Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 pp. 3-5
  • Intane Yadda Za Mu Yi Amfani da Shi a Hanyar da Ta Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Intane Yadda Za Mu Yi Amfani da Shi a Hanyar da Ta Dace
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Shin Labarin Gaskiya Ne Ko Kuma Ƙarya?
  • Shin Intane Yana Keɓe Lokaci ne ko kuwa Yana Cinye Lokaci?
  • Wane Irin Abu ne Kake Kallo?
  • Me Ya Kamata Mu Aika wa Mutane?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 pp. 3-5

Intane Yadda Za Mu Yi Amfani da Shi a Hanyar da Ta Dace

INTANE yana sa ya yiwu mu san game da kusan kome a ko’ina da kuma a kowanne lokaci. Ba abin mamaki ba ne da mutane a ko’ina a duniya suke yin amfani da shi don tattaunawa da mutane.

Ingancin yin magana baiwa ce mai ban al’ajabi daga wurin Mahaliccinmu. Yana sa ya yiwu mu tattauna da kuma bayyana ra’ayinmu da mutane. Jehobah ne ya fara tattaunawa da ’yan Adam. Ya yi musu bayyani dalla-dalla game da yadda za su yi rayuwa mai ma’ana. (Far. 1:28-30) Amma kamar yadda tarihin mutane na farko ya nuna, ana iya yin amfani da baiwar tattaunawa a hanyar da ba ta dace ba. Shaiɗan ya yi wa Hauwa’u ƙarya. Ta yarda da abin da ya ce, kuma ta gaya wa Adamu. Adamu ya aikata bisa labarin ƙaryar, kuma ayyukansa ya sa dukan ’yan Adam suke shan wahala.—Far. 3:1-6; Rom. 5:12.

Mene ne za a iya cewa game da Intane? Ko da yake Intane yana iya sa mu samu bayani mai muhimmanci kuma ya taimaka mana mu yi abubuwa da sauri, amma kuma yana iya gaya mana labarin ƙarya, ya cinye lokacin yin wasu abubuwa kuma ya sa ya yi mana sauƙin kallon lalata. Bari mu yi magana game da yadda za mu iya yin amfani da Intane a hanyar da ta dace.

Shin Labarin Gaskiya Ne Ko Kuma Ƙarya?

Shin kana ganin cewa dukan bayanin da ke cikin Intane suna da kyau? Muna iya samun bayani mafi kyau ko kuma mafi ƙazamta sa’ad da muka yi bincike a Intane. Muna bukatar mu zama masu hikima kuma mu ware bayani mai kyau da kuma marar kyau.

A wata sananniyar mujalla a shekara ta 1993, an zana hoton karnuka biyu da suke gaban kwamfuta. Ɗaya daga cikin karen ya ce wa ɗan’uwansa: “Ka san cewa a cikin Intane babu wanda ya san cewa kai kare ne?” Shekaru da yawa da suka shige, Shaiɗan ya yi amfani da maciji wajen soma tattaunawa da Hauwa’u a ɓoye kamar yadda mutane suke ɓoye ainihin kamaninsu a Intane. A yau, duk wanda yake da hanyar shiga Intane zai iya yi kamar shi gwani ne ko kuma mai ilimi sosai. Kuma mutane ba sa bukatar yin amfani da sunayensu. Kowa yana iya wallafa ra’ayoyi da bayani da hotuna da kuma shawarwari.

Kada ka gaskata da bayanin nan da nan. Kafin ka yi hakan, ka yi tambaya: (1) Wane ne ya wallafa bayanin? Shin muna iya gaskata da marubucin? (2) Me ya sa aka wallafa shi? Me ya sa aka rubuta shi? Shin marubucin mai sanin ya kamata ne ko kuwa yana ɗaukaka ra’ayinsa ne kawai? (3) A ina ne marubucin ya samu bayanin? Shin ya faɗa inda ya samu bayanin domin mutane su duba? (4) Shin bayanin ya yi daidai da abin da aka sani a yau? A ƙarni na farko, manzo Bulus ya ba Timotawus shawara da take da muhimmanci a gare mu a yau. Bulus ya rubuta: “Ka tsare abin da aka danƙa maka, kana kauce wa maganganu na saɓo da kuma surutai na banza irin ilimin da ake fadinsu haka nan kawai a ƙaryace.”—1 Tim. 6:20.

Shin Intane Yana Keɓe Lokaci ne ko kuwa Yana Cinye Lokaci?

Idan muka yi amfani da Intane a hanyar da ta dace, zai taimaka mana mu samu lokaci kuma mu rage yawan amfani da kuzarinmu da kuma rage kashe kuɗinmu. Muna iya sayen wani abu ba tare da mun bar gida ba. Zai taimaka mana mu samu kaya mai araha. Maimakon zuwan banki, mutane suna iya biyan kuɗinsu da kuma aika kuɗi da kuma wasu abubuwa kamar hakan a gidajensu. Intane yana iya taimaka mana mu yi shirin tafiya da sauri kuma mu yanki tikiti. Yana kuma da sauƙi a nemi lambar wayoyi da adireshi da kuma bayanai. Ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah a dukan duniya suna yin amfani da intane kuma suna amfana da hakan.

Amma akwai wasu haɗarurruka da ya kamata mu yi la’akari da su. Alal misali, ya kamata mu yi tunanin yawan lokacin da muke amfani da shi a kan Intane. Wasu suna amfani da lokaci da yawa suna wasa da sayayya da taɗi da aika saƙo da yin bincike da kuma neman abubuwa a Dandali. A wasu lokatai suna manta da iyalinsu da abokai da kuma ikilisiya. Suna iya shaƙu da Intane. Alal misali, binciken da aka wallafa a shekara ta 2010 ya nuna cewa kashi 18.4 cikin ɗari na matasan ƙasar Koriya sun shaƙu da yin amfani da Intane. Masu bincike a ƙasar Jamus sun faɗa cewa “mataye da yawa suna gunaguni cewa mazajensu sun shaƙu da yin amfani da Intane.” Wata mata ta yi gunaguni cewa yadda maigidanta ya shaƙu da Intane ya canja halinsa kuma ya ɓata aurensu.

Wani wanda ya shaƙu sosai da Intane ya aika wa wani ofishin reshe na Shaidun Jehobah wata wasiƙa. Yana zama a gaban Intane sa’o’i goma a wasu ranaku. Ya ce “da farko kamar babu matsala.” Amma sai ya soma daina zuwan taro da kuma yin addu’a. Ba ya shirya tarurruka kafin ya halarta, kuma sai ya riƙa tunani game da lokacin da zai “iya sake shiga dandali kuma.” Da shigewar lokaci, sai ya gane cewa yana da matsala mai tsanani, kuma ya yi canje-canje da suka dace. Bai kamata mu yi sa’o’i da yawa a gaban Intane har mu shaƙu da hakan ba.

Wane Irin Abu ne Kake Kallo?

1 Tasalonikawa 5:21, 22 ta ce: “Ku auna abu duka; ku riƙe mai-kyau; ku hanu ga kowace sifar mugunta.” Sa’ad da muka bincika abu a cikin Intane, muna bukatar mu tuna yadda Jehobah ya ɗauki abin. Ya kamata abin da muke kallo ya kasance da tsabta a ɗabi’a kuma ya dace don Kirista. Batsa na Intane ta zama ruwan dare gama gari. Idan ba mu mai da hankali ba, zai iya zama mana matsala.

Don a taimaka mana mu tsai da shawara a kan abin da ya kamata mu kalla a Intane ko babu, ka yi tunanin wannan tambayar: ‘Shin abin da nake kallo wani abu ne da zan ɓoye da sauri idan mijina (ko matata) da iyayena da ’yan’uwana Kiristoci suka shigo ɗakin?’ Idan haka ne, zai fi kyau mu yi amfani da Intane lokacin da mutane suke tare da mu. Intane ya canja yadda mutane suke tattaunawa da kuma yin sayayya. Amma kuma ya nuna wa mutane sabuwar hanyar yin zina a zuciyarsu.—Mat. 5:27, 28.

Me Ya Kamata Mu Aika wa Mutane?

Sa’ad da muka yi amfani da Intane, muna yawan aika wa mutane bayani. Dole ne mu tabbata cewa labarin da muka rubuta ko kuma tura wa mutane gaskiya ne, ba na lalata ba ne kuma bayanin da muke da izinin bayarwa ne.a Ya kamata mu yi tunani game da wannan: Shin bayanin zai taimaki mutane? Me ya sa muke son mutane su san wannan bayanin? Don mu burge su ne kawai?

I-mel yana da amfani sosai sa’ad da muka yi amfani da shi a hanyar da ta dace. Amma yana iya gaya mana abubuwa da yawa da ba su da muhimmanci. Shin muna aika wa mutane abubuwa da yawa ainun da za su karanta, wataƙila muna cinye lokacinsu sosai fiye da yadda ya kamata? Shin bai kamata mu yi tunani game da abin da ya sa muke aika saƙon I-mel kafin mu danna botin aika saƙon? A dā, mutane sukan rubuta wa iyalinsu da abokansu wasiƙu don su gaya musu abin da yake faruwa a rayuwarsu. Hakan ne ya kamata saƙonmu na I-mel ya kasance. Me ya sa za mu aika wa mutane abin da ba za mu iya faɗan tushensu ba?

Saboda haka, me ya kamata ka yi game da Intane? Shin bai kamata ka yi amfani da shi sam-sam ba? Ga wasu mutane hakan ya wajaba. Wanda muka yi maganarsa ɗazun da ya shaƙu da Intane ya yi hakan. Intane zai iya kasance da taimako a gare ka idan ka yi amfani da “hankali” kuma ka sa ya riƙa “tsaronka.”—Mis. 2:10, 11.

[Hasiya]

a Hakan ma ya shafi hotuna. Muna iya ɗaukan hotunan mutane don amfaninmu. Amma ba mu da izinin nuna wa kowane mutum hotunan ko kuma gaya musu sunayen mutane da ke cikin hotunan da inda suke da zama ba.

[Hoto a shafi na 4]

Ta yaya za mu tabbata cewa bayanin da muke samu gaskiya ne?

[Hoto a shafi na 5]

Mene ne ya kamata ka yi tunaninsa kafin ka danna botin aika saƙo?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba