Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 14 pp. 138-147
  • Jehobah Ya Yi Tanadin Fansa don “Mutane da Yawa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Yi Tanadin Fansa don “Mutane da Yawa”
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Bukatar Fansa ta Kasance
  • Fansa—Abar Daidaita
  • ‘Fansa da ta Yi Daidai’
  • Waye Ya Yi Tanadin Fansar?
  • Kammala Aikinsa na Fansa
  • Fa’idar Fansar
  • Fansa, Kyauta ce Mafi Girma Daga Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • A Wace Hanya ce Hadayar Yesu Ta Zama “Abin Fansar Mutane da Yawa”?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ku Riƙa Nuna Godiya don Yesu Ya Fanshe Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 14 pp. 138-147
Yesu yana tsaye a gaban sikeli na gwaji.

BABI NA 14

Jehobah Ya Yi Tanadin Fansa don “Mutane da Yawa”

1, 2. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yanayin ’yan Adam, kuma mecece kaɗai hanyar tsira?

“Dukan halitta tana nishi kamar yadda mace mai jin zafin haifuwa takan yi.” (Romawa 8:22) Da waɗannan kalmomi, manzo Bulus ya kwatanta yanayi na ban tausayi da muke ciki. Daga matsayin mutum, kamar dai babu hanyar tsira daga wahala, zunubi, da kuma mutuwa. Amma Jehobah ba shi da iyaka irin ta mutane. (Littafin Ƙidaya 23:19) Allah mai shari’a ya yi mana tanadin hanyar tsira daga wahalarmu. An kira ta fansa.

2 Fansar ita ce kyauta mafi girma da Jehobah ya bai wa ’yan Adam. Ta sa tsira daga zunubi da mutuwa ta yiwu. (Afisawa 1:7) Ita ce tushen begen rai madawwami, ko a sama ko kuma a aljanna a duniya. (Luka 23:43; Yohanna 3:16; 1 Bitrus 1:4) Amma shin mecece ainihi ita fansar take nufi? Ta yaya ta koya mana game da girmar shari’ar Jehobah?

Yadda Bukatar Fansa ta Kasance

3. (a) Me ya sa fansa ta wajaba? (b) Me ya sa Allah kawai bai canja hukuncin kisa a kan ’ya’yan Adamu ba?

3 Fansa ta wajaba domin zunubin Adamu. Ta wajen rashin biyayya ga Allah, Adamu ya bar gadōn ciwo, wahala, azaba, da kuma mutuwa ga zuriyarsa. (Farawa 2:17; Romawa 8:20) Allah ba zai miƙa kai ga motsin zuciya ya rage tsananin hukuncin kisa ba. Idan ya yi haka, to, yana taka dokarsa da kansa da ta ce: “Sakamakon zunubi shi ne mutuwa.” (Romawa 6:23) To, idan Jehobah ya taka nasa ƙa’ida na shari’a, hargitsi a dukan duniya da kuma yin laifi za su zama ruwan dare!

4, 5. (a) Ta yaya Shaiɗan ya ɓata wa Allah suna, kuma me ya sa Jehobah ya ga dole ne ya mai da martani ga waɗannan ƙalubalai? (b) Wace tuhuma ce Shaiɗan ya yi wa bayin Jehobah masu aminci?

4 Kamar yadda muka gani a Babi na 12, tawaye a Adnin ya jawo babbar batu. Shaiɗan ya ɓata suna mai kyau na Allah. Hakika, ya zargi Jehobah da yin ƙarya da kuma cin zali, wanda ke hana halittarsa ’yanci. (Farawa 3:1-5) Kuma domin kamar ya lalata nufin Allah na cika wannan duniyar da mutane masu adalci, ya ce Allah ya kasa. (Farawa 1:28; Ishaya 55:10, 11) Da Jehobah ya ƙyale wannan ƙalubalantarsa da aka yi, da yawa cikin halittarsa masu basira wataƙila za su yi rashin tabbaci da sarautarsa.

5 Shaiɗan kuma ya yi ƙarya a kan bayin Jehobah masu aminci, ya tuhume su da bauta wa Allah kawai domin son kai, kuma wai idan aka matsa musu, babu wanda zai kasance da aminci ga Allah. (Ayuba 1:9-11) Waɗannan batutuwa sun fi yanayi mai wuya na ’yan Adam muhimmanci. Jehobah ya ga tilas ne ya mai da wa Shaiɗan martani. Amma ta yaya Allah zai warware wannan batun kuma ya ceci ’yan Adam?

Fansa—Abar Daidaita

6. Waɗanne furuci ne aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki wajen kwatanta hanyar ceto da Allah ya shirya ya ceci mutane?

6 Warwarewar da Jehobah ya yi, ta jinƙai ne ƙwarai kuma cikakken adalci ne—wanda babu mutumin da zai iya ƙirƙirowa. Amma, tana da sauƙi sosai. An kira ta da suna iri-iri, fanshe, sulhu, da kuma kafara. (Zabura 49:8; Daniyel 9:24; Galatiyawa 3:13; Kolosiyawa 1:20; Ibraniyawa 2:17) Amma furuci da wataƙila ya kwatanta batun da kyau shi ne wanda Yesu kansa ya yi amfani da shi. Ya ce: “Ɗan Mutum bai zo domin a bauta masa ba, sai dai domin ya yi bauta, ya kuma ba da ransa domin ceton [fansa, NW] [Helenanci, lyʹtron] mutane da yawa.”—Matiyu 20:28.

7, 8. (a) Mece ce kalmar nan “fansa” take nufi a cikin Nassosi? (b) A wace hanya ce fansa ta ƙunshi daidaita?

7 Mece ce fansa? Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan ta samo asali ne daga aikatau da take nufin “a ƙyale, ko a sake.” Wannan kalmar an yi amfani da ita wajen kwatanta kuɗi da aka biya domin musanya a saki ɗan fursuna na yaƙi. Saboda haka, za a iya bayyana ma’anar fansa da cewa abin da aka biya a sayo wani abu ne. A Nassosin Ibrananci, kalmar “fansa” (koʹpher) ta samo asali ne daga aikatau mai ma’anar “a rufe.” Alal misali, Allah ya gaya wa Nuhu cewa ya “samtse” (wani fasali na wannan kalmar) shi da ƙaro ciki da baya.—Farawa 6:14.

8 Abin lura kuma, Theological Dictionary of the New Testament ya lura cewa wannan kalmar (koʹpher) “ko da yaushe tana nufin daidaita,” ko kuma kasancewa iri ɗaya. Saboda haka, domin a yi fansa, ko kuma a rufe zunubi, dole ne a biya farashi da zai yi daidai da, ko kuma zai rufe ɓarna da zunubi ya yi. Dokar Allah ga Isra’ila ta ce: “Zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”—Maimaitawar Shari’a 19:21.

9. Me ya sa mutane masu bangaskiya suka miƙa hadaya ta dabba, kuma yaya Jehobah ya ɗauki irin wannan hadayar?

9 Mutane masu bangaskiya daga Habila zuwa sama sun miƙa hadayar dabbobi ga Allah. Ta wajen wannan, sun nuna cewa suna sane da zunubi da kuma bukatar fansa, kuma sun nuna bangaskiyarsu ga alkawarin Allah na ’yanci ta wajen ‘ɗa.’ (Farawa 3:15; 4:1-4; Littafin Firistoci 17:11; Ibraniyawa 11:4) Jehobah ya ɗauki hadayunsu da muhimmanci kuma ya ba wa waɗannan masu bauta salihanci. Duk da haka, miƙa dabba, da kyaunta, nuna godiya ce. Dabbobi ba za su iya rufe zunuban mutane ba, domin ba su kai mutane ba. (Zabura 8:4-8) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba yadda zai yiwu jinin bijimai da na awaki ya kawar da zunubai.” (Ibraniyawa 10:1-4) Irin waɗannan hadayu alama ne kawai, ta fansa ta gaskiya da za ta zo.

‘Fansa da ta Yi Daidai’

10. (a) Ga wa mai ba da fansar zai daidaita, kuma me ya sa? (b) Me ya sa hadayar mutum ɗaya ce ta wajaba?

10 Duka suna “mutuwa saboda Adamu,” in ji manzo Bulus. (1 Korintiyawa 15:22) Saboda haka fansar dole ta ƙunshi mutuwar wanda ya yi daidai da Adamu—mutum da kamili ne. (Romawa 5:14) Babu wata irin halitta da za ta daidaita kan mizanin shari’a. Sai dai kamilin mutum, wanda ba ya cikin hukuncin kisa na Adamu, shi ne zai iya ba da ‘fansa da ta yi daidai’—wadda ta yi daidai da kamilin mutum Adamu. (1 Timoti 2:6) Ba zai wajaba a yi hadayar mutane miliyoyi babu iyaka domin su yi daidai da kowannen ’ya’yan Adamu ba. Manzo Bulus ya yi bayani: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa.” (Romawa 5:12) “Tun da yake mutuwa ta zo ne ta wurin mutum,” Allah ya shirya fansa domin mutane ta “wurin mutum.” (1 Korintiyawa 15:21) Ta yaya?

‘Fansa da ta yi daidai ga duka’

11. (a) Ta yaya mai ba da fansar zai “mutu saboda kowa”? (b) Me ya sa Adamu da Hauwa’u ba za su amfana ba daga fansar? (Duba hasiya.)

11 Jehobah ya shirya ya samu kamilin mutum ya ba da hadayar ransa da son rai. In ji Romawa 6:23, “sakamakon zunubi shi ne mutuwa.” Ta wajen ba da hadayar ransa, mai ba da fansar zai “mutu saboda kowa.” Wato, zai biya hakkin zunubin Adamu. (Ibraniyawa 2:9; 2 Korintiyawa 5:21; 1 Bitrus 2:24) Wannan yana da babbar ma’ana ga sakamakon hukunci. Ta wajen shafe hukuncin kisa da yake kan ’ya’yan Adamu masu biyayya, fansar ta cire ikon halakarwa na zunubi daga tushensa.a—Romawa 5:16.

12. Ka ba da misalin yadda biyan bashi ɗaya zai iya amfanar da mutane da yawa.

12 Ga misali: A ce kana da zama a birnin da yawancin mazaunan suna aiki a wata babbar masana’anta. Kai da maƙwabtanka ana biyan ku kuɗi mai yawa domin aikinku kuma kuna da kwanciyar hankali. Har sai ranar da masana’antar ta rufe ƙofofinta. Me ya sa? Manajan masana’antar ya zama malalaci, ya karya jarin masana’antar. Farat ɗaya ba ku da aiki, kai da maƙwabtanka ba za ku iya biyan bashinku ba. Mata, yara, da kuma waɗanda suka ba da bashi dukansu sun wahala domin lalacin wannan mutumin. Akwai makawa kuwa? Hakika! Wani attajiri ya yi taimako. Ya san amfanin masana’antar. Kuma yana jin tausayin ma’aikata da yawa da iyalansu. Saboda haka, ya shirya ya biya bashin masana’antar kuma ya zuba jari. Biyan bashin ya kawo sauƙi ga ma’aikata da yawa da kuma iyalansu da masu binsu bashi. Hakanan, biyan bashin Adamu ya kawo amfani ga miliyoyin mutane.

Waye Ya Yi Tanadin Fansar?

13, 14. (a) Ta yaya Jehobah ya yi tanadin fansa ga ’yan Adam? (b) Ga wa aka ba da fansar, kuma me ya sa wannan ya wajaba?

13 Jehobah ne kaɗai zai iya tanadin “Ɗan Rago . . . wanda yana ɗauke da zunubin duniya.” (Yohanna 1:29) Amma Allah bai aiko da wani mala’ika kawai ba ya ceci ’yan Adam. Maimakon haka, ya aiko da Wanda zai ba da amsa ta ƙarshe ga ƙalubalantar Shaiɗan game da bayin Jehobah. Hakika, Jehobah ya ba da hadaya mafi girma ta wajen aiko da Ɗansa makaɗaici, “abin daularsa.” (Karin Magana 8:30, Littafi Mai Tsarki) Da son rai, Ɗan Allah ya “mai da kansa kamar ba kome ba.” (Filibiyawa 2:7) A mu’ujizance, Jehobah ya mai da ran Ɗan farinsa zuwa cikin budurwa Maryamu Bayahudiya. (Luka 1:27, 35) Da yake shi mutum ne, za a kira shi Yesu. Amma a shari’ance, za a kira shi Adamu na biyu, domin ya daidaita da Adamu. (1 Korintiyawa 15:45, 47) Saboda haka, Yesu zai iya ba da kansa domin hadaya ta fansa ga mutane masu zunubi.

14 Ga wa za a ba wannan fansar? Zabura 49:7 ta faɗi cewa an biya kuɗin fansar “ga Allah.” Amma ba Jehobah ba ne ainihi ya shirya fansar? Ƙwarai kuwa, amma wannan bai mai da fansar ta zama musanya marar ma’ana ba—kamar cire kuɗi daga aljihu kuma a mai da shi wani aljihu. Dole ne a fahimci cewa fansar ba musanya ba ce ta zahiri amma hulɗa ce ta shari’a. Ta wajen yin tanadin biyar fansar, ko da yake ta yi masa zafi ƙwarai, Jehobah ya tabbatar da mannewarsa ga kamiltacciyar shari’arsa.—Farawa 22:7, 8, 11-13; Ibraniyawa 11:17; Yakub 1:17.

15. Me ya sa ya wajaba Yesu ya wahala kuma ya mutu?

15 A farkon shekara ta 33 A.Z., Yesu Kristi da son rai ya miƙa kai ga azabar da ta kai ga ba da fansar. Ya yarda aka kama shi bisa tuhumar ƙarya, aka same shi da laifi, kuma aka kafa shi da ƙusa a kan itacen kisa. Amma ya wajaba ne Yesu ya wahala haka ƙwarai? I, domin batun aminci na bayin Allah dole ne a kammala shi. Saboda haka, Allah bai yarda Hirudus ya kashe jariri Yesu ba. (Matiyu 2:13-18) Amma lokacin da Yesu ya zama mutum, ya jure wa ƙunar farmakin Shaiɗan da cikakken fahimtar batun.b Da yake shi “mai tsarki ne, marar laifi, marar tabo, an ware shi daga masu zunubi,” duk da azaba da ya sha, Yesu ya tabbatar ƙwarai cewa Jehobah yana da bayi da za su kasance da aminci a lokacin jarraba. (Ibraniyawa 7:26) Saboda haka, babu mamaki, kafin mutuwarsa, Yesu ya yi kukar nasara: “An gama!”—Yohanna 19:30.

Kammala Aikinsa na Fansa

16, 17. (a) Ta yaya Yesu ya ci gaba da aikinsa na fansa? (b) Me ya sa ya wajaba Yesu ya shiga “gaban Allah a yanzu saboda mu”?

16 Har yanzu da saura Yesu ya gama aikinsa na fansa. A rana ta uku bayan mutuwar Yesu, Jehobah ya ta da shi daga matattu. (Ayyukan Manzanni 3:15; 10:40) Ta wannan aikin da ba za a manta da shi ba, Jehobah ba kawai ya saka wa Ɗansa domin hidimarsa ta aminci ba amma ya ba shi zarafin ya gama aikinsa na fansa na Babban Firist na Allah. (Romawa 1:4; 1 Korintiyawa 15:3-8) Manzo Bulus ya yi bayani: Sa’ad da Almasihu “ya zo a matsayin Babban Firist . . . Ya shiga wannan Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak. Bai shiga ta wurin jinin awaki ko na ’ya’yan shanu ba, amma ta wurin nasa jini ne, wanda ya samo mana fansa ta har abada. Gama Almasihu bai shiga Wuri Mafi Tsarki wanda mutum ne ya gina ba, wanda yake kamanni ne kawai na ainihin wurin. A’a, sama ne da kansa ya shiga, domin ya bayyana a gaban Allah a yanzu saboda mu.”—Ibraniyawa 9:11, 12, 24.

17 Kristi ba zai ɗauki jininsa na zahiri zuwa sama ba. (1 Korintiyawa 15:50) Maimakon haka, ya ɗauki abin da jinin yake alama: tamani na shari’a na hadayarsa na ran kamiltaccen mutum. A gaban Allah, ya miƙa tamani na ransa na fansa domin musanya da mutane masu zunubi. Shin Jehobah ya karɓi wannan hadayar? Hakika, wannan ya bayyana a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka zubo da ruhu mai tsarki bisa almajirai 120 a Urushalima. (Ayyukan Manzanni 2:1-4) Ko da yake wannan aukuwa abin farin ciki ne, fansar a lokacin farin tanadin amfani masu kyau ne.

Fa’idar Fansar

18, 19. (a) Waɗanne rukuni biyu na mutane ne suke amfana daga sulhu da jinin Kristi ya sa ya yiwu? (b) Ga waɗanda suke cikin “babban taro,” mene ne wasu amfani na yanzu da kuma na nan gaba na fansar?

18 A wasiƙarsa ga Kolossiyawa, Bulus ya yi bayanin cewa Allah ya ga yana da kyau ta wajen Kristi Ya sulhunta da dukan abu ta wajen yin salama ta jinin Yesu da ya zuba bisa gungumen azaba. Bulus kuma ya yi bayani cewa sulhun ya ƙunshi rukuni biyu dabam dabam, wato, “abubuwan da suke a sama” da kuma “abubuwan da suke a ƙasa.” (Kolosiyawa 1:19, 20; Afisawa 1:10) Rukuni na farko ya ƙunshi Kiristoci 144,000 waɗanda aka ba su begen hidimar firistoci a sama da kuma sarauta ta bisa duniya da Kristi Yesu. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:9, 10; 7:4; 14:1-3) Ta wajen su za a bai wa mutane masu biyayya amfanin fansar a hankali a cikin shekara dubu.—1 Korintiyawa 15:24-26; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:6; 21:3, 4.

19 “Abubuwa da suke a ƙasa” mutane ne waɗanda suke kan hanyar more kamiltaccen rayuwa a Aljanna a duniya. Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:9-17 sun kwatanta su da “babban taro” da za ta tsira daga “azabar nan mai zafi” da ke zuwa. Amma ba za su jira har sai wannan lokacin ba kafin su more amfanin fansar. Sun riga “sun wanke rigunansu da jinin Ɗan Ragon, suka zama farare.” Domin sun ba da gaskiya ga fansar, suna samun amfani na ruhaniya daga wannan tanadi na ƙauna. An riga an ce da su amintattun abokanan Allah! (Yakub 2:23) Domin hadaya ta Yesu, za su iya su “zo kusa da kujerar mulkin Allah, wato wurin alheri.” (Ibraniyawa 4:14-16) Idan suka yi zunubi, suna samun gafara ta gaske. (Afisawa 1:7) Ko da yake ajizai ne, suna da lamiri mai kyau. (Ibraniyawa 9:9; 10:22; 1 Bitrus 3:21) Saboda haka, sulhuntuwa da Allah, ba abin da ake tsammaninsa ba ne, amma abu ne da ke faruwa yanzu! (2 Korintiyawa 5:19, 20) A cikin Alif ɗin, za su “sami tsira daga bautar da take wa ruɓewa” kuma a ƙarshe, su “sami ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.”—Romawa 8:21.

20. Ta yaya bimbini a kan fansar ta shafe ka?

20 ‘Godiya ta tabbata ga Allah gama ya cece mu ta wurin [hadayar] Yesu Almasihu.’ (Romawa 7:25) Mizani ne mai sauƙi, amma tana cike da hikima da za ta cika mu da mamaki. (Romawa 11:33) Ta wajen bimbininmu na godiya a kanta, fansar ta taɓa zukatanmu, ta jawo mu kusa da Allah mai shari’a. Kamar mai Zabura, muna da dalilai na yabon Jehobah domin “yana son adalci da gaskiya.”—Zabura 33:5.

a Adamu da Hauwa’u ba za su amfana ba daga fansar. Dokar Musa ta faɗi wannan mizanin game da mai kisa da gangan: “Kada ku karɓi abin fansa domin rai na mai kisan kai, wanda kuma an riga an yanka masa hukuncin mutuwa.” (Littafin Ƙidaya 35:31) A bayyane yake, Adamu da Hauwa’u sun cancanci su mutu domin sun yi wa Allah rashin biyayya da saninsu kuma da gangan. Saboda haka, sun yasar da begen rayuwa ta har abada.

b Domin ya daidaita zunubin Adamu, Yesu dole ya mutu, ba kamilin yaro ba, amma kamilin mutum. Ka tuna cewa zunubin Adamu da son rai ne, da cikakken sanin tsananinsa da kuma sakamakonsa. Saboda haka domin ya zama “Adam na ƙarshe” kuma ya rufe wannan zunubi, Yesu dole ne ya zama mutum, ya zaɓi ya kasance da aminci ga Jehobah. (1 Korintiyawa 15:45, 47) Saboda haka, dukan rayuwarsa ta aminci—haɗe da mutuwarsa ta hadaya—ta kasance “aikata adalci na mutum ɗaya.”—Romawa 5:18, 19.

Tambayoyi don Bimbini

  • Littafin Ƙidaya 3:39-51 Me ya sa yake da muhimmanci cewa fansar ta daidaita?

  • Zabura 49:7, 8 Me ya sa Allah yake binmu bashi ta wajen yi mana tanadin fansa?

  • Ishaya 43:25 Ta yaya wannan nassi ya taimake mu muka ga cewa ceton mutane ba shi ne ainihin dalilin da ya sa Jehobah ya yi tanadin fansa ba?

  • 1 Korintiyawa 6:20 Yaya ya kamata fansar ta taɓa halayenmu da kuma yayin rayuwarmu?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba