Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Wasiƙa ga Romawa
A KUSAN shekara ta 56 A.Z., sa’ad da yake tafiyarsa ta uku na wa’azi, manzo Bulus ya isa birnin Koranti. Ya fahimci cewa Kiristoci Yahudawa da ’yan Al’umma da ke Roma suna da ra’ayi dabam dabam. Bulus ya ɗauki nauyin rubuta musu wasiƙa don ya daidaita ra’ayinsu.
A wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya bayyana yadda aka sanar da ’yan adam masu adalci da kuma yadda waɗannan mutane za su yi rayuwa. Wasiƙar tana sa mu ƙara sanin Allah da Kalmarsa, ta nanata alherin Allah, da kuma ɗaukaka matsayin Kristi a wajen samun cetonmu.—Ibran. 4:12.
TA YAYA AKA SANAR DA MU MASU ADALCI?
Bulus ya rubuta: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” “Bisa ga alherinsa [Allah] an barata a yalwace ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi.” Bulus ya kuma ce: “Mutum ta wurin bangaskiya ya ke barata banda ayukan shari’a.” (Rom. 3:23, 24, 28) Ta wurin bangaskiya “aiki guda ɗaya mai-adalci,” za a ce da dukan shafaffun Kiristoci da “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” masu adalci, wato, shafaffu za su yi rayuwa a sama a matsayin masu tarayyar gado da Kristi kuma taro mai girma abokanan Allah, suna da begen tsira daga “babban tsananin.”—Rom. 5:18; R. Yoh. 7:9, 14; Yoh. 10:16; Yaƙ. 2:21-24; Mat. 25:46.
Bulus ya yi tambaya, “mu yi zunubi, domin ba mu ƙalƙashin shari’a ba, amma ƙalƙashin alheri?” Ya amsa “Daɗai!” Bulus ya ba da bayani, “bayi ku ke . . . ko na zunubi zuwa mutuwa, ko kuwa na biyayya zuwa adilci?” (Rom. 6:15, 16) Ya ce, “idan bisa ga ruhu kuna matasda ayukan jiki, za ku rayu.”—Rom. 8:13.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
1:24-32—Lalaci da aka kwatanta a nan yana nuni ne ga Yahudawa ko kuma ’yan Al’umma? Ko da yake wannan kwatancin yana iya yin daidai da kowane rukuni, Bulus ainihi yana maganar Isra’ilawa na dā da suka yi ridda ne. Ko da yake sun san dokar Allah na adalci, “ba su lamunta su riƙe Allah a cikin saninsu ba.” Ba su cancanta su sami saninsa ba.
3:24, 25—Ta yaya ne “fansa da ke cikin Yesu Kristi” ta share “zunubai marigaya” kafin a biya ta? Annabci na Almasihu na farko da ke rubuce a Farawa 3:15 ya cika a shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka kashe Yesu a kan gungumen azaba. (Gal. 3:13, 16) Amma, sa’ad da Jehobah ya ambata wannan annabci, a ra’ayinsa an riga an biya fansar, domin ba abin da zai hana Allah cika nufinsa. Saboda haka, bisa ga hadayar Yesu Kristi, Jehobah zai iya gafarta zunuban ’ya’yan Adamu da suka ba da gaskiya a wannan alkawarin. Fansa ta sa ya yiwu a ta da waɗanda suka mutu kafin zamanin Kiristanci.—A. M. 24:15.
6:3-5—Menene ake nufi da baftisma a cikin Yesu Kristi da baftisma a cikin mutuwarsa? Sa’ad da Jehobah ya shafa mabiyan Kristi da ruhu mai tsarki, sun haɗa kai da Yesu kuma suka zama waɗanda suke cikin ikilisiyar, wato, jikin Kristi wanda shi ne shugaba. (1 Kor. 12:12, 13, 27; Kol. 1:18) Wannan shi ne abin da baftisma cikin Kristi yake nufi. An yi wa shafaffu Kiristoci baftisma zuwa cikin ‘mutuwar Kristi’ tun da yake sun yi rayuwar hadaya kuma sun ƙi kowane bege na rayuwa a duniya har abada. Saboda haka, mutuwarsu ta hadaya ce, kamar mutuwar Yesu, ko da yake mutuwarsu ba ta fansa ba ce. Sun yi wannan baftisma cikin mutuwar Kristi sa’ad da suka mutu kuma aka ta da su zuwa rayuwa a sama.
7:8-11—Ta yaya ne, ‘zunubi ta samu kafa ta wurin Doka’? Dokar ta taimaki mutane su fahimci dukan abubuwan da zunubi ya ƙunshi, ta sa su san cewa su masu zunubi ne. Saboda haka, sun ƙara fahimtar laifofin da su masu zunubi suka aikata, kuma mutane da yawa sun fahimci cewa su masu zunubi ne. Za a iya cewa zunubi ta sami kafa ta wurin Doka.
Darussa Dominmu:
1:14, 15. Muna da dalilai masu yawa na yin shelar bishara da himma. Dalili ɗaya shi ne, hakkin mutanen da aka saya da jinin Yesu yana kan mu kuma wajibi ne mu taimake su a ruhaniya.
1:18-20. Mutane da ba sa bin Allah kuma marasa adalci ba su da “hujja,” domin an bayyana musu al’amuran Allah da ba a gani.
2:28; 3:1, 2; 7:6, 7. Bayan da ya ambata abubuwa da wataƙila sun ɓata wa Yahudawa rai, Bulus ya faɗi abubuwan da suka sauƙaƙa musu rai. Hakan ya nuna mana misali game da yadda za mu amsa batutuwa masu wuyan fahimta a cikin basira da hikima.
3:4. Sa’ad da kalaman mutum suka bambanta da abin da Allah ya faɗi a Kalmarsa, zai yi kyau mu “bari Allah ya zama mai-gaskiya” ta wajen dogara da kalaman Littafi Mai Tsarki da kuma yin abubuwa bisa ga nufin Allah. Ta wajen kasancewa da himma a aikin wa’azin mulki da almajirantarwa, za mu iya taimakon wasu su fahimci cewa shi ne Allah na gaskiya.
4:9-12. Domin bangaskiyar Ibrahim shi ya sa aka ce shi mai adalci ne kafin a yi masa kaciya a shekara ta 99. (Far. 12:4; 15:6; 16:3; 17:1, 9, 10) Ta haka, Allah ya nuna cewa kasancewa da adalci a gabansa zai yiwu.
4:18. Bege sashe ne mai muhimmanci ga bangaskiya. Imaninmu ta dangana ga bangaskiya.—Ibran. 11:1.
5:18, 19. Ta wajen nuna yadda Yesu ya yi kama da Adamu, Bulus ya ɗan bayyana yadda mutum ɗaya zai iya “bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Mat. 20:28) Ya kamata mu yi koyi da wannan misali na yin koyarwa da hujja kuma a taƙaice.—1 Kor. 4:17.
7:23. Gaɓaɓuwan jiki kamar hannuwa, ƙafafuwa, da harshe za su iya sa mu “ƙarƙashin shari’ar zunubin,” saboda haka ya kamata mu yi amfani da su yadda ya kamata.
8:26, 27. Idan muna fuskantar yanayi mai wuya har ba mu san abin da za mu yi addu’a a kai ba, “Ruhu da kansa yana roƙo dominmu.” Jehobah kuma, “mai-jin addu’a,” zai karɓi addu’o’in da suka dace da Kalmarsa kamar daga gare mu ne.—Zab. 65:2.
8:38, 39. Jaraba, miyagun halittu na ruhu, da kuma gwamnatin ’yan adam ba za su iya sa Jehobah ya daina ƙaunarmu ba; ko kuma su hana mu ƙaunar sa.
9:22-28; 11:1, 5, 17-26. Ikilisiyar shafaffun Kiristoci da aka “kira . . . ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba, amma daga cikin Al’ummai” sun cika annabce-annabce da yawa game da maidowar Isra’ilawa.
10:10, 13, 14. Domin muna ƙaunar Allah da kuma ’yan’uwanmu, kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah da kuma alkawuransa za su iya motsa mu mu kasance da ƙwazo a hidimar Kirista.
11:16-24, 33. “Nagarta da rashin siyasa na Allah” sun daidaita. Hakika, “aikin [Allah] cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne.”—K. Sha 32:4.
YIN RAYUWA DA TA JITU DA ADALCI
“Ina roƙonku fa, yan’uwa, bisa ga jiyejiyenƙai na Allah,” in ji Bulus, “ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah.” (Rom. 12:1) Da yake an sanar da Kiristoci masu adalci domin bangaskiyarsu, abin da Bulus ya faɗa a gaba ya kamata ya shafi halinsu ga mutane da kuma masu mulki.
Bulus ya rubuta: “Ni ke fāɗa ma kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata.” Ya ba da gargaɗi: “Bari ƙauna ta zama ba tare da riya ba.” (Rom. 12:3, 9) “Bari kowane mai-rai shi yi zaman biyayya da ikon masu-mulki.” (Rom. 13:1) Game da abubuwa da suka shafi lamiri, ya ƙarfafa Kiristoci ‘kada fa su ƙara zartas ma juna.’—Rom. 14:13.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
12:20—Ta yaya muke ‘tara garwashin wuta’ a kan maƙiyi? A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ana saka kuza a cikin wuta kuma a zuba gawayi a kanta da ƙarƙashin ta. Zafin wutan zai narkar da ƙarfen kuma a cire dattin da ke ciki. Hakazalika, muna zuba gawayi mai zafi a kan maƙiyi ta wurin yi masa alheri don ya gyara halinsa marar kyau kuma ya fara nuna halaye masu kyau.
12:21—Ta yaya za mu ci gaba da ‘rinjayar mugunta da nagarta’? Hanya ɗaya da za mu yi hakan ita ce ta wajen nace wa aikin da Allah ya ba mu na yin wa’azin bishara har sai Jehobah ya gamsu da aikin.—Mar. 13:10.
13:1—A wace hanya ce masu mulki “sanyayyu ne na Allah”? Masu mulki “sanyayyu ne na Allah” domin Allah ne ya ƙyale su su yi sarauta, a waɗansu yanayi kuma Allah ya annabta yadda za su yi sarauta. Littafi Mai Tsarki ya nuna hakan ta abubuwan da ya annabta game da sarakuna masu yawa.
Darussa Dominmu:
12:17, 19. Za mu rama mugunta idan muka yi abin da Jehobah ne kaɗai ya cancanta ya yi. Idan muka “sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta,” zai nuna cewa muna da girman kai.
14:14, 15. Kada mu ɓata wa ɗan’uwanmu rai ko kuma mu sa shi tuntuɓe da irin abinci ko kuma abin sha da muka ba shi.
14:17. Kasancewa da aminci a gaban Allah bai dangana a kan abin da mutum yake ci ko sha ko kuma abin da ya ƙi ci ko ya ƙi sha ba. Maimakon haka, mutum zai zama mai adalci, mai salama kuma ya kasance da farin ciki.
15:7. Ba tare da nuna bambanci ba, mu marabci dukan waɗanda suke son gaskiya a cikin ikilisiya kuma mu sanar da saƙon Mulki ga dukan waɗanda muka sadu da su.
[Hotuna a shafi na 31]
Fansa yana nufin zunuban da aka yi ne kafin a biya?