‘Umarnanka Su Ne Annishu’ata’
“Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu.”—ROMAWA 15:4.
1. Ta yaya Jehobah yake ba mu umurni, kuma me ya sa muke bukatarsa?
JEHOBAH yana ba mutanensa umurni domin ya taimake su su jimre wa matsi na wannan zamani mai wuya. Ana samun wannan umurni sa’ad da aka karanta Littafi Mai Tsarki, wasu kuma ta bayani ko kuma kalami a taron Kirista. Mun riga mun san yawancin abin da muka karanta ko kuma muka ji a waɗannan taron. Wataƙila, mun tattauna irin wannan bayani a dā. Tun da yake muna iya mantuwa, muna bukatar mu ci gaba da tuna wa kanmu ƙudurin Jehobah, dokokinsa, da umurninsa. Ya kamata mu yi godiya don tunasarwar Allah. Suna ƙarfafa mu ta taimakonmu mu mai da hankali ga abin da ya motsa mu mu zaɓi bin tafarki na ibada. Shi ya sa mai zabura ya rera wa Jehobah waƙa cewa: ‘umarnanka su ne annishu’ata.’—Zabura 119:24.
2, 3. (a) Me ya sa Jehobah ya adana tarihin mutane a cikin Littafi Mai Tsarki har zuwa zamaninmu? (b) Waɗanne tarihi ne na Nassosi za a bincika a wannan talifin?
2 Ko an rubuta Kalmar Allah ƙarnuka da yawa da ta shige, har ila tana da iko. (Ibraniyawa 4:12) Ta ba mu tarihin mutane a cikin Littafi Mai Tsarki. Ko da al’adu da ra’ayi sun canja tun lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, matsaloli da muke fuskanta sau da yawa sun yi daidai da waɗanda suka faru a lokacin. Tarihi da yawa da aka adana don amfaninmu a cikin Littafi Mai Tsarki sun ba da misalai masu daɗaɗa rai na mutane da suka ƙaunaci Jehobah kuma suka bauta masa da aminci duk da yanayi mai wuya. Wasu tarihin sun nuna mana irin halin da Allah ba ya so. Jehobah ya adana waɗannan tarihi na mutane masu kirki da miyagu a cikin Littafi Mai Tsarki don tunasarwa. Kamar yadda manzo Bulus ya rubuta ne: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyyar littattafai mu zama da bege.”—Romawa 15:4.
3 Bari mu mai da hankali ga wasu tarihi uku a cikin Nassosi: tarihin yadda Dauda ya bi da Saul, na Hananiya da Safiratu, da na Yusufu da matar Fotifar. Kowane cikin waɗannan tarihin sun koya mana darassi mai kyau.
Aminci ga Tsarin Allah
4, 5. (a) Wane yanayi ne ya kasance tsakanin Sarki Saul da Dauda? (b) Yaya Dauda ya aikata ga ƙiyayyar Saul?
4 Sarki Saul ya yi wa Jehobah rashin aminci kuma bai cancanci ya yi sarauta bisa mutanen Jehobah ba. Saboda haka, Allah ya ƙi shi kuma ya ja-goranci annabi Sama’ila ya naɗa Dauda sarkin Isra’ila na gaba. Sa’ad da Dauda ya nuna shi jarumi ne kuma mutanen suka yaba masa, Saul ya soma gāba da Dauda. A kai a kai Saul ya yi ƙoƙari ya kashe shi. Dauda ya tsira domin Jehobah yana tare da shi.—1 Samuila 18:6-12, 25; 19:10, 11.
5 An tilasta wa Dauda rayuwar gudun hijira na shekaru da yawa. Sa’ad da ya sami zarafin ya kashe Saul, abokan Dauda sun aririce shi ya yi hakan, sun gaya masa cewa Jehobah ne ya ba shi abokin gabansa cikin hannunsa. Duk da haka, Dauda ya ƙi. Amincinsa ga Jehobah da kuma darajar matsayin Saul na sarkin mutanen Allah da aka naɗa ya motsa shi ya ƙi aikata hakan. Jehobah ne ya naɗa Saul sarkin Isra’ila, ko ba haka ba ne? Jehobah zai cire shi sa’ad da ya ga ya dace ya yi hakan. Dauda ya ga cewa bai kamata ya sa hannu ba. Bayan ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya rage ƙiyayyar Saul a gare shi, Dauda ya ce: “Ubangiji za ya buga shi: ko kuwa ranar mutuwatasa za ta zo: ko kuwa ya tafi yaƙi ya hallaka. Ubangiji ya sawaƙa in miƙa hannuna a kan shafaffe na Ubangiji.”—1 Samuila 24:3-15; 26:7-20.
6. Me ya sa yake da muhimmanci mu bincika labarin Dauda da Saul?
6 Wannan tarihin yana ɗauke da darassi mai muhimmanci. Ka taɓa iske kanka kana mamakin abin da ya sa wasu matsaloli suke tasowa a cikin ikilisiyar Kirista? Mai yiwuwa wani yana aikata abin da bai dace ba. Abin da yake yi ba laifi mai tsanani ba ne, amma yana damunka. Yaya ya kamata ka aikata? Domin ka damu da ɗan’uwanka kuma kana son ka nuna aminci ga Jehobah, kana iya yi wa mutumin magana a hanya mai kyau don ku magance matsalar. Idan matsalar ta ci gaba fa? Bayan ka yi iyakar ƙoƙarinka, ka bar batun a hannun Jehobah. Abin da Dauda ya yi kenan.
7. Ta koyi da Dauda, yaya ya kamata mu aikata idan mun fuskanci rashin adalci ko kuma wariya?
7 Wataƙila kana fuskantar matsalar rashin adalci ko kuma wariya ta addini. Mai yiwuwa ba abin da za ka iya yi game da matsalar a yanzu. Irin wannan yanayin yana da wuyar jimrewa, amma yadda Dauda ya aikata ga rashin adalci ya koya mana wani darassi. Zabura da Dauda ya rubuta labari ne mai ban tausayi na addu’a da ya yi ga Allah da dukan zuciyarsa don Allah ya tsare shi daga hannun Saul da kuma amincinsa ga Jehobah da kuma yadda ya damu da tsarkakewar sunan Allah. (Zabura 18:1-6, 25-27, 30-32, 48-50; 57:1-11) Dauda ya kasance da aminci ga Jehobah ko da yake Saul ya ci gaba da aikata rashin adalci a gare shi na shekaru da yawa. Ya kamata mu ma mu kasance da aminci ga Jehobah da ƙungiyarsa kowane irin rashin adalci muke fuskanta kuma ko da menene wasu suke yi. Mu tabbata cewa Jehobah ya san abin da yake faruwa.—Zabura 86:2.
8. Yaya Shaidun Jehobah a ƙasar Mazambik suka aikata sa’ad da aka gwada amincinsu ga Jehobah?
8 Kiristoci a ƙasar Mazambik misalai ne na mutane a zamani da suka manne wa Jehobah cikin aminci a lokacin gwaji. A shekara ta 1984, ƙungiyar ’yan tawaye masu ɗauke da makamai, suka yi ta zuwa suna yi masu fashi a ƙauyuka, suna ƙona gidaje, da kuma kashe mutane. Ba abin da waɗannan Kiristoci na gaskiya za su iya yi don su kāre kansu. An matsa ma mazaunan wurin su shiga rukunin ’yan tawayen ko kuma an tilasta musu su tallafa a wasu hanyoyi. Shaidun Jehobah sun ɗauki yin hakan bai jitu da matsayinsu na tsaka tsaki na Kirista ba. Ƙi da suka yi ya fusata rukunin sosai. An kashe wajen Shaidu 30 a wannan lokaci na wahala, amma har barazanar kisa bai karya amincin mutanen Allah ba.a Kamar Dauda, sun jimre rashin adalci amma daga baya sun yi nasara.
Misali na Gargaɗi
9, 10. (a) Ta yaya za mu amfana daga wasu misalan Nassosi? (b) Me ya sa abin da Hananiya da Safiratu suka yi ba shi da kyau?
9 Wasu mutane da aka ambata cikin Nassosi tunasarwa ne game da hali da za a guje wa. Hakika, da akwai labaran mutane da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, har a cikin bayin Allah, da suka yi abin da ba shi da kyau kuma suka sha wahalar sakamakon haka. (1 Korinthiyawa 10:11) Muna da labarin Hananiya da Safiratu, mata da miji da suke cikin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko a Urushalima.
10 Bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an sami bukatar kula da sababbi masu bi da suka kasance a Urushalima don su amfana ta wajen yin tarayya da manzannin. Wasu cikin ikilisiyar sun sayar da kayakinsu domin su tabbata cewa babu wanda yake cikin bukata. (Ayukan Manzanni 2:41-45) Hananiya da Safiratu suka sayar da fili kuma suka ba manzannin ɓarin kuɗin, suna da’awa cewa dukan kuɗin da suka sayar ke nan. Hakika, ba a gaya wa Hananiya da Safiratu ainihin nawa za su bayar ba, amma muradinsu ba shi da kyau kuma ayyukansu na rashin gaskiya ne. Suna so su burge mutane su nuna cewa abin da suka yi yana da yawa ko da yake bai kai yawan abin da suka nuna ba. Da taimakon ruhu mai tsarki manzo Bitrus ya tona asirin rashin gaskiyarsu da riyarsu, kuma Jehobah ya kashe su.—Ayukan Manzanni 5:1-10.
11, 12. (a) Ka ba da wasu misalai game da yin gaskiya. (b) Waɗanne sakamako ake samu don yin gaskiya?
11 Idan aka jarabe mu mu yi ƙarya don mu sa mutane su ce mu masu kirki ne, bari labarin Hananiya da Safiratu ya kasance gargaɗi. Muna iya ruɗin mutane, amma ba za mu iya yaudarar Jehobah ba. (Ibraniyawa 4:13) Nassosi sun yi mana gargaɗi a kai a kai mu riƙa faɗa wa juna gaskiya, don maƙaryata ba za su kasance cikin duniya da aka kawar ta rashin adalci ba. (Misalai 14:2; Ru’ya ta Yohanna 21:8; 22:15) Dalilin wannan a bayane yake. Shaiɗan Iblis ne mai ɗaukaka dukan rashin gaskiya.—Yohanna 8:44.
12 Idan mun ci gaba da faɗan gaskiya a rayuwarmu za mu samu amfani masu yawa. Kasancewa da lamiri mai tsabta da gamsuwa cewa wasu za su amince da mu na cikin amfani da za mu samu. A misalai da yawa, Kiristoci sun sami aiki, ko kuma sun ci gaba da aikinsu, domin sun faɗi gaskiya. Amma, amfani mafi muhimmanci shi ne cewa yin gaskiya na sa mu zama abokan Allah maɗaukaki.—Zabura 15:1, 2.
Kasancewa da Tsabta ta Ɗabi’a
13. A wane yanayi ne Yusufu ya iske kansa, kuma me ya yi?
13 An sayar da Yusufu ɗan Yakubu uban iyali zuwa bauta sa’ad da yake ɗan shekara 17. Bayan haka ya soma zama a gidan Fotifar Bamasare ma’aikacin kotu, inda matar shugaban Yusufu ta sa idonta a kansa. Ta yi sha’awar jima’i da Yusufu, da yake saurayi ne kyakkyawa, kullum tana ce masa: “Ka kwana da ni.” Yusufu yana nesa da iyalinsa a ƙasar da babu wanda ya san shi. Zai iya kwana da wannan matar kuma mutane ba za su sani ba. Duk da haka, sa’ad da matar Fotifar ta kama shi, Yusufu ya gudu.—Farawa 37:2, 18-28; 39:1-12.
14, 15. (a) Me ya sa labarin Yusufu yake da muhimmanci a gare mu? (b) Me ya sa wata Kirista ta yi godiya don ta bi umurnin Allah?
14 An yi renon Yusufu a iyali mai jin tsoron Allah, kuma ya fahimci cewa ba daidai ba ne mutane da ba mata da miji ba ne su yi jima’i. Ya ce: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?” Mai yiwuwa ya kammala hakan domin ya san mizanin da Allah ya furta ga ’yan adam a Adnin, wato mutum ya auri mace guda. (Farawa 2:24) Mutanen Allah a yau za su amfana ta wajen bimbini a kan yadda Yusufu ya aikata a wannan yanayin. A wasu wurare, mutane suna jima’i yadda suka ga dama, matasa da suka ƙi yin lalata, tsaransu na musu ba’a. Zina ta zama ruwan dare game gari. Saboda haka, labarin Yusufu tunasarwa ne na kan ƙari a gare mu. Har ila, a mizanin Allah fasikanci da zina zunubi ne. (Ibraniyawa 13:4) Mutane da yawa da suka faɗa wa matsi na yin lalata sun yarda cewa da dalili mai kyau na ƙin yin haka. Sakamakon yin haka zai zama rashin mutunci, lamirin mutum zai riƙa damunsa, kishi, ɗaukan ciki, da cuta da ake ɗauka ta jima’i. Yadda Nassosi suka tuna mana, mutumin da ke fasikanci yana “yi ma jiki nasa zunubi.”—1 Korinthiyawa 5:9-12; 6:18; Misalai 6:23-29, 32.
15 Jenny,b Mashaidiyar Jehobah da ba ta yi aure ba, tana da dalilin yin godiya ga umurnin Allah. A wajen aiki, wani abokin aikinta kyakkyawa ya nuna yana sonta. Da Jenny ba ta kula da shi ba, sai ya daɗa kuzari wajen nuna soyayyarsa. Ta ce: “Na iske kaina ina fama in kasance da tsabta ta ɗabi’a, domin abin farin ciki ne idan na miji ya nuna yana sonki.” Duk da haka, ta fahimci cewa mutumin na ƙoƙari ya saka ta cikin adadin matan da ya yi jima’i da su. Sa’ad da ta ga tana sanyi a ƙudurinta na yin tsayayya da shi, sai ta yi wa Jehobah addu’a ya taimake ta ta kasance da aminci a gare shi. Jenny ta lura cewa abubuwa da ta koya sa’ad da ta yi bincike cikin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Kirista suna kama da abin motsawa da ke sa ta ta mai da hankali. Ɗaya cikin abubuwan da ta tuna shi ne labarin Yusufu da matar Fotifar. Ta kammala da cewa, “muddin na ci gaba da tuna wa kaina yadda nake ƙaunar Jehobah, ba na bukatar na ji tsoro cewa zan yi wannan mugunta mai girma, in yi zunubi ga Allah kuma.”
Ka Bi Umurnin Allah!
16. Ta yaya za mu amfana ta wurin maimaita da kuma bimbini a kan labarin rayuwar mutane da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki?
16 Za mu ƙara godiya ga mizanan Jehobah ta wajen yin ƙoƙari mu fahimci abin da ya sa ya adana wasu labaran Nassosi domin mu. Menene suka koyar? Waɗanne halaye da mutane cikin Littafi Mai Tsarki suka nuna ya kamata mu yi koyi da su ko kuma mu kauce musu? An rubuta game da mutane da yawa a cikin Kalmar Allah. Dukan waɗanda suke son koyarwa na Allah za su amfana ta wajen koyan hikima da ke ba da rai, har da darussa da za mu iya koya daga misalai da Jehobah ya adana. Sau da yawa, a wannan jaridar an fito da talifofi da sun yi magana game da irin waɗannan mutane da labaransu za su koya mana darasi. Ka ɗan ba da lokaci ka bincika su.
17. Yaya kake ji game da tunasarwar Jehobah, kuma me ya sa?
17 Za mu yi godiya ga yadda Jehobah ya nuna ya damu da waɗanda suke ƙoƙari su yi nufinsa! Mu ajizai ne kamar mata da maza da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki. Amma, tarihin ayyukansu suna da amfani sosai a gare mu. Ta wajen bin umurnin Jehobah, za mu kauce yin kuskure mai tsanani, kuma za mu yi koyi da misalai masu kyau na waɗanda suka bi hanyoyin adalci. Idan muka yi haka, za mu iya rera waƙa irin ta mai zabura: “Masu-albarka ne waɗannan da ke tsare shaidunsa [Jehobah], suna kuwa nemansa da dukan zuciya. Raina ya lura da shaidunka; ina ƙaunarsu kuma ƙwarai.”—Zabura 119:2, 167.
[Hasiya]
a Ka dubi 1996 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafofi na 160-162.
b An canja sunan.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Menene za mu koya daga halin Dauda game da Saul?
• Labarin Hananiya da Safiratu ya koya mana menene?
• Me ya sa labarin rayuwar Yusufu yake da muhimmanci a yau?
[Hoto a shafi na 14]
Me ya sa Dauda ya ƙi ƙyale a kashe Saul?
[Hoto a shafi na 15]
Menene muka koya daga labarin Hananiya da Safiratu?
[Hoto a shafi na 16]
Menene ya sa Yusufu ya ƙi lalata?