Allah Ya Tabbatar Mana Da Ƙaunarsa
“Alheri zai kai ga adalci zuwa rai na har abada.”—ROM. 5:21.
1, 2. Wacce baiwa ce mutane da yawa suke ɗaukan da tamani, amma wacce cikin baiwar biyu ce ta fi tamani?
“WANI farfesa da ke Jami’ar Melbourne, a ƙasar Ostareliya ya ce dokokin Daular Roma baiwa ce da take da amfani na dindindin don wayewar kai. Amma dai, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah ya ba mu baiwa da ta fi wannan tamani. Wannan baiwa ce daga Allah da za ta sa mu sami amincewa da kuma matsayi na adalci a gaban Allah da ceto da kuma rai na har abada.
2 A wani azanci, da akwai fannoni na yadda Allah ya yi tanadin wannan baiwar. A littafin Romawa sura ta biyar, manzo Bulus bai gabatar da waɗannan fannoni a matsayin jerin dokoki da ba su da amfani ba. Maimakon haka, ya soma da wannan tabbaci mai ban sha’awa: “Mun barata bisa ga bangaskiya, bari mu kasance da salama wurin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi.” Hakan ya sa waɗanda suka karɓi baiwar Allah su ƙaunace shi. Bulus yana cikinsu. Ya rubuta: “An baza ƙaunar Allah cikin zukatanmu ta wurin Ruhu Mai-tsarki.”—Rom. 5:1, 5.
3. Waɗanne tambayoyi ne aka yi?
3 Amma, me ya sa wannan baiwa mai kyau take da muhimmanci? Ta yaya Allah zai ba da wannan baiwar daidai ba tare da yin wariya ba? Mene ne kuma aka gaya wa mutane su yi don su cancanci samunta? Bari mu nemi amsoshi masu gamsarwa kuma mu ga yadda suka nanata ƙaunar Allah.
Ƙaunar Allah da Kuma Zunubi
4, 5. (a) A wace hanya mai girma ce Jehobah ya nuna ƙaunarsa? (b) Sanin mene ne zai taimaka mana mu fahimci Romawa 5:12?
4 Ta wurin nuna ƙauna mai girma, Jehobah ya aiko Ɗansa makaɗaici ya taimaki ’yan Adam. Bulus ya furta batun haka: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:8) Ka yi tunanin abu ɗaya da wurin ya ambata: “Tun muna masu-zunubi.” Dukan ’yan Adam suna bukatar su san yadda muka zama masu zunubi.
5 Bulus ya tsara wannan batun, kuma ya soma da wannan bayanin: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Rom. 5:12) Ya kamata mu fahimci wannan domin Allah ya sa aka rubuta tarihi na yadda rayuwar ’yan Adam ta soma. Jehobah ya halicci mutane biyu, Adamu da Hauwa’u. Mahaliccin kamiltacce ne, kuma kakanninmu waɗannan mutane biyu na farko kamiltattu ne. Allah ya ba su umurni ɗaya kuma ya gaya musu cewa rashin bin wannan dokar zai jawo musu mutuwa. (Far. 2:17) Amma, sun zaɓi su yi wauta, sun taka umurnin Allah, ta hakan sun ƙi shi a matsayin Mai Ba Su Doka da Mai Ikon Mallaka.—K. Sha 32:4, 5.
6. (a) Me ya sa zuriyar Adamu suka mutu kafin Allah ya ba da Doka ta hannun Musa da kuma bayan hakan? (b) Da mene ne za a iya kwatanta ciwon da aka gāda?
6 Bayan da Adamu ya yi zunubi ne ya zama mahaifi, ta hakan dukan ’ya’yansa sun gāji zunubi da sakamakonsa. Hakika, ’ya’yansa ba su karya dokar Allah kamar yadda Adamu ya yi ba, saboda haka, ba a yi musu tuhumar irin wannan zunubi ba, kuma ba a ba da tsarin doka ba tukun. (Far. 2:17) Duk da haka, zuriyar Adamu sun gāji zunubi. Shi ya sa zunubi da mutuwa suka kasance har lokacin da Allah ya ba Isra’ilawa tsarin doka, wanda ya nuna sarai cewa su masu zunubi ne. (Karanta Romawa 5:13, 14.) Ana iya kwatanta sakamakon zunubi da aka gāda da wasu cututtuka da za mu iya gāda daga iyayenmu. Ko da wasu yara a cikin iyali suna gādan wata cuta daga iyayensu, ba dukan yara ba ne a cikin wannan iyalin suke gādan wannan cutar ba. Amma ba hakan yake da zunubi ba. Dukanmu mun gāji zunubi daga Adamu kuma saboda hakan za mu mutu. Shin za a taɓa sha kan irin wannan yanayi mai wuya?
Abin da Allah Ya Yi Tanadinsa ta Wurin Yesu Kristi
7, 8. Ta yaya tafarkin maza biyu kamiltattu ya kawo sakamako dabam dabam?
7 Don yana ƙaunarmu, Jehobah ya yi wa ’yan Adam tanadi na shawo kan zunubi da aka gāda. Bulus ya bayyana cewa hakan ya yiwu ta wurin wani mutum kamiltacce, wato, Adamu na biyu. (1 Kor. 15:45) Amma tafarkin kowane mutum cikin mazaje biyun kamiltattu ya kawo sakamako dabam dabam. Ta yaya?—Karanta Romawa 5:15, 16.
8 Bulus ya rubuta: “Ba kamar takar shari’a haka kuma kyautan ta ke ba.” Adamu ya ɗauki alhakin wannan zunubin, kuma an yi masa hukuncin da ya dace, sai ya mutu. Duk da haka, ba shi kaɗai ba ne zai mutu. Mun karanta: “Takar shari’a ta [mutum] ɗayan masu-yawa suka mutu.” Hukuncin da ya dace da aka yi wa Adamu ya bukaci a yi hakan ga dukan ’ya’yansa ajizai, har da mu. Har ila, mun samu ƙarfafa don sanin cewa Yesu, wani mutum kamiltacce, zai kawo wani sakamako dabam. Mene ne sakamakon? Mun samu amsar sa’ad da Bulus ya ambata sanar da ‘dukan mutane [iri-iri] zuwa kuɓutar rai.’—Rom. 5:18.
9. Mene ne Allah ya yi don ya sanar da mu masu adalci, kamar yadda Romawa 5:16, 18 ya ambata?
9 Mene ne asalin ma’anar waɗannan kalamai na Helas “baratarwa” da kuma “kuɓutar rai”? Wani mai fassarar Littafi Mai Tsarki ya rubuta: Wannan ba kalma ce ta doka gabaki ɗaya ba, amma sashe ne na doka. Ta yi magana ne a kan yadda matsayin mutum yakan canja game da Allah, ba canji na zahiri ba . . . Kalmar ta kwatanta Allah a matsayin mai hukunci wanda shari’ar da ya yi ta ’yantar da wanda aka yi wa zargi, da aka kawo gaban fadar Allah, aka ce yana rashin adalci. Amma Allah ya ’yantar da shi.”
10. Mene ne Yesu ya yi da ya sa aka sanar da ’yan Adam masu adalci?
10 Bisa mene ne “Mai-shari’an dukan duniya” mai adalci ya ’yantar da mutum marar adalci? (Far. 18:25) Mataki na farko da Allah ya ɗauka cikin ƙauna shi ne ya aiko da Ɗansa makaɗaici zuwa duniya. Duk da gwaje-gwaje da ba’a da kuma zagi, Yesu ya yi nufin Ubansa. Ya kasance da nagarta har ya mutu a kan gungumen azaba. (Ibran. 2:10) Ta yin hadaya da kamiltaccen ransa, Yesu ya ba da fansa da za ta iya ’yantar da ’ya’yan Adamu daga zunubi da kuma mutuwa.—Mat. 20:28; Rom. 5:6-8.
11. Hadayar tana bisa wane daidaici?
11 A wata aya, Bulus ya kira wannan “daidaitacciyar fansa.” (1 Tim. 2:6, NW) Mene ne daidaicin? Adamu ya kawo ajizanci da mutuwa ga dukan biliyoyin ’ya’yansa. Kuma da Yesu a matsayinsa na kamili ya haifi biliyoyin ’ya’ya kamiltattu.a Saboda haka, mun fahimci a dā cewa rayuwar Yesu tare da na ’ya’ya kamiltattu da ya kamata ya samu ta sa aka samu hadayar da ta yi daidai da ta Adamu da kuma ’ya’yansa ajizai. Amma, Littafi Mai Tsarki bai ce ’ya’yan da Yesu ya kamata ya samu sun kasance cikin sashen fansar ba. Romawa 5:15-19 ya faɗa cewa mutuwar “mutum ɗaya” ya kawo ’yanci. Hakika, kamiltaccen ran Yesu ya yi daidai da na Adamu. Yesu Kristi ne kaɗai ya cika wannan nufin. Ya yiwu mutane iri-iri su samu kyauta da kuma rai saboda “aiki guda ɗaya mai-adalci” na Yesu, wato, biyayyarsa da kuma amincinsa har mutuwa. (2 Kor. 5:14, 15; 1 Bit. 3:18) Ta yaya aka samu wannan sakamakon?
’Yanci Bisa Fansa
12, 13. Me ya sa waɗanda aka sanar da su masu adalci suke bukatar jinƙai da kuma ƙaunar Allah?
12 Jehobah ya karɓa hadayar fansa da Ɗansa ya bayar. (Ibran. 9:24; 10:10, 12) Duk da haka, almajiran Yesu na duniya, haɗe da manzanninsa amintattu, ajizai ne. Ko da sun ƙoƙarta su daina yin abu marar kyau, amma sun kasa. Me ya sa? Domin sun gāji zunubi. (Rom. 7:18-20) Amma Allah zai iya kuma ya yi abu don ya ’yantar da su. Ya karɓi daidaitacciyar “fansa” kuma ya kasance a shirye ya sa ta amfani dukan bayinsa ’yan Adam.
13 Ba wai don nagargarun ayyuka da manzannin da kuma wasu mutane suka yi ba ne ya sa suka cancanci su amfana daga fansar. Maimakon haka, Allah ya sa sun amfana daga fansar domin jinƙansa da kuma ƙauna. Ya tsai da shawara ya ’yantar da manzannin da kuma wasu mutane daga hukunci. Bulus ya bayyana hakan dalla-dalla: “Bisa ga alheri an cece ku ta wurin bangaskiya; wannan kuwa ba daga gareku ba ne; kyauta ce ta Allah.”—Afis. 2:8.
14, 15. Wanne lada ne waɗanda Allah ya sanar da su masu adalci za su samu nan gaba, amma wane ƙarin abu ne suke bukata su yi?
14 Ka yi tunanin irin kyautar da Maɗaukaki ya ba da ta gafarta zunuban da mutum ya gāda da kuma kurakuren da ya yi! Ba za a iya ƙirga yawan zunuban da mutum ya yi ba kafin ya zama Kirista, amma bisa ga fansar, Allah ya gafarta waɗannan zunuban. Bulus ya rubuta: “Kyautan daga wurin zunubai da yawa ta zo ga baratarwa.” (Rom. 5:16) Manzanni da kuma wasu mutane da suka karɓi wannan kyautar, wato, sanar da su masu adalci, suna bukatar su ci gaba da bauta wa Allah na gaskiya cikin imani. Wanne lada ne za su samu a nan gaba? “Waɗanda ke karɓan yalwar alheri da kyautar adalci za su mallaka cikin rai ta wurin ɗayan, Yesu Kristi.” Hakika kyautar adalci ta saɓa wa sakamakon zunubin Adamu. Sakamakon kyautar shi ne rai.—Rom. 5:17; karanta Luka 22:28-30.
15 Waɗanda suka karɓi wannan kyautar, wato, waɗanda aka sanar da su amintattu sun zama ’ya’yan Allah na ruhaniya. A matsayinsu na masu tarayyar gādo da Kristi, suna da zarafin tashiwa daga matattu zuwa sama a matsayin ’ya’ya na ruhu don su yi sarauta tare da Yesu Kristi.—Karanta Romawa 8:15-17, 23.
Ƙaunar Allah ta Bayyana ga Mutane
16. Ta yaya waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya za su iya samun kyauta?
16 Ba dukan waɗanda suka yi imani kuma suke bauta wa Allah ba ne za su yi “mallaka” a matsayin sarakuna tare da Kristi a sama ba. Mutane da yawa suna da bege da ke bisa Littafi Mai Tsarki irin na bayin Allah da suka wanzu kafin zamanin Kiristoci. Suna begen yin rayuwa cikin aljanna a duniya har abada. Shin za su iya samun kyauta da ke bisa ƙauna daga wurin Allah yanzu kuma a ɗauke su a matsayin masu aminci da za su yi rayuwa a duniya a nan gaba? Amsar E ce, bisa ga abin da Bulus ya rubuta ga Romawa!
17, 18. (a) Yaya Jehobah ya ɗauki Ibrahim saboda bangaskiyarsa? (b) Me ya sa ya yiwu Jehobah ya sanar da Ibrahim mai adalci?
17 Bulus ya kwatanta Ibrahim a matsayin misali mai kyau na mutum mai bangaskiya da ya yi rayuwa kafin Jehobah ya ba Isra’ilawa doka kuma shekaru da yawa kafin Yesu ya kawo sabon bege na yin rayuwa a sama. (Ibran. 10:19, 20) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ta wurin shari’a ba alkawari ya zo ga Ibrahim ko ga zuriyarsa, shi zama magajin duniya, amma ta wurin adalci na bangaskiya.” (Rom. 4:13; Yaƙ. 2:23, 24) Saboda haka, Allah ya sanar da Ibrahim a matsayin mai adalci.—Karanta Romawa 4:20-22.
18 Hakan ba ya nufin cewa Ibrahim bai taɓa wani zunubi ba cikin shekaru da yawa da ya bauta wa Jehobah. Ba abin da adalcinsa yake nufi kenan ba. (Rom. 3:10, 23) Amma dai, bisa ga hikimar Jehobah marar iyaka, Jehobah ya yi la’akari da bangaskiya da babu irinta na Ibrahim da kuma ayyukansa. Musamman, Ibrahim ya yi imani ga “zuriya” da aka yi alkawari cewa zai fito daga ’ya’yansa. Wannan Zuriyar ta zama Almasihu, ko Kristi. (Far. 15:6; 22:15-18) Saboda haka, bisa ga “fansa da ke cikin Yesu Kristi,” Allah Mai Hukunci ya samu damar gafarta zunuban da aka yi a dā. Saboda haka, Ibrahim da wasu mutane masu bangaskiya kafin zamanin Kirista suna da gatar tashiwa daga matattu.—Karanta Romawa 3:24, 25; Zab. 32:1, 2.
Ka More Matsayi na Adalci Yanzu
19. Me ya sa yadda Allah ya ɗauki Ibrahim ya kamata ya ƙarfafa mutane da yawa a yau?
19 Sanar da Ibrahim a matsayin mai adalci da Allah na ƙauna ya yi ya kamata ya ƙarfafa Kiristoci a yau. Jehobah bai sanar da shi mai adalci ba kamar yadda ya yi da waɗanda ya shafa da ruhu su zama “masu-tarayyan gādo da Kristi.” Amma “kirayayyu [ne] su zama tsarkaka” kuma an amince da su a matsayin “’ya’yan Allah.” (Rom. 1:7; 8:14, 17, 33) Akasin haka, Ibrahim ya zama “abokin Allah,” kuma hakan ya faru kafin Yesu ya ba da hadayar. (Yaƙ. 2:23; Isha. 41:8) Kiristoci na gaskiya da suke da begen yin rayuwa cikin sabuwar Aljanna a duniya kuma fa?
20. Mene ne Allah yake bukata daga waɗanda yake ɗauka a matsayin masu adalci a yau, kamar yadda ya yi da Ibrahim?
20 Waɗannan ba su samu “yalwar alheri da kyautar adalci” a cikin sama “ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi” ba. (Rom. 3:24; 5:15, 17) Duk da haka, suna da cikakkiyar bangaskiya ga Allah da kuma tanadodinsa, kuma suna nuna bangaskiyarsu ta ayyukansu masu kyau. Ɗaya cikin aikin nan shi ne ‘wa’azin mulkin Allah da koyarwa da al’amura na wajen Ubangiji Yesu Kristi.’ (A. M. 28:31) Saboda haka, Jehobah zai iya ɗauki waɗannan a matsayin masu adalci kamar yadda ya yi da Ibrahim. Kyautar da irin waɗannan suke samu, wato, abokantaka da Allah, ya bambanta da “kyautar” da shafaffu suke samu. Duk da haka, suna karɓar wannan kyautar da godiya sosai.
21. Waɗanne amfani ne muke samu don ƙaunar Jehobah da kuma adalcinsa?
21 Idan kana begen yin rayuwa a duniya har abada, ya kamata ka san cewa ba ka samu wannan zarafin don ayyukan wani shugaban ’yan Adam ba. Maimako, hakan ya nuna manufar hikima na Mamallakin Dukan Halitta. Jehobah ya yi abubuwa da yawa don ya cim ma manufarsa. Waɗannan matakan sun jitu da shari’a ta gaske. Kuma sun nuna ƙauna mai girma ta Allah. Shi ya sa Bulus ya ce: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.”—Rom. 5:8.
[Hasiya]
a Alal misali, an saka bayani game da zuriya a littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafi na 736, sakin layi na 4 da 5.
Ka Tuna?
• Mene ne ’ya’yan Adamu suka gāda, kuma da wane sakamako?
• Ta yaya aka ba da daidaitacciyar fansa, kuma a wace hanya ce hakan ya kasance daidaici?
• Wane zarafi ne kyautar sanar da mu masu adalci yake kawowa?
[Hoto a shafi na 13]
Adamu kamiltaccen mutum ya yi zunubi. Yesu kamiltaccen mutum ya ba da daidaitacciyar “fansa”
[Hoto a shafi na 15]
Albishir ne sosai cewa, za a iya sanar da mu masu adalci ta hanyar Yesu!