Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 7/1 pp. 10-15
  • Ka Yi Koyi Da Jehovah, Allahnmu Da Ba Ya Tara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi Da Jehovah, Allahnmu Da Ba Ya Tara
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Aka Aikata ga Sunan Jehovah
  • Yadda Jehovah Ya Bi da Ibrahim da Isra’ila
  • Yesu, Malami da ba Ya Tara
  • Sakamako Mai Kyau
  • Shan Kan Wariya
  • Ka ‘Buɗe Zuciyarka’
  • Joshua da Gibeyonawa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Darussa Daga Littafin Joshuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Mutanen Isra’ila Sun Shiga Ka’anan
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Maganar Jehobah Tana Cika A Kullayaumi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 7/1 pp. 10-15

Ka Yi Koyi Da Jehovah, Allahnmu Da Ba Ya Tara

“A wurin Allah babu tara.”—ROMAWA 2:11.

1, 2. (a) Menene nufin Jehovah game da Kan’aniyawa gabaki ɗaya? (b) Menene Jehovah ya yi, kuma waɗanne tambayoyi wannan ya ta da?

DA SUKA kafa sansani a Filayen Mowab a 1473 K.Z., Isra’ilawa sun saurari Musa sosai. Yanayi mai wuya na jiran Isra’ila gaba da Kogin Urdun. Musa ya sanar da ƙudurin Jehovah cewa Isra’ila za ta ci manyan al’ummai bakwai na Kan’ana a Ƙasar Alkawari. Kalmomin Musa suna da ban ƙarfafa: “Ubangiji Allahnka ya bada su a gabanka, ka kuwa buge su; sai ka halaka su sarai”! Isra’ila ba za ta yi alkawari da su ba, ba su cancanci alheri ba.—Kubawar Shari’a 1:1; 7:1, 2.

2 Duk da haka, Jehovah ya ceci iyali ɗaya daga birni na farko da Isra’ila ta kai musu farmaki. Mutane daga wasu garuruwa huɗu sun samu kāriyar Allah. Me ya sa? Menene aukuwa na ban mamaki da ke haɗe da ceton waɗannan Kan’aniyawa ya koya mana game da Jehovah? Kuma yaya za mu yi koyi da shi?

Yadda Aka Aikata ga Sunan Jehovah

3, 4. Yaya labaran nasara da Isra’ilawa suka ci ya shafi wasu mutane a Ka’ana?

3 Lokacin da Isra’ila take cikin jeji shekara 40 kafin su shiga Ƙasar Alkawari, Jehovah ya kāre kuma yi fāɗa domin mutanensa. A ta kudu na Ƙasar Alkawari, Isra’ila ta fuskanci sarki Bakan’ana na Arad. Da taimakon Jehovah Isra’ilawa suka ci shi da mutanensa a Hormah. (Litafin Lissafi 21:1-3) Bayan haka, Isra’ila ta bi ta gefen ƙasar Edom kuma yi tafiya ta arewa zuwa arewa maso gabas na Tekun Gishiri. A wannan wurin, da Mowab take dā, Amoriyawa ne suke wajen yanzu. Sarki Ba’amori Sihon ya ƙi Isra’ilawa su wuce ta yankinsa. Suka yi yaƙi a Jahaz, a arewa ta Kwarin Ruwan Arnon, inda aka kashe Sihon. (Litafin Lissafi 21:23, 24; Kubawar Shari’a 2:30-33) Can arewa da nisa, sarki Og yana sarauta bisa Amoriyawa a Bashan. Ko da Og gwarzo ne, bai iya kāre kansa daga Jehovah ba. Aka kashe Og a Edrei. (Litafin Lissafi 21:33-35; Kubawar Shari’a 3:1-3, 11) Labaran wannan nasara har da tarihin Fitowar Isra’ila daga Masar ya shafi mutane da ke zama a Kan’ana sosai.a

4 Sa’ad da Isra’ila ta shiga Kan’ana da farko bayan sun ketare Urdun, sun kafa sansani a Gilgal. (Joshua 4:9-19) Bangon birnin Jericho ba shi da nisa daga wurin. Abin da Rahab Bakan’aniya ta ji game da ayyukan Jehovah ya motsa ta ta aikata cikin bangaskiya. Domin haka, sa’ad da Jehovah yake halaka Jericho, ya cece ta da waɗanda suke cikin gidanta.—Joshua 2:1-13; 6:17, 18; Yaƙub 2:25.

5. Me ya motsa Gibiyonawa suka aikata da hikima?

5 Sai Isra’ila ta haura zuwa tuddai na musamman a yanki na ƙasa-ƙasa kusa da kogin. Ta bin ja-gorar Jehovah, Joshua ya yi amfani da dabarun kwanto a kan birnin Ai. (Joshua, sura 8) Labaran nasarar yaƙi da aka ci ya sa sarakunan Kan’ana da yawa su taru don yaƙi. (Joshua 9:1, 2) Mazaunan birnin Bahibi na Gibiyon da ke kusa sun aikata dabam. “Suka yi dabara da hila,” in ji Joshua 9:4. Kamar Rahab, sun ji labarin cewa Jehovah ya ceci mutanensa a Fitowa kuma a halaka Sihon da Og. (Joshua 9:6-10) Gibiyonawa sun fahimci cewa yin tsayayya wauta ce. Saboda haka, domin Gibiyon da garuruwa uku kusa da su—Chephirah, Beeroth, da Kiriath-jearim—suka aika wa Joshua a Gilgal mutane da suka canja kama da cewa sun zo daga ƙasa mai nisa. Dabararsu ta yi nasara. Joshua ya ɗaura alkawari da su da ya sa suka tsira. Kwana uku bayan haka Joshua da Isra’ilawa suka san cewa an ruɗe su. Amma, sun yi rantsuwa da Jehovah su riƙe alkawarin kuma su manne masa. (Joshua 9:16-19) Jehovah ya amince da shi ne?

6. Menene Jehovah ya yi game da alkawari da Joshua ya yi da Gibiyonawa?

6 An ƙyale Gibiyonawa su zama matsaran itace da masu ɗaukan ruwa wa Isra’ilawa, har da “na bagadin Ubangiji” a mazauni. (Joshua 9:21-27) Ban da haka, sa’ad da sarakunan Amoriyawa da rundunansu suka yi wa Gibiyonawa barazana, ta mu’ujiza Jehovah ya saka hannu. Ƙanƙarar duwatsu ta kashe magabtan da yawa fiye da waɗanda sojojin Joshua suka kashe. Jehovah ya amsa roƙon da Joshua ya yi cewa rana da wata su tsaya cik don su gama cin nasarar abokan gābansu. “Ba a taɓa yini kamar wannan ba, ko gabansa, ko bayansa,” in ji Joshua, “har da za a ce Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra’ila.”—Joshua 10:1-14.

7. Wace gaskiya da Bitrus ya amince da ita aka nuna a batun wasu Kan’aniyawa?

7 Rahab Bakan’aniya da iyalinta, da kuma Gibiyonawa, sun ji tsoron Jehovah kuma aikata daidai. Abin da ya faru musu ya nuna gaskiya da Kirista manzo Bitrus ya faɗa daga baya: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.”—Ayukan Manzanni 10:34, 35.

Yadda Jehovah Ya Bi da Ibrahim da Isra’ila

8, 9. Ta yaya Jehovah ya nuna cewa ba ya tara a sha’aninsa da Ibrahim da al’ummar Isra’ila?

8 Almajiri Yaƙub ya jawo hankali ga alherin Allah a sha’aninsa da Ibrahim da ’ya’yansa. Bangaskiyar Ibrahim ne, ba inda ya fito ba, ya sa ya zama “abokin Allah.” (Yaƙub 2:23) Bangaskiyar Ibrahim da ƙauna ga Jehovah ya kawo wa zuriyarsa albarka. (2 Labarbaru 20:7) Jehovah ya yi wa Ibrahim alkawari: “Zan albarkace ka; wajen daɗuwa, zan riɓanɓanya tsatsonka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” Amma ka lura da alkawari da ke aya ta gaba: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.”—Farawa 22:17, 18; Romawa 4:1-8.

9 Ba tare da yin tara ba, Jehovah ya nuna ta sha’aninsa da Isra’ila abin da zai yi wa waɗanda suke masa biyayya. Irin wannan sha’ani misali ne na yadda Jehovah yake ƙaunar bayinsa masu aminci. Ko da Isra’ila “keɓaɓiyar taska” ce ga Jehovah, wannan ba ya nufin cewa an cire sauran mutane daga samun alherin Allah. (Fitowa 19:5; Kubawar Shari’a 7:6-8) Hakika, Jehovah ya sake fansar Isra’ila daga bauta a Masar kuma ya sanar: “Ku kaɗai na sani daga cikin dukan dangogin duniya.” Amma ta bakin annabi Amos da wasu, Jehovah kuma ya yi alkawarin bege mai ban al’ajabi ga mutanen “dukan al’ummai.”—Amos 3:2; 9:11, 12; Ishaya 2:2-4.

Yesu, Malami da ba Ya Tara

10. Ta yaya Yesu ya yi koyi da Ubansa da ba ya tara?

10 A lokacin hidimarsa a duniya, Yesu wanda shi ne ainihin kamanin Ubansa, ya yi koyi da Jehovah wanda ba ya tara. (Ibraniyawa 1:3) Damuwarsa ta farko a lokacin shi ne ya nemi “ɓatattun tumaki na gidan Isra’ila.” Duk da haka, bai ƙi yi wa mata Basamariya wa’azi a rijiya ba. (Matta 15:24; Yohanna 4:7-30) Ya kuma yi mu’ujiza sa’ad da wani soja, da ba daga Yahuda ba ya nemi taimakonsa. (Luka 7:1-10) Waɗannan domin ya daɗa nuna ta wurin ayyukansa ne yadda yake ƙaunar mutanen Allah. Almajiran Yesu sun yi wa’azi a ko’ina su ma. Ya zama a bayyane cewa matakin samun albarkar Jehovah ba daga inda mutum ya fito ba ne, amma ta halinsa ne. Mutane masu tawali’u da zuciyar kirki da suke son gaskiya sun yi na’am da bisharar Mulki. Dabam da haka, mutane masu fahariya da girman kai sun rena Yesu da saƙonsa. “Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa,” in ji Yesu, “da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai: i, ya Uba; gama hakanan ya gamshe ka sarai.” (Luka 10:21) Sa’ad da muka bi da wasu bisa ƙauna da bangaskiya, ba ma tara, da sanin cewa wannan hanya ce da Jehovah ya amince da ita.

11. Ta yaya ba a yi tara ba cikin ikilisiyar Kirista na farko?

11 A ikilisiyar Kirista ta farko, Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba daidai suke. Bulus ya yi bayani: “Ɗaukaka da girma da salama ga dukan wanda ya ke aika nagarta, dafari ga Bayahudi, kāna Baheleni: gama a wurin Allah babu tara.”b (Romawa 2:10, 11) Abin da ya nuna ko sun amfana daga alherin Jehovah, ba inda suka fito ba amma yadda suka aikata sa’ad da suka koya game da Jehovah da bege cikin fansa da Ɗansa, Yesu ya bayar. (Yohanna 3:16, 36) Bulus ya rubuta: “Ba shi ne Bayahudi ba, wanda shi ke Bayahudi a jiki; ba kuwa ita ce kaciya ba, wadda ke cikin jiki a waje: amma wanda ke Bayahudi a zuciya, shi ne Ba-yahudi; kaciya kuwa ta zuciya ce, cikin ruhu, ba cikin haruffa ba.” Ta yin amfani da kalmomi da sun ƙunshi kalmar nan “Bayahudi” (da ke nufin “na Yahuda,” watau, wanda aka yaba wa), Bulus ya daɗa: “Wanda yabonsa daga Allah ne, ba daga mutane ba.” (Romawa 2:28, 29) Jehovah yana yabo ba tare da tara ba. Muna haka ne?

12. Ru’ya ta Yohanna 7:9 ya ba da wane bege, kuma ga su waye?

12 Daga baya, cikin wahayi, manzo Yohanna ya ga Kiristoci shafaffu masu aminci da aka nuna su al’umma na 144,000 ta ruhaniya, “hatimtattu ne daga cikin kowacce kabila ta ’ya’yan Isra’ila.” Bayan wannan, Yohanna ya ga “taro mai-girma, . . . daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna, suna tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon, suna yafe da fararen riguna, da ganyayen dabino cikin hannuwansu.” (Ru’ya ta Yohanna 7:4, 9) Saboda haka, ba ƙabila ko kuma yare da aka ware daga ikilisiyar Kirista na zamani ba. Mutane daga dukan wurare suna da begen tsira wa “babban tsananin” mai zuwa su sha daga “maɓulɓulan ruwaye na rai” cikin sabuwar duniya.—Ru’ya ta Yohanna 7:14-17.

Sakamako Mai Kyau

13-15. (a) Ta yaya za mu sha kan bambanci na ƙabila da na al’ada? (b) Ka ambata misalai da ke nuna amfanin abokantaka.

13 Jehovah ya san mu da kyau, yadda uba nagari ya san yaransa. Haka nan ma, sa’ad da muka fahimta wasu ta wurin nuna muna son al’adarsu ko inda suka fito, bambanci ba zai kasance da muhimmanci ba. Ba za a samu wariya ba, sai a ƙarfafa gami na abuta da ƙauna. A kyautata haɗin kai. (1 Korinthiyawa 9:19-23) Ana ganin wannan sosai ta ayyukan masu wa’azi a ƙasashen waje, da suke hidima a wata ƙasa. Suna damuwa da mutanen da suke zama a yankin, ta haka, ba da daɗewa ba masu wa’azi a ƙasashen waje sai su soma cuɗanya da mutanen ikilisiyar.—Filibbiyawa 2:4.

14 Ana ganin sakamako mai kyau na rashin tara a ƙasashe da yawa. Aklilu, wanda ya fito daga Habasha, ya kaɗaita a London babban birnin Britaniya. Kaɗaicinsa ya ƙaru da abin da a gare shi rashin abuta ne wurin mutane daga wasu ƙasashe, abu da ake gani a manyan biranen Turai na zamani. Abin da Aklilu ya gani dabam yake sa’ad da ya halarci taron Kirista a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah! Sun yi masa maraba, ba da daɗewa ba ya ji kamar yana gida. Ya samu ci gaba da hanzari a zurfafa godiyarsa ga Mahalicci. Ba da daɗewa ba ya nemi zarafin sa hannu a yaɗa bisharar Mulki ga wasu a gundumar. Hakika wata rana, wanda suke tafiyar wa’azi tare da Aklilu ya tambaye shi maƙasudinsa yanzu a rayuwa, Aklilu ya ce yana fatan wata rana ya kasance cikin ikilisiya da ake yarensa, Amharic. Sa’ad da dattawa na ikilisiya da ake Turanci suka ji haka, suka shirya jawabin Littafi Mai Tsarki ga jama’a a yaren Aklilu. Gayyatar su halarta ya kawo baƙi daga wasu ƙasashe da kuma mutane daga yankin tare su tallafa wa taro na farko na yaren Amharic a Britaniya. Yau, Habashawa da wasu a wannan wajen suna da haɗin kai a cikin ikilisiya mai ci gaba. Mutane da yawa a wajen sun iske cewa babu abin da zai hana su bauta wa Jehovah kuma suka nuna wannan ta yin baftisma ta Kirista.—Ayukan Manzanni 8:26-36.

15 Halaye da inda mutane suka fito sun bambanta. Ba domin a nuna an fi wasu ba, ko kuma ba a kai wasu ba, kawai dai bambanci ne. Sa’ad da suke kallon baftisma na sababbin bayin Jehovah da suka keɓe kansu a tsibirin Malita, Shaidun cikin farin ciki sun tallafa wa hawayen farin ciki da ya cika idanun baƙi daga Britaniya. Dukan rukunin Malita da Britaniya sun nuna yadda suka ji amma a hanyoyi dabam dabam, kuma ƙaunarsu mai ƙarfi ga Jehovah ta liƙe gami na abuta na Kirista.—Zabura 133:1; Kolossiyawa 3:14.

Shan Kan Wariya

16-18. Ka ba da labari da ya nuna yadda za a sha kan wariya cikin ikilisiyar Kirista.

16 Yayin da ƙaunarmu ga Jehovah da ’yan’uwa Kirista ta zurfafa, za mu fi yin koyi da Jehovah a hanyar da muke ɗaukan wasu. Za mu iya sha kan kowacce wariya da muke da shi dā game da wasu ƙasashe, ƙabilu, ko kuma al’adu. Yi la’akari da misalin Albert, da ya yi aikin Soja a Britaniya lokacin Yaƙin Duniya na ll kuma ’yan Japan suka kama shi lokacin da aka ci Singapore a shekara ta 1942. Ya yi shekara uku yana aiki a inda ake kira “hanyar jirgi na mutuwa,” kusa da inda daga baya aka kira gadan kogin Kwai. Da aka sake shi a ƙarshen yaƙin, ya rame har nauyinsa ya yi awo 32 kawai, ƙashin muƙamuƙi da na hanci sun karye, ya yi ciwon atini, makero, da zazzaɓi. Yanayin waɗanda suke kurkuku tare da shi ya fi muni; mutane da yawa sun mutu. Domin wahala da Albert ya sha kuma fuskanta, ya koma gida a shekara ta 1945 mutum mai baƙin ciki, ba ya son abin da zai shafe shi da Allah ko addini.

17 Matar Albert, Irene, ta zama Mashaidiyar Jehovah. Don ya gamsar da ita, Albert ya ɗan halarci taro na ikilisiyar Shaidun Jehovah. Wani saurayi Kirista da yake hidima ta cikakken lokaci da ake kira Paul ya ziyarci Albert ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ba da daɗewa ba Albert ya fahimta cewa Jehovah yana duba mutane bisa yanayin zuciyarsu. Ya keɓe kansa ga Jehovah kuma ya yi baftisma.

18 Daga baya Paul ya kaura zuwa London, ya koyi Japanisanci, kuma yana cikin ikilisiyar da ake Japanisanci. Sa’ad da ya ce zai ziyarci ikilisiyarsa ta dā da wasu Shaidu daga Japan, ’yan’uwan suka tuna da yadda Albert ba ya son mutane da suka fito daga wurin. Tun lokacin da ya koma Britaniya, Albert ba ya son saduwa da ko waye daga Japan, shi ya sa ’yan’uwan suka damu yadda zai bi da yanayin. Bai kamata su damu ba—Albert ya karɓi baƙin da ƙauna ta ’yan’uwanci marar iyaka.—1 Bitrus 3:8, 9.

Ka ‘Buɗe Zuciyarka’

19. Wace shawara na manzo Bulus zai taimake mu idan muna da halin yin tara?

19 “Ba ya yi kyau a yi tara ba,” in ji Sarki Sulemanu mai hikima. (Misalai 28:21) Yana da sauƙi mu matsa kusa ga waɗanda muka san su da kyau. Amma, wani lokaci ba ma son waɗanda ba mu san su ba sosai. Irin wannan wariya bai dace ba da bawan Jehovah. Babu shakka, zai yi kyau mu bi shawarar Bulus da ke a bayyane “ku buɗe zuciyarku”—hakika mu buɗe zuciya ta ƙaunar ’yan’uwa Kiristoci daga wurare dabam dabam.—2 Korinthiyawa 6:13.

20. A waɗanne fasalolin rayuwa ya kamata mu yi koyi da Jehovah, Allahnmu da ba ya tara?

20 Ko muna da gatar zuwa sama ko begen rayuwa har abada a duniya, idan ba ma tara zai taimake mu mu more haɗin kai na garke ɗaya, Makiyayi ɗaya. (Afisawa 4:4, 5, 16) Ƙoƙarinmu mu yi koyi da Jehovah, Allahnmu da ba ya tara, zai taimake mu a hidimar Kirista, cikin iyalinmu, da kuma cikin ikilisiya, hakika, a dukan ɓangarorin rayuwa. Ta yaya? Talifi na gaba zai bincika wannan batun.

[Hasiya]

a Sunan Jehovah daga baya ya zama jigon waƙoƙi masu tsarki.—Zabura 135:8-11; 136:11-20.

b A nan, furci “Baheleni” na nuni ga mutanen Al’umma gabaki ɗaya.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Jehovah ya nuna ba ya tara a batun Rahab da Gibiyonawa?

• Ta yaya Yesu ya nuna ba ya tara a koyarwarsa?

• Menene zai taimake mu mu sha kan wariya na al’ada da na ƙabila?

[Hoto a shafi na 11]

Cin nasarar Isra’ila bisa Kan’ana ta soma

[Hoto a shafi na 13]

Yesu bai ƙi yi wa mace Basamariya wa’azi ba

[Hoto a shafi na 14]

Taro ga jama’a a yaren Amharic a Britaniya

[Hoto a shafi na 14]

Ƙaunar Albert ga Jehovah ta taimake shi ya sha kan wariya

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba