Ku Ɗaukaka Allah Da‘baki Ɗaya’
“Ku ɗaukaka Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, . . . bakinku ɗaya.”—ROMAWA 15:6.
1. Wane darasi game da bi da ra’ayi da ya bambanta ne Bulus ya koya wa ’yan’uwa masu bi?
BA DUKAN Kiristoci suke zaɓe iri ɗaya ko kuma suke son abu iri ɗaya ba. Duk da haka, dukan Kiristoci dole ne su yi tafiya da zuciya ɗaya a kan hanya ta rai. Wannan zai yiwu kuwa? Hakika, idan ba mu ƙyale ɗan jayayya ya zama babban matsala ba. Darasin da manzo Bulus ya koya wa ’yan’uwa masu bi ke nan a ƙarni na farko. Ta yaya ya bayyana wannan muhimmin darasin? Kuma ta yaya za mu yi amfani da wannan hurarren gargaɗi a yau?
Muhimmancin Haɗin Kai na Kirista
2. Ta yaya Bulus ya nanata bukatar haɗin kai?
2 Bulus ya sani cewa haɗin kai na Kirista yana da muhimmanci, kuma ya ba da gargaɗi mai kyau don ya taimaki Kiristoci su jimre da juna cikin ƙauna. (Afisawa 4:1-3; Kolosiyawa 3:12-14) Duk da haka, bayan ya kafa ikilisiyoyi da yawa da kuma ziyarar wasu fiye da shekara 20, ya sani cewa ci gaba da haɗin kai zai iya zama ƙalubale. (1 Korantiyawa 1:11-13; Galatiyawa 2:11-14) Da haka, ya aririce ’yan’uwa masu bi da suke zama a Roma: “Allah mai ba da haƙuri da ta’aziyya, ya ba ku . . . domin ku ɗaukaka Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.” (Romawa 15:5, 6) A yau, mu ma dole ne mu ɗaukaka Jehovah Allah da ‘baki ɗaya’ da yake mu rukunin mutanensa ne masu haɗin kai. Yaya muke yi a wannan batun?
3, 4. (a) A waɗanne hanyoyi Kiristoci da suke a Roma suka bambanta? (b) Ta yaya Kiristoci a Roma za su iya bauta wa Jehovah da ‘baki ɗaya’?
3 Kiristoci da yawa a Roma abokan Bulus ne na kud da kud. (Romawa 6:3-16) Ko da sun fito daga wurare dabam dabam, Bulus ya ɗauki dukan ’yan’uwansa cewa su “ƙaunatattun Allah” ne. Ya rubuta: “Ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.” Hakika, Romawan abin koyi ne a hanyoyi da yawa. (Romawa 1:7, 8; 15:14) Amma, wasu cikin ikilisiyar suna da ra’ayi dabam dabam a kan wasu batutuwa. Tun da yake Kiristoci a yau sun fito daga wurare da al’adu dabam dabam, nazarin hurarren gargaɗin Bulus a yadda za mu bi da bambanci zai taimake mu mu yi magana da ‘baki ɗaya.’
4 A Roma akwai Yahudawa da ’yan Al’umma ne masu bi. (Romawa 4:1; 11:13) Wasu Yahudawa Kiristoci ba su iya daina ayyuka na wasu al’adu da suka yi a ƙarƙashin Dokar Musa ba, ko da ya kamata su fahimci cewa irin waɗannan ayyuka ba su da muhimmanci don samun ceto. A wata sassa, adadin Yahudawa Kiristoci da yawa sun yarda cewa hadayar Kristi ya ’yantar da su daga hani da suke bi kafin su zama Kiristoci. Shi ya sa suka canja wasu halayensu da ayyuka. (Galatiyawa 4:8-11) Duk da haka, yadda Bulus ya nuna dukansu “ƙaunatattun Allah” ne. Dukansu na iya yabon Allah da ‘baki ɗaya’ idan sun kasance da halin da ya dace ga juna. Mu a yau, muna iya kasance da ra’ayi dabam dabam a kan wasu batutuwa, ya kamata mu bincika sosai yadda Bulus ya bayyana wannan muhimmiyar ƙa’ida.—Romawa 15:4.
“Ku Karɓi Juna Hannu Biyu Biyu”
5, 6. Me ya sa ake da ra’ayi dabam dabam a ikilisiyar Roma?
5 A wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus ya yi maganar yanayi da ra’ayi da ya bambanta. Ya rubuta: “Wani, bangaskiya tasa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.” Me ya sa hakan? A Dokar Musa, ba a cin naman alade. (Romawa 14:2; Littafin Firistoci 11:7) Amma, da Yesu ya mutu ba a bin wannan dokar kuma. (Afisawa 2:15) Shekara uku da rabi bayan mutuwar Yesu, wani mala’ika ya gaya wa Bitrus cewa a ra’ayin Allah bai kamata a ɗauki wani abinci da ƙazanta ba. (Ayyukan Manzanni 11:7-12) Domin haka, wasu Yahudawa Kiristoci sun ga cewa za su iya cin alade—ko kuma su ci wasu abinci da Dokar ta hana.
6 Amma, tunanin cin waɗannan abinci na dā marar tsabta abin ƙyama ne ga wasu Yahudawa Kiristoci. Irin waɗannan ƙila sun ji haushin ganin ’yan’uwansu Yahudawa Kiristoci suna cin irin abincin. Ƙari ga haka, wasu Kiristoci na Al’umma da wataƙila domin addininsu ba su da wani hani a kan abinci, ƙila sun yi mamaki cewa wani zai yi musu game da abinci. Hakika, ba laifi ba ne wani ya ƙi wani abinci, muddin bai nace ba cewa sanadin samun ceto ne. Duk da haka, waɗannan ra’ayi da suka bambanta da sauƙi suna iya ta da jayayya a ikilisiya. Kiristoci da suke Roma za su mai da hankali kada irin waɗannan bambanci ya hana su ɗaukaka Allah da ‘baki ɗaya.’
7. Wane ra’ayi dabam dabam ya kasance a batun kiyaye rana ta musamman kowane mako?
7 Bulus ya ba da misali na biyu: “Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa.” (Romawa 14:5a) A Dokar Musa ba za a yi aiki ba a Asabarci. Ba za a ma yi tafiya ba a ranar. (Fitowa 20:8-10; Matiyu 24:20; Ayyukan Manzanni 1:12) Amma, sa’ad da aka kawar da Dokar, waɗannan hani ba su da amfani kuma. Har ila, wasu Yahudawa Kiristoci mai yiwuwa ba su saki jiki ba game da yin kowane aiki ko tafiya da nisa a ranar da dā suna ɗaukarta da tsarki. Har bayan sun zama Kiristoci, ƙila sun keɓe rana ta bakwai don ayyuka na ruhaniya, ko da a ra’ayin Allah kiyaye Asabarci ba shi da muhimmanci. Daidai ne su yi hakan? E, muddin ba su nace ba cewa Allah yana bukata a kiyaye Asabarci. Domin yana la’akari da lamirin ’yan’uwansa Kiristoci, Bulus ya rubuta: “Kowa dai yā zauna cikin haƙƙaƙewa a kan ra’ayinsa.”—Romawa 14:5b.
8. Ko da za su yi la’akari da lamirin wasu, menene Kiristoci da suke Roma ba za su yi ba?
8 Amma, ko da yana ƙarfafa ’yan’uwansa su yi haƙuri da waɗanda suke fama da batun lamiri, Bulus ya hukunta waɗanda suke ƙoƙarin su tilasta wa ’yan’uwa masu bi su su bi Dokar Musa domin su sami ceto. Alal misali, kusan shekara ta 61 A.Z., Bulus ya rubuta littafin Ibraniyawa, wasiƙa mai iko ga Yahudawa Kiristoci da take bayyana cewa yin biyayya da Dokar Musa ba ta da amfani saboda Kiristoci suna da bege mafifici ta wurin hadayar fansa ta Yesu.—Galatiyawa 5:1-12; Titus 1:10, 11; Ibraniyawa 10:1-17.
9, 10. Menene ya kamata Kiristoci su guji yi? Ka ba da bayani.
9 Yadda muka gani, Bulus ya ce yin zaɓe da ya bambanta bai kamata ya hana haɗin kai ba muddin ba a taka ƙa’idodi na Kirista ba. Shi ya sa Bulus ya tambayi Kiristoci masu raunannen lamiri: “Kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan’uwanka?” Kuma ya tambayi waɗanda suka fi ƙarfi (wataƙila waɗanda lamirinsu ya yarda su ci wasu abinci da Dokar ta hana ko su yi aiki a ranan Asabarci): “Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan’uwanka?” (Romawa 14:10) In ji Bulus, Kiristoci da suke da raunannen lamiri dole su daina hukunta ’yan’uwansu da ba sa nace wa abu. Amma, Kiristoci da suke da ƙarfi ba za su raina waɗanda har ila lamirinsu raunanne ne a wasu wurare ba. Ya kamata dukansu su daraja ra’ayin juna kuma kada su “ɗauki [kansu] fiye da yadda ya kamata.”—Romawa 12:3, 18.
10 Bulus ya bayyana ra’ayin da ya daidaita haka: “Kada fa mai cin kome ɗin nan ya raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan ya ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu.” Ƙari ga haka, ya ce: “Almasihu ya karɓe [mu] hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.” Tun da Allah da Kristi sun karɓi rarrauna da mai ƙarfi, ya kamata mu ma mu kasance da wannan halin mu “karɓi juna hannu biyu biyu.” (Romawa 14:3; 15:7) Wanene zai yi musun wannan?
Ƙauna ta ’Yan’uwanci Tana Kawo Haɗin Kai a Yau
11. Wane yanayi na musamman ya kasance a kwanakin Bulus?
11 A wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus yana maganar yanayi na musamman. Ba da daɗewa ba Jehovah ya kawar da wani alkawari kuma ya kafa sabo. Yana wa wasu wuya su daidaita da sabuwar dokar. Ba mu da irin wannan yanayin a yau, amma irin waɗannan batutuwa na iya tasowa wani lokaci.
12, 13. A waɗanne yanayi ne Kiristoci a yau za su yi la’akari da lamirin ’yan’uwansu?
12 Alal misali, ƙila mace Kirista tana bin wani addini da ba sa damuwa da yin ado. Sa’ad da ta san gaskiya, za ta iske shi da wuya ta yi gyara ga ra’ayin cewa ba a hana yin ado mai kyau ba a yanayi da ya dace ko kuma ta yi kwalliya. Tun da bai ƙetare ƙa’ida na Littafi Mai Tsaki ba, ba zai dace ba kowa ya yi ƙoƙari ya rinjayi mace Kirista ta taka lamirinta ba. Amma kuma, za ta fahimci cewa bai kamata ta zargi mata Kirista da lamirinsu ya ƙyale su su yi amfani da irin waɗannan abubuwa ba.
13 Ga wani misali. Ƙila Kirista ya yi girma a wurin da ba a son shan giya. Da ya san gaskiya, ya koya cewa Littafi Mai Tsarki yana ɗaukan giya kyauta ce daga Allah kuma cewa za a yi amfani da ita daidai kima. (Zabura 104:15) Ya yarda da wannan ra’ayi. Amma, domin inda ya fito ya fi son kada ya sha giya sam sam, kuma ba ya zargin waɗanda suke shanta daidai kima ba. Ta haka, yana bin kalmomin Bulus: “Sai mu himmantu ga yin abubuwan da ke kawo salama, su kuma inganta juna.”—Romawa 14:19.
14. A waɗanne yanayi Kiristoci za su iya yin amfani da gargaɗin Bulus ga Romawa?
14 Wani yanayi yana iya tasowa da ke bukatar mu yi amfani da gargaɗin Bulus ga Romawa. A cikin ikilisiyar Kirista akwai mutane da yawa, kuma suna son abubuwa dabam dabam. Shi ya sa suke zaɓe dabam dabam—alal misali, a batun sa tufafi da yin ado. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya tsara ƙa’idodi da dukan Kiristoci na gaskiya suke bi. Bai kamata kowannenmu ya sa tufafi ko kuma salon yin gashi da bai dace ba ko kuma wanda ke nuna cewa muna tarayya da duniya. (1 Yahaya 2:15-17) Kiristoci suna tunawa cewa a kowane lokaci, ko sa’ad da suke hutawa, su masu hidima ne da ke wakiltar Mamallakin Dukan Halitta. (Ishaya 43:10; Yahaya 17:16; 1 Timoti 2:9, 10) Amma, a wurare da yawa Kiristoci suna da zaɓe mai kyau da za su yi.a
Ka Kauce wa Sa Mutane Tuntuɓe
15. Yaushe ne Kirista ba zai yi abin da yake so ba don amfanin ’yan’uwansa?
15 Akwai muhimmiyar ƙa’ida ta ƙarshe da Bulus ya jawo hankalinmu a cikin gargaɗinsa ga Kiristoci a Roma. Wani lokaci, Kirista mai lamiri da aka koyar sosai zai iya ya ƙi yin abin da ya sani cewa daidai ne. Me ya sa? Domin ya fahimci cewa yin wannan abu zai iya yi wa wasu lahani. A irin wannan yanayin, me ya kamata mu yi? Bulus ya ce: “Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan’uwanka yin tuntuɓe.” (Romawa 14:14, 20, 21) Da haka, “mu da ke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai. Kowannenmu yā faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa da kuma inganta shi.” (Romawa 15:1, 2) Tun da za mu iya bakanta wa lamirin ’yan’uwa Kirista ta abin da muka yi, ƙaunar ’yan’uwa za ta motsa mu mu yi la’akari da mutane kuma mu ƙi yin abin da zai sa wasu fushi. Misalin wannan zai iya zama shan barasa. An yarda Kirista ya sha giya da kima. Amma idan yin hakan zai sa ɗan’uwansa tuntuɓe, ba zai nace ya sha giya ba don yana da daman yin haka.
16. Ta yaya za mu yi la’akari da waɗanda suke yankinmu?
16 Za a iya yin amfani da wannan ƙa’ida a sha’aninmu da waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista. Alal misali, muna iya zama a wurin da addini da ke wajen ya koya wa mabiyansa su ɗauki rana ɗaya a mako don hutu. Saboda haka, don kada mu sa maƙwabtanmu tuntuɓe kuma mu kawo damuwa ga aikin wa’azinmu, za mu kauce wa yin kome yadda ya yiwu a wannan ranar da zai sa maƙwabtanmu fushi. A wani yanayi, Kirista mai kuɗi ƙila ya ƙaura zuwa inda ake da bukata mai girma tsakanin matalauta. Zai iya zaɓi ya yi la’akari da sababbin maƙwabtansa ta yin ado mai sauƙi ko kuma yin salon rayuwa mai sauƙi ko idan ma yana da kuɗin.
17. Me ya sa ya dace mu yi la’akari da wasu a zaɓe da muke yi?
17 Za a bukaci “ƙarfafa” su yi gyara ne? To, ka yi tunanin wannan misalin: Yayin da muke tuƙi a hanya, sai ga yara suna tafiya suna wasa kusa da hanya. Za mu ci gaba da tuƙi yadda muke yi domin muna da ikon yin hakan? A’a, za mu rage gudu domin kada mu ji wa yaran rauni. Wani lokaci, ana bukatar mu daina yin abin da muke yi domin dangantakarmu da ’yan’uwa masu bi ko kuma wasu. Ƙila muna yin abin da muke da damar yi. Ba a taka wata ƙa’ida na Littafi Mai Tsarki ba. Duk da haka, idan za mu baƙanta wa wasu ko kuma yi wa waɗanda suka raunana a lamiri lahani, ƙauna ta Kiristoci za ta motsa mu mu aikata da hikima. (Romawa 14:13, 15) Haɗin kai da kuma ɗaukaka al’amura ta Mulki ya fi muhimmanci da yin abin da muke da daman yi.
18, 19. (a) A yin la’akari da mutane, yaya muke bin misalin Yesu? (b) A waɗanne batutuwa dukanmu muke aikata da cikakken haɗin kai, kuma menene za a tattauna a talifi na gaba?
18 Sa’ad da muka aikata haka, muna bin misalin da ya fi kyau. Bulus ya ce: “Ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, ‘zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.’ ” Yesu yana shirye ya ba da hadayar ransa dominmu. Hakika za mu daina wasu abubuwa idan wannan zai taimaki waɗanda ke “raunana” su haɗa kai a ɗaukaka Allah tare da mu. Hakika, nuna halin yarda ga Kiristoci da suke da lamiri mai raunana—ko kuma rage zaɓenmu da kuma daina nacewa a kan damarmu—na nuna “halin Almasihu, Yesu.”—Romawa 15:1-5.
19 Ko da ra’ayinmu a batutuwa da ba su shafi ƙa’idodi na Nassi ba zai iya bambanta, a batutuwan bauta muna da haɗin kai. (1 Korantiyawa 1:10) Ana ganin irin wannan haɗin kai a yadda mu ke aikata ga waɗanda suke hamayya da bauta ta gaskiya. Kalmar Allah ta kira waɗannan masu hamayya baƙi kuma ta yi mana gargaɗi mu mai da hankali da “muryar baƙo.” (Yahaya 10:5) Ta yaya za mu san irin waɗannan baƙi? Yaya ya kamata mu aikata? Za a bincika waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Iyayen ƙananan yara ne suke musu ja-gora a batun sa tufafi.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa ra’ayi dabam dabam a kan batutuwa na kanmu ba zai sa a daina haɗin kai ba?
• Me ya sa ya kamata mu Kiristoci mu yi la’akari da juna?
• A waɗanne hanyoyi za mu yi amfani da gargaɗin Bulus a kan haɗin kai a yau, kuma me zai motsa mu mu yi hakan?
[Hoto a shafi na 20]
Gargaɗin Bulus game da haɗin kai yana da muhimmanci a ikilisiya
[Hoto a shafi na 21]
Kiristoci suna da haɗin kai ko da sun fito daga wurare dabam dabam
[Hoto a shafi na 23]
Me ya kamata wannan direba ta yi yanzu?