Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 8/15 pp. 16-20
  • Yadda Jehobah Yake Kusantar Mu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Jehobah Yake Kusantar Mu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DARASI DAGA ABIN DA YA FARU A DĀ
  • JEHOBAH YA JAWO MU KUSA TA WURIN FANSA
  • JEHOBAH YANA JAWO MU KUSA TA WURIN RUBUTACCIYAR KALMARSA
  • KA ƘULLA DANGANTAKA NA KUD DA KUD DA ALLAH
  • ‘Za Ka Sami Ladan Aikinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Yi Amfani da Zarafin da Kake da Shi Yanzu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kana Tambaya Kuwa, “Ina Ubangiji?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 8/15 pp. 16-20

Yadda Jehobah Yake Kusantar Mu

“Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”—YAƘ. 4:8.

MENE NE RA’AYINKA GAME DA . . .

  • gayyatar da Jehobah ya yi mana don mu kusace shi?

  • tanadin da Allah ya yi na hadayar fansa?

  • yadda aka rubuta Kalmar Allah a hanyar da za mu fahimta?

1. Wane muradi ne ’yan Adam suke da shi, kuma wane ne zai iya biya mana wannan muradin?

’YAN ADAM suna da muradin kusantar juna sosai. Idan mutane biyu sun san juna sosai kuma suna ƙaunar juna, ana yawan cewa sun “kusaci juna sosai.” Muna farin ciki idan muna tare da iyalai da abokai masu ƙauna, da suke ɗaukanmu da mutunci kuma sun fahimci yanayinmu. Amma, wanda ya kamata mu ƙulla dangantaka na kud da kud da shi shi ne Mahaliccinmu.—M. Wa. 12:1.

2. Wane alkawari ne Jehobah ya yi mana, amma me ya sa mutane da yawa ba su gaskata da hakan ba?

2 Jehobah ya ƙarfafa mu a cikin Littafi Mai Tsarki cewa mu “kusato” gare shi, kuma ya ce idan muka yi hakan, zai “kusato” gare mu. (Yaƙ. 4:8) Sanin haka yana da ban ƙarfafa, ko ba haka ba? Duk da haka, mutane da yawa suna gani cewa Allah ba ya so ya kusace su. Sun ɗauka cewa ba su cancanta su kusaci Allah ba, ko kuma ya nisanta kansa da mutane, saboda haka, ba za a iya kusantar sa ba. Shin zai yiwu mu kusaci Jehobah kuwa?

3. Mene ne ya kamata mu gaskata game da Jehobah?

3 Gaskiyar al’amarin ita ce Jehobah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu” da yake so ya san shi. (Karanta Ayyukan Manzanni 17:26, 27; Zabura 145:18.) Nufin Allah ne ’yan Adam ajizai su kasance da dangantaka na kud da kud da shi, kuma yana a shirye da kuma marmarin amincewa da mu a matsayin aminansa. (Isha. 41:8; 55:6) Wani marubucin zabura ya shaida hakan kuma ya yi wannan furucin game da Jehobah: ‘Ya mai jin addu’a, a gareka dukan masu rai za su zo. Mai-albarka ne mutum wanda ka zaɓa, wanda ka ke sa shi gusa gareka.’ (Zab. 65:2, 4) Bari mu tattauna wani misali daga Littafi Mai Tsarki game da Sarki Asa na Yahuda da ya kusaci Allah, da kuma matakin da Allah ɗauka.a

DARASI DAGA ABIN DA YA FARU A DĀ

4. Wane misali ne Sarki Asa ya kafa wa Yahudawa?

4 Sarki Asa ya yi himma sosai a bauta ta gaskiya, kuma ya kawo ƙarshen karuwanci a haikali da bautar gumaka da suka zama ruwan dare a ƙasar. (1 Sar. 15:9-13) Da yake ya ɗauki waɗannan matakan, ya gaya wa mutanen su ‘biɗi Ubangiji, Allah na ubanninsu, su kiyaye shari’a da umurni.’ Jehobah ya albarkaci Asa da zaman lafiya a shekaru goma na farko na sarautarsa. Asa ya san cewa Jehobah ne ya albarkace su kuma ya gaya wa Yahudawa cewa: “Ƙasa tana nan gabanmu, domin mun biɗi Ubangiji Allahnmu; mun neme shi, ya kuma ba mu hutu a kowane wuri.” (2 Laba. 14:1-7) Shin mene ne ya faru bayan haka?

5. A wane yanayi ne Asa ya nuna cewa ya dogara da Allah, kuma mene ne sakamakon haka?

5 Zerah Ba-kushi, wato Ba-habashe ya zo da mutane miliyan ɗaya da kuma karusa ɗari uku don ya yaƙi Yahuda. (2 Laba. 14:8-10) Da a ce kai ne Asa, wane mataki ne za ka ɗauka sa’ad da ka ga wannan babbar rundunar soja suna shiga cikin yankinka? Ƙari ga haka, sojojinka guda dubu ɗari biyar da tamanin ne kawai! Da yake rundunarsa ta ninka naka sau biyu, shin za ka yi tunani cewa me ya sa Allah ya ƙyale a kai muku wannan farmakin ne? Shin za ka dangana ga hikimarka a yadda za ka bi da matsalar ne? Matakin da Asa ya ɗauka ya nuna cewa yana da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma ya dogara gare shi. Asa ya yi addu’a ga Jehobah, ya ce: “Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama muna dogara gareka, a cikin sunanka kuma mun zo yaƙi da wannan babban taro. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu: kada ka bar mutum shi rinjaye ka.” Yaya Jehobah ya amsa addu’ar Asa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji fa ya buga Kushawa” kuma a sakamakon haka, ko ɗaya daga cikinsu bai tsira ba!—2 Laba. 14:11-13.

6. Mene ne ya kamata mu koya game da Asa?

6 Me ya sa Asa ya tabbata cewa Allah zai yi masa ja-gora kuma ya kāre shi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Asa kuwa ya yi abin da ke daidai a gaban” Jehobah, kuma ya ce “zuciyar Asa ta kamalta a gaban Ubangiji.” (1 Sar. 15:11, 14) Ya kamata mu bauta wa Allah da zuciya ɗaya. Yin hakan yana da muhimmanci idan muna so mu kasance da dangantaka na kud da kud da shi yanzu da kuma a nan gaba. Muna godiya cewa Jehobah ya ɗauki mataki don mu kusace shi kuma mu kasance da dangantaka mai kyau da shi! Bari mu tattauna hanyoyi biyu da Jehobah ya yi hakan.

JEHOBAH YA JAWO MU KUSA TA WURIN FANSA

7. (a) Mene ne Jehobah ya yi don ya jawo mu kusa? (b) Wace hanya mafi muhimmanci ce Jehobah ya jawo mu kusa da kansa?

7 Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam sa’ad da ya halicci wannan kyakkyawar duniyar don mu zauna a cikinta. Ya ci gaba da ƙaunarmu ta wajen tanadar mana da abinci don mu rayu. (A. M. 17:28; R. Yoh. 4:11) Mafi muhimmanci ma, Jehobah yana tanadar da abubuwan da za su taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. (Luk 12:42) Ya kuma tabbatar mana cewa yana jin addu’armu. (1 Yoh. 5:14) Amma, hanya mafi muhimmanci da Jehobah yake jawo mu kusa kuma muke kusantarsa ita ce ta ƙaunar da ya nuna wajen yi mana tanadin fansa. (Karanta 1 Yohanna 4:9, 10, 19.) Jehobah ya aiko “Ɗansa, haifaffe shi kaɗai” zuwa duniya don ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa.—Yoh. 3:16.

8, 9. Ta yaya Yesu ya taka rawar gani a cikar nufin Jehobah?

8 Jehobah yana so dukan mutane su amfana daga fansar, har da waɗanda suka rayu kafin Yesu ya zo duniya. Daga lokacin da Jehobah ya yi annabci game da wanda zai ceci ’yan Adam, a ganinsa, an riga an biya fansar don ya san cewa nufinsa zai cika tabbas. (Far. 3:15) Ƙarnuka da yawa bayan haka, manzo Bulus ya nuna godiya ga Allah don “fansa” da “Yesu Kristi” ya biya. Bulus ya ƙara cewa Allah ya bayyana haƙurinsa ta wurin gafarta ‘zunuban marigaya.’ (Rom. 3:21-26) Babu shakka, Yesu ya taka rawar gani don mu kasance da dangantaka da Jehobah!

9 Ta wurin Yesu ne kaɗai mutane za su iya sanin Jehobah kuma su kasance da dangantaka na kud da kud da shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:6-8) Jehobah ya tanadar mana da hadayar fansa ta Kristi, ba don mun cancanta ba, amma don yana ƙaunarmu. Yesu ya ce: ‘Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.’ A wani lokaci kuma, ya ce: “Ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yoh. 6:44; 14:6) Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya jawo mutane gare shi ta wurin Yesu kuma yana taimaka musu su kasance da dangantaka mai kyau da shi don su sami rai na har abada. (Karanta Yahuda 20, 21.) Bari mu yi la’akari da wata hanya da Jehobah ya jawo mu wurinsa.

JEHOBAH YANA JAWO MU KUSA TA WURIN RUBUTACCIYAR KALMARSA

10. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce da zai taimaka mana mu kusaci Allah?

10 Da a ce babu Littafi Mai Tsarki, da ba za mu iya sanin Jehobah kuma mu kusace shi ba. Alal misali, mun yi amfani da nassosi daga littattafai guda 14 da ke cikin Littafi Mai Tsarki a wannan talifin. Da a ce babu Littafi Mai Tsarki, da ba za mu sami masaniya game da fansa da kuma yadda Yesu ya taimaka mana mu kusaci Jehobah ba. Jehobah ya hure mutane da ruhunsa don su rubuta Littafi Mai Tsarki kuma wannan littafin yana bayyana halayensa da kuma nufe-nufensa. Alal misali, sa’ad da yake bayyana kansa wa Musa a Fitowa 34:6, 7, ya ce shi “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi.” Wane ne ba zai so ya kusaci mai irin waɗannan halayen ba? Jehobah ya san cewa idan muka ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki don mu ƙara saninsa, za mu tabbata wa kanmu cewa shi Allah ne da gaske kuma za mu kusace shi.

11. Me ya sa za mu ƙoƙarta mu koyi halayen Allah da hanyoyinsa? (Ka duba hoton da ke shafi na 16.)

11 Gabatarwar littafin nan, Ka Kusaci Jehovah ya bayyana yadda za mu iya kasancewa da dangantaka da Allah, ta ce: “A kowacce dangantaka da muka ƙulla, maɗaurin ya dangana ne bisa yadda muka san mutumin, yadda muke sha’awar halayensa waɗanda farda ne kuma muke ɗaukansu da tamani. Halayen Allah da kuma hanyoyinsa, da aka bayyana su cikin Littafi Mai Tsarki, batutuwa ne da za a yi nazarinsu.” Muna godiya cewa Jehobah ya sa a rubuta Littafi Mai Tsarki a hanyar da za mu iya fahimta!

12. Me ya sa Jehobah ya yi amfani da ’yan Adam wajen rubuta Littafi Mai Tsarki?

12 Jehobah zai iya yin amfani da mala’iku wajen rubuta Littafi Mai Tsarki in da ya so yin hakan. Balle ma, mala’iku suna sha’awar abubuwan da muke yi. (1 Bit. 1:12) Babu shakka, da mala’iku za su iya rubuta Littafi Mai Tsarki. Amma mala’iku ba sa kamar ’yan Adam. Da ba za su iya rubuta abubuwan da suka shafi bukatunmu da kasawarmu da kuma sha’awarmu ba. Jehobah ya san cewa mala’iku sun bambanta da mu sosai. Saboda haka, ya sa ’yan Adam suka rubuta Littafi Mai Tsarki, kuma ta yin hakan, ya sa mun fahimci tunanin waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki da kuma yadda suka ji. Sa’ad da muka karanta game taƙaici da shakka da tsoro da kurakurai da baƙin ciki da kuma nasarorin da suka yi, muna fahimtar yanayinsu. Kamar Iliya, dukan marubutan Littafi Mai Tsarki suna da “tabi’a kamar tamu.”—Yaƙ. 5:17.

13. Yaya kake ji sa’ad da ka karanta addu’ar da Yunana ya yi?

13 Ka yi la’akari da yadda Yunana ya ji sa’ad ya gudu ya bar aikin da Allah ya ba shi. Da a ce mala’ika ne ya rubuta abin da ya faru, da bai bayyana dalla-dalla yadda Yunana ya ji ba. Ya dace da Jehobah ya sa Yunana ya rubuta abin da ya faru da shi, kuma wannan ya haɗa da addu’ar da ya yi cikin natsuwa sa’ad da yake cikin teku. Yunana ya ce: “Lokacin da raina ya yi suwu a cikina, na tuna da Ubangiji.”—Yun. 1:3, 10; 2:1-9.

14. Me ya sa za ka iya fahimtar abin da Ishaya ya rubuta game da kansa?

14 Ka yi la’akari kuma da abin da Ishaya ya rubuta game da kansa. Bayan ya ga wahayin Allah a cikin ɗaukakarsa, ya gane cewa shi mai zunubi ne ƙwarai, ya ce: “Kaitona! gama na lalace; da shi ke ni mutum mai-leɓuna marasa-tsarki ne, ina kuwa zaune a tsakiyar mutane masu-leɓuna marasa tsarki: gama idanuna sun ga Sarki mai runduna.” (Isha. 6:5) Shin wane mala’ika ne zai iya faɗin hakan game da kansa? Amma, Ishaya ya faɗi hakan kuma za mu iya fahimtar yanayinsa.

15, 16. (a) Me ya sa za mu iya fahimtar yadda ’yan Adam suke ji? Ka ba da misalai. (b) Me zai taimaka mana mu kusaci Jehobah?

15 Shin da Mala’iku za su iya ce su “mafi ƙaramta” ne kamar yadda Yaƙubu ya faɗa, ko kuma su ce su ‘masu-zunubi ne,’ kamar yadda Bitrus ya ji? (Far. 32:10; Luk 5:8) Kana ganin da sun “ji tsoro” ne kamar almajiran Yesu, ko kuma da mala’iku masu adalci sun bukaci su “yi ƙarfin hali” don su yi wa’azi kamar yadda Bulus da wasu suka yi don tsananin da suka fuskanta? (Yoh. 6:19; 1 Tas. 2:2) A’a, dalilin shi ne don mala’iku kamiltattu ne kuma sun fi ’yan Adam iko sosai. Sa’ad da ’yan Adam ajizai suka bayyana yadda suke ji, muna fahimta don mu ma ’yan Adam ne. Sa’ad da muke karanta Kalmar Allah, za mu iya yin ‘farin zuciya tare da waɗanda ke farin zuciya; mu yi kuka tare da masu-kuka.’—Rom. 12:15.

16 Idan muka yi bimbini a kan yadda Jehobah ya bi da bayinsa a dā, za mu koyi abubuwa masu kyau game da Allahnmu, kuma za mu ga yadda yake kusantar ’yan Adam ajizai. Ta hakan, za mu san Jehobah sosai kuma mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu. A sakamakon haka, za mu kusace shi.—Karanta Zabura 25:14.

KA ƘULLA DANGANTAKA NA KUD DA KUD DA ALLAH

17. (a) Wace shawara mai kyau ce Azariah ya ba Asa? (b) Ta yaya Asa ya ƙi bin shawarar Azariah, kuma mene ne sakamakon haka?

17 Bayan Sarki Asa ya yi gagarumar nasara bisa rundunar Kushawa, sai annabi Azariah ya ba shi da mutanensa shawara mai kyau. Azariah ya ce: “Ubangiji yana tare da ku, muddar kuna tare da shi; idan kun neme shi, yā samu a gareku; amma idan kun yashe shi, shi kuma za ya yashe ku.” (2 Laba. 15:1, 2) Amma daga baya, Asa ya ƙi ya bi wannan shawarar. Sa’ad da mai mulkin arewacin Isra’ila ya yi masa barazanar yaƙi, Asa ya nemi taimako daga Assuriyawa. Maimakon ya nemi taimako daga wajen Jehobah, ya ƙulla yarjejeniya da Assuriyawa masu bautar gumaka. Saboda haka, Jehobah ya gaya masa: “Ka yi aikin wauta; gama daga nan gaba za ka sha yaƙi.” Abin da ya faru da Asa ke nan. (2 Laba. 16:1-9) Wane darasi ne za mu koya?

18, 19. (a) Mene ne ya kamata mu yi idan mun nisanta kanmu da Allah? (b) Ta yaya za mu iya kusantar Jehobah?

18 Bai kamata mu nisanta kanmu da Jehobah ba. Idan ba mu kusace shi yadda ya kamata ba, ya kamata mu bi umurnin nan: “Ku koma wurin Allahnku, Ku yi alheri, ku yi adalci, Ku saurari Allahnku kullayaumin.” (Hos. 12:6, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, bari mu ci gaba da kusantar Jehobah ta wajen yin bimbini a kan fansar Yesu da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki.—Karanta Kubawar Shari’a 13:4.

19 Wani marubucin zabura ya ce: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah.” (Zab. 73:28) Bari dukanmu mu ci gaba da koyo game da Jehobah kuma hakan zai sa mu ƙaunace shi sosai. Idan mun yi hakan, Jehobah zai ci gaba da kusantar mu har abada!

a Ka duba talifin nan game da Asa mai jigo: ‘Za Ka Sami Ladan Aikinka,’ a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2012.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba