Ka Ɗokanta A Yin Shelar Bishara
“Kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta ma Ubangiji.”—ROMAWA 12:11.
1, 2. Wane hali ne Kiristoci suke ƙoƙarin kasance da shi su masu wa’azin bishara?
SAURAYI yakan yi marmarin sabon aikinsa sosai. A rana ta fari wajen aiki, zai riƙa alla-alla maigidansa ya gaya masa abubuwan da zai yi. Yana jiran aiki na farko, kuma zai yi aikin tare da himma sosai. Zai ɗokanta ya yi iyakacin ƙoƙarinsa.
2 Haka, mu Kiristoci ya kamata mu ɗauki kanmu, waɗanda suka fara sabon aiki. Tun da yake begenmu na rayuwa har abada ne, za a iya cewa yanzu muka fara aiki wajen Jehovah. Lallai Mahaliccinmu yana da ayyuka masu yawa dominmu, mu shagala ciki har abada. Amma aiki na farko da muka samu shi ne na yin shelar bisharar Mulkinsa. (1 Tassalunikawa 2:4) Yaya muke ji game da wannan aikin daga wajen Allah? Kamar saurayin, muna son mu cika shi wajen yin iyakar ƙoƙarinmu, da himma, da farin ciki—hakika, mu ɗokanta a yin haka!
3. Menene ake bukata don mai hidimar bishara ya yi nasara?
3 Gaskiya ne cewa riƙe irin wannan hali mai kyau yana da wuya. Ban da hidima da muke yi, muna da wasu nawayoyi da yawa, waɗanda ke iya gajiyar da mu a jiki da kuma a tunani. Yawanci dai, muna ƙoƙarin mu kula da waɗannan abubuwa yayin da muke mai da hankali ga hidimar. Duk da haka, yakan zama kokawa na yau da kullum. (Markus 8:34) Yesu ya nanata cewa yin nasararmu ta Kiristoci, yana bukatar fama ƙwarai.—Luka 13:24.
4. Ta yaya shagulgula na kullum za su shafi ra’ayinmu game da ruhaniya?
4 Da yake akwai abubuwan yi da yawa, da sauƙi yake abubuwa su sha kanmu ko kuma nawaita mu a wasu lokatai. “Shagulgula na wannan rai” za su iya shaƙe himmarmu da godiya ga ayyuka na tsarin Allah. (Luka 21:34, 35; Markus 4:18, 19) Saboda yanayinmu na ajizanci, muna iya barin ‘ƙauna da muke da shi da farko.’ (Ru’ya ta Yohanna 2:1-4) Yana yiwuwa wasu fasalolin hidimarmu ga Jehovah su zama abu na yau da kullum ne kawai. Yaya ne Littafi Mai-Tsarki ya tanadar mana da ƙarfafa da muke bukata don mu saka himmarmu don hidimar ta ci gaba?
Kamar “Wuta Mai-Ƙonewa” Cikin Zukatanmu
5, 6. Yaya ne manzo Bulus ya ɗauki gatarsa ta wa’azi?
5 Hidima da Jehovah ya ba mu amanarta, tana da tamani sosai ba wanda za mu sa ta zama banza ba ce. Manzo Bulus ya ɗauki wa’azin bishara gata ce mai girma sosai, kuma ya ga bai cancanta a ba shi amanarta ba. Ya ce: “Ni, wanda na zama koma bayan baya cikin tsarkaka duka, a gareni aka bada wannan alheri, in yi wa’azin wadatar Kristi wurin Al’ummai, wadata wadda ta fi ƙarfin a biɗa; domin kuma a gwada ma mutane duka ko menene wakilcin asirin da ke a ɓoye tun dukan zamanu cikin Allah wanda ya halitta abu duka.”—Afisawa 3:8, 9.
6 Hali mai kyau na Bulus game da hidima, misali mafi kyau ne garemu. A cikin wasiƙarsa zuwa ga Romawa, ya ce: “Gwargwadon ƙarfina, a shirye ni ke in yi wa’azin bishara.” Ba shi da kunyar bisharar. (Romawa 1:15, 16) Yana da hali da ya dace, ya ɗoki ya cika hidimarsa.
7. A cikin wasiƙarsa zuwa ga Romawa, menene Bulus ya yi kashedi a kai?
7 Manzo Bulus ya gane bukatar kasancewa da himma, saboda haka, ya yi wa Kiristoci na Roma kashedi: “Cikin ƙwazo kada ku yi ragonci; kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta ma Ubangiji.” (Romawa 12:11) Kalmar Helenanci da aka fassara “ragonci” yana da ma’anar “mai son jiki, maƙyuyaci.” Ko da yake ba ma ragonci cikin hidimarmu, mu duka muna bukatar mu kasance a farke ga wasu alamu na ƙyuya na ruhaniya, mu yi gyara kuma da ta dace cikin halayenmu idan muka ga irin alamun nan cikin halinmu.—Misalai 22:3.
8. (a) Menene ya zama kamar “wuta mai-ƙonewa” cikin zuciyar Irmiya, kuma me ya sa? (b) Wane darasi za mu iya koya daga abin da ya faru da Irmiya?
8 Ruhun Allah zai taimake mu lokacin da muka kasala. Alal misali, wani lokaci da annabi Irmiya ya kasala, ya yi tunanin daina aikinsa na annabci. Har ma ya ce game da Jehovah: “Ba ni ambatonsa, ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.” Wannan tabbacin ciwo mai tsanani na ruhaniya ne da ke cikin Irmiya? A’a. Hakika, ruhaniyar Irmiya mai ƙarfi ce, ƙaunarsa ga Jehovah, da kuma himmarsa don gaskiya sun ƙarfafa shi ya ci gaba da yin annabci. Ya bayyana cewa: “Cikin zuciyata in ji kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana, in gaji kuma da haƙuri, in kasa jimrewa.” (Irmiya 20:9) Ba baƙon abu ba ne bayin Allah masu aminci su yi kasala a wasu lokatai. Amma yayin da suka yi addu’a ga Jehovah don taimakonsa, yakan fahimci zukatansu kuma ya ba su ruhunsa mai-tsarki idan kamar Irmiya, suna da maganarsa cikin zukatansu.— Luka 11:9-13; Ayukan Manzanni 15:8.
‘Kada Ku Bice Maganar Ruhu Mai Tsarki’
9. Menene zai iya hana ayyukan ruhu mai-tsarki dominmu?
9 Manzo Bulus ya yi kashedi ga Tassalunikawa: ‘Kada ku bice maganar ruhu mai-tsarki.’ (1 Tassalunikawa 5:19) Hakika, ayyuka da halaye da suka saɓa da ƙa’idodin ibada sa iya hana ayyukan ruhu mai-tsarkin dominmu. (Afisawa 4:30) Kiristoci a yau suna da aikin wa’azin bishara. Muna ɗaukar wannan gatar da daraja sosai. A garemu ba abin mamaki ba ne cewa waɗanda ba su san Allah ba suna ɗaukan aikin wa’azi da muke yi da wulaƙanci. Amma yayin da Kirista da gangan ya yi banza da hidimarsa, zai iya zama yana bice ikon yin aiki na Allah.
10. (a) Yaya ra’ayin maƙwabcinmu zai iya rinjayarmu? (b) Wane ra’ayi mai daraja ne game da hidimarmu aka furta a 2 Korinthiyawa 2:17?
10 Wasu da ba sa cikin ikklisiyar Kirista za su iya ɗaukar hidimarmu cewa na ba da littattafai ne kawai. Wasu za su iya kammalawa cikin kuskure cewa muna zuwa gida zuwa gida don kawai mu karɓi kyauta ne. Idan mun yarda irin waɗannan ra’ayoyin sun shafi halayenmu, hakan zai iya rage ƙwazonmu cikin hidima. Maimakon yarda irin wannan tunanin su rinjaye mu, bari mu riƙe ra’ayin da Jehovah da Yesu suke da shi game da hidimarmu. Manzo Bulus ya furta ra’ayin nan mai daraja yayin da ya ce: “Gama ba mu ɓata maganar Allah kamar yawanci su ke yi ba: amma cikin sahihanci, daga wurin Allah, a gaban Allah kuma, muna magana cikin Kristi.”—2 Korinthiyawa 2:17.
11. Menene ya taimake Kiristoci na farko su riƙe himmarsu ko a cikin tsanani ma, kuma yaya ya kamata misalinsu ya shafe mu?
11 Ba da daɗewa ba bayan mutuwar Yesu, almajiransa cikin Urushalima suka fuskanci tsanantawa. Aka yi masu barazana kuma aka umurce su su daina wa’azi. Duk da haka, Littafi Mai-Tsarki ya ce “suka cika da Ruhu Mai-tsarki, suka faɗi maganar Allah da ƙarfinzuciya.” (Ayukan Manzanni 4:17, 21, 31) Kalmomin Bulus zuwa ga Timothawus wasu shekaru daga baya sun nuna wannan hali mai kyau da Kiristoci ya kamata su riƙe. Bulus ya ce: “Gama Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo. Kada fa ka ji kunyar shaidar Ubangijinmu, ko ni ɗaurarrensa: amma ka daure shan wuya tare da bishara bisa ga ikon Allah.”—2 Timothawus 1:7, 8.
Wane Nawaya Muke da Shi Wajen Maƙwabcinmu?
12. Menene dalili na musamman da ya sa muke wa’azin bishara?
12 Domin mu kasance da halin da ya dace wajen hidimarmu, tilas ne abin da yake motsa mu ya zama mai kyau. Me ya sa muke wa’azi? Dalili na musamman yana bayyane cikin kalmomin mai zabura: “Tsarkakanka kuma za su albarkace ka [Jehovah]. Za su yi zancen ɗaukakar mulkinka, su kama maganar ikonka: Domin a sanar ma ’yan Adam ayyukansa masu-iko da darajar ɗaukaka ta mulkinsa.” (Zabura 145:10-12) Hakika, muna wa’azi don mu yabi Jehovah a fili kuma domin mu tsarkake sunansa a gaban dukan mutane. Ko idan kalilan ne suka saurare mu, yin shelar saƙon ceto cikin aminci yana kawo wa Jehovah yabo.
13. Menene ke motsa mu mu gaya wa wasu begen ceto?
13 Muna wa’azi kuma domin ƙauna da muke yi wa mutane domin kuma mu guje wa alhakin jini. (Ezekiel 33:8; Markus 6:34) Mai kama da wannan shi ne kalmomin Bulus yayin da yake zancen waɗanda ba sa cikin ikklisiyar Kirista: “Ni mabarci ne ga Helenawa duk da Baibayi, ga masu hikima duk da marasa-hikima.” (Romawa 1:14) Bulus yana ji shi mabarci ne wajen mutane ya yi shelar bishara garesu, tun da yake nufin Allah ne cewa “dukan iri irin mutane su tsira.” (1 Timothawus 2:4, NW ) A yau, haka muke da ƙauna da jin mu mabarta ne ga maƙwabtanmu. Ƙaunar da Jehovah yake yi wa mutane ya motsa shi ya aiko da Ɗansa zuwa duniya ya mutu dominsu. (Yohanna 3:16) Lallai wannan babbar hadaya ce. Kwaikwayon ƙaunar Jehovah muke yi yayin da mun ba da lokaci kuma muka yi ƙoƙari mu gaya wa wasu bisharar ceto ta wajen hadayar Yesu.
14. Yaya Littafi Mai-Tsarki ya kwatanta duniya da ba ta cikin ikklisiyar Kirista?
14 Shaidun Jehovah suna ɗaukan ’yan’uwansu bil Adam waɗanda za su iya zama cikin ’yan’uwanci ne na Kirista wata rana. Dole mu yi wa’azi da ƙarfin zuciya, amma, ƙarfin zuciyar ba na zafin rai ba ce. Gaskiya ne, Littafi Mai-Tsarki yana yin amfani da furci mai ƙarfi a zancen duniya gaba ɗaya. Kalmar nan “duniya,” Bulus ya yi amfani da ita a baƙar hanya yayin da yake zancen “hikimar wannan duniya” da kuma “sha’awoyi na duniya.” (1 Korinthiyawa 3:19; Titus 2:12) Bulus ya tunatar da Kiristoci na Afisus cewa yayin da suka yi tafiya “bisa ga zamanin wannan duniya” a ruhaniya kuwa su “matattu” ne. (Afisawa 2:1-3) Waɗannan furci da wasu kamar su daidai suke da kalmomin manzo Yohanna: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.”—1 Yohanna 5:19.
15. Menene ya kamata kada mu yi game da mutane da ba sa cikin ikklisiyar Kirista, kuma me ya sa?
15 Ka tuna dai cewa, irin furcin nan suna nufin duniya gaba ɗaya da take bare daga Allah, ba mutane ɗai ɗai ba. Kiristoci ba sa ɗaukan mataki su shar’anta yadda wani zai mayar da martani ga aikin wa’azin ba. Ba su da wani dalilin kwatanta wasu da awaki. Ba mu ba ne za mu faɗa ko menene sakamakon zai zama lokacin da Yesu zai zo don ya ware “tumaki” daga “awaki.” (Matthew 25:31-46) Yesu ne aka naɗa alƙali; ba mu ba. Ballantana ma, abin da ya taɓa faruwa ya nuna cewa wasu da suka dulmiya cikin mugun hali sun karɓi saƙon Littafi Mai-Tsarki, sun canja rayuwarsu kuma suna rayuwa mai tsabta na Kirista. Gaskiya ne cewa ba za mu so mu yi tarayya da wasu mutane ba, ba za mu ƙi yin magana da su game da begen Mulkin ba duk lokacin da akwai zarafi. Nassosi sun yi zancen wasu mutane waɗanda, ko da ba masu bi ba ne tukuna, suna “da zuciyar kirki don rai na har abada.” Daga baya sun zama masu bi. (Ayukan Manzanni 13:48, NW ) Ba mu san ko wanene yake da zuciyar kirki ba sai mun yi masa wa’azi—wataƙila ma sau da yawa. Idan mun tuna da wannan, za mu bi da waɗanda ba su karɓi saƙon ceto ba tukuna cikin “tawali’u” da “ladabi,” da fatar cewa wasu cikinsu nan gaba za su karɓi saƙon rai.—2 Timothawus 2:25; 1 Bitrus 3:15.
16. Menene dalili ɗaya da ya sa muke son mu gina ‘fasahar koyarwa’?
16 Gina fasaha yadda muke masu koyarwa zai daɗa ɗokiyanmu a yin shelar bisharar. Ga misali: Wani ba zai so wani wasa mai kyau ko kuma guje-guje ba domin bai san yadda ake yin sa ba. Amma ga wanda ya iya, zai ji daɗinsa. Hakazalika, Kiristoci da suka gina ‘fasahar koyarwa’ suna daɗa farin cikinsu cikin hidima. (2 Timothawus 4:2; Titus 1:9) Bulus ya shawarce Timothawus da cewa: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiyar sosai.” (2 Timothawus 2:15) Yaya za mu iya gina fasaharmu ta koyarwa?
17. Ta yaya za mu gina “marmari” don sanin Littafi Mai-Tsarki, kuma yaya irin sanin nan zai amfane hidimarmu?
17 Hanya ɗaya ita ce ta samun ƙarin cikakken sani. Manzo Bitrus ya ƙarfafa mu: “Kamar jarirai sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai-ruhaniya wadda ke sahihiya, domin ta wurinta ku yi girma zuwa ceto.” (1 Bitrus 2:2) Lafiyayyen jariri yana marmarin madara. Amma, wani lokaci ya kamata Kirista ya “yi marmarin” sanin Littafi Mai-Tsarki. Ana iya yin haka wajen kasancewa da halin yin nazari da karatu da kyau. (Misalai 2:1-6) Ana bukatar ƙoƙari da kuma horar da kai idan za mu zama masu koyar da Kalmar Allah da fasaha, amma ƙoƙarce-ƙoƙarcen nan suna kawo albarka. Farin ciki da ke zuwa daga bincika Kalmar Allah zai sa mu huru a cikin ruhun Allah, kuma mu ɗokanta mu gaya wa wasu abubuwan da muka koya.
18. Ta yaya taro na Kirista suke shirya mu mu rarrabe maganar gaskiyar daidai?
18 Taro na Kirista ma yana da muhimmin matsayi a yadda muke da fasaha a yin amfani da Kalmar Allah. Yayin da ake karanta ayoyin Littafi Mai-Tsarki a lokacin ba da jawabi da wasu tattaunawa na Nassi, zai yi kyau mu bi cikin Littafi Mai-Tsarki. Hikima ce mu mai da hankali sosai a sashen taro, haɗe da waɗanda musamman suke game da aikinmu na wa’azi. Bai kamata mu raina amfanin gwadi da ake yi ba, wataƙila mu raba hankalinmu. Haka kuma, ana bukatar mu hori kanmu kuma mu mai da hankali. (1 Timothawus 4:16) Taro na Kirista suna gina bangaskiyarmu, suna taimakonmu mu gina marmari na Kalmar Allah, kuma suna koyar da mu mu zama masu shela da suke ɗokanta a yin bishara.
Za Mu Iya Tabbacin Goyon Bayan Jehovah
19. Me ya sa shagala yau da gobe cikin aikin wa’azi yake da muhimmanci?
19 Kiristoci da suke “huruwa a cikin ruhu” kuma waɗanda suke ɗokanta a yin shelar bisharar suna ƙoƙari su yi hidima yau da gobe. (Afisawa 5:15, 16) Hakika, yanayi sun bambanta, kuma ba duka ne za su iya ɓad da yawan lokaci ɗaya a wannan aikin cetar da rai ba. (Galatiyawa 6:4, 5) Amma, wataƙila abin da ya fi muhimmanci da yawan lokaci da muke ɓatar cikin aikin wa’azin shi ne sau nawa muke gaya wa wasu game da begen da muke da shi. (2 Timothawus 4:1, 2) Idan muna wa’azi yau da gobe, za mu zo ga fahimtar muhimmancin wannan aikin. (Romawa 10:14, 15) Za mu daɗa nuna juyayi da kuma jinƙai idan muna magana da mutane sahihai da suke baƙin ciki da damuwa, waɗanda ba su da bege.—Ezekiel 9:4; Romawa 8:22.
20, 21. (a) Wane aiki ne har ila yake a nan gabanmu? (b) Ta yaya ne Jehovah yake goyon bayan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu?
20 Jehovah ya riga ya ba mu amanar bisharar. Wannan shi ne aiki na farko da muka samu daga wajensa cewa mu “abokan aiki” ne. (1 Korinthiyawa 3:6-9) Muna ɗokanta cikin wannan nawaya da Allah ya bayar da dukan zuciyarmu, da gwargwadon iyawarmu. (Markus 12:30; Romawa 12:1) Da akwai mutane masu zukatan kirki da yawa a cikin duniya, da suke bukatar gaskiya. Da akwai aiki mai yawa da za a yi, amma mun tabbata za mu sami goyon bayan Jehovah yayin da muke cika hidimarmu.—2 Timothawus 4:5.
21 Jehovah yana ba mu ruhunsa kuma yana shirya mu da “takobin Ruhu,” Kalmar Allah. Tare da taimakonsa muna iya buɗe bakinmu ‘domin cikinta mu yi maganar asiri na bishara da gaba gaɗi, yadda ya kamata mu yi.’ (Afisawa 6:17-20) Bari a faɗi game da mu abin da manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci a Tassalunika: “Bishararmu ba da magana kaɗai ba ta zo wurinku, amma da iko kuma, cikin Ruhu Mai-tsarki kuma, da sakankancewa ƙwarai.” (1 Tassalunikawa 1:5) Hakika, bari mu yi shelar bishara cikin ɗokiya!
Ɗan Maimaitawa
• Saboda shagulgular rayuwa, me zai iya faruwa da himmarmu cikin hidima?
• A wace hanya ce muradinmu na yin shelar bishara zai zama kamar “wuta mai-ƙonewa” cikin zukatanmu?
• Waɗanne munanan halaye ne game da hidima ya kamata mu guje musu?
• Yaya ya kamata mu ɗauki waɗanda imaninmu dabam ne da nasu?
• Yaya Jehovah yake taimakonmu mu riƙe himmarmu cikin aikin wa’azi?
[Hotuna a shafi na 21]
Kiristoci suna koyi da himmar Irmiya da Bulus
[Hotuna a shafi na 22]
Ƙauna ga Allah da kuma maƙwabta ne ke motsa mu mu ɗokanta cikin hidima