Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/15 pp. 13-15
  • Kana Barin Jehobah Ya Yi Maka Tambaya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Barin Jehobah Ya Yi Maka Tambaya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Gama Zan Tambaye Ka”
  • Yadda Za Mu Bari Jehobah Ya Yi Mana Tambaya
  • Tambayoyi Sukan Jawo Mu Kusa da Jehobah
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/15 pp. 13-15

Kana Barin Jehobah Ya Yi Maka Tambaya?

LITTAFI MAI TSARKI yana ƙunshe da ɗarurruwan tambayoyi da suke sa tunani. A gaskiya, Jehobah Allah da kansa ya yi amfani da tambayoyi domin ya koyar da muhimman gaskiya. Alal misali, Jehobah ya yi amfani da tambayoyi da yawa a lokacin da yake yi wa Kayinu gargaɗi ya daidaita tafarkinsa mai ɓarna. (Far. 4:6, 7) A wasu lokatai, tambayoyi daga Jehobah suna sa mutum ya ɗauki mataki mai kyau. Daga jin tambayar Jehobah: “Wa zan aika, kuma wanene za ya tafi domin mu?” annabi Ishaya ya amsa: ‘Ga ni! ka aike ni.’—Isha. 6:8.

Yesu, Babban Malami, ya yi tambayoyi masu amfani. Linjiloli suna ɗauke da tambayoyi fiye da 280 da Yesu ya yi. Ko da yake a wasu lokatai yana yin tambayoyi domin ya sa masu nemansa da laifi su yi shiru, sau da yawa manufarsa ita ce ya shiga zuciyar masu sauraronsa, ya motsa su su yi tunani game da yanayin ruhaniyarsu. (Mat. 22:41-46; Yoh. 14:9, 10) Hakazalika, manzo Bulus, wanda ya rubuta littattafai 14 na Nassosin Helenanci na Kirista, ya yi amfani da tambayoyi domin shawo kai. (Rom. 10:13-15) Alal misali, wasiƙarsa ga Romawa tana ɗauke da tambayoyi masu yawa. Tambayoyin Bulus sun motsa masu karatu su gane “zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa.”—Rom. 11:33.

Yayin da wasu tambayoyi suna neman amsa da baki nan da nan, wasu kuma manufarsu ita ce motsa yin tunani mai zurfi. Linjila ta ba da labari mai yawa game da yadda Yesu ya yi amfani da na biyen. A wani lokaci, Yesu ya gargaɗi almajiransa: “Ku yi lura, ku yi hankali da yeast na Farisawa da na Hiridus,” manufa riyar su da kuma koyarwar ƙaryarsu. (Mar. 8:15; Mat. 16:12) Almajiran Yesu ba su fahimci abin da yake nufi ba sai suka soma yin gardama akan gurasar da suka manta su kawo. Ka lura da yadda Yesu ya yi amfani da tambayoyi a taƙaitaccen magana wani na bin wani. “Ya ce musu, Don me kuke yin bincike ko domin ba ku da gurasa ne? Ba ku gane ba tukuna, ba ku fahimta ba kuma? Kuna da zuciya tattaura ne? Kuna da idanu, ba ku gani; kuna da kunnuwa, ba ku ji? . . . Ba ku tuna da komai?” Tambayoyin da Yesu ya yi masu sa tunani ne, wanda hakan ya motsa almajiransa su yi tunani akan ainihin manufar kalmominsa.—Mar. 8:16-21.

“Gama Zan Tambaye Ka”

Jehobah ya yi amfani da tambayoyi domin ya gyara tunanin bawansa Ayuba. Ta hanyar tambayoyi masu yawa, Jehobah ya koya wa Ayuba ƙanƙantarsa idan aka kwatanta shi da Mahalicci. (Ayu, sura 38-41) Jehobah yana sa ran cewa Ayuba zai amsa kowanne cikin waɗannan tambayoyin da baki? Da kyar. Tambayoyi kamar su “Ina ka ke sa’anda na sanya tussan duniya?” an yi su ne domin motsa tunanin Ayuba da kuma yadda yake ji. Bayan waɗannan tambayoyi masu zafi, Ayuba ya rasa abin da zai ce. Sai kawai ya ce: “Mi zan amsa maka? Na sa hannuna a bakina.” (Ayu. 38:4; 40:4) Ayuba ya gane batun kuma ya ƙasƙantar da kansa. Amma, ba wai Jehobah yana koya wa Ayuba ya zama mai tawali’u kawai ba ne ba. An daidaita tunanin Ayuba. A wace hanya?

Ko da yake Ayuba “kamili ne, mutum mai-adalci,” a wasu lokatai kalmominsa suna nuna ra’ayin da bai dace ba, wanda Elihu ya ambata sa’ad da yake tsauta wa Ayuba “domin ya maida kansa ya fi Allah gaskiya.” (Ayu. 1:8; 32:2; 33:8-12) Da haka, tambayoyin Jehobah sun daidaita fahimin Ayuba. Sa’ad da yake magana daga cikin hadari, Allah ya ce: ‘Wanene wannan da ke duhunta shawara da maganganu marasa-ilimi? Ka yi ɗamara yanzu kamar namiji, gama zan tambaye ka, sai ka shaida mini.’ (Ayu. 38:1-3) Ta wajen yin amfani da tambayoyi, Jehobah ya jawo hankali ga hikimarsa da ikonsa marar iyaka kamar yadda ayyukansa masu ban al’ajabi suka nuna. Wannan ƙarin hasken ya taimaka wa Ayuba ya dogara sosai fiye da dā ga hukuncin Jehobah da kuma yadda yake yin abubuwa. Abu ne mai ban al’ajabi da kuma tsoro ga Ayuba, wato, Allah Maɗaukaki Duka da kansa ya yi masa tambaya!

Yadda Za Mu Bari Jehobah Ya Yi Mana Tambaya

Mu kuma fa? Mu ma za mu iya amfana daga tambayoyin da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki? Ƙwarai kuwa, za mu iya! Barin waɗannan tambayoyi su sa mu dakata mu yi tunani zai iya kawo mana albarka masu yawa na ruhaniya. Tambayoyi masu iko da ke cikin Kalmar Allah su ne suka daɗa ga amfaninta. Hakika, “maganar Allah . . . mai-aikatawa . . . tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) Domin mu amfana sosai, muna bukatan mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyi. (Rom. 15:4) Bari mu bincika wasu misalai.

“Mai-shari’an dukan duniya ba za ya yi daidai ba?” (Far. 18:25) Ibrahim ya yi wannan tambayar da ba ta bukatar amsa ga Jehobah a lokacin da Allah yake son ya hukunta Saduma da Gwamrata. Ibrahim ya san cewa ba zai taɓa yiwu ba Jehobah ya yi rashin adalci, ta wajen kashe masu aminci tare da miyagu. Tambayar da Ibrahim ya yi ta nuna zurfin bangaskiyarsa a adalcin Jehobah.

A yau, wasu suna iya yin hasashe a kan batutuwan da suka shafi hukunce-hukuncen da Jehobah zai yi a nan gaba, kamar su, wanene ainihi zai tsira a Armageddon ko kuma wanene za a ta da daga matattu. Maimakon mu ƙyale irin waɗannan tunanin su dame mu, muna iya tunawa kanmu tambayar da Ibrahim ya yi. Sanin Jehobah a matsayin Uba na samaniya mai kula da kuma kasancewa da cikakken aminci a adalcinsa da kuma jin ƙansa, kamar yadda Ibrahim ya yi, zai hana mu ɓata lokaci da kuzari a kan damuwar da ba ta dace ba, shakka mai kawo raunana, da kuma mahawara marar amfani.

“Wanene a cikinku, don damuwa tasa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwa tasa?” (Mat. 6:27, Littafi Mai Tsarki) Da yake magana da taron jama’a da suka haɗa da almajiransa, Yesu ya yi amfani da wannan tambayar ce don ya nanata bukatar su dogara ga Jehobah mai ƙauna. Kwanakin ƙarshe na wannan mugun zamanin yana jawo damuwa masu yawa, amma mai da hankali a kansu ba zai ƙara tsawon rayukanmu ba ko kuma su kyautata ranmu.

A duk lokacin da muka ji cewa muna damuwa game da kanmu ko kuma ƙaunatattunmu, tuna wa kanmu tambayar da Yesu ya yi zai iya taimaka mu kasance da ra’ayin da ya dace game da damuwarmu. Zai iya taimaka mana mu daina damuwa kuma mu kawar da tunanin da bai da kyau da zai shafi hankalinmu, yadda muke ji, da kuma jikinmu. Kamar yadda Yesu ya ba mu tabbaci, Ubanmu na samaniya, wanda yake ciyar da tsuntsayen sama da kuma yi wa ganyaye sutura, ya san abin da muke bukata.—Mat. 6:26-34.

“Ya yiwu mutum shi sa wuta a ƙirjinsa, tufafinsa su rasa ƙonewa?” (Mis. 6:27) Surori tara na farko na littafin Misalai sun haɗa da ’yar gajerar tattaunawa da uba yake yi da ɗansa don ya koya masa hikima mai amfani. Tambayar da aka yi ƙaulinsa a sama ya nuna mugun sakamakon zina. (Mis. 6:29) Idan muka ga cewa mun soma sha’awar yin kwarkwasa ko kuma muna marabtar sha’awa marar kyau na jima’i, wannan tambayar za ta tuna mana haɗarin da ke tattare da yin hakan. A ƙa’idance, mutum zai iya yi wa kansa wannan tambayar a duk lokacin aka jarabta shi ya bi tafarki marar kyau. Ta bayyana wannan ƙa’idar da ke cikin Littafi Mai Tsarki dalla-dalla: ‘Za ka girbe abin da ka shuka’!—Gal. 6:7.

“Wanene kai da ka ke zartas ma baran wani?” (Rom. 14:4) A wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya tattauna matsaloli da suka taso a ikilisiya na ƙarni na farko. Wasu Kiristoci, da suka zo daga al’adu dabam-dabam, suna da nufin yanke hukunci a kan shawarwari da ayyukan ’yan’uwansu masu bi. Tambayar da Bulus ya yi ta tuna musu su marabci juna kuma su bar hukunci a hannun Jehobah.

Hakazalika a yau, mutanen Jehobah sun zo ne daga wurare dabam-dabam. Duk da haka, Jehobah ya kawo mu tare cikin haɗin kai mai tamani. Muna daɗa ga wannan haɗin kan? Idan muna da nufin saurin furta rashin amincewa akan wani abin da ɗan’uwa ya yi bisa ga lamirinsa, zai kasance hikima mu yi wa kanmu tambayar da Bulus ya yi a sama!

Tambayoyi Sukan Jawo Mu Kusa da Jehobah

Waɗannan misalai ƙalilan sun nuna yadda mutum zai bincika kansa ta wurin tambayoyin da ke cikin Kalmar Allah. Yin la’akari da mahallin kowace tambaya zai iya taimaka mana mu yi amfani da ita a yanayin mu. Yayin da muke karanta Littafi Mai Tsarki, za mu ga ƙarin tambayoyi masu taimakawa.—Duba akwati da ke shafi na 14.

Barin tambayoyi masu sa tunani da ke cikin Kalmar Allah su taɓa mu sosai zai taimaka mana mu daidaita zuciyarmu da hankalinmu da hanyoyi masu adalci na Jehobah. Bayan da Jehobah ya yi masa tambayoyi, Ayuba ya ce: “Na ji labarinka ta wurin ji na kunne; amma yanzu idona ya gan ka.” (Ayu. 42:5) Hakika, Ayuba ya zo ya san Jehobah sosai, kamar yana ganin Jehobah ido da ido. Almajiri Yakubu daga baya ya furta batun kamar haka: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙ. 4:8) Bari mu bar duk wani sashe na Kalmar Allah, har da tambayoyin da ke ciki, su taimake mu mu girma a ruhaniya kuma mu “ga” Jehobah sosai!

[Akwati da ke shafi na 14]

Ta yaya yi wa kanka waɗannan tambayoyi za su taimake ka ka kasance da ra’ayin Jehobah game da batutuwa?

▪ “Ko Ubangiji yana murna dayawa da hadayu na ƙonawa da sacrifices kamar yadda yake murna da biyayya ga muryar Ubangiji?”—1 Sam. 15:22.

▪ “Shi wanda ya sifanta ido, ba za ya gani ba?”—Zab. 94:9.

▪ “Kana ganin mutum yana da hikima a ganin kansa?”—Mis. 26:12.

▪ “Ka yi kyau da kana fushi ne?”—Yun. 4:4.

▪ “Gama ina abin da mutum ya ribato, ko da ya sami dukan duniya, ya ruɓusadda ransa?”—Mat. 16:26.

▪ “Wa za ya raba mu da ƙaunar Kristi?”—Rom. 8:35.

▪ “Me ke gareka da ba ka karɓa kuwa?”—1 Kor. 4:7.

▪ “Wace tarayya haske ya ke da duhu?”—2 Kor. 6:14.

[Hoton da ke shafi na 15]

Menene Ayuba ya koya daga tambayoyin da Jehobah ya yi masa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba