“Mu Bi Waɗannan Abu fa da ke Nufa Wajen Salama”
SABUWAR hanya takan bayyana kamar ba za ta taɓa lalacewa ba. Amma bayan wani lokaci, hanyar za ta iya soma tsagewa kuma ta yi gargada. Ana bukatar a gyara hanyar don a tabbatar da lafiyar mutane da kuma kyaun hanyar.
Hakazalika, a wasu lokatai, muna iya samun matsala a dangantakarmu da mutane. Manzo Bulus ya bayyana cewa Kiristocin da ke Roma sun sami saɓani a ra’ayinsu. Ya shawarci ’yan’uwa Kiristoci: “Mu bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama, da abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.” (Rom. 14:13, 19) Me ya sa muke bukatar biɗan “waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama”? Ta yaya za mu iya biɗan salama sosai da gaba gaɗi?
Me ya Sa Za Mu Biɗi Salama?
Idan aka ƙi gyarawa, ’yar ƙaramar tsagewa a kan hanya za ta iya yin faɗi ta zama muguwar gargada. Ƙin magance rashin jituwa zai iya jawo masifa. Manzo Yohanna ya rubuta: “Idan wani ya ce, Ina ƙaunar Allah, shi kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne shi: domin wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yoh. 4:20) Matsalar da aka ƙi warwarewa tana iya sa Kirista ya ƙi jinin ɗan’uwansa.
Yesu Kristi ya nuna cewa Jehobah ba zai karɓi bautarmu ba idan muka ƙi daidaitawa da mutane. Yesu ya umurci almajiransa: “Idan fa kana cikin miƙa baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.” (Mat. 5:23, 24) Hakika, ainihin dalilin da ya sa muke bukatar mu biɗi salama shi ne, muna son mu faranta wa Jehobah Allah rai.a
Wani abin da ya faru a ikilisiyar Filibbi ya nuna wani dalilin da zai sa mu biɗi salama. Wata matsalar da ba a ambata ba da ke tsakanin mata biyu Kiristoci, Afodiya da Sintiki ta so ta shafi salamar ikilisiyar gabaki ɗaya. (Filib. 4:2, 3) Saɓanin da aka ƙi warwarewa zai iya bazuwa nan da nan. Domin mun son mu kāre ƙauna da haɗin kan ikilisiya, hakan yana motsa mu mu biɗi salama da ’yan’uwanmu masu bi.
“Masu-albarka ne masu-sada zumunta,” in ji Yesu. (Mat. 5:9) Biɗar salama tana kawo farin ciki. Bugu da ƙari, salama tana sa ƙoshin lafiya, domin “natsatsiyar zuciya rai ce ga jiki.” (Mis. 14:30) A wani ɓangare kuma, riƙe mutum a zuciya yana iya sa mu rashin lafiya.
Ko da yake yawancin Kiristoci sun yarda cewa suna bukatar su biɗi salama, wataƙila kuna mamakin yadda za ku iya sasanta matsalar da ke tsakaninku da wani. Bari mu bincika mizanai na Nassi da za su yi mana ja-gora.
Tattaunawa Cikin Natsuwa Tana Kawo Salama
Ana iya gyara ƙananan wuraren da suka lalace a kan hanya ta wajen zuba kwalta. Zai yiwu mu gafarta kuma mu rufe ’yan kurakuran ’yan’uwanmu? Wataƙila, hakan zai taimaka mana mu daidaita matsalolinmu, domin manzo Bitrus ya rubuta cewa “ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.”—1 Bit. 4:8, Littafi Mai Tsarki.
A wasu lokatai kuwa, matsalar tana iya kasancewa mai tsanani wadda ba za mu iya yin watsi da ita ba kawai. Yi la’akari da abin da ya faru da Isra’ila jim kaɗan da shigarsu Ƙasar Alkawari. Kafin “’ya’yan Reuben da ’ya’yan Gad da rabin kabilar Manasseh” su tsallaka Kogin Urdun, sun gina “babban bagadi abin hanga.” Sauran ƙabilun Isra’ila sun ɗauka cewa suna amfani da bagadin ne su bauta wa gunki kuma suka kasa yin watsi da matsalar. Sai suka shirya kai yaƙi.—Josh. 22:9-12.
Wataƙila wasu Isra’ilawa sun yi tunanin cewa suna da isashiyar shaidar da ta nuna cewa an yi zunubi, kuma idan suka kai hari ba zato, waɗanda za su rasa ransu ba za su yi yawa ba. Maimakon su aikata aniyarsu cikin garaje, ƙabilun da ke yammacin Urdun sun aika wakilai su je su tattauna matsalar da ’yan’uwansu. Sun tambaye su: “Wane laifi ne wannan da kuka yi ma Allah na Isra’ila, har da kuka juya yau ga barin bin Ubangiji?” Gaskiyar ita ce, ƙabilun da suka gina bagadin ba su aikata rashin aminci ba. Amma me za su yi game da wannan tuhumar da ake musu? Za su gaya wa waɗanda suke tuhumarsu baƙar magana ce ko kuwa za su ƙi tattaunawa da su? Ƙabilun da ake tuhuma sun amsa cikin natsuwa, kuma sun bayyana dalla-dalla cewa sun yi abin da suka yi ne domin muradinsu na bauta wa Jehobah. Yadda suka mai da martani ya kāre dangantakarsu da Allah da kuma rayuka da yawa. Tattaunawar da suka yi cikin natsuwa ta daidaita batun kuma ta kawo salama.—Josh. 22:13-34.
Kafin su ɗauki mataki, waɗannan Isra’ilawan sun tattauna matsalarsu da ƙabilun Reuben, Gad, da rabin ƙabilar Manasseh. “Kada ka yi garaje a ranka garin yin fushi,” in ji Kalmar Allah, “gama wawa ke riƙe da fushi cikin ƙirjinsa.” (M. Wa. 7:9) Hanyar da Nassi ta tsara ta magance matsalar da ke tsakanin mu da wani ita ce, ka tattauna da shi cikin natsuwa da kuma gaskiya. Muna tsammanin cewa Jehobah zai albarkace mu ne idan muka riƙe mutum a zuciya, kuma muka ƙi zuwa mu tattauna da mutumin da muke ganin ya yi mana laifi?
A wani ɓangare kuma, menene za mu yi idan ɗan’uwanmu Kirista ya zo ya gaya mana cewa mun yi masa laifi, ko da hakan ba gaskiya ba ce? “Mayarda magana da taushi ya kan juyadda hasala,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Mis. 15:1) Ƙabilun Isra’ilawan da ake ganin cewa sun yi laifi sun bayyana matsayinsu sarai kuma cikin natsuwa, kuma hakan ya sasanta matsalar da ke tsakaninsu da ’yan’uwansu. Ko da mu ne muka fara zuwa wajen ɗan’uwanmu ko kuwa shi ne ya soma zuwa ya gaya mana game da wata matsala, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Waɗanne irin kalamai, murya, da hali ne za su iya ɗaukaka salama?’
Ka Yi Amfani da Harshe da Kyau
Jehobah ya san cewa muna bukatar mu faɗi yadda muke ji. Idan muka ƙi daidaita matsalar da ke tsakanin mu da wasu, muna iya soma gaya wa wasu batun. Riƙe mutum a zuci na iya kai ga baƙar magana. Game da yin amfani da harshe yadda bai dace ba, Misalai 11:11 ta ce: “Ta bakin miyagu a kan kaɓanta [birni].” Hakazalika, yin maganar banza game da ɗan’uwa Kirista zai iya shafan salamar ikilisiya mai kama da birni.
Biɗar salama ba ta nufin cewa ba za mu yi magana ba sam game da ’yan’uwa maza da mata ba. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa masu bi: “Kada kowanne ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku.” Ya kuma daɗa: “Sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda a ke bukata, domin shi bada alheri ga waɗanda su ke ji. . . . Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku.” (Afis. 4:29-32) Idan wani ɗan’uwa ya zo ya same ka ya gaya maka cewa bai ji daɗin abin da ka ce ko abin da ka yi ba, zai yi maka sauƙi ka ba shi haƙuri kuma ku yi sulhu idan bai taɓa faɗin abin da bai dace ba game da kai ga wasu, ko ba haka ba? Saboda haka, yin amfani da furcin da ke ƙarfafawa sa’ad da muke tattaunawa game da ’yan’uwanmu Kiristoci zai sa yin sulhu ya yi sauƙi sa’ad da matsaloli suka taso.—Luk 6:31.
Mu Bauta wa Allah da “Zuciya Ɗaya”
Halin mu mutane ajizai shi ne mu janye daga waɗanda suka yi mana laifi, ta wajen ware kanmu. Amma hakan wawanci ne. (Mis. 18:1) A matsayin mutane masu haɗin kai da suke kiran sunan Jehobah, mun ƙudurta “bauta masa da zuciya ɗaya.”—Zeph. 3:9.
Kada mu taɓa barin maganar banza ko hali marar kyau na wasu ya raunana ƙwazon da muke da shi a bauta ta gaskiya. ’Yan kwanaki kafin hadayar Yesu ta sauya hadayun da ake yi a haikali, kuma ba da daɗewa ba da Yesu ya yi wa marubutan horo, ya ga wata gwauruwa matalauciya ta zuba “dukan iyakar abin zaman gari da ta ke da shi” cikin baitulmalin haikalin. Yesu bai hana ta yin hakan ba. Maimakon haka, ya yi furci mai kyau game da tallafin da ta ba ikilisiyar Jehobah a wannan lokacin. (Luk 21:1-4) Rashin amincin wasu bai hana ta cika hakkinta na tallafa wa bautar Jehobah ba.
Ko da yake muna iya ganin cewa ɗan’uwa ko ’yar’uwa Kirista ya ko ta yi wani abin da bai dace, ko kuwa ya ko ta ƙi nuna adalci, me za mu yi? Za mu ƙyale hakan ya shafi bautar da muke yi wa Jehobah da dukan zuciyarmu ne? Ko kuwa da gaba gaɗi za mu ɗauki mataki mu daidaita duk wata matsala don mu kāre salama mai tamani ta ikilisiyar Allah a yau?
Nassosi ya ba mu wannan shawarar: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” (Rom. 12:18) Bari mu kudurta yin hakan don mu ci gaba da kasancewa a kan hanyar rai.
[Hasiya]
a Game da shawarar Yesu da ke rubuce a Matta 18:15-17, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1999, shafuffuka na 15-19
[Hoto a shafi na 17]
Afodiya da Sintiki suna bukatar su biɗi salama
[Hoto a shafi na 18]
Waɗanne irin kalamai, murya, da hali ne za su iya kawo salama?