Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 7/1 pp. 15-20
  • Ka Koya Kuma Ka Koyar Da Ɗabi’a Ta Kirista

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koya Kuma Ka Koyar Da Ɗabi’a Ta Kirista
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Za Ka Koyar da Kanka?
  • Ka Koyar da Ɗabi’a ta Kirista
  • Ka Yi Nazari Domin Ka Koyar
  • Kada Ka Bar ‘Hikimar Wannan Duniyar’ ta Yaudare Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 7/1 pp. 15-20

Ka Koya Kuma Ka Koyar Da Ɗabi’a Ta Kirista

“Kai fa mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba?”—ROMAWA 2:21.

1, 2. Waɗanne dalilai kake da shi na son yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

KANA da dalilai masu yawa na yin nazarin Kalmar Allah. Wataƙila kana son ka san gaskiya—game da mutane, aukuwa, wurare, da kuma wasu abubuwa. Kana son ka san koyarwar gaskiya, yadda take saɓawa da kuskure na addini, irinsu Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ko kuma wutar jahannama. (Yohanna 8:32) Kuma kana so ka zo ga sanin Jehovah da kyau domin ka zama kamarsa kuma ka yi tafiya a hanya mai kyau.—1 Sarakuna 15:4, 5.

2 Wani muhimmin dalili kuma na yin nazarin Kalmar Allah shi ne mu shirya kanmu mu koyar da wasu—waɗanda muke ƙauna, da idon sani, da kuma waɗanda ba mu san su ba tukuna. Yin haka tilas ne ga Kirista na gaskiya. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—Matta 28:19, 20.

3, 4. Me ya sa daraja ce gare ka ka koyar yadda Yesu ya umurta?

3 Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da burin son koyar wa wasu yana da kyau kuma tushen gamsuwa ne. Da daɗewa ana daraja fasahar koyarwa. Littafin nan Encarta Encyclopedia ya ce: “A tsakanin Yahudawa, mutane da yawa suna ɗaukan malamai masu ja-gora ne zuwa ceto kuma suna ariritar yara su daraja malamansu fiye ma da iyayensu.” Abin ɗaukaka ne musamman ga Kiristoci su koyar da kansu ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma su koyar da wasu.

4 “Mutane da yawa suna daɗa sa hannu cikin aikin koyarwa fiye da ko wane irin aiki. Da akwai kusan mutane maza da mata miliyan 48 a dukan duniya da suna malanta.” (The World Book Encyclopedia) Malami yana da hakkin ya koyar da matasa kuma wannan yana rinjayarsu na shekaru da yawa. A kan samu sakamako mafi kyau ma idan ka yi biyayya da umurnin Yesu ka koyar wa wasu; za ka iya rinjayar su da begen rai madawwami a nan gaba. Manzo Bulus ya nanata wannan lokacin da ya aririce Timothawus: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.” (1 Timothawus 4:16) Hakika, koyarwarka ta ƙunshi ceto.

5. Me ya sa koyarwa ta Kirista ce ta fi kowacce?

5 Koya wa kanka sai kuma ka koyar da wasu doka ce da ja-gora daga Mamallakin dukan halitta, Tushe mafi girma. Wannan ya sa koyarwar ta fi kowacce irin sana’a a duniya, ko koyarwar adabi ne, fasaha, har ma tsarin magani. Koyarwa ta Kirista ta haɗa da koyar da ɗalibai su koyi yin koyi da Ɗan Allah, Kristi Yesu, kuma su koya wa wasu su yi hakan.—Yohanna 15:10.

Me Ya Sa Za Ka Koyar da Kanka?

6, 7. (a) Me ya sa dole ne mu koyar da kanmu da farko? (b) A wane azanci ne Yahudawa na ƙarni na farko suka kasa a zama masu koyarwa?

6 Me ya sa aka ce mu koyar da kanmu da farko? To, ba za mu iya koyar da wasu da kyau ba idan ba mu koyar da kanmu ba da farko. Bulus ya nanata wannan cikin maganarsa na sa tunani da take da ma’ana ga Yahudawa a lokacin, da take da ma’ana ƙwarai kuma ga saƙon Kiristoci a yau. Bulus ya yi tambaya: “Kai fa mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba? kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata? kai da ka ke faɗi kada a yi zina, kana yin zina? kai da ka ke ƙyamar gumaka, mai saɓon haikali ne kai? kai da ka ke fahariya cikin shari’a, ta wurin ƙetaren shari’a da ka ke yi kana ɓāta girman Allah?”—Romawa 2:21-23.

7 Ta yin tambayoyi, Bulus ya fito da laifi biyu da Dokoki Goma suka ƙasaita: Kada ka yi sata, kuma kada ka yi zina. (Fitowa 20:14, 15) Wasu Yahudawa a zamanin Bulus suna fahariyar suna da Dokar Allah. ‘Suna sane da nufinsa, suna shaida al’amuran da ke mafifita, koyayyu ne daga cikin Attaurat, sun kuwa sakankance su da kansu masu-ja-goran makafi ne, haske ga waɗanda su ke cikin duhu, masu-koya ma jarirai.’ (Romawa 2:17-20) Amma, wasun su masu riya ne domin a ɓoye suna sata ko kuma zina. Wannan yana ƙasƙantar da Dokar da kuma Mawallafinta da ke sama. Za ka ga cewa ba su ma ƙware su koyar da wasu ba; hakika ba sa ma koyar da kansu.

8. Wataƙila ta yaya ne wasu Yahudawa a zamanin Bulus suke ‘saɓa wa haikali’?

8 Bulus ya ambaci saɓon haikali. Da gaske ne cewa wasu Yahudawa sun yi haka? Menene Bulus yake nufi? Hakika, domin babu cikakken bayani a kan wannan ayar, ba za mu faɗi da tabbas yadda wasu Yahudawa suka ‘saɓa wa haikali’ ba. Da farko marubucin tarihi na Afisas ya sanar da cewa abokan Bulus ba ‘masu saɓon haikali’ ba ne, da ya nuna cewa ana tuhumar Yahudawa da wannan. (Ayukan Manzanni 19:29-37) Shin suna amfani ne ko kuma sayar da kayayyaki masu tamani na haikalin arna da ’yan addini masu zafin rai da suka ci su ganima? Dokar Allah ta ce, zinariya da azurfar gumaka a halaka su, ba su dace a yi amfani da su ba. (Kubawar Shari’a 7:25)a Saboda haka, Bulus ƙila yana nufin Yahudawa da suke taka dokar Allah kuma suke amfani ko samun riba daga kayayyaki da asali daga haikalin arna ne.

9. Waɗanne munanan ayyuka da suka shafi haikalin a Urushalima ya yi daidai da saɓa wa haikali?

9 A wata sassa kuma, Josephus ya faɗi game da wani ɓata suna da Yahudawa huɗu suka yi a Roma, waɗanda shugabansu mai koyar da Dokar ne. Waɗannan mutane huɗu sun rinjayi mace ’yar Roma ta ba su zinariya da wasu kayayyaki masu tamani domin haikali a Urushalima. Da suka karɓa daga hannunta, suka zuba a aljihunsu—daidai da yin ƙwace a haikali.b Wasu kuma a wata sassa suna saɓa wa haikali ta wurin yin hadaya da dabbobi masu lahani suna gabatar da kasuwanci na haɗama a cikin farfajiyarta, sun mai da haikalin ya zama “kogon mafasa.”—Matta 21:12, 13; Malachi 1:12-14; 3:8, 9.

Ka Koyar da Ɗabi’a ta Kirista

10. Bai kamata mu ƙyale menene ba game da kalmomin Bulus da ke a Romawa 2:21-23?

10 Ko da waɗannan ayyuka ne na ƙarni na farko game da sata, zina, da kuma saɓa wa haikali da Bulus ya yi zancensu, kada mu ƙyale ainihin abin da yake nufi. Ya yi tambaya: “Kai fa mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba?” Abin lura ne cewa misalai da Bulus ya ambata game da ɗabi’a ne. Ba koyarwa ko tarihin Littafi Mai Tsarki ne manzo yake mai da hankali ba. Koyar da kanka da kuma koyar da wasu da Bulus yake nufi a nan batun ɗabi’ar Kiristanci ne.

11. Me ya sa ya kamata ka mai da hankali ga ɗabi’ar Kiristanci yayin da kake nazarin Kalmar Allah?

11 Domin mu yi amfani da darasi da ke a Romawa 2:21-23 yana nufin koyon ɗabi’ar Kirista daga Kalmar Allah, muna aikata daidai da abin da muka koya, sai kuma mu koyar da wasu wannan. Saboda haka, yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, ka lura da nuni na mizanan Jehovah, waɗanda daga su aka samo ɗabi’a ta Kiristanci na gaskiya. Ka yi bimbini a kan gargaɗi da kuma darussa da ka gani cikin Littafi Mai Tsarki. Sai kuma da gaba gaɗi ka yi amfani da abin da ka koya. Kuma yin haka fa yana bukatar gaba gaɗi tare da ƙuduri. Yana da sauƙi mutane ajizai su nemi hujja, ko dalilai na cewa yanayi ne ya jawo lalata ɗabi’ar Kirista a wani fanni. Wataƙila waɗancan Yahudawa da Bulus ya ambata suna da irin wannan hujja a kaikaice ko kuma su ruɗi wasu. Amma kalmomin Bulus ya nuna cewa ba za a rage ko kuma yi banza da ɗabi’ar Kiristanci ba domin zaɓen mutum.

12. Yaya halin kirki da mummunar hali yake shafan Jehovah Allah, kuma me ya sa abin taimako ne a tuna da wannan?

12 Manzon ya fid da muhimmin dalilin koyo da kuma yin amfani da ɗabi’a da ka gani cikin Littafi Mai Tsarki. Rashin ɗabi’a na Yahudawan ya shafi Jehovah: “Kai da ka ke fahariya cikin shari’a, ta wurin ƙetaren shari’a da ka ke yi kana ɓāta girman Allah? Gama a wurin Al’ummai ana saɓon sunan Allah saboda ku.” (Romawa 2:23, 24) Gaskiya ne cewa idan muka yi banza da ɗabi’ar Kiristanci, muna raina Tushenta. Akasarin haka, idan muka riƙe mizanan Allah, tana kawo masa daraja, tana ɗaukaka shi. (Ishaya 52:5; Ezekiel 36:20) Idan ka san wannan, zai iya ƙarfafa niyyarka yayin da ka fuskanci gwaji ko yanayi da ke sa ya zama da sauƙi a ƙyale ɗabi’ar Kiristanci. Ban da haka ma, kalmomin Bulus sun koya mana wani abu kuma. Ban da yadda halinmu ke shafar Allah, yayin da kake koyar da wasu, ka taimake su su ga cewa yadda suke amfani da mizanan ɗabi’a da suke koya zai shafi Jehovah. Ba a cewa ɗabi’ar Kiristanci na kawo gamsuwa kuma na kāre lafiyar mutum kawai ba. Yana shafan Wanda ma yake yin tanadin kuma ke ƙarfafa irin wannan ɗabi’ar.—Zabura 74:10; Yaƙub 3:17.

13. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya taimake mu game da ɗabi’a? (b) Ka ba da ɗan bayanin 1 Tassalunikawa 4:3-7?

13 Halin ɗabi’a ma yana shafan wasu mutane. Za ka iya ganin wannan a cikin misalai cikin Kalmar Allah da ke nuna darajar yin amfani da mizanan ɗabi’a na Allah da kuma sakamakon ƙin su. (Farawa 39:1-9, 21; Joshua 7:1-25) Za ka iya samun irin gargaɗin nan kai tsaye a kan ɗabi’a cewa: “Gama nufin Allah ke nan, tsarkakewarku, ku hanu daga fasikanci; kowanne daga cikinku shi san yadda za shi riƙe santali nasa cikin tsarkakewa da daraja, ba cikin zafin guri na sha’awa ba, kamar Al’ummai da ba su san Allah ba; kada kowa shi zarce, shi ciwuci ɗan’uwansa cikin wannan al’amari. . . . Gama Allah ya kira mu, ba domin ƙazanta ba, amma cikin tsarkakewa.”—1 Tassalunikawa 4:3-7.

14. Me za ka iya tambayar kanka a batun gargaɗin da ke a 1 Tassalunikawa 4:3-7?

14 Kusan kowa zai fahimta daga wannan ayar cewa lalatar jima’i yana karya dokar ɗabi’a ta Kirista. Amma, za ka iya samun ƙarin bayani game da ayar nan. Wasu matani sun ba da zarafi na yin nazari da kuma na bimbini da zai ƙara fahimi ƙwarai a kansu. Alal misali, kana iya tunanin abin da Bulus yake nufi da ya ce yin fasikanci zai iya sa mutum ya “zarce, shi cuci ɗan’uwansa cikin wannan al’amari.” Wane irin cuta wannan ya ƙunsa, kuma ta yaya fahimtar wannan sosai zai taimake ka ka so riƙe ɗabi’a ta Kirista? Ta yaya sakamakon wannan bincike zai shirya ka ka koya wa wasu kuma ka taimake su su daraja Allah?

Ka Yi Nazari Domin Ka Koyar

15. Waɗanne kayayyakin aiki za ka iya amfani da su a koyar da kanka a nazarinka?

15 Shaidun Jehovah suna da kayayyakin da suke amfani da su su yi bincike a kan tambayoyi ko mahawwara da suka taso yayin da suke nazari su koyar da kansu ko kuma su koyar da wasu. Wani abin bincike da ke akwai a harsuna da yawa shi ne Watch Tower Publications Index. Idan kana da shi, za ka iya yin amfani da shi wajen neman bayani da ke daga littattafan Shaidun Jehovah da ke daga Littafi Mai Tsarki. Kana iya yin binciken somawa bisa jigon ko jerin ayoyin Littafi Mai Tsarki. Wani abin bincike kuma da Shaidun Jehovah suke da shi a manyan harsuna shi ne Watchtower Library. Wannan tsari na kwamfuta da ake samu cikin CD-ROM yana cike da littattafai da aka zaɓa ya yi aiki da na’ura. A cikin tsarin, za ka iya bincike jigo da kuma wasu batutuwa na nassosi. Idan ɗaya ko duka biyun kake da su, ka yi amfani da su a kai a kai yayin da kake nazarin Kalmar Allah domin ka iya koyar da wasu.

16, 17. (a) A ina za ka samu wayewar kai a kan cuci da aka ambata a 1 Tassalunikawa 4:6? (b) A waɗanne hanyoyi ne fasiƙanci yake cucin wasu?

16 Bari mu yi amfani da misalin da aka nuna a baya, 1 Tassalunikawa 4:3-7. An yi tambaya game da cuta. Cutar wa? Yaya za a iya cutar wani? Cikin kayan binciken da aka ambata, ƙila za ka iya samun kalami da zai wayar da kai game da ayoyin nan, har a batun cuta da Bulus ya ambata. Kana iya karanta wannan daga Insight on the Scriptures, Kundi na 1, shafuffuka 863-864; True Peace and Security—How Can You Find It?, shafi na 145; Hasumiyar Tsaro, 15 ga Nuwamba, 1989 (Turanci), shafi na 31.

17 Idan ka ci gaba da nazarin, za ka ga cewa waɗannan littattafai sun bayyana gaskiyar kalmomin Bulus. Fasiƙi yana zunubi ne ga Allah kuma yana saka kansa cikin haɗarin ɗaukan cututtuka. (1 Korinthiyawa 6:18, 19; Ibraniyawa 13:4) Mutumin da yake fasiƙanci yana cutar macen da ya yi zunubin da ita. Ya cuce ta daga samun zaman ɗabi’a da samun lamiri mai tsabta. Idan marar aure ce, ya cuce ta ba za ta yi aure tana budurwa ba kuma mijin da zai aure ta an cuce shi daga samun wannan. Ya cuci iyayen macen da kuma mijinta idan tana da aure. Malalacin nan ya cuci iyalinsa daga samun sunan kirki. Idan yana cikin ikilisiya ne, ya jawo kunya a kan ikilisiyar, yana ɓata sunanta.—1 Korinthiyawa 5:1.

18. Ta yaya za ka amfana daga nazarin Littafi Mai Tsarki a batun ɗabi’a ta Kirista?

18 Kalamin nan a batun cuta bai taimake ka ka ga kyan ayar nan ba? Irin nazarin nan hakika yana da amfani mai girma. Yayin da kake biɗan haka, koyar da kanka kake yi. Fahiminka game da gaskiyar daga saƙon Allah yana ƙaruwa. Za ka ƙuduri aniyar riƙe ɗabi’a ta Kirista ko da wane gwaji ne ya zo. Yanzu ka yi tunanin ƙwarewarka na mai koyarwa! Alal misali, yayin da kake koyar da wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki, za ka iya koyar da darasin 1 Tassalunikawa 4:3-7, kana daɗa fahiminsu da godiya don ɗabi’ar Kiristanci. Saboda haka, nazarinka zai taimake ka da kuma wasu da yawa su ɗaukaka Allah. Kuma mun ambaci misali guda tak daga wasiƙar Bulus zuwa ga Tassalunikawa. Da akwai wasu fannoni na ɗabi’ar Kiristanci, kuma da akwai wasu misalai na Littafi Mai Tsarki tare da darasin da za ka iya yin nazarinsu, yi amfani da su, kuma ka koyar da su.

19. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙe ɗabi’a ta Kirista?

19 Babu abin shakka game da hikimar yin haka. Yaƙub 3:17 ta ce “hikima mai-fitowa daga bisa,” daga Jehovah Allah kansa, “tsatsarka ce dafari.” Wannan a bayyane yake a bin ɗabi’ar mizanan Allah. Hakika, Jehovah yana bukatar waɗanda suke wakiltarsa a koyar da Littafi Mai Tsarki su kansu su zama misalan kirki a “tsabtar rai.” (1 Timothawus 4:12) Tafarkin rayuwar almajirai na farko kamarsu Bulus da Timothawus ya nuna sun yi rayuwar tsabta; sun guje wa lalata, har Bulus ya rubuta cewa: “Fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, gama haka ya kamata ga tsarkaka; ko dauɗa, ko kuwa zancen wauta, ko alfasha.”—Afisawa 5:3, 4.

20, 21. Me ya sa ka yarda da abin da manzo Yohanna ya rubuta, yadda yake a 1 Yohanna 5:3?

20 Ko da yake mizanan ɗabi’a an nuna su cikin Kalmar Allah a bayyane kuma takamammu, ba kaya ne na zalunci ba. Yohanna ya ga haka, shi da ke manzo da ya fi daɗewa. Daidai da abin da ya lura da shi a rayuwa, ya san cewa ɗabi’ar Kiristanci ba ta da lahani. Akasarin haka, tana da kyau, na da amfani, da albarka kuma. Yohanna ya nanata wannan, ya rubuta cewa: “Wannan ne ƙaunar Allah: mu kiyaye dokokinsa. Dokokinsa ba sa nawaita mu.”—1 Yohanna 5:3, New English Translation.

21 Amma ka lura cewa Yohanna bai nuna cewa yin biyayya ga Allah abu mafi kyau ne ta bin ɗabi’a ta Kirista kawai domin tana kāre mu daga matsaloli ba, daga munanan sakamakon yin lalata. Ya daidaita abubuwa ta yadda a farko ya fahimci cewa ƙaunar Jehovah Allah ce, zarafi mai tamani da za mu nuna ƙaunarmu gare shi. Hakika, koyar da kanmu ko kuma wasu su yi ƙaunar Jehovah na bukatar mu amince kuma mu yi amfani da mizanansa masu girma. Babu shakka, yana nufin koyar da kanmu da kuma wasu ɗabi’a ta Kirista.

[Hasiya]

a Yayin da yake nuna cewa Yahudawa ba sa ƙazantar da tsarkakkun abubuwa, Josephus ya maimaita dokar Allah a wannan hanyar: “Kada kowa ya raina allolin da wasu birane suke bauta wa, ko ka saɓa wa haikali na baƙi, kada ka ɗauko dukiya da an keɓe cikin sunan wani allah.”(Tafiyar tsutsa tamu ce.)—Jewish Antiquities, Littafi na 4, sura ta 8, izifi na 10.

b Jewish Antiquities, Littafi na 18, sura ta 3, izifi na 5.

Ka Tuna?

• Me ya sa dole ne mu yi nazari mu koyar da kanmu kafin mu koyar da wasu?

• Yaya halinmu ke shafan Jehovah?

• Wa fasiƙi yake cuta?

• Menene ka ƙudura za ka yi a batun ɗabi’a ta Kirista?

[Hoto a shafi na 20]

“Dokokinsa ba sa nawaita mu”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba