Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 pp. 24-29
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Mu na Allah Ne”
  • “Mulkina Ba na Wannan Duniya Ba Ne”
  • Manzanni da Barori ne Madadin Kristi
  • Ƙauna ta Sanar da Su
  • Yadda Kiristoci Suke Ɗaukar Duniya
  • Dokar Allah da ta Kaisar
  • Za Mu Tsaya Tsayin Daka
  • “Ba na Duniya Su Ke Ba”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Yadda Za Mu Ware Kanmu Daga Duniya
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Yadda Za Mu Ki Saka Hannu A Harkokin Duniya
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • “Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 pp. 24-29

Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe

“Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.”—YOHANNA 17:16.

1, 2. Menene Yesu ya ce game da dangantakar mabiyansa da duniya, kuma waɗanne tambayoyi ne suka taso?

A DAREN ƙarshe na rayuwarsa ta kamilci, Yesu ya yi doguwar addu’a almajiransa suna ji. A cikin wannan addu’ar ya faɗi wani abin da ya kwatanta rayuwar dukan Kiristoci na gaskiya. Da yake magana game da mabiyansa ya ce: “Na ba su maganarka; duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.”—Yohanna 17:14-16.

2 Sau biyu Yesu ya ce mabiyansa ba na duniya ba ne. Bugu da ƙari, wannan bambanci zai kawo matsala—duniya za ta ƙi su. Duk da haka, bai kamata Kiristoci su kasala ba; domin Jehovah zai kula da su. (Misalai 18:10; Matta 24:9, 13) Domin kalmomin Yesu, ya kamata mu yi tambaya: ‘Me ya sa ne Kiristoci ba na duniya ba ne? Me ya ke nufi a kasance ba na duniya ba? Idan duniya ta ƙi Kiristoci, yaya ya kamata su ɗauki duniya? Musamman ma, yaya suke ɗaukan gwamnatocin duniya?’ Amsoshin da Nassosi suka bayar ga waɗannan tambayoyi suna da muhimmanci domin sun shafi dukanmu.

“Mu na Allah Ne”

3. (a) Menene ya sa muka bambanta daga duniya? (b) Wane tabbaci ne muke da shi cewa duniya tana kwance cikin ikon Mugun?

3 Dangantakarmu ta kusa da Jehovah ita ce dalili ɗaya da ya sa mu ba na duniya ba ne. Manzo Yohanna ya rubuta: “Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Kalmomin Yohanna game da duniya hakika gaskiya ne. Yaƙe-yaƙe, yin laifi, ƙeta, zalunci, rashin gaskiya, da kuma lalata da suka zama ruwan dare sun ba da tabbacin rinjayar Shaiɗan, ba ta Allah ba. (Yohanna 12:31; 2 Korinthiyawa 4:4; Afisawa 6:12) Sa’ad da mutum ya zama Mashaidin Jehovah, ba zai yi irin waɗannan ayyukan ba marasa kyau ko kuma ya yarda da su, kuma wannan zai sa ya zama ba na duniya ba.—Romawa 12:2; 13:12-14; 1 Korinthiyawa 6:9-11; 1 Yohanna 3:10-12.

4. A waɗanne hanyoyi ne muke nuna cewa mu na Jehovah ne?

4 Yohanna ya ce Kiristoci sun bambanta da duniya, domin su “na Allah ne.” Dukan waɗanda suka keɓe kansu ga Jehovah nasa ne. Manzo Bulus ya ce: “Ko muna rayuwa, ga Ubangiji mu ke rayuwa; ko mutuwa mu ke yi, ga Ubangiji mu ke mutuwa; ko mu rayu fa, ko mu mutu, na Ubangiji mu ke.” (Romawa 14:8; Zabura 116:15) Domin mu na Jehovah ne, muna yi masa ibada da zuciya ɗaya. (Fitowa 20:4-6) Saboda haka, Kirista na gaskiya ba ya ba da rayuwarsa domin wani buri na duniya. Ko da yake yana daraja kan sarki na ƙasa ba ya bauta musu, ko ta wajen ayyuka ko kuma a zuciyarsa. Hakika ba ya bauta wa zakarun wasanni ko kuma wasu gumaka na zamani. Babu shakka, yana daraja ’yancin wasu su yi yadda suke so, amma shi Mahalicci kaɗai yake bauta wa. (Matta 4:10; Ru’ya ta Yohanna 19:10) Wannan ma ya bambanta shi da duniya.

“Mulkina Ba na Wannan Duniya Ba Ne”

5, 6. Ta yaya miƙa kai ga Mulkin Allah ta bambanta mu da duniya?

5 Kiristoci mabiyan Kristi Yesu ne kuma talakawan Mulkin Allah ne, wannan ma ya sa sun kasance ba na duniya ba. Sa’ad da ake yi wa Yesu hukunci a gaban Bilatus Babunti, ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne: da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana su a yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa, amma yanzu mulkina ba daga nan ya ke ba.” (Yohanna 18:36) Mulkin hanya ne da za a tsarkake sunan Jehovah, a kunita mulkin mallakarsa, kuma a yi nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a sama. (Matta 6:9, 10) A dukan lokacin da yake hidimarsa, Yesu ya yi wa’azin bishara na Mulkin kuma ya ce mabiyansa za su sanar da wannan har zuwa ƙarshen wannan zamanin. (Matta 4:23; 24:14) A shekara ta 1914 kalmomin annabci na Ru’ya ta Yohanna 11:15 ta cika: “Mulkin duniya ya zama na Ubangijinmu, da na Kristinsa: za ya yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai.” (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Ba da daɗewa ba, Mulkin sama shi ne zai kasance sarauta kawai mai iko bisa ’yan Adam. (Daniel 2:44) A wani lokaci, za a tilasta wa sarakunan duniya su miƙa kai ga sarautarsa.—Zabura 2:6-12.

6 Tuna da dukan wannan, Kiristoci na gaskiya a yau talakawa ne na Mulkin Allah, kuma suna bin gargaɗin Yesu ‘ku fara biɗan mulkin Allah, da adalcinsa.’ (Matta 6:33) Wannan bai sa su kasance marasa aminci ba ga ƙasa da suke zaune cikinta, amma ya sa sun bambanta a ruhaniya daga duniya. Ainihin aikin Kiristoci a yau, kamar yadda yake a ƙarni na farko, shi ne ‘su shaida mulkin Allah da kyau.’ (Ayukan Manzanni 28:23) Babu wani gwamnati na mutum da zai iya hana wannan aikin da Allah ya bayar.

7. Me ya sa Kiristoci na gaskiya suke tsakatsaki, kuma ta yaya suka nuna hakan?

7 Cikin jituwa da kasancewa na Jehovah kuma kasancewa mabiyan Yesu da kuma talakawan Mulkin Allah, Shaidun Jehovah sun kasance da tsakatsaki a yaƙe-yaƙe na ƙarni na 20 da kuma ƙarni na 21. Ba su zaɓi wani ɓangare ba, ba su ɗauki makamai ba, su yaƙi kowa, kuma ba su yaɗa jita-jita ba domin wani abu cikin duniya. A nuna bangaskiya na musamman lokacin da suka fuskanci hamayya mai tsanani, sun bi mizanan da aka gaya wa Nazi masarauta na Jamus a shekara ta 1934: “Ba mu da sha’awar ayyukan siyasa, amma muna ibada ga mulkin Allah a hannun Sarkinsa Kristi. Ba za mu yi wa kowa mugunta ba ko kuma mu yi masa rauni. Za mu yi farin ciki mu zauna lafiya kuma mu yi kirki ga dukan mutane idan mun samu zarafin haka.”

Manzanni da Barori ne Madadin Kristi

8, 9. A wace hanya ce Shaidun Jehovah jakadai ne kuma barori ne, ta yaya wannan ya shafi dangantakarsu da wasu al’ummai?

8 Bulus ya kwatanta kansa da kuma ’yan’uwansa Kiristoci da aka shafa su da “manzanni ne madadin Kristi, sai ka ce Allah yana yin roƙo ta wurinmu.” (2 Korinthiyawa 5:20; Afisawa 6:20) Tun daga shekara ta 1914, Kiristoci da ruhu ya naɗa za a iya cewa da su jakadodi na Mulkin Allah, wanda a nan su “ ’ya’ya” ne. (Matta 13:38; Filibbiyawa 3:20; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) Bugu da ƙari, Jehovah ya ciro daga al’ummai “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki,” Kiristoci da suke da begen rayuwa a duniya har abada, su tallafa wa shafaffun ’ya’ya a ayyukansu na jakadai. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Waɗannan “waɗansu tumaki” za a iya cewa da su ‘barori’ na Mulkin Allah.

9 Jakada da ma’aikatansa ba sa saka baki cikin al’amuran ƙasar da suke hidima a cikinta. Hakazalika, Kiristoci sun kasance da tsakatsaki game da sha’anin siyasa na wannan duniyar. Ba sa goyon bayan al’umma, wani launin fata, wasu rukunin mutane ko kuma su yi hamayya da su. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Maimakon haka, suna “aika nagarta zuwa ga dukan mutane.” (Galatiyawa 6:10) Tsakatsaki na Shaidun Jehovah yana nufin cewa babu mutumin da da gaske zai ƙi saƙonsu domin yana da’awar cewa suna goyon bayan launin fata, al’umma, ko kuma ƙabila da take hamayya.

Ƙauna ta Sanar da Su

10. Yaya muhimmancin ƙauna ga Kirista?

10 Ƙari ga dalilan bayan nan, Kiristoci suna tsakatsaki a al’amuran duniya domin dangantakarsu da wasu Kiristoci. Yesu ya ce wa mabiyansa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Ƙauna ta ’yan’uwanci muhimmin ɓangare ne na kasancewa Kirista. (1 Yohanna 3:14) Yadda dangantakar mutum da Jehovah da Yesu take, haka ma dangantakar Kirista yake da wasu Kiristoci. Ƙaunarsa ba ga waɗanda suke cikin ikilisiyarsa ba ne kawai. Ta kai ga dukan ‘ ’yan’uwansa na dukan duniya.’—1 Bitrus 5:9.

11. Ta yaya ƙaunar Shaidun Jehovah take rinjayar halinsu ga junansu?

11 A yau, Shaidun Jehovah suna cika ƙaunarsu ta ’yan’uwanci ta wajen cika kalmomin Ishaya 2:4: “Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.” Domin Jehovah ne ke musu ja-gora, Kiristoci na gaskiya suna da salama da Allah da kuma junansu. (Ishaya 54:13) Domin suna ƙaunar Allah da kuma ’yan’uwansu, ba zai yiwu ba su ɗauki makamai su kashe ’yan’uwansu—ko ma wasu—a wasu ƙasashe. Salamarsu da kuma haɗin kai ɓangare ne mai muhimmanci na bautarsu, wannan ya nuna da gaske cewa suna da ruhun Allah. (Zabura 133:1; Mikah 2:12; Matta 22:37-39; Kolossiyawa 3:14) Suna ‘biɗan salama, suna bin ta kuma’ domin sun sani cewa “idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci.”—Zabura 34:14, 15.

Yadda Kiristoci Suke Ɗaukar Duniya

12. Wane hali ne na Jehovah game da mutanen duniya Shaidun Jehovah suke yin koyi da shi, ta yaya?

12 Jehovah ya riga ya furta matsananciyar hukunci bisa wannan duniya, amma bai hukunta dukan mutane da suke cikinta ba tukuna. Zai yi hakan ta wajen Yesu idan lokacinsa ya yi. (Zabura 67:3, 4; Matta 25:31-46; 2 Bitrus 3:10) A yau, ya nuna ƙauna ƙwarai ga ’yan Adam. Har ya ba da Ɗansa makaɗaici saboda dukan mutane su samu zarafin samun rai madawwami. (Yohanna 3:16) Tun da mu Kiristoci ne, muna yin koyi da ƙauna ta Allah ta wajen gaya wa wasu game da tanadin Allah domin ceto, ko da sau da yawa ana ƙin ƙoƙarin da muke yi.

13. Yaya ya kamata mu ɗauki masu iko na duniya?

13 Yaya ya kamata mu ɗauki masu iko na duniya? Bulus ya amsa wannan tambayar sa’ad da ya rubuta: “Bari kowane mai-rai shi yi zaman biyayya da ikon masu-mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah.” (Romawa 13:1, 2) Mutane suna riƙe da ‘ɗan’ matsayi ne na iko (manya ko ƙanana idan aka gwada su da juna, amma ba su kai na Jehovah ba) domin Mai Iko Duka ya ƙyale su. Kirista zai miƙa kai ga masu iko domin wannan ɓangaren biyayyarsa ce ga Jehovah. To, yaya idan rashin jituwa ya taso tsakanin abin da Allah yake bukata da abin da gwamnatocin mutane suke bukata?

Dokar Allah da ta Kaisar

14, 15. (a) Ta wace hanya ce Daniel ya guji matsala a batun biyayya? (b) Wane matsayi Ibraniyawa uku suka ɗauka sa’ad da matsala a batun biyayya ba a iya guje mata ba?

14 Daniel da abokanansa uku sun ba da misali mai kyau na yadda za a daidaita biyayya ga gwamnatocin mutane da biyayya ga iko na Allah. Sa’ad da samari huɗun suke bauta a Babila, suna biyayya ga dokokin ƙasar saboda haka, ba da daɗewa ba aka zaɓe su domin a koyar da su musamman. Daniel, ya fahimci cewa wannan koyarwa babu shakka za ta kai ga rashin jituwa da Dokar Jehovah, ya tattauna batun da ma’aikacin da yake shugabanci. Domin haka, aka yi shiri na musamman domin a daraja lamiri na Ibraniyawa huɗun. (Daniel 1:8-17) Shaidun Jehovah suna bin misalin Daniel sa’ad da suka bayyana matsayinsu cikin basira ga ma’aikata masu ja-gora domin su guji ƙananan matsaloli.

15 A wani lokaci, kuma matsala game da biyayya ba za a iya guje mata ba. Sarkin Babiloniyawa ya kafa gunki a filin Dura ya umurci dukan manyan ma’aikata, haɗe da hakimai, su taru domin su yi bikin kafa shi. A lokacin, abokai uku na Daniel an riga an naɗa su hakimai na yankunan Babila, saboda haka dokar ta shafe su. A wani lokaci na bikin, dukan waɗanda suka hallara an bukace su su yi sujjada a gaban gunkin. Amma Ibraniyawan sun sani cewa wannan ya saɓa wa dokar Allah. (Kubawar Shari’a 5:8-10) Saboda haka, sa’ad da dukan mutane suka yi sujjada, su suka kasance a tsaye. Domin sun taka dokar sarki, za a iya yi musu kisan wulakanci, amma an ceci rayukansu ta mu’ujiza ne; domin sun zaɓi su mutu maimakon su yi wa Jehovah rashin biyayya.—Daniel 2:49–3:29.

16, 17. Yaya manzannin suka amsa sa’ad da aka umurce su su daina wa’azi, kuma me ya sa?

16 A ƙarni na farko, manzannin Yesu Kristi an kira su gaban shugabannin Yahudawa a Urushalima kuma aka umurce su su daina wa’azi cikin sunan Yesu. Yaya suka yi? Yesu ya umurce su su almajirantar da mutane a dukan al’ummai, wanda ya haɗa da Yahudiya. Ya gaya musu su yi shaidarsa a Urushalima da kuma dukan duniya. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 1:8) Manzannin sun sani cewa umurnin Yesu nufin Allah ne a gare su. (Yohanna 5:30; 8:28) Saboda haka suka ce: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 4:19, 20; 5:29.

17 Manzannin ba tawaye suka yi ba. (Misalai 24:21) Duk da haka, sa’ad da mutane masu sarauta suka hana su su yi nufin Allah, abin da za su iya cewa shi ne, ‘Dole ne mu yi wa Allah biyayya, ba mutane ba.’ Yesu ya ce mu “ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” (Markus 12:17) Idan muka taka dokar Allah domin mutum ya umurce mu, muna bai wa mutum abin da yake na Allah. Maimakon haka, muna ba wa Kaisar dukan abin da ke na shi, amma mun fahimci iko mafi girma na Jehovah. Shi ne Mamallakin Dukan Halitta, Mahalicci, Tushen dukan iko.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.

Za Mu Tsaya Tsayin Daka

18, 19. Wane matsayi mai kyau ne wasu ’yan’uwanmu suka ɗauka, kuma ta yaya za mu bi misalinsu?

18 A yanzu, yawancin gwamnatoci sun fahimci matsayin Shaidun Jehovah na tsakatsaki, domin wannan muna godiya. A wasu ƙasashe, Shaidu suna fuskantar tsanani ƙwarai. A cikin dukan ƙarni na 20 ya ci gaba har wa yau, wasu ’yan’uwanmu maza da mata sun yi kokawa ƙwarai, a hanya ta ruhaniya sun “yi yaƙin kirki na imani.”—1 Timothawus 6:12.

19 Ta yaya za mu tsaya tsayin daka yadda suka yi? Da farko, dole ne mu tuna cewa za mu fuskanci hamayya. Bai kamata mu razana ba ko kuma mu yi mamaki sa’ad da mun fuskance ta. Bulus ya yi wa Timothawus gargaɗi: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12; 1 Bitrus 4:12) A duniya inda rinjayar Shaiɗan take mulki, yaya za a ce ba za mu fuskanci hamayya ba? (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Idan muka kasance da aminci, dole ne ya kasance cewa da akwai wasu da za su yi ‘mamaki kuma su ci gaba da aibatanmu.’—1 Bitrus 4:4.

20. Game da wace gaskiya ce mai ƙarfafawa aka tunasar da mu?

20 Na biyu, mun tabbata cewa Jehovah da kuma mala’ikunsa za su taimake mu. Kamar yadda Elisha na dā ya ce, “waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su yawa.” (2 Sarakuna 6:16; Zabura 34:7) Wataƙila domin nufinsa mai kyau Jehovah ya ƙyale matsi na ’yan hamayya ya ci gaba na ɗan lokaci. Duk da haka, zai ba mu ƙarfi da za mu jimre. (Ishaya 41:9, 10) An kashe wasu, amma wannan ba zai tsoratar da mu ba. Yesu ya ce: “Kuma kada ku ji tsoron waɗannan da su ke kisan jiki, ba su kuwa da iko su kashe rai: gwamma dai ku ji tsoron wannan wanda yana da iko ya halaka rai duk da jiki cikin Jahannama.” (Matta 10:16-23, 28) Mu “baƙi ne” a wannan zamanin. Muna amfani ne da lokacinmu a nan mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.” (1 Bitrus 2:11; 1 Timothawus 6:19) Babu mutumin da zai iya hana mu wannan ladar idan muka kasance da aminci ga Allah.

21. Menene ya kamata mu riƙa tunawa kullayaumi?

21 Saboda haka, bari mu tuna da gata da muke da ita na dangantaka da Jehovah Allah. Kuma mu yi godiya kullum domin fa’idodin kasancewa mabiyan Kristi kuma talakawan Mulkin. Bari mu ƙaunaci ’yan’uwanmu da zuciya ɗaya, kuma bari kullum mu yi farin ciki cikin ƙauna da muke samu daga wurinsu. Fiye da kome, bari mu bi kalmar mai Zabura: “Ka yi sauraro ga Ubangiji: Ka ƙarfafa, ka bar zuciyarka ta ɗauki ƙarfin rai; I, ka yi sauraro ga Ubangiji.” (Zabura 27:14; Ishaya 54:17) Sa’ad da mu, kamar wasu Kiristoci da yawa kafin mu, muka tsaya tsayin daka da begenmu tabbatacce—Kiristoci masu aminci waɗanda suka kasance da tsakatsaki, waɗanda ba na duniya ba.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ta yaya dangantakarmu da Jehovah take sa mu bambanta daga wannan duniya?

• Tun da mu talakawan Mulkin Allah ne, ta yaya muke kasancewa da matsayi na tsakatsaki a wannan duniyar?

• A wace hanya ce ƙaunar ’yan’uwanmu take sa mu kasance da tsakatsaki, mu bambanta da duniya?

[Hoto a shafi na 25]

Ta yaya miƙa kanmu ga Mulkin Allah ya shafi dangantakarmu da duniya?

[Hoto a shafi na 26]

Iyalin Hutu da ta Tutsi suna aiki tare cikin farin ciki

[Hoto a shafi na 27]

Kiristoci ’yan’uwa Yahudawa da kuma Larabawa

[Hoto a shafi na 27]

Kiristoci daga Sabiya, Bosniya, Croatiya suna more tarayya da juna

[Hoto a shafi na 28]

Menene za mu yi sa’ad da masu mulki suka umurce mu mu taka dokar Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba