiri. Da a ce bukata ba ta kama ba na bi da ajizancin ’yan Adam, zunubansu, da kasawarsu, da halayen Jehobah na haƙuri da tsawon jimiri ba su bayyana ba sosai. Dubban shekaru da Jehobah ya yi yana nuna waɗannan halaye da son rai ya nuna cewa yana da waɗannan halaye masu kyau sosai, kuma ya kamata mu nuna godiya don hakan. Ya dace da manzo Bitrus ya faɗi cewa mu “maida jimrewar Ubangijinmu ceto ne.”—2 Bit. 3:9, 15.
16. Me ya sa gafartawa da Jehobah yake yi abin farin ciki ne sosai?
16 Son Gafartawa. Mu duka masu zunubi ne, kuma muna yin tuntuɓe lokatai da yawa. (Yaƙ. 3:2; 1 Yoh. 1:8, 9) Ya kamata mu yi godiya cewa Jehobah yana shirye ya gafarta “a yalwace.” (Isha. 55:7) Ka yi la’akari da wannan gaskiya: Da yake an haife mu a matsayin ajizai masu zunubi, za mu yi farin ciki sa’ad da Allah ya gafarta mana kurakuranmu. (Zab. 51:5, 9, 17) Shaida irin wannan halin Jehobah mai daɗaɗawa yana ƙarfafa ƙaunarmu a gare shi kuma yana ƙarfafa mu mu bi misalinsa a sha’aninmu da mutane.—Karanta Kolosiyawa 3:13.
Abin da ya sa Duniya Take Cikin Mugun Yanayi
17, 18. A waɗanne hanyoyi ne sarautar Shaiɗan ba ta yi nasara ba?
17 Yanayin duniyar Shaiɗan gabaki ɗaya, wadda take nuna yadda yake sarauta, bai taɓa yin nasara ba a dukan shekarun nan. Hakan gaskiya ne! Sa’ad da Shaiɗan ya rinjaye su, iyayenmu na farko sun zaɓi sarautar ’yan Adam fiye da sarautar Jehobah. Ta hakan sun kafa sarautar da ba za ta yi nasara ba. Azaba da kaito da mutane suke fuskanta a dukan duniya alamu ne da suke nuna cewa sarautar ’yan Adam ta kasa gabaki ɗaya.
18 Sarautar Shaiɗan tana cike da son kai. Amma, son kai bai zai taɓa yin nasara bisa ƙauna ba, wadda ita ce tushen sarautar Jehobah. Sarautar Shaiɗan ta kasa kawo zaman lafiya, farin ciki, ko kuma kwanciyar hankali. Hakan ya ɗaukaka yadda yake sarauta! Muna da shaidar da ta tabbatar da hakan a zamani kuwa? Hakika, za mu ga hakan a talifi na gaba.
Menene Muka Koya Game da Sarauta ta Wajen Karanta . . .
• Misalai 21:30?
• Irmiya 10:23?
• Kolosiyawa 3:13?
[Hotuna da ke shafi na 25]
Sarautar Shaiɗan ba ta taɓa amfanar ’yan Adam ba
[Wuraren Da Aka Ɗauko]
U.S. Army photo
WHO photo by P. Almasy
[Hoton da ke shafi na 26]
Jehobah yana da ikon ta da matattu
[Hoton da ke shafi na 27]
Jehobah ya nuna ƙaunarsa da adalcinsa sa’ad da ya miƙa Ɗansa hadaya